Showing 81001 words to 84000 words out of 355604 words

Chapter 28 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2840

💖RIMSHA💖


Yau ta kama ranar Laraba, a yau a ke cin kasuwar Eyankorin market, tun safe Kausar ta takura musu a kan su shirya su je kasuwa, da farko Rimsha ta ki yarda, sai da iya ta ce mata

"Rimsha ki shirya ku je, dan ki kalli kasuwar mu, kin dai ga baban Kausar ranar litinin zai dawo, kuma yana dawowa zan karɓa mu ku kuɗin mota ku koma gida, to ki je ki ga yanda kasuwar mu yake" to kawai Rimsha ta amsa da shi, sannan suka yi wanka suka shirya.

Sai wani murna Kausar ta ke yi kamar ba lafiya ba, Rimsha dai kullun doguwar riga take sanyawa, dan bata son fita da kananan kayan nan na Kausar, ga shi Kausar bata da Hijabi babba, sai yan kanana zuwa kirji, ita kuma bata son hakan. Haka ita ma Ayla doguwar riga ta sanya, ita kuma Kausar riga da skit.

Jerawa suka yi suka fito daga gidan, Rimsha da Ayla sun sanya hijabi, ita kuma Kausar ta sanya hula kawai ta rufe gashin kanta.

Duk in da suka wuce sai an kalli Rimsha an sake, masu gajen hakuri har magana suke yi mata, amma bata kula kowa, ba wanda ta tanka a cikinsu.

Daidai za su shiga kasuwa Rimsha ta hango wata yar matashiyar budurwa ta yi wani irin banzan dressing abin ba'a magana, ba kyan gani, zuba mata ido Rimsha ta yi, har kan bakin nononta ana iya gani, saboda bata sanya breziya ba, ga shi rigar ya matseta sosai da sosai, wandon kuma ya fito mata da zanen shatin gabanta gaba É—aya, abin ma kunya ya bawa Rimsha, cikin sauri ta sanya hannunta a kirjinta, dan ta ji ko akwai in da ya bayyana a waje.

Rimsha akwai tattalin kirgan dangin nan nata, bata son su sha iska ko kaÉ—an, da zarar ta ji wuyar rigarta ya zamo, a sukwane ta ke yin maza ta janye ta mai da, akwai ranar da ta watsawa Iya miya mai zafi a kan hakan, suna cikin yin girki a kitchen, Iya na zaune a gefen murhun tana tsinka ganyen ugun, ita kuma Rimsha tana juya kayan miyar dake kanwuta yana soyuwa, ta É—ebo kayan biyar a ludayi sai ta fasa yake yi, tana son gane ya soyune ko bai soyu ba, dan ba wani kwarewa ta yi da aikin ba, hakan yasa take bin abin dalla dalla.

Tana riƙe da miyar cikin ludayi sai tafasa yake, kasan cewar tana duke hakan yasa wuyar rigarta ya ɗan zazzago, a sukwane ta yi wurgi da ludayin ta kama wuyar rigar tata, bata ma san a fuskar iya ta wurga ludayin ba, har sai da ta ji ihun Iya hakan yasa ta farga ta fara bata hakuri.

Kasan cewar Iya ta san abin dake faruwa, tasan halin Rimsha, ita da wannan kirgan dangin tata, sai bata damu ba.

"Rimsha me ki ke kallo? Mu tafi mana, ga can Kausar ta tafi ta barmu" Cewar Ayla.

Ajiyar zuciya Rimsha ta sauƙe tana faɗin "Ga abin da nake kallo can Ayla, kina ganinta kamar tsirara, ai wannan dama cire kayar kawai ta yi, ta tafi a haka sai a san ta cika tantiriyar yar iska".

Yar dariya Ayla ta yi, sannan ta jawo hannunta tana faÉ—in "Ke dai ba ruwan ki, wuce mu tafi, idan kuma duka kike son sha tom zaki samu, ke kowa ne sai kin masa wa'azi, to wlh ni a yadda na ji labari, yarabawa da kike gani ba kananan masu ilimin addini ba ne, sune fa suka kawo saka nikaf a Nigeria, dan haka ba ruwan ki, komai ki kalle shi da ido, idan ya miki munin kallo to ki rufe ido, alshekiya, dan ke ba al Sheikh za'a ce ba"

Shiru Rismha ta yi bata sake magana ba har suka shige cikin kasuwa. Sai dai kuma menen? ko da suka duba ba su ga Kausar ba, tsuru-tsuru suka yi da ido sun rasa ina za su nufa.

Sai haÉ—a zufa suke yi kasan cewar sun tsaya a rana, sai yi musu magana jama'a suke yi a kan su baro rana su dawo inuwa, amma ina basan jin me jama'a ke faÉ—e, saboda ba wani iya yarabanci sosai suka yi ba.

Sun jima tsaye a wajen, dan sun fi awa guda, sun ga ji bayin Allah, suna kuma tsoron komawa gida ba tare da Kausar ba, ita kuwa Kausar da gangan ta shige wani masallaci kusa da wajen, ta laɓe, tana leƙo su ta window, tana ganin yadda suke haɗa zufa a wannan uban ranar, kuma tasan ba za su koma gida su barta bane shiyasa ta yi mu su hakan, kuma dama ta kudiri niyar basu wahala har sai sun gwammaci dama basu zo gidan su ba.

Bayin Allah sai magana jama'a suke musu a kan suzo su zauna, idan ma wata suke jira, ga wajen zama a inuwa, amma saboda basa jin yaren sosai sun ki kula kowa, har jama'a suka ga ji suka kyale su, kuma Ayla daman ta san haka zata faru, dan tasan koda ma da English jama'a suka yi musu magana, mawuyacin abu ne Rimsha ta yarda ta shiga cikin shagon mutun, ko kuma runfarsa ta zauna, ba zata taba yarda ba kome zai faru, dan Rimsha tana kula da jikinta da mutuncinta fiye da tunanin mai tunani, kuma bata son shiga harkar kowa, haka zalika bata son rainin hankali da wulakanci, shi ya sa bata kula kowa.


Sai wajen awa É—aya da rabi, sai da taga sun kusa zubewa kasa sannan ta fito, tana dariya, ba su ce mata komai ba, hakuri ta ba su, ta ce musu ai tana can wata kawar ta ce ta tsayar da ita, binta da ido kawai suka yi, ba su ce ko uppan ba.

Wucewa gaba ta yi tana faÉ—in "Muje wajen takardun koyar girki, Rimsha ke ki gani, dan nasan kece mai son iya girki.

Da farko Rimsha ta ce bazata sake zuwa ko ina ba, idan ba gida ba, amma da ta ji takardar koyar girki sai ta daure kamar zata faÉ—i ta bi bayan Kausar.

Wajen wani shagon sai da takardun koyar girki suka je, sosai Rimsha ta ji daɗi, ta kuma yi sa'a takardar ba tsada sosai 200 Naira ne ko wani guda ɗaya, wananna ragowar 500 ɗin wadda ya rage musu Shikenan, ta ɗauko ta miƙa masa ta ce Abata takardu guda biyu, kala daban-daban, karɓa ya yi, ya ce su zaba.

Masu kyau kala biyu Rimsha ta zaɓa sannan ya basu canjin Naira 100, suka wuce zuwa gida, sai neman su da magana Kausar take yi, idan sunki kulata, sai ta fara yi musu habaici, suna jin ta, kuma sun san da su take yi, amma basu nuna wani damuwa ba.

Bayan sun koma gida, bai fi da minti 40 ba Kausar ta sake sako su a gaba a kan lallai sai sun ta shi sun rakar wani gida.

Kamar za su yi kuka haka suka hakura suka tashi, dama ita Rimsha bata cire hijabin jikinta ba, suna dawowa ta zauna ta fara karanta takardar girki abinta.

Kausar ta riga su fita, sannan suka bi bayanta. Sai tafiya suke yi, Kausar na wani babbuÉ—e jiki kamar wata niga.

Wani gida mai ƙaramin gate ta shiga da su, su dai duk in da ta yi nan suke yi. Tun da suka shiga gidan Kausar ta fara baya baya, basu ankara ba suka ji ihun wasu mahaukatan karnuka, juyawar da za su yi dan su yi wa Kausar magana, sai su ka ga ba Kausar ta ware, kafin su yi wani yunkuri wayan nan mayun karnuka sun fito daga cikin wani lungu a cikin gidan.

A guje suma suka juya, Rismha ta fi Ayla iya gudu.
Suna fita gidan karnukan suka dakata daga cikin gida, su kuma saboda sun tsorata sai gani suke yi kamar karnukan suna binsu, hakan yasa suka rinƙa tikar gudu, Ayla ta faɗi, ta buga bakin ta saman wani dutse, sai jini ya fara zuba, amma haka ta miƙe dan a tunaninta, karnukan suna binta.

Ko da suka koma gida Kausar bata Nan. A palo suka sami iya, tana ganin sun shigo a guje ta miƙe tsaye tana faɗin Lafiya Rimsha me yasa ku gudu haka.

Ka sa magana suka yi, suka zube gwiwowinsu a kasa, suna hawaye, ga Ayla baki ya kunbura sai jini yake zubarwa. Ganin Jinin yasa Iya ta kariso wajen su, a ruÉ—e ta rungumesu tana faÉ—in "Ina kuka je? Me ya same ki Ayla" har lokacin ba su iya buÉ—e baki sun yi magana ba, sai haki suke yi suna mai da numfashi.

Miƙewa iya ta yi taje ta ɗauko musu ruwa mai sanyi roba ɗaya, ta dawo ta miƙa musu, har suna rige-rigen wajen sanya hannu su karɓa.

Ganin Ayla tafi shan wahala ya sa Rimsha ta hakura Ayla ta fara shan ruwan, sai dai bata kai ga gama sha ba, gaba ɗaya ruwan ya ɓaci da jini, haka Rimsha ta hakura da ruwan sanyin ta sha na rijiya, dama ruwan guda ɗaya ya rage a fridge ɗin, Iya bata ji daɗin hakan ba, ita ma Ayla bata ji daɗi ba.

Sai da suka huta, sannan iya ta ɗan gasawa Ayla bakinta da ruwan zafi, ya kumbura suntum, Allah sarki sai fuskar tata ya koma kamar ruɓaɓen alale.

Bayan Iya ta gama gasa mata bakin ne teka tambayar ina suka je, Rismha ce ta bata labarin sun je wani gida ne, kare ya biyo su, ta ɓoye mata cewa a kan Kausar ce ta kai su ta gudo ta baro su.

Sosai Iya ta musu sannu, sannan ta gaya musu kada su sake zuwa gidan, domin gidan wani pastor ne, kuma kabilar Ebo ne, sannan ko da ya É—aure karnukansa ma, kada su sake zuwa dan É—an iska ne yana lalata mata.

Sosai suka ji tsoro tare da yiwa Iya alkawarin ba zasu sake zuwa ba.

"Ina Kausar?" Iya ce ta tambaye su tana ƙoƙarin miƙewa. Cikin sauri suka fara kallon juna, Ayla kam bata iya yin magana sosai saboda bakin nata ya kunbura sosai.

"Iya ba mu ganta ba" Rimsha ta bata amsa, Iya na ƙoƙarin shiga Kitchen ta ce "Wannan yarinya, wata kila tana gidan su Waliya ce, to shikenan ni bari na ɗaura mana girki" cikin sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayan Iya zuwa kitchen dan taya ta Aiki.

Ayla na zaune a wajen har Kausar ta dawo, tana shigowa cikin palon ko sallama babu, idon ta ya sauƙa a kan Ayla, wani mahaukacin dariya ta kwanshe da shi tana faɗin "Ayla me a bakin ki haka kamar an hura balo-balo" ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariyar shakiyanci, har da rike ciki.

Binta da ido kawai Ayla ta yi tana tunanin yadda yan uwanta maza ke kokarin lalata musu rayuwa, ita shine ma babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, shine ma abin da ya fi jefa ta cikin tashin hankali, duk abin da Kausar zata yi musu, mai sauƙi ne a kan wadda Jami'u ke kokarin yi musu.

Kausar sai da ta yi dariyar ta mai isar ta sannan ta wuce zuwa cikin dakinta, a ranta tana faÉ—in "Allah yasa ita kuma Rimsha karyewa ta yi" sai dai ta manta cewa, ita Rimsha duk rintsi duk wuya bata manta askar, haka duk rintsi duk yuwa bata fita gida ba tare da ta yi addu'a ba, dan haka duk in da zata je tana karkashin kulawar Mala'ikun Allah ta'ala.

After some hours💖

Iya da Rimsha sun kammala girki, yau sun girka, semo da miyar ɗanyen kuɓewa, yanzu Rimsha ta kware a iya tuka tuwon semo, kuma yanzu ta iya girki kusan kala bakwai kenan.

Da yarabanci Iya ta ce mata ta fito musu da abincin Palo, yanzu tana gane yaren duk da ba sosai ba, sama sama haka take ganewa, idan aka yi mai ɗan tsawo, kamar yadda ɗazun a kasuwa, jama'a suka rinƙa ce musu su fita a rana suzo su zauna a inuwa, ta dai ji suzo su zauna, amma bata gane su fita a rana ba domin bata san sunan rana da yaren ba, hakan yasa ta yi banza da su, kuma dama ko da ta ji me suka ce ma, ba zata taɓa shiga cikin shagon su ko rumfarsu ta zauna ba.

Bayan ta kawo abincin palo ne ta koma É—aki ta cire kayan cikin ta, ta É—aura towel É—in Kausar ta wuce toilet dan yin wanka.

Lokacin da ta yi wanka ta fito Kausar na zaune a É—akin, sannu ta ce mata sannan ta wuce wajen drawer kayan ta, kamar ba Kausar a cikin É—akin haka ta yi banza da ita bata amsa sannun ba.

Dogon riga Rimsha ta É—auko, tana kokarin sakawa a jikinta, Kausar ta yi saurin cewa "A'a Meesha kayan nan nake son sakawa yau" cikin sauri Rimsha ta juyo tana kallonta, kawar da kai Kausar ta yi kamar ba ita ba.

Mamaki Rimsha ta ke yi, domin farkon zuwansu ko da Kausar ta yi niyar saka kaya, idan Rimsha ta É—auki kayan, hakura Kausar ta ke yi, amma yau shine zata ce kayan take son sakawa lallai.

Mayar mata da kayar Rimsha ta yi, ta É—auko wani zata saka, nan ma Kausar ta ce "Kai Rimsha ki nayar da wannan saboda bana son a saka shi yau, kinga last week kin saka, kuma idan kika cika saka kaya mutuwa yake yi" wasu zafafan hawaye Rimsha ta ji sun cika mata ido.

Haka ta hakura ta mayar da kayan, sau huÉ—u tana É—auko kaya Kausar tana cewa ba zata saka ba, daga karshe ma cewa ta yi "Ni fa Rimsha jikin ki na kashe min kaya, da alama ke renon miyar kuka da tuwon dawa ce, idan ba haka ba, da kin saka kaya sai ya koÉ—e kamar ba lafiya ba, to ni gaskiya na ga ji, ba zan iya ba"

Hawayen da Rimsha ke kokarin ɓoyewa ne suka zubo mata, wani na bin wani, dogon tsaki Kausar ta ja, tare da miƙe wa ta nufi waje tana habaici "An zo an zauna mana a gida, a ci a sha a saka sutura amma sai a laɓe a cikin ɗaki ana zagin yan gida, kai butulu kam bai yi ba, a canza hali ko za'a ji daɗin rayuwa". Ta kai karshen maganar tare da ficewa daga cikin ɗakin.

Zubewa kasa a wajen Rimsha ta yi tare da dafe kanta tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Iya na falo tana ta jiran ta, ganin ta jima bata fito bane yasa ta ce "Kausar ki kira Rimsha tazo kuci abinci". Toro baki ta yi tare da miƙe wa ta koma cikin ɗakin.

Rimsha tana duke a kasa kan gwiwowinta tana shan kukan ta, a haka Kausar ta iskota, wani daÉ—i ta ji ta saka Rimsha kuka, ta fara kuntata musu.

Ta ɗauki yan mintoci tana kallon Rimsha kafin ta ce "Ki ta shi ki ɗauki wando da riga ki saka ba dan halinki ba, sai dan na lura kina son ɓoye abin, baki so a gani, amma daga yau ni zan rinƙa baki kayan da zaki saka" ta kai karshen maganar tare da bushewa da dariya, cikin sauri ta sanya hannu ta toshe bakinta, kada Iya ta jiyo dariyar tata.

Miƙewa Rismha ta yi, tazo ta raɓa gefenta ta wuce tana goge hawaye.

"Kizo ki saka kayan mana, ko haka zaki fita?" Banza da ita Rimsha ta yi, bata kula ta ba

(Ni ko nace baki san jinin Nawazudden da bala'i zuciya bane, zuciya da izza a cikin jinin su yake kawai dan dai Rimsha tun tana karama mum É—in ta ta koya mata hakuri ne, da Jehan ne ai baki isa ba, ke da gidan ku Jehan zata mai daki baiwa, jinjina Jehan Nawazudden yau ga ranarki)

Tsohon kayanta da ta cire suka mai da tsumma shi ta É—auka ta sanya a jikinta, ta fito palo.

"Subhanallah Rimsha yau kuma wannan dattin kika saka a jikin ki, ke da kike da tsabta baki son datti ko kaɗan?". Cewar Iya, kakalo murmushi Rimsha ta yi tare da zama kusa da Ayla tana faɗin "E iya yau ina son tuna gida ne shiyasa" "To na ji, amma me ya saki kuka?" Cikin sauri ta ce "Ba komai Iya ni ban yi kuka ba" da yake iya bata son matsa musu sosai, ta san halin su yanzu kila akan gida ta yi kuka, sai ta kyaleta, tare da miƙa musu abincin su.

Karɓa suka yi suka faraci kenan Kausar ta fito tana wakar habaice habaicen ta.

Cike da ɓacin rai Rimsha ta cire hannunta daga cikin abincin, ta miƙe ta nufi Kitchen ta wanko hannun tata, sannan ta dawo ta zauna.

"Rimsha lafiya? Me yake damun kine?" Cewar Iya, ita dai Ayla ta san matsalar dan haka sai ta yi shiru, kuma da yake ita bata kai Rimsha zuciya ba, sai ta ci gaba da cin abincin ta.

"Iya ba wani abin da ke damuna, kawai dai na ƙoshi da abincin ne"

Wani sanyi Kausar ta ji a ranta, ta jawo abincin Rimsha tana faɗin "To tun da ta ƙoshi ni bari na haɗa". Tsawa Iya ta daka mata a kan ta ajiye abincin, ba musu ta ajiye tana turo baki, a zuciyarta tana tunanin ta yadda zata cusawa iya tsanar su Rimsha.

Ita kuma Iya miƙewa ta yi, ta dawo kusa da Rimsha ta zauna ta hau lallashin ta, dan ta lura Rimsha tana da bala'i zuciya, ga zurfin ciki, ko zaka kwana kana tambayarta meke damunta, idan ba ta yi niyya ba bazata faɗa ba, sai dai ka gaji ka yi shiru.

Da kyar ta iya shawo kan Rismha ta hakura, hakan ma sai da ta haÉ—a ta da Allah da annabi, sanan ta yarda. Sai godiya Ayla take yi ga Allah daya sanya Rimsha ta hakura, dan tasan halin ta, idan ta yi fushi da abinci, to ko kashe ta yinwa zai yi, ba zata ci wannan abincin ba, a hakan ma tana duba abin da annabi ya ce na latatba kada ku yi fushi, ba dan haka ba, Rimsha da ta jima da hallaka kanta da zuciya.

Iya tana zaune tana kallonsu har sai da Rismha ta ci abincin nan tas, sannan ta ce da Kausar ta É—aukowa Rismha kaya, Rimsha na kokarin cewa bata so, Iya ta yi sauri É—aga mata hannu tana faÉ—in "In dai kika ce baki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login