Showing 315001 words to 318000 words out of 355604 words
a karjin Irfan kina yi mashi dariya, heartbeat ya kike so na yi da rayuwata ne? Baki san yadda nake da zafin kishi da kuma zafin zuciya bane shiyasa, wlh tun da naje school yau na kasa iya komai, duk lecture da aka yi mana a banza ya tafi, ban iya jin me suke faɗe ba, ke kawai nake tunani, ba zan ɓoye maki ba yau kin cutar da zuciyata sosai da sosai".
"Na tuba ba zan kara ba ka ji? Kada ka sake yi mani hakan kai ma, idan ka sake yi mani hakan ya zo da karar kwana zan iya mutuwa wlh".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Nima kada ki sake rungumar wani a gaban idanuna ko da kuwa su Yaya Akil ne, bana so, ni kaɗai kawai zaki runguma, kuma ina nan zuwa har gida nan ba da jimawa sosai ba, amma dai ba yanzu ba kuma ba a kwanakin nan ba, za'a ɗan jima".
Jinjina mashi kai ta yi tana kara tabbatar mashi ba zata kara ba ta tuba. To ya amsa mata da shi tare da tambayarta ina Ammie da Abba, Akil da kuma Imran.
Su na ɗaki ta bashi amsa, kara tambayarta ya yi suna lafiya ko? Nan ma e ta amsa mashi da shi.
Shiru ya ɗan yi kafin ya sake cewa "To ayi mani dariya mana ko zan ji sanyi a raina". Tana daga cikin bargon ta turo baki tana faɗin "Ni ba zan yi ba, kuma daga yau ma na daina yin dariya".
"Kai innalillahi menene a bayan ki yake tafiyar nan heartbeat?!" Ya faɗa da ɗan karfi. Ihu ta kurma tare da miƙewa ta fito daga cikin bargon, a sukwane ta diro kasa daga saman gadon tana zare idanu kuma har lokacin wayar tana a kunnenta.
Karo na farko data fara jin sautin dariyarsa mai ɗaukar hankali, tun da ta ji yana dariya tasan da gangan ya yi mata hakan dan haka sai ta sa mashi kuka ita kuma.
"Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, na tuba ba zan kara ba, amma dai idan kika sake cewa ba zaki yi mani dariya ba to fin hakan ma sai na yi maki". Zama ta yi a gefen gadon tana dafe kirjinta dan har ga Allah ba ƙaramin tsoratata ya yi ba, a tunanin ta ma snake ne ko wani abin tsoron.
Sosai ya shiga rarrashinta tare da bata hakuri yana kara gaya mata ba zai kara ba, da kyar ta yarda ta koma saman gadon ta kwanta tana zuba mashi shagwaɓa.
Dariya ya yi yana gaya mata idan wani abin ne ma zai taɓa ta ai shine na farko da zai fara tare mata shi dan kada ya taɓa ta, to ta amsa mashi da shi
Daga karshe dai shima shagwaɓar ya fara zuba mata abin gwanin burgewa dan ya iya shagwaɓa tare da rarrashin mace, duk abin da zai sanya mutun farinciki ya iya shi sosai, ga iya saka mutun dariya, hakan ma yasa Akila ta yi saurin kamuwa da kaunarsa ba kaɗan ba, hakan yasa ba zata iya jure rashin jin wannan zazzakar murya tasa ko kuma daddaɗar massages ɗin nan nasa masu kwantar wa da mutun hankali duk ɓacin rai ɗin da yake a ciki ba.
Sun sha hira sun biya missed na juna da suka yi wunin yau, ba sune suka kwanta ba sai karfe huɗu na asuba sannan ne ya ce ta kwanta ta samu barci awa ɗaya da ya rage shi kuma bari ya yi nafilar da ta hana shi yi tun ɗazun, da haka suka yi sallama cike da kaunar juna, a wani ɓangare na zuƙatansu kuma suna bakin cikin zasu yi missing na juna.
Suna katse kiran ta ɗaura wayar saman bedside drawer tare da runtse idanunta ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
Asuba ta gari, nima kuma na dasa aya sai gobe idan mai dukka ya kai mu zamu haɗu a Washington DC dan mu ji wani hali Musharraf da Aseef tare da su daddy suke a ciki....... Ma'assalam ✍️🥱
💖💖TRIPLETS💖💖
E83-84💖
💖WASHINGTON DC💖
Yau yana da class karfe 8 tun karfe 6 ya tashi ya nufi gym, good 1 hour ya ɗauka yana motsa jikinsa kafin ya sha ruwan lemon cup ɗaya sannan ya wuce ya koma cikin gida yana ta faman haɗa zufa.
Kai tsaye toilet ya kufa ya yi wanka tare da fitowa ya shirya cikin shigarsa ta mutunci ta cikakken musulmi.
Bayan ya kammala sai tashin kamshi yake yi, ya yi wani irin kyau na musamman, ba zaka taɓa cewa Michael na baya bane, ya zama cikakken gwarzon namiji, yanzu haka jikinsa ta fara murɗewa irin na ƴan uwansa saboda baya wasa da gym, safe da yamma dukka sai ya yi, da yake shi yafi siffantuwa da Lion yanzu sai ya dawo kusan kammanin Lion ɗin sak, kuma kamannin Josephine ya kara bayyana karara akan face nasa, da kallo ɗaya zaka yi mashi ba sai ka tambayi me a tsakaninsa da Josephine da kuma William ba saboda kammani, ta kowani ɓangare akwai Kamannin iyayen nasu a tattare da shi, kusan ma zaace shi kaɗai ne ya ɗauko kamanin su dukkansu, domin kuwa Lion dai da iya daddy kawai ya siffantu sai dai kama ta jini da idan ka gan shi ka ga Josephine zaka san e lallai akwai jini, shi kuma James ainahi da Michael ɗin suke ɗan kama, amma ba sosai can can ba, shi kuma Michael idan ka kalle shi kallon farat ɗaya sak fuskar Josephine zaka gani, idan kuma ka kalleshi da kyau zaka kalli fuskar daddy, kuma kunga Lion ya suffantu da daddy kaɗan shiyasa Michael yake kama da shi Lion ɗin, idanu kuma kowa da tasa, Lion dai idanun daddy ne blue eyes, brown eyes kuma na Josephine ne, dan ita ke da brown eyes irin na Michael, shi kuma James idanunsa irin na Tyson ne wato TGA kenan.
Ƴan kwana biyun nan Aseef yana busy sosai saboda shirye shiryen Exams, baya zama sosai hakan yasa ya bar gashin kansa ta taru sosai har ta ɗan sauƙo mashi a bayan wuyarsa, kuma ba karamin kyau ta yi mashi ba, shine dai kawai baya so yake askewa.
Yanzu ma tsayawa ya yi a gaban mirror yana ƙoƙarin fara rage tsawon gashin nasa, daga ta bayansa ya ji Musharraf yana faɗin "A'a my Aseef ka bar gashin nan dan Allah, wlh ba karamin kyau ya yi maka ba".
Fuska ɗauke da kayatatcen murmushi ya juyo da kallonsa zuwa kan Musharraf ɗin yana faɗin "To shikenan Uncle ai duk abin da kake so nima ina son shi, yanzu dai ina kwana?".
Murmushi Musharraf ya yi yana faɗin "Lafiya lou my pleasure what about you? How was your night?".
"Am fine uncle, kasan me nake so da kai?" Girgiza mashi kai Musharraf ya yi alamar A'a.
"Good, uncle tun da Allah yasa tafiyarka Nigeria yau bata yi wu ba sai jibi ina son daga yau zuwa jibin nan mu fita tare, akwai abubuwa da zamu je mu yi ciki kuma harda shopping zan je na yi maka". Jinjina kai Musharraf ya yi alamar to.
"Okey uncle ka shirya da wuri mu fita tare ka je ka kalli school namu, daga nan kuma sai mu wuce yawo, yanzu dai je ka shirya bari na duba daddy mu gaisa" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi waje, shi kuma Musharraf ya wuce zuwa nasa bedroom ɗin.
Aseef yana fita kai tsaye bedroom na daddy ya nufa, babu ko excuse ya faɗa cikin ɗakin, tsaye a gaban mirror ya isko daddy yana shafa mayukansa masu balain tsada da kuma kyau, kyakkywar farar towel ne ɗaure a kugunsa da alama wanka ya fito.
Mutuwar tsaye Aseef ya yi yana kallon zanen tattoo dake a bayan daddy, zanen Lion ne wato zaki ita ce daddy ya zana a bayansa ta buɗe baki da waƴan nan zabga zabgan hakwaran nata, daga gefen kafaɗarsa kuma zanen kunama ne.
Shi kuwa daddy jin an shigo mashi ɗaki ne yasa ya ɗago blue eyes ɗin nan nasa ta cikin mirror dan ya ga wanene, dama kuma ya san cewa Aseef ne, dan ba bu mai shigo mashi ɗaki da safen nan sai Aseef.
"My son what happened? Why are you looking at me like this?" Ya faɗa yana ƙoƙarin juyowa.
"Daddy I saw something like tattoo on your back". Ya faɗa da mamaki a face nasa. Jinjina mashi kai daddy ya yi alamar yah tabbas tattoo ne.
"Daddy tattoo? Do you know what tattoo means?". Juyawa daddy ya yi tare da cigaba da abin da yake yi yana faɗin "Do you know my name before?".
Girgiza mashi kai Aseef ya yi mamaki ya hana shi yin magana. "My name is dangerous Boss, i want you to know my story before, alokacin da nake da 20 to 35 year, mummyn ku ita ce first parson da ta fara sanya William ya risinar da kansa kasa, time da muke school yadda ka kalli Romeo haka nake, kowa tsorona yake ji a school, wannan tattoo da ka gani ba irin tattoo da kake tunani na shahrarrun ƴan iskan duniya bane, no wannan tattoo ne da yake nuna cewa mune manya a cikin school na mu a time ɗin, ni before ko wine bana sha, sanadiyar bakin cikin da mum ɗinku ta saka mani me yasa na fara shan wine dan na rage damuwa, a lokacin da muka yi tashe, muna kula da lafiyar mu sosai da sosai domin karantun lafiya kuke yi a time ɗin, duk soyayyar mum ɗin ku ya sanya na zama haka, lokacin dana fara ganinta a school ranar da ta fara zuwa a sabuwar student, faɗa ya fara haɗani da ita, bata san cewa mune manya a school ɗin ba, ta zo zata wuce ta jefar mani da ledar sweet a gabana, da nace ta ɗauke shine ta ki saboda tana ji da kai a lokacin ita ma, ni kuma zuciya ta ɗebeni na mareta, ai kuwa ita ma bata yi kasa a gwiwa ba ta ɗaukeni da marin da na kasa mantawa da shi har yau, dayawa daga cikin matan school namu suna haukar so na saboda kyan da nake da shi, kuma kowa yana tsorona amma sai ga mum ɗin ku ta mareni a ganan kowa da kowa, raina ya yi mugun ɓaci ba kaɗan ba, ban san time da na fara dukanta ba dan haushi, da kyar su HERRY suka ruƙe ni, daga nan ne fa muka saka kafar wando ɗaya da ita a school ɗin, kullun idan ta zo sai na takurawa rayuwarta, ga shi kuma kasa da mu take, lokacin muna kusa da shekarar kammala wa, ma'ana saura shekara ɗaya mu gama, na saka mata ido na dameta, duk abin da take yi sai na takura mata, daga takura ya zama soyayya har ya kai mu ga aure, abin da ya sa kaga ban cire tattoo ɗin nan ba saboda ina tuna lokacin samartakan mu, mu biyar ne a lokacin, amma yanzu uku sun mutu remain me and herry, sannan wannan kunamar da kaga na zana a kafaɗata ba ni na yi ba, mummynku ta zana mani da hannunta, ina matukar kaumarta fiye da tunaninka, shiyasa na kasa goge wannan tattoo ɗin dan ita ta yi mani kuma tana kaunar shi, shiyasa na barshi dan in rinƙa tunata da shi, mutuniyar kirki ce, daga baya ne ta canza kamar ba ita ba".
Ya kai karshen maganar yana hawaye, da sauri Aseef ya kariso wajensa tare da fara rartashinsa yana bashi hakuri, rungume juna suka yi.
Sun ɗan jima a haka kafin nan Aseef ya sake shi yana gaya mashi zai ta fi school, to ya amsa da shi suka yi sallama Aseef ya manna mashi kiss a goshi kafin shima ya mannawa Aseef ɗin a kumatu, Aseef yana matuƙar kaunar daddynsa while shima yana kaunar ƴaƴan nasa, Allah ne kawai yasan dalilin da yasa su basu wani son shi sai Aseef ɗin, shima Aseef dan yana sabon mutun ne Shiyasa, babu komai a ransa sai kaunar mutane.
Aseef na fita daddy ya zauna saman table chair yana hawaye, yau ya tuna da soyayyarsa ta baya, ya tuna irin diramar da suka kwasa da Mummynsu a school, tsumin soyayyarta ta taso mashi, ji yake yi kamar ya ganshi ga shi ga ita sun koma kamar lokacin da suke zuba soyayya a school nasu, mum ta haɗu over, daga baya kuma kome ya tuna sai ya goge hawayen nasa ya miƙe ya cigaba da abin da yake yi kamar ba shi ba.
Shi kuwa Aseef yana fita part nasa ya koma. A palo ya isko Musharraf yana tsaye ya shirya cikin kananan kaya, ya yi kyau over, sosai Aseef ya ya bawa kyan da ya yi sannan suka jera suka fita zuwa palon kasa.
"Uncle mu wuce ko mu tsaya mu yi breakfast?" Cewar Aseef. Musharraf na ƙoƙarin amsa mashi magana sai suka ji uncle Herry ta bayansu yana faɗin "Michael wai ya har yanzu TGA shiru ne?".
Juyowa Aseef ɗin ya yi yana kallonsa fuska ɗauke da murmushi ya ce "Uncle Herry uncle T yana nan dawo soon, wani aiki suka tafi" to uncle Herry ya amsa da shi.
Dawo da kallonsa kan Musharraf ya yi yana kara tambayar shi, shin su yi breakfast ne ko dai su wuce kawai, da yake Musharraf ya san halinsu sarai basu cin abinci a waje dan tsabar shegen kyankyani da suke da shi kamar me, basu yarda su ci abincin da wata hannu ta girka bayan sojojin gidan, suma sojojin dan saboda suna kallon duk yadda suke yi masu girkin ne Shiyasa, suna kallon komai a tsabtace suke yin sa, ba dan haka ba da ba zasu iya ci ba, Triplets gabaɗayansu ne masu wannan shegen kyankyani kamar me, harta James mai ɗan saukin kan, idan kana son ka ga ɓacin ransa to ka kawo datti a filin da yake, yanzun nan zai haɗa maka jini da majina a fuska, sun yi mugun tsanar abin kyama ko datti. Musharraf ya san ko sun fita Aseef ba zai taɓa yarda ya ci abinci a wani waje ba, sai dai ya kai Musharraf ɗin wajen cin abinci shi kuma ya zauna har sai sun dawo gida ya ci, yasan halinsa sarai, sanin hakan yasa ya ce a'a su hakura su yi breakfast a gida tukun nan su fita, to Aseef ya amsa da shi sannan suka nufi dining room shi kuma uncle Herry ya koma bedroom nasa.
Suna zuwa wajen waƴan nan jibga jibgan bodyguards ɗin suka fara sara masu kamar yadda sojojin gidan suke yi masu.
Shafa kumatun ɗaya daga cikin bodyguards ɗin Aseef ya yi yana faɗin "Wai ku bakwa gajiya da tsayuwa ne? Haba mana ku rinƙa samun huto, kowace rai tana son hutu fa my people's". Mamaki ne ya kama bodyguards ɗin nan, har wani kallon kallo suke yi wa junansu.
Zama Aseef ya yi yana faɗin "Bodyguards shidda kuje ku kwanta ku huta idan karfe 2 na rana ta yi sai ku zo ku karɓi ƴan uwanku shiddan nan suma su je su huta sai can dare ku haɗu gaba ɗaya ku kwanta ku huta. Abin nufi a nan Aseef ya raba masu aikin kenan, bawan Allah mai adalci yanzu kwata kwata baya son yaga wani ko wata suna wahala, Allah sarki musulci duniya ne wlh, babu abin da ya kai shi daɗi, kuduba kafin ya musulta shine fa yake cewa zai yankewa masu girki hannu da wuƙa, yanzu kuma ya musulta yau an wayi gari har hira da wasa da dariya yake yi da su, Allahu Akbar, Allah Alhamdulila da ya kasance muna a cikin adddinin musulci, zama musulmi babbar ni'ima ce wadda ba kowa yake samun wannan damar ta ni'imar ba.
Tsabar mamaki da farinciki bodyguard ɗin nan sun kasa magana, sai kallon juna kawai suke yi. Ganin haka yasa Aseef ɗin ya sake ce masu "Mamakin me kuke yi? Ni ɗin dai Michael nine, kuma nine na baku wannan hutun, duk kuma wanda ya zo saman table ya ce ina sauran, ku ce nine na basu hutu, wai ni kam shin mu nawane ma a gidan nan da bodyguards uku ba zasu isa su yi serving namu abinci ba? Kawai dai sai an wahalar da bayin Allah a rayuwar nan ta duniya, kai kaɗai sai ka ce sai ka tattare komai ya zama naka, to idan da kowa sai ya tattara komai ai da mu kam ma kwata kwata duniyar ma ba zamu zo ba, Allah mai iko, to daga yau ma na raba ku, bodyguards huɗu ne zasu yi serving na abincin safe, idan mun gama breakfast su tafi suje su kwanta su huta, sai kuma idan lokacin cin abincin rana ta yi, kafin mu zo saman table sai bodyguards huɗu waƴan da zasu yi serving abincin rana su kuma sai suzo su kara gyara table ɗin kafin mu zo, da daddare ma haka, kun ga ku sha biyun nan kowa da hurhuɗu zaku yi aiki".
Zube gwiwowinsu a kasa suka yi tsabar murna da farinciki har da hawaye suka yi, bayin Allah ashe suna gajiya da tsayuwar da suke yi na 24 hours ɗin nan, ashe suna shan wahala sosai.
Ganin sun zube a hasa suna hawayene yasa Aseef ya miƙe shima ya tsugunna a gabansu yana tambayarsu ko lafiya? Ko dai hutun ne basu so?".
Har wani ja baya suka yi ganin shima ya zube gwiwowinsa a ganansu, sun tsorata sosai, addu'a suke yi kada Lion ya ga Michael ya zube a gabansu ko wani daga cikin gidan ya ce sun yi wa Michael ɗin wani abin ne a kashe su a banza.
Da kyar Aseef ya shawo kansu suka yarda suka kuma gane cewa e lallai Aseef ɗin ne, kuma shi ne ya zama mai adalci haka, sun yi murna sosai, Aseef bawan Allah da kansa ya yi ta goge masu hawaye yana mai gaya masu addinin musulunci addinine wadda ya ƴanta ko wani ɗan adam, dan haka suma ƴantattune, suna da ƴanci, nan take biyu daga cikinsu suka ce ai sun san addinin musulunci sosai, suna ƴawan ganin musulmai a Media sun san musulmai suna da kirki sosai, addinin akwai adalci sosai dan haka su zasu musulta.
Ba karamin daɗi Aseef ya ji ba, a wajen ya basu kalmar shada tare da basu