Showing 126001 words to 129000 words out of 355604 words

Chapter 43 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2767

kasa gaya mashi cewar kukan rabuwa da Rimsha take yi, domin a yanzu Rimsha ita ce duniyarta, saboda mamanta ta rasu ga shi ita bata san waye babanta ba.

Sai da daddyn Jelly ya tabbatar ya sanya Ayla murmushi sannan ya mata izinin tafiya, ran ta ya ɗan yi fes kaɗan, amma ba zata iya dai'na tunanin Rimsha ba.

Bayan tafiyar tane Imran ya ce "Bappa wlh yarinyar nan tana mini kama da Ustadz"

"waye kuma Ustadz Imran?" "Bappa ka manta Ustadz da muka taɓa zuwa da shi Kano, A,A Salahuddeen, wannan babban abokina ɗin nan, yanzu ma ya je gyara wani abin dan gane da makarantar sane, amma idan ya dawo zan kawo maka shi kaga ni, wlh muryan sune ma ya fi kama da na juna".

Shiru daddyn Jelly ya yi kafin ya ce "Kamannin ne kila kawai, domin a labarin da ta bamu ba ta da ɗan uwa AA Salahuddeen" "No bappa dama nima bance ɗan uwanta bane, AA Salahuddeen me zai haɗa shi da wannan yarinyar? Kai bappa AA Salahuddeen fa nace maka, ina ai ba su ma haɗu ba, kawai dai kamar murya ce data fuskar, ita ma ta fuskar ai ba sosai ba ce, muryar dai ta fi sosai, bacin haka ai yan uwan A.A Salahuddeen ma kwata-kwata ba wanda yake kasar nan, shima bai jima da dawowa ba, kai bappa in takaice maka zance duk yan uwan sa babu wadda yake ɗaga ido ma ya kalli mutun da daraja, sai shi kaɗai, shine ya fita zakka a cikinsu, yana son mutane, ga shi da taimako, kuma dukkansu yaran Salahuddeen mazauna Englan ne basu zama a nan Naija".

Shiru daddy jelly ya ɗan yi kafin ya ce "Yanzu dai Imran yaushe za ku koma Kano?" Shiru ya ɗan yi kamar mai tunani, can kuma sai ya ce "E to jibi zamu je Katsina ni da Dr dan ya takura mini a kan nazo na ga matar da zai aura, wai yar Katsina ce, idan muka dawo washegari sai mu wuce Kano ba" "wani Dr kuma?" Daddy ya tambaya

Miƙewa ya yi yana faɗin "Wani abokina ne wadda muka yi primary tare da shi, shine ya takura mini ya samu mata a Katsina nazo na ganta" Fatan alkhari daddyn Jelly ya yi musu sannan Imran ya wuce ya koma cikin bedroom nasu dan ya duba shin Irfan ya gama wanka ne ko ya ya.

Shi kuma daddyn jelly kishingiɗa ya yi yana tunanin rayuwa.

To mu koma Katsina dan jin ya ake ciki.

💖💖KATSINA💖💖

After 1 day👌

Abubuwa sun faru a cikin wannan kwana ɗayar, ciki hadda bayan Sadiq ya dawo da yamma daga gareji, ya sanar da Rismha su mummy sun ce za su je neman Jehan ne, idan sun ganta kuma za su wuce Maiduguri su nemi yan uwan mum ɗin, Rimsha ta sha kuka har kamar ranta zai fita, yanzu shikenan ta rabu da su mummy kenan, idan ta tuna hakan sai ta sake sakin wani sabon kuka. Da kyar Sadiq ya lallaɓata ta yi shiru, amma bata iya samun barcin dare ba har sai can tsakiyar dare barcin ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

Washegari tun karfe 7 na safe Ibraheem ya yi musu dirar mikiya a kofar gidansu, domin yau kwanan Jehan huɗu kenan bata je restaurant ba, kuma babu wani bayani, shine ya biyo sahu.

Sallama ya yi a kofar gidan, lokacin Rimsha na sharar tsakar gida. Baiwar Allah tun da ta yi sallar asuba bata koma barci ba, ta tattara wanke-wanke ta yi yanzu tana shara, kamar dai yadda take yi a gidan su Kausar.

Jin sallama yasa ta ajiye tsintsiyar ta fito dan taga waye ne, sallama ita ma ta yi masa sannan ta gaishe shi, sai kallonta yake yi, abun ku da jini sai ya yi mata kallon kama da Jehan "Ke ina Jehan take?". Daidai lokacin Sadiq ya fito daga ɗakin su dake cikin zauren, dan shima ya ji sallamar.

"Rimsha me kike yi a nan?" Sadiq ne ya tambaya. Cikin girmamawa ta gaishe shi, da fara'a ya amsa sannan ya miƙa wa Ibraheem hannu suka gaisa. "Rimsha ki shiga ciki mana?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "A'a yaya Sadiq na ji yana tambayar ina Jehan ne, to ina son in ji me ya kawo shi wajen Jehan"

Kallon Sadiq Ibraheem ya yi ya fara magana rai a matukar ɓace "Sadiq ina Jehan? Me yasa kwana biyu bata zuwa aiki? Kasan dai yarjejeniyar dake a tsakanin mu ko? To ni gaskiya ma na fara gajiya da wulakancin Jehan, ba zan iya ba, na taimaka mata na rufa mata asiri, amma ni kuma tana kokarin ta tona mini nawa asirin akan menene? Me yasa take yi mini hakan? Wlh ku ja mata kunne, idan ba haka ba, to ni gaskiya ta biya ni kuɗi na a dunkule".

Tun da ya fara magana Sadiq da Rimsha suka tsare shi da ido, har sai da ya kai aya sannan Sadiq ya ce "To Ibraheem ni dai ba abin da zan ce maka sai dai na ce Allah ya baka hakuri, domin kuwa Jehan da iyayenta basu nan, sun bar Katsina saboda wata jarabawa da ta hau kan su....". Kun san Katsinawa da iya zagi, tun Sadiq bai kai karshen maganar ba Ibraheem ya banka wani uban ashar mai tashin kan mai sauraro.

Nan fa ya fara ruwan bala'i, wai Jehan bata isa ba, dan ubanta sai ta biya shi kuɗin sa. Ganin yana kokarin ya tara musu jama'a ne yasa Rimsha ta yi saurin cewa "Ka yi hakuri zamu biya kuɗin yanzu dai ka yi shiru".

Dawo da kallonsa kan ta ya yi from head to toe yake kallonta, jikinta na sanye da wannan hijabin nata har kasan, ita kuma kallon Sadiq ta yi ta ce "Yaya Sadiq me ya faru? Me ya haɗa Jehan da mutumin nan har ta karɓa masa kuɗin sa? Kuma naira nawa ne ma kuɗin nasa?"

Ba tare da ɓata lokaci ba Sadiq ya shiga bata labarin abin da ya faru sama-sama dai haka, shiru ta yi tana tunain ko dai ta cire sarkar wuyarta nan ne ta ba shi, domin sarkar da gwaggo ta bata, za tafi kuɗin sa da yake ikirari tsada, to amma idan ta bashi sarkar bata da tabbacin zata sake haɗuwa da su gwaggo domin suma sun cire rai da ita kwata-kwata, sun hakura da ita.

Ganin ta yi shiru ne yasa Sadiq ya ce "Rimsha lafiya kuwa?" Yar firgita ta yi sannan ta ce "Lafiya yaya Sadiq, idan ba damuwa ni zan karisa aikin da Jehan ɗin ta fara, domin na biya bashin, ni bana bukatar ma ya rinƙa zarar wani abu daga cikin kuɗin kamar yadda suka tsara da Jehan, kai tsaye kawai ya ɗauki albashi na ɗin gaba ɗaya har sai kuɗin shi sun kare".

Cikin sauri ya ce ",Ai ni yanzu kuɗi na sun karu, daga 500k ya koma 700k, domin ammini wulakanci". Ɗaure fuska sosai Rimsha ta yi, rai a matukar ɓace ta ce "Da cewa ka yi na yi aiki na kara maka saboda Allah to zan kara maka, amma kuɗin riba kuɗin ruwa baka isa ba wlh, ni Rimsha ba zan yi wannan saɓon Allah ba, wato ka bada bashi kuma ka kara kuɗin ruwa, to ba ka isa ba, ina maka aiki na daidai kuɗin ka zan bar restaurant ɗin". Ta kai karshen maganar tare da wucewa cikin gida abinta,

Jinjina kai dukkansu suka yi daga Ibraheem ɗin har Sadiq ɗin, a fili Sadiq ya ce "Jini ba karya ba, jini ba ruwa ba, kai tab ɗi jam". A ɓangaren shima Ibraheem abin da yake tunani kenan a cikin zuciyarsa, jini ba karya ba kuma ba ruwa ba, dole a sami ɗabiun Jehan ko ma yayane a tattare da Rimsha, ga kuma zahiri sun gani da idonsu, ita ma Rimsha bata takuwa.

Sun jima tsaye shiru kafin nan Ibraheem ya katse musu shirun da cewa "Ka ce ta shirya mu wuce aiki yanzun nan, domin Jehan ta ɓata kwanaki huɗu bata zuwa aiki, dan haka dole ta fara aiki daga yau" Sadiq ya yi kokarin rokar shi a kan ya bari sai gobe, amma ina ya ce shi ba zai yarda ba dole tazo su tafi, haka Sadiq ya hakura ya kirata a kan ta zo su tafi, ba musu ta shirya suka wuce da Ibraheem, ya goyata a bayan mashin nasa, Sadiq ya ce mata da yamma zai zo ya ɗauke ta.

A ɓangaren Ahmad kuwa, tun da Rimsha ta jefa wayar nan nata a cikin trolleynta bata sake bi ta kan wayar ba, ya kira har ya gaji, ya shiga damuwa sosai, ya rasa meke yi masa daɗi bawan Allah, har ya fara tunanin zuwa Katsina dan ya duba ko lafiya take.

(Ni kuwa nace in dai Rimsha ce baka ga komai ba ma🤣)

To Rimsha dai ta isa restaurant lafiya kuma ta fara aikin da Jehan ta fara ta bari, kasan cewar ita Rimsha baa san fuskar ta media sosai ba, sai ba wanda ya gane ta, kuma ga zahiri ma kun gani, ita Jehan lokacin da take tare da wayarta, kullun zaku ga waya a hannunta, sannan kuma tana yawan hawa media, amma ita kuma Rimsha kun dai gani tun da ta sanya wayar cikin trolley bata sake bi ta kanshi ba, so ita bata wani damu da media sosai ba.

Ma'aikatan wajen daga mazan su har matansu sai da Rimsha ta burgesu, sai kallonta suke yi, ga shi tana da girmama mutane, sai dai fa ita ma bata murmushi bare dari, fuskar nan nata a ɗaure tamau, taki sake musu fuska, dan bata son a kawo mata shirmen banza a lamuranta, sai ɗaure fuska take yi, amma tana aiki lafiya lou tare da su, sannan tana basu girma, shi kanshi Ibraheem ya fi jin daɗin aiki da ita fiye da Jehan, domin ita idan ya saka ta yin abu, bata yi mashi musu, tana yi, tsabanin Jehan da sai ta ga dama, ko kuma idan aiki ya saɓawa dokar da ta sawa kanta tofa ba zata yi shi ba.

(Tofa wannan shine reshe ya juye da mujiya, ga Rimsha a restaurant, ko me zai faru?🤔 Mu dai je zuwa)

Idan muka koma ɓangaren gidan Abbo kuwa.

Lafiya lou Nawid ya fita shopping nasa shi da jelly, daga nan suka je suka yi kallo, ya sai mata Ice cream kala-kala tare da chocolate dayawa kamar yarda ya faɗa.

Bayan sun dawo gida, da misalin karfe huɗu na yamma washegari kenan, gaba ɗaya gidan shiru babu kowa, Ummi tana bedroom nata tana barci.

Sanye da wando da riga Jelly ta fito daga bedroom nata, sai dai ta ɗaura wani irin riga mai kama da after dress a kan kayan nata, amma shi wannan bai kai mata har kasa ba, iya gwiwarta ya tsaya mata, kanta babu ɗankwali, ta saki wannan stubborn hair nata.

Gaban Tv ta je ta tsaya tana ganin wani India film da suka sanya, ganin Film ɗin ya yi mata kyau ne yasa ta koma saman sofa ta zauna.

Tana tsaka da kallo ta ga ansanya wakar kutchi kutchi hotaye, haba ai a ɗari Jelly ta miƙe ta fara tikar rawa, kamar wata yar tsana haka Jelly ke rawa tana juyi, sai ka rantse da Allah babu kashi a jikinta, har wani karairaya take yi tana lankwasa kugunta.

(Kai jama'a ashe ba iya baiwar cin kaza ke gareta ba, har da baiwar rawa🤣)

Har wani wurgi da hannu sama take yi tana yin wani abu kamar yadda maciji ke juyawa, dama gata ba kiba yar siririya, sai abin ya bata abin da ake bukata.

Yafi minti biyar yana tsaye yana kallonta, tun lokacin da ta fara rawar ya shigo cikin gidan, bata ji shigowar shi ba, kuma bata gan shi ba, sakamakon ta kure Volume na Tv, dan a cewar ta idan Tv na kara sosai wakar ta fi daɗi.

Sai wani kallonta yake, duk ta yadda ta juya haka shima yake juya idanuwansa yana binta da kallo, har sai da aka gama wakar sannan ta zube saman sofa tana dariya tana mai da numfashi, har lokacin bata lura da shi a wajen ba.

Shi kuma ganin ta gama rawar ne yasa ya shigo cikin palon hannunsa ɗaya riƙe da jakar computer ɗayar kuma ya ratayo coat nasa, daya cire ya bar na cikin.

Cike da murna ta tashi tana faɗin "Yaya Nawid baka dawo da wuriba da ka kalli rawana". Wani irin farinciki yake ciki kamar wadda akayi wa albishir da gidan aljanna, Jelly ta tafi da imaninsa yau, lokacin da take rawarnan, kamar yarda take rawa haka zuciyarsa ke kaɗawa a kanta, yanzu duk wani shirme da zata yi masa, burge shi take yi, komai nata kyau yake yi mashi.

Miƙa mata jakar hannunsa ya yi yana faɗin "Ga shi rike mini wannan dan a gajiye na dawo" to ta ce tare da karɓar jakar. Saman sofa mai zaman mutun 3 ya zauna yana sauke numfashi a hankali. "Baby jeki kawo mini ruwan sha". Ajiye mashi jakar ta yi da sauri ta juya zuwa wajen fridge.

Kallo ya bita da shi, yana mai jin wani abin da ba zai iya misaltawa ba a zuciyarsa. Ruwan faro mai sanyi sosai ta ɗauko masa, sannan ya ɗauko glass cup kamar yadda taga Ummi na yi wa Abbo.

Bayan ta kawo mashi, sai ya ce ta zuba mashi ruwan, to ta ce sannan ta sanya karfinta tana kokarin buɗe robar ruwan, amma ina ta kasa, ɗan kishingiɗa ya yi tare da karɓar robar ruwan ya buɗe mata sannan ya miƙa mata a kan ta zuba mashi a cup, ai kuwa yana miƙa mata ta karɓa ta fara zuba mashi daga tsakiyar kanshi har zuwa jikinshi.

A sukwane ya tashi ba shiri, ita kuma ganin ya ta shi, sai ta ce "Yaya Nawid ko dai ruwan bai maka yadda kake so bane?" sanyin ruwan yasa ya ji tamkar ya kifa mata mari, amma ina zuciyarsa ba zata iya barin shi ya mare ta ba, daurewa ya yi ya ce "Haba baby meyasa zaki zuba mini ruwa mai bala'in sanyi haka?" Turo ɗan bakin nan nata ta yi, cikin shagwaɓa ta ce "Kai yaya Nawid, ka manta ne?, Kai fa ka ce na zuba maka ruwan".

Dafe kansa ya yi yana faɗin "Kash baby nifa a cup na ce ki zuba ki bani na sha, ba a jikina na ce ki zuba mini ba..." Cikin sauri ta katse shi da cewa "A'a yaya Nawid wlh karya kake yi, ni baka ce na zuba maka a cup ba, cewa ka yi in zuba maka ruwan, shine ni kuma na zuba maka, amma shine zaka zaje ni" ta kai karshen maganar tare da sakin kuka ta nufi hanyar ɗakin Ummi.

Cikin sauri ya yi maza ya riƙo hannunta yana faɗin "To ki yi hakuri kin ji ko? Na ji nine nayi laifi yanzu ɗauko wani ruwan ki zuba mini a cup ki bani na nasha kishi nake ji" To kawai ta amsa mashi da shi, sannan ta wuce ta ɗauko wani ruwan.

Shi kuwa ɓalle botir ɗin rigar jikin nasa ya yi, ya cire ya ɗaura saman sofa, ya zauna daga shi sai farar singlet.

Ya yi Sa'a yanzu da ta kawo ruwan ya buɗe mata a cikin cup ta zuba mashi, sannan ta miƙa mashi, karɓa ya yi ya kafa a bakinsa, wani sanyi ya ji tana ratsa mashi zuciyarsa a lokacin da sanyayyar ruwannan ke ratsa maƙogwaransa.

Tas ya shanye ruwan tare da miƙa mata cup ɗin, karɓa ta yi ta mai da mazauninsu, sannan ta dawo ta zauna kusa da shi.

"Baby sai yaushe zaki koyi girki ne?" Ya tambaya yana kallonta, Cikin nuna ko in kula, ba tare da kalli in da yake ba ta ce "Sai ka auro wannan matar taka da kace kake so, ranar auren ni zan yi muku girki". Mamakine ya kama shi, dama ta ji abin da suka ce shi da Ummi ne? Lokacin da suka yi maganar tana cin kaza fa, kenan tana sane da abin da yake faruwa kawai magana ne bata yi? Lallai kam yarinyar nan akwai kwakwalwa sai dai iskanci ya cika mata ƙwaƙwalwar tata over.

Sai tunani yake yi ita kuma hankalin ta na kan kallon da yake gaban ta.

A wannan hali Abbo ya dawo ya samesu, wani irin kululun bakin ciki ya ji lokacin da ya kallesu a haka, ga Nawid ya cire riga daga shi sai singlet, ita kuma Jelly ta zauna kusa da shi tana kallo, ga fuskokinsu dukkansu ɗauke da annuri na farinciki, alamar zaman su a inuwa ɗaya ya yi bala'in yi musu daɗi, sannan shi Nawid sai kallon Jelly yake yi yana murmushi, ita kuma tana kallon film.

Ganin Abbo yasa Nawid ya ce "Amma baby ai nace ina son ki ko?" Hankalinta na a kan kallo ta ce "E ka ce wa Ummi dai ka yarda zaka aureni amma zaka haɗa ni da wancan".

Murmushi ya yi sannan ya ce "To dai na ji yanzu ki faɗa mini kina sona? Dan dai ni kin san ina son ki ko? Baki ga jiya a baki na baki ice cream bane?" Sai lokacin ta juyo da kallonta kanshi, fuska ɗauke da murmushi ta ce "Zaka sake saya mini Ice cream irin na juya ɗin ne?" Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "Dayawa ma kuwa, amma yanzu dai ki faɗa mini kina so na?" Ita ma gyaɗa masa kai ta yi tana dariya ta ce "E mana ina Sonka".

Abbo ji yake yi kamar ya shake Nawid saboda bakin ciki, rai a makutar ɓace ya wuce cikin bedroom nasa, shi kuma Nawid ya ci-gaba da jan Jelly da hira, domin ya ja raayinta ta rinƙa sakin jiki da shi, ta bashi haɗin kai a kan abin da yake son yi na takurawa Abbo har sai ya dai na yin duk wani tunani da yake yi a kan ta.

(Ni kuma na kwanshe kayana zuwa Washington DC)

💖💖Washington DC💖💖


Musharraf and Asif wato Michael

Sun yi Sa'a har suka idar da sallah ba wanda ya shigo cikin ɗakin, bayan sun idar da sallah ne, Musharraf ya zauna ya fara koya masa wasu abubuwa daya kamata ya fara iyawa.

Abin mamaki ƙwaƙwalwar Michael da take da matsala a baya, amma yanzu duk wani abin da Musharraf ya gaya masa sau ɗaya yana haddacewa, hatta kalmar shahada da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login