Showing 324001 words to 327000 words out of 355604 words
su ga ana ci wa kishiyarsu mutunci amma ban da Aunty, da zarar sun fara faɗa zata wuce ɗakinta dan ma kada ta ga abin da yake faruwa, bata son hayaniya kuma bata son abin haushi, tana da zuciya mai kyau sosai, har cikin ransa yau Abbi ya ji wani irin mugun daɗi abin da Aunty ta aikata, ta san abin da take yi.
Shi kuma Imran sama ya haura domin ya je ya kira su jelly.
Jim kaɗan sai ga Ommu ta fito riƙe da wayarta ta canza shiga zuwa doguwar riga, da alama ya fasa fitan kenan.
Kusa da Abbi ta zo ta tsaya tare da miƙa mashi wayarta tana faɗin "Saka Mani number Umaisha ko kuma na mijinta a nan bari na kira shi ya kawo mani ita yanzun nan zan yi magana da ita".
Kallon daddyn Jelly Abbi ya yi, mamaki ya hana su magana, tun da ta dawo bata nemi yaran ba sai da ta ji Umaisha na auren Akil sannan ne zata ne me su dan ta ji ruwan kuɗi.
Sosai daddy yake addu'ar kada ta lalatawa yaran nan aurensu, dan yasan halinta sarai, zata iya kai Umaisha ta barota, kuma kun san tsakanin uwa da ƴa, sannan Ommu ba ruwanta da wai ƴar cikinta ce, idan bukatar ta ya biya shikenan ai.
Ƙin saka mata number Abbi ya yi, ya ce bashi da shi, ba dan ta so ba ta hakura ta koma sama tana tunanin yadda zata yi.
Tana komawa ba jimawa sai ga su Imran sun sauƙo kasa, jelly ta canza kaya zuwa doguwar riga ash color, shi kuma Imran yana manne da waya a kunne yana magana da Akil akan su zo gidan Abbi yanzu an gane Jelly.
Aunty na rungume da Ayla suka sauƙo kasa. Jikin daddy jelly ta je ta haye tana zuba mashi shagwaɓa akan tana kewarsa, da hannu ya yi wa Ayla alama akan ta zo ita ma, ba musu ta je dan dama bata taɓa yin musu da shi ba.
Ta gefen jikinsa ya jawota yana faɗin "Babyn daddy wannan ita ce Jelly" jin abin da daddy ya ce yasa Jelly ta yi saurin ɗago kai tana maimaita sunnan da daddy ya kira Ayla da shi.
Kamar wadda aka yi wa allura haka Jelly ta diro kasa ta yi zaman ƴan bori a tsakiyar carpet ɗin tare da fara wuwwurga kafafu a kasa tana ihu kamar ba lafiya ba, daddy ya san me take yi wa ihu, wato dan ya kira Ayla da babyn daddy shi ne take kuka, sunan babyn daddy sunan Jelly ɗin ne da yake kiranta da shi lokacin suna Kano.
Imran ne ya yi saurin marisowa wajenta tare da riƙota yana faɗin "Jelly menene?".
Cikin kuka ta ce "Yaya Imran daddy fa yanzu ya daina so na, kana ganin wata babyn ya samu". Babbar magana wai ɗan sanda ya ga gawar soja, dama shi daddy already yasan za'ayi hakan, yasan ba zata taɓa yarda da Ayla ba, shiyasa ya ce tana dawowa za'a ɗaura mata aure da Imran kowa ma ya huta.
Cikin sigar rarrashi Imran ya ce "Jelly wannan fa mummynki ce ba wai wata ba, mummy zaki ce mata".
Cak ta tsaya da kukan nata tare da ɗago idanu da sauri ta sauƙe akan Ayla ɗin. Kallon minti ɗaya ta yi mata kafin kuma ta kwashe da dariya kamar wata zautatciya, daddy kam ko ajikinsa dan ya san halin kayarsa, in dai jelly ce to fin hakan ma zata yi, sai ta sa ka ka yi tunanin ko kaine mahaukaci, wlh tsab jelly zata sanya ka fara tunanin anya kana lafiya kuwa? Anya kai ba mahaukaci bane kuwa?.
Shi kuwa Imran da yake har yanzu yana da sauran karatu akanta sai ya ce "Jelly lafiya kike dariya kuma?" Kara sautin dariyar tata ta yi har da rike ciki, kamar ba ita ba ce mai yin kuka yanzun nan.
Sai da ta yi dariyarta mai isarta sannan ta ce "Amma yaya Imran a sanina dai kafin mu zo nan lafiya lou kake, ya akayi kuma yanzu ka canza kamar mara lafiya?" Ɗan kallon kansa ya yi dan ko zai ga abin da ta gani a tattare da shi da ta ce mashi ba shi da lafiya.
Shikam daddy a zuciyarsa cewa ya yi kaɗan ka gani Imran ba dai jelly ba, wata rana sai ta sanya ka tuɓe wando a cikin jama'a, Abbi kuwa ban da murmushi ba abin da yake yi, ita kuwa Aunty yau ta ga duniya a wajen jelly, ta ga abin mamaki, Rimsha kam ko a jikinta, Hanan ce ma ta ɗan tsorata da ganin abin da jellyn take yi.
"Jelly wai me yake faruwa ne?" Cewar Imran, cikin dariya ta ce "Yaya Imran wannan ƴar karamar yarinyar da bata wuce na kamata na haɗiyeta na kora ruwa bace mummyna? Wai ka manta mummyna ta rasu ne? To idan ka manta na tuna maka, mummyna bata nan wannan kuma ai ko mai....." Bata karasa ba ta ja birki sakamakon karewa fuskar Ayla kallo da take yi.
Zubur ta miƙe tana faɗin "Ya na kalli tana kama da mumnyn kuma?" Da yake ta san fuskar mumnynta a hoto, da sauri ta koma jikin daddy tana tambayarsa ya akayi take kama da mummynta kuma.
Daddy bai san time ɗin da ya ce mata "kanwar mummyn ki ce ai". Imran yana ƙoƙarin gaya mata ita ce matar daddy, daddy ya yi saurin dakatar da shi domin kuwa yasan a yanzu dai jelly ba zata taɓa yarda da Ayla matarsa ba, for now dai a barta a kanwar mummyn kawai zai fi, sai ta kara hankali idan ta je gidan mijinta, idan ba haka ba yanzu zata yi masu karamin hauka.
Suna a haka wayar Imran ta fara kara, hannu yasa a aljihun nasa ya ciro wayar, Nawid ne yake kiransa, picking ya yi tare da manna wayar a kunnensa.
Maganar minti 5 suka yi, sannan Imran ya ce sai kun zo, daga nan suka yi sallama, hakan kuma ya yi daidai da danno hancin motar Akil cikin gidan.
Zama Imran ya koma ya yi a saman sofa, ita kuma Jelly tuni ta rungumi Ayla sun fara hira a matsayin kanwar mummynta, dama ta jima tana cewa daddy ya kai ta wajen ƴan uwan mumnynta ko kuma ya kawo mata su gida ta gansu, amma kullun sai ya rinƙa ce mata zai yi zai yi amma bai taɓa yi ɗin ba, sai ga shi yau ta ga kanwar mummyn nata ai farinciki ba'a magana, har da rungumar Ayla ta yi suna ta hira.
A haka Akil ya shigo ya same su, tare da Akila, Umaisha da kuma A'afia suke tafe, duk ya haɗo kansu dan su zo su sake kulla zumunci.
Sai murna suke yi kamar me, daddy ne ya ce da Akila ta tashi ta je ta ɗauko mashi kuɗi a cikin drawer mirror a ɗakinsa ta kawo mashi, to ta amsa mashi da shi tare da miƙe wa da sauri ta nufi waje.
Tana shiga palon suka ci karo da Irfan zai fito, cikin sauri ta yi baya zata faɗi, yana ƙoƙarin riƙota ta kauce mashi ta faɗi kasa, bata son ya taɓa ta dan kada ɓoyayyen masoyi ya ɓata rai.
Yadda ta kauce mashin ba ƙaramin mamaki ta ba shi ba, amma kuma bai kawo komai a ransa ba ya duka yana son ɗagota tare da yi mata sannu, kin yarda ya ɗagota ta yi, nan ta ce mashi a'a ya bari zata tashi, bai damu ba dan shima dama ba wani son cika taɓa jikinta ya yi ba, dan tsaro.
Bayan ta miƙe suka gaisa ya tambayeta yaushe suka zo, nan ta gaya mashi yanzun nan kuma daddy ne ya aiketa su Imran suna palo, da Muryarsa ya ce to ta ɗauko saƙon daddyn sai su wuce zuwa cikin gidan tare, to ta amsa da shi sannan ta wuce zuwa bedroom ɗin na daddy tare da taimakonsa wajen nuna mata bedroom ɗin.
Kuɗi ta ɗauko mashi wadda a kalla zasu iya kai 500k, Irfan na tsaye har ta fito suka jera zuwa cikkn gida.
Kamar yadda ta barsu haka ta shigo ta same su, sai hira ake zubawa kamar ba gobe, miƙawa daddy kuɗin ta zo ta yi tana faɗin "ga shi nan bappa".
Karɓa daddy ya yi tare da miƙawa Abbi ya ce ga sadakin Jelly, a matsayinsa na waliyin Imran, yana neman alfarmar da a ɗaura auren nan yanzu, Allah sarki kuruci dangin hauka, jin hakan yasa jelly ta rungume shi tana dariya tana faɗin zata zama matar yaya Imran, zata zama matar yaya Imran, shi kuwa Imran kasa da kansa ya yi duk kunya ta rufe shi, nan take Akil da Irfan suka fara tsokanarsa, aunty ce ta ce da Jelly ta ta so ta zo su ɗan yi magana.
To jelly ta amsa da shi tare da tashi ta je, har ga Allah duk wanda ya zauna da Aunty dole zata shiga ransa domin tana da halayya masu kyau, kowa ya zo gidan ita yake so ba Ommu ba, tana da tarin masoya ciki kuma har da ƴaƴan Ommu ɗin, domin Irfan yana kaunarta sosai saboda kirkinta, haka su Aafia ma, suna sonta, kowa nata ne bata da mugunta ko kaɗan.
Miƙewa Abbi ya yi ya ce su je waje bari ya kira makwabtansa sai a ɗaura auren. A tare gaba ɗaya mazan suka fita, su kuma matan suka cigaba da hira Aunty tana yiwa Jelly nasiha akan ta natsu, tare da kara mata haske a kan abubuwa.
Mu koma baya kaɗan, lokacin da daddyn Jelly ya ce su haura sama, time da Ommu take yi masu rashin mutunci, da suka shiga aunty ta kalli jini a jikin jelly hakan yasa ta saka jelly ta shiga toilet ta wanke jikinta ta bata sabon pant da kuma always ta saka, wannan dalilin yasa jelly ta fara kaunar Aunty, saboda kirkinta, bata share mutane. Bayan ta saka always ɗin Aunty ta kara bata doguwar rigarta ta sanya a jikin ta, wannan shine abin da ya faru bayan shigarsu ɗaki. MU KOMA IN DA MUKE A STORY.
Suna tsaka da hira aka sako waƙar bodyguard na Salman Khan a Tv, a ɗari Jelly ta miƙe tare da kure Volume na Tv ta fara tikar rawa.
Sai murmushi kowa yake yi yana kallonta, jawo hannun Rismha ta yi akan ta taso su yi, ai kuwa Rimsha bata ki ba suka shiga yin rawa a tare, sake jawo hannun Ayla ta yi, nan fa ita kuma Ayla ta saka kuka dan ba zata iya ba, jelly a tunaninta dan bata so ne yasa take kuka saboda idan baku mance ba halin jelly ɗin ce, idan bata son abu sai ta kama kuka, to tana tunanin kamar kowa ma haka ne, shiyasa sai ta kyale Ayla ɗin kawai suka cigaba da rawa da Rimsha, miƙewa ita ma Akila ta yi suka fara takawa a tare, da kaɗan da kaɗan Umaisha ma ta bi bayansu suka bar Aafia, Hanan da kuma Ayla sai Aunty, sun zuba masu idanu suna kallon yadda suke taka rawa kamar ba gobe, abin ba ƙaramin ƙayatarwa ya yi ba. HAPPINESS IS FREE.
A can waje kuma ana famar ɗaura aure.
After some minutes.
Bayan an ɗaura aure an dawo a palo suka sake ba je wa, Imran, Akil ba wanda ya tuna da Ammie zata karɓi wannan aure ne ko ba zata karɓa ba, sannan idan baku mance ba, jelly tun kafin ta san waye Hajiya Umaiya ta nuna bata son ta, idan baku mance ba bakar muguwa munafuka take kiran Hajiya Umaiya, ya kuke tunanin wannan zama zata kasan ce? Anya Ammie zata karɓi Jelly kuwa?. Ko dai zata gasa jelly kamar yadda ta gasa Umaisha? Mu dai je zuwa.
Sai murna suke yi, duk fuskar wadda ka kalla a cikin palon nan zaka kalli tsantsan farinciki a tattare da shi.
A wanann halin su Nawid suka iso suka same su, shi da Umminsa da kuma Hajiya Batula.
Abin da ya faru a gida bayan komar Nawid da ya kawo wa Imran Jelly shine, da ya koma bai sami Abbo a gidan ba, abin ya ɗaure mashi kai, kwata kwata babu Abbo babu alamar sa, kuma ga kofar ɗakin a rufe kamar yadda ya rufe Abbo ɗin, shi ne da ya dawo ya buɗe kofar, to ta ina Abbo ya fita?.
Ransa cike da tunani tare da mamaki ya kwanta kawai, amma ya kasa yin barci har wayewan gari.
Da gari ya waye ne Ummi ta tambayi ina baby, sai ya ce tana gidansu Abokinsa, bai gaya mata me ya faru, me Abbo ya aikata ba, ya rufe abin shi kaɗai domin bai kawo a ransa cewa tsafi Abbo zai yi da jelly ba, ya yi tunanin raping ɗin ta kawai zai yi, shiyasa ya rufe maganar dan a cewarsa abin kunya ne ya faɗi hakan, ya rufawa mahaifinsa asiri.
Nan fa Ummi ta fara faɗa akan me zai ɗauki baby ya kaita wani waje, ita ba ta yarda ba sai dai su je gidansu abokin a tare, hakuri ya rinƙa bata akan bari ya je ya ɗauko babyn, ina ta ki yarda ta ce sai dai su tafi tare, haka kuwa akayi shine suka taho tare, shi kuma Abbo shiru ba labarinsa, Allah kaɗai ya san ina ya tafi, ita ma Ummi bata neme shi ba, saboda ana hidimar biki tasan ba zama yake yi a gidan ba.
STORY💖
Hannu Nawid ya miƙawa dukka mazan cikin palon, ɗaya bayan ɗaya suka gaisa, su kuma matan suka gaisa da baki, ya sha mamakin ganin jelly a jikin daddy, kamar zai magana sai kuma dai ya danne ya yi shiru, ita ma Ummi gaisawa suka yi da mutanen cikin Palon, ita kuma Hajiya Batula mamakin ganin su daddyn Jelly ya hana ta magana, shima daddyn ido kawai ya bita da shi dan bai san me zai ce mata ba, Abbi ne kawai ya ce "Batula dama kin san hanyar gidana? Kin san in da nake shine baki taɓa zuwa ba?".
Shiru ta yi ta kasa magana, abubuwan da suka faru a baya ne kawai suka fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwarta. Hannu Abbi ya sa ya nuna mata sofa akan ta zauna, ba musu ta zauna gaba ɗaya palon suka yi shiru.
Ummi ne ta katse masu shirun da cewa "Baby kin san shine da kika zauna a jikinsa?" Ta yi maganar tana kallon daddy da jelly ke a jikinsa, Jelly kam ko kallon in da take ma bata yi ba, domin bata sansu ba.
Imran ne ya ce "Ummi babanta ne ai". A razane suka miƙe a tare ita da Nawid, kallon juna suka yi kafin su sake kallon Imran ɗin. Abbi ne ya ce masu su zauna sai ayi magana a nutse, ba musu suka zauna, Imran Abbi ya fara tambaya akan me ya faru a ina kanwar Hadiza wato Ummi ta san Jelly?.
Nan Imran ya basu labarin duk abin da ya faru daga lokacin da Nawid ya kira shi a waya akan zai kawo mashi jelly har zuwa yanzu. Kallon Ummi Abbi ya yi kafin ya tambayeta me ya faru, a ina kuma ta sami jelly da har ta riƙeta na tsawon wannan watanni. Ita ma dai Ummi ba ɓoye ɓoye ta fara basu labari tun daga farko har izuwa yau da take zaune a gabansu.
Lokacin da ta kai karshen maganar ba wanda bai nisa ba a cikin Palon, haka zalika ba wanda bai yi hamdala ga Allah ba, ita ma jelly sai da ta ɗago ta kalli Ummin ɗin, nan take ta ji Kaunar matar ta kamata, Ummi mai zuciyar imani, duk da jelly ta manta su amma tana kaunar Ummi, bare ma da Ummi ta bada labarin irin zaman da suka yi, sai ta kara jin tana son Ummin sosai.
Shiru palon ya ɗan yi na tsowon mintuna kafin daddyn Jelly ya fara magana a nutse, "A gaskiya bani da bakin da zan iya gode maki na wannan abin da kika yi Mani, sai dai na yi maki addu'ar Allah ya baki gidan aljanna, kai kuma Nawid ina mai baka hakuri domin ba'afi minti 20 ba dana cika alkawarin dana ɗauka na aurawa Imran auren jelly, yanzu jelly matar Imran ce, amma kuma a matsayina na mahaifi a garesu na baka auren Aafia kuma a yanzu za'a ɗaura ba sai anjuma ba". Gaba ɗaya palon zubawa Daddyn Jelly idanu suka yi.
Ita dai Aafia bata damu ba, idan baku manta ba tana bala'in kaunar Dr Nawid tun suna school da su Rufee, hakan yasa bata wani damu ba dan ance za'a aura mata shi.
Shi kuwa Nawid kallon ƴan matan dake wajen ya yi yana son tantance wace ce Aafia a cikinsu, ganin hakan yasa daddy ya ce "Ga Aafia ɗin nan mai black dressing".
Kwata kwata Nawid bata yi mashi ba, amma ba yadda zai yi, yama fi son Hanan akanta, domin A'afia irin siraran matan nan ne, shi kuma ya fi so ya ga ko'ina a cike. Ba dan ya so ba ya karɓi aurenta, Daddyn Jelly dai shi ya sake biyan sadaki, a ranar aka ɗaura auren, jin abin suke yi kamar mafarki Nawid dai zuciya bata so ba, sai dai kuma ya cire son jelly a zuciyarsa, domin yasan irin son da Imran yake yi mata, sai dai bai san ita ɗin ba ce, amma kullun idan sun haɗu Imran ba shi da magana da ta wuci na jelly'nsa matarsa hakan yasa ma ya cire ta zuciyarsa, kuma koda an ɗaura mashi aure da ita kafin su gane iyayenta, idan ya san cewa ita Imran yake so to zai saketa, dan shi zai bawa wani labarin irin son da Imran yake yi wa Jelly ba dai wani ya ba shi ba.
Karin wata Haske Abbo shine wannan alhajin da yake neman Aafia ruwa a jallo a baya, wadda ya yi sanadiyar mutuwar Yusuf yayan Rufee, kuma shine wannan man ɗin na school ɗin su A'afia wadda ya kashe Amal kanwar Rufee ɗin, akwai abin da yake so a tattare da Aafia wadda shi kaɗai ya barwa kansa sani, ya rasa Aafia ce sanadiyar koma warta gidan su Akil wadda babu wani ɗan iskan matsafi ko aljanin da ya isa ya nufi gidansu Akil ɗin, hakan yasa Aafia ta kubcewa Abbo, amma ba