Showing 177001 words to 180000 words out of 355604 words

Chapter 60 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2816

yana ɗaukarta kamar baby to amma me yasa zai ɗauki Rimsha bayan ba matarsa bace? Abin ya bata haushi kamar zata yi kuka ta wuce ta fita daga palon zuwa part nasu.

Shi kuwa bai ma lura da ita ba, saman sofa ya kwantar da Rimsha sai lokacin ta fara dawowa hayyacin ta, kokarin cire mata Hijabin jikinta ya yi domin ta samu iska sosai, amma ina ta fara dawowa hayyacin bata bari hakan ta faru ba, sai ta yi maza ta ruƙe hannunsa, ganin haka shima sai ya saki mata hijabin ya dubi Akila da ta yi sumar tsaye tana mamakin yau yaya Akil ne har mace ta faɗa mashi a jiki ba Umaisha ba kuma ba ita Akilar ba, amma har ya nuna bai damu ba, kuma bai wani ɗauki action a kan hakan ba, abin ya bata mamaki sosai, dan ta san halinsa sarai, shi kuma ba da wata manufa ya yi hakan ba, saboda ya ga bata a hayyacin tane shi yasan, da tana hayyacinta ba zata taɓa yarda ko hijabinta ya taɓa ba bare kuma har jikinta, wannan dalilin yasa bai damu ba ya ɗauko ta.

"Heartbeat ɗauko mani ruwa". To Akila ta ce sannan ta wuce cikin Kitchen tana tunanin ya wannan al'amari zai ka san ce, ga dai Umaisha a can ta tafi da alama kuma fushi ta yi, me yake shirin faruwa ne, ko dai yaya Akil ya kamu da son Rimsha ne? Allah yasa ba hakan bane domin ni bana son zumuncin da kuma ƙawancen mu ya ɓaci, haka ta rinƙa tunane-tunanenta har ta ɗauko mashi ruwan ta kawo mashi.

Karɓa ya yi ya buɗe bakin robar ruwan, ba tare da ɓata lokaci ba ya karanta mata ayatul kursiyu kafa bakwai ya tofa acikin ruwan ya bata ta sha, ba musu ta karɓa ta sha, Allah da ikonsa kuma, tana sha sai ta zama daidai, ban da sauke nannauyar ajiyar zuciya ba wani abin da take yi.

After some minutes da ba su fi goma ba, cikin natsuwa Akil ya ce "Rimsha kina lafiya?" Ya yi maganar yana tsareta da ido, lokacin ta ɗago da idanuwanta a kansu, yar murmushi ta sakar masu kafin ta ce "Kayi hakuri yaya Akil" "Hakurin me kuma Rimsha?". Shiru ta yi kamar mai tunani, can kuma sai ta ce "Babu komai bari na yi sallar mangariba ba" To ya amsa mata, da shi sannan ya miƙe ya nufi waje, yana faɗa musu akan yana zuwa, to suka amsa da shi, a tare suka wuce ita da Akila zuwa cikin ɗaki, shi kuma Akil part nasu ya koma.

Bayan sunyi sallar mangariba ne za su miƙe sai suka ji ana kiran sallar isha, hakan yasa suka gabatar da sallar isha ɗin ma kafin su fita zuwa Kitchen, Rimsha tana biyewa Akila ce kawai, amma ita kaɗai tasan me acikin zuciyarta, tunani kala-kala take yi, tana son sake ganinsa dan ta tabbatar da shi ɗin ne, duk da cewa tasan ko a cikin barci aka tasheta ta ganshi to ba makawa zata gane shi ɗin ne, amma tana son sake ganin shi, tabbas ta san shine, ba makawa, domin irin sanin da ta yi wa face nasa a zane da kuma irin kaunar da take yi mashi, ya wuci tunanin mai tunani, sannan abin mamaki yadda take zana shi kullum haka ya bayyana mata a yau, duk da cewa a mafarkinta ta fara ganin ainahin face nasa, hakan yasa ta kware a zanen.

Tana aiki girkin nan tana tunane-tunanenta, wayar Akila dake a hannunta ne ya fara kara, dubawa da zata yi sai taga Yaya Imran, cikin sauri ta ɗauki wayar tare da karawa a kunnanta tana faɗin "Hello yaya Imran" daga ɗayar ɓangaren Imran ya ce "Heartbeat ki ba wa Rimsha wayar". To ta amsa mashi da shi tare da miƙawa Rimsha wayar.

Karɓa ta yi ita ma ta kara a kunnanta, "Hello yaya Imran" daga ɗayar ɓangaren ya ce "First lady dan Allah ki girka abinci mafi daɗi wata kila Saif zai ci, idan kin gama ki kai mashi ɗaki, ya yi azumi amma yake cin komai, saboda bai saba da kasar mu ba, ni ban ma san ya zan yi ba, narasa me zan ba shi, yanzu dai bari muga ko zai iya cin abincin kasar mu, ki yi tsantsarerren girki kin ji ko? Yanzu za mu dawo gida". To ta amsa mashi da shi, cike da zumuɗi ta fara ƙoƙarin haɗa mashi abinci mafi daɗi, sai murna take yi ta wani ɓangaren kuma har hawaye ta yi mashi, ya bata tausayi, bai saba cin irin abubuwan mu ba, zai sha bakar wuya sosai, ga shi ko ruwar Faro bata yi mashi ba, kenan sai dai ya yi ta shan maltina? Ko yaya abin zai kasance? To mu je dai zuwa.

A ɓangaren su kuwa, lokacin da ɓarawon ya kwace wayar yana gudu, zuba mashi ido Lion ya yi yana mamakin wai har shi za'a kwace wa waya a hannunsa. Ni kuwa nace mamaki kake yi ne? Nigeria fa kake, to garama ka yi hankali idan ba haka ba, kai ma anemeka a rasa🤣 waya ga an sace The General of The Army Usa ɗungurunrum a Nigeria abin zai bada sugar🤣

Zura hannu kawai ya yi a aijihun jallabiyar jikinsa ya cigaba da tafiya yana kallon yadda gari yake, Imran sai wani kame jikinsa yake yi saboda sanyi shi kuma Lion zafi yake ji yana buƙatar sanyi, tun da yake bai taɓa fita cikin gari ya sake haka ba, yau ga shi ya fita ba sojoji ba komai, shi kaɗai ɗin shi, daga nan sai ya ji rayuwa ba wata kuƙami ma akwai matikar daɗi, yanzu a nan ba wanda ya san fuskarsa, ba yan jarida masu ɗaukarsa hoto, jet nasa ma ba da ita ya zo ba, ya kyaleta a Spain da jirgin kasuwa ya shigo Nigeria, hakan ma ya kara sanya tafiyar ta yi sirri sosai, abin da ya sa kuma ya fita da jet ɗin daga Washington DC domin kowa ya yi zaton Spain ya tafi, saboda yasan da cewa tabbas komai tafiyar sirrin da zai yi akwai wayan da suka sa mashi ido sosai, ciki harda irin kungiyar su James, dan haka suna ankare da motsin shi, yasan za su bibiyi a ina jet nasa ta nufa, a ina ta tsaya, shiyasa ya yi masu basaja kamar hakan.

"Saif mu koma gida dan Allah". Cewar Imran domin sanyi yake ji sosai. Ba musu Lion ya juya suka nufi hanyar komawa, domin sun ɗan yi nisa da tafiyar ya fara riyo kamshin abubuwan da ake soyawa a bakin hanya, irin su kosai da doya su kifi, shi kuma baya son warinsu, hakan yasa ya juya dan su koma.

Suna juyawa sai ga ɓarawon wayar ya dawo a guje, yana zuwa ya zube gwiwowinsa a kasa a gabansu, yana kuka yana basu hakuri, a nan ne Imran ya koma gefe ya kira Rimsha a waya, shi kuma Lion hannu yasa ya karɓi wayarsa, dan dama yasan ba wanda zai iya riƙe wayar sai shi, dan ba waya ce kamar ko wace waya ba, sannan kuma idan suka kunna wutar screen ɗin to ya zama dole su razana su dawo mashi da wayarsa shiyasa bai wani damu ba, hankalinsa a kwance lokacin da aka kwace wayar.

Abin da ya faru yasa suka dawo da wayar shine, ɓarawon da ya kwace wayar ogansa ya kai mawa, yana faɗa mashi sun yi babban kamu, ogan yana karɓar wayar tun bai kunna wutar screen nata ba sai da ya ranaza, bai san lokacin da ya furta "Wannan wayar bata irin ƴan Nigeria ba ce, ban taɓa ganin irinta ba". Bai gama rufe baki ba, Michael ya sake kiran wayar domin da suna waya ɓarawon ya kwace wayar sai ya daina jin Lion hakan yasa ya katse kiran ya sake kira.

Suna riƙe da wayar kirar Michael ta shigo nan fa suka ga abin mamaki, domin wayar ba ringin take yi kamar ko wace waya ba, no gaya mashi ta ke yi ga wanda ya kira ga kuma number da ya kira sannan ga daga location da aka kira, shine a matsayin ringintone na wayar, kasa ɗaukar kiran suka yi, domin ma ba za su iya ba, ita ba ɗaukarta ake yi kamar sauran wayoyi ba, a'a idan ba Lion ba ba mai iya picking nata, sai kuma idan akayi Sa'a aka samu masu danne danne suyi ta latse jikinta har su samu su yi picking, haka suka riƙeta har kiran Michael ta katse.

Bayan ta katse ne, sai suka samu wayar ta kawo wutar screen ɗin da kanta, wani mahaukacin razana ogan nasu ya yi lokacin da ya halli abin da yake a gaban screen ɗin wayar, Hoton Lion ne a fuskar wayar, wadda kowa ya san shi da shi, wato da face mask, shi da James da Michael ne, shi kaɗai ya sanya face mask a cikinsu, suna tsaye a saman balcony ɗakinsa, sun rungume juna, sun yi kyau sosai, da sosai. Sun shagala da kallon hoton kiran Michael ya sake shigowa a karo na biyu kuma Vedio call ne na yanzun, rashin sa'ar su yasa ba su san ina suka danna ba, dan ya dakumi wayar da hannunsa, suna picking sai ganin Michael suka yi yana zaune saman dining table na palon kasa yana cin abinci, domin shima ya yi azumin litinin, ihu ogan nasu ya kurma tare da bawa wanda ya sato wayar a kan ya mai dawa mai waya wayarsa.

Abin da ya faru suka dawo da wayar kenan.

Cikin harshen turanci ya ce "Me yasa kake kwacewa mutane abu?" Shiru ɓarawon ya yi domin baya jin turanci ko kaɗan, sai da Imran ya gama magana da Rimsha ya dawo wajan ne ya shiga yi wa ɓarawon fassara yana mayarwa Lion da amsa, daga ƙarshe dai Lion ya ce a mai da shi makaranta a bashi sana'a, domin alamu sun nuna jahilci yasa yake sata, bai samu ilimiba kuma babu sana'ar yi, shiya jefa shi shaye-shaye da kuma sata, da haka suka yi sallama Imran zai je har gidan su gobe ya duba shi, dan ya karɓi address ɗin sa.

Kamar yadda suka fito gida a tare haka suka koma, kai tsaye bedroom na Imran suka wuce. Suna shiga ya nufi toilet dan yin wanka, komai na cikin ɗakin Imran daga waje aka kawo su, hasalima daga kasar su wato Usa aka kawo su, amma Lion ya ce ba su yi mashi ba, shi gidan nema gaba ɗaya ta yi mashi kama da keji kaji, dan haka shi ba zai zauna ba, dole adaran nan a sama mashi katafaren gida wadda aka gama gina wa aka zuba komai na kasarau, ya saya ya koma can, cike da zolaya Imran ya ce "Idan ka sayi wannan gida ka zama ɗan Nigeria kenan?". Karisa shiga cikin Toilet ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, wucewa saman bed Imran ya yi ya kwanta yana mamakin yau Lion ne a Nigeria abin da bai taɓa zato ba, a Nigeria ma a gidan su.

A daddafe ya yi wanka ya fito, gaba ɗaya tsadaddun Towels dake a cikin toilet ɗin wai ba su yi mashi ba, da nashi da su Tga suka sanya mashi a cikin trolley sa ya yi amfani, ya saba da shiga dressing room ya shirya, amma yau daga cikin trolley ya ciro kaya, hakan yasa ya sake tsanar gidan su Imran, ba iya gidan kawai ba, gaba ɗaya kasar bata yi mashi ba, ransa ya ɗan ɓaci, haka ya shirya cikin wandon jeans fara tas da riga polo t-shirt blue, ya feshe jikinsa da perfume nasa mai bala'in kamshi bayan ya shafa mayukansa kenan, daga nan ya gyara gashinsa. Bakin gado ya koma ya zauna kusa da Imran yana ganin gadon ma wani local, ko gadon Bradyn sa ta fi wannan kyau.

Ni kuwa nace yau dai ba yadda zaka yi Nigeria ka zo ato, dole ayi hakuri da mu.

Shiru suka zauna domin Imran ya yi degree a sanin halin Lion, yasan baya son magana, dan haka suke zama shiru kamar kurame.

After 1 hour.

Suna zaune a in da suke ba su motsa ba, kuma ba wanda ya ce da ɗan uwansa uppan, kamar gumaka, zama da Lion sai an kai zuciya nesa, karfi da ya ji sai ya mai da ka kurma

Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo cikin ɗakin, still hijabi ne a kijinta, hannunta na ɗauke da wani kyakkyawar katuwar tray mai ɗauke da kyawawan kololin abinci, da su plates and spoons da sauransu. Wani irin lumshe idanuwanta ta yi lokacin da ta shaki Kamshin perfume nasa, ji take kamar bata a duniya, ta lula sama jannati, zuba mata ido Imran ya yi, sai da ta shaki kamshinsa son ranta sannan ta buɗe idanuwanta karaf a kan fuskar Imran, wani irin kunya ta ji ya kamata, shi kuwa bai damu ba, dan yasan daɗin kamshin perfume ɗin Lion abin so ne, kowa zai so ya yi ta shaƙarta kada ya daina. Da hannu ya yi mata nuni da shi akan ta kai mashi gabansa, jikinta sai kerma yake yi ta nufe shi, banda hasbunallahu wanimal wakil babu abin da take nanatawa a cikin zuciyarta.

Gaban sa ta zo ta tsgunna cikin natsuwa ta buɗe kular abincin ta fara zuba mashi, yau ga Rimsha ga Lion waje guda, yana duke da kansa kamar yadda yake tun farko, da alama ma bai san da mutun a wajen ba.

Tana tsaka da zuba mashi abin ne, a zafafe ya yi wani irin ball da gaba ɗaya tray ɗin abinci, ciki kuma ya haɗa har da hannunta, domin hannun nata yana kan tray ɗin alokacin. Tarwatse abincin ya yi har saman bed, kular miya kuma da jikin bangon wajen mirror ya bugu miyar ta watse, kusan rabi na miyar ya watsun mata a jikin milk color hijabinta, ga shi kuma miyar steew ce, su cabbage and cucumber da ta yayyaka gaba ɗaya sun watse sama suka warwasu a cikin ɗakin, a takaice dai ball da tray ɗin abincin da ya yi ta watsa komai. Abin da kuma yasa ya yi ball da abincin a cewar sa ta kawo mashi wari gaban fuskarsa ta canza mashi iskar da yake shaƙa, dama kuma da kyar yake shakar wannan iskar ba dan yana so ba, tazo ta wani kawo mashi warin steew a gaba.

Tsabar razana Rimsha bata san lokacin da ta miƙe jikinta na kerma ba, a guje ta juya zata fice sai dai kuma ina tsorata ya yi mata yawa, numfashin ya rigata fita daga jikinta, saboda bala'in razana yasa ta zube kasa a wajen, shi kuma wayarsa da laptop nasa ya ɗauka ya fice daga cikin ɗakin, Imran ya rasa wajen waye zai je ɗaya daga cikin su, ga Rimsha a sume ga Lion ya yi waje da alama kuma ransa a matukar ɓace.

Ganin tunani ba nashi bane yasa ya ɗauki Rimsha ya ɗaurata saman bed nasa ya fita waje dan ya bi bayan Lion. Sai dai ko da ya fito babu Lion babu alamarsa, hakan yasa ya dawo cikin gida da sauri ya ɗauki wayarsa, member Lion ya fara kira dan ya ji a ina yake ya biyo shi, amma ina har 3 miss call ya yi mashi Lion bai ɗauka ba, daga karshe dai ya hakura a ajiye wayar ya kira su Akila domin su gyara mashi ɗakinsa, ita kuma Rimsha ya yayyafa mata ruwa. Baiwar Allah nan a matuƙar razane ta farfaɗo, gaba ɗaya ta fice a hayyacinta, numfashinta sai fita yake da sauri-sauri, idan baku mance ba, tun ainahi tana mutuwar son shi kuma tana bala'in tsoron shi, hakan yasa zuciyarta ta kasa jurar ɗaukar ganin fuskarsa, haka zalika ta kasa iya cire tunanin lokacin da ya zo zai yi mata kiss a mafarki, hakan kuma ba karamin birkita mata kwakwalwa yake yi ba, Allah sarki.

Wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta saki, sosai Imran ya shiga rarrashinta yana bata hakuri tare da gaya mata kada ta damu shi Lion haka halinsa yake, Allah ya kiyayye ma yanzu bala'in zafin zuciyar nan tasa ta ɗan ragu saboda hasken musulunci da kuma imani da ta ratsa shi, amma ba dan haka ba, da Rimsha bata isa ta zo in da yake ba, yanzu ko ba komai yana ɗaukan mutane da daraja kaɗan, haka zalika yanzu ya san Allah ke yin komai, kuma laifin wani baya shafan wani.

Imran bawan Allah bai san da tsohon soyayyar da Rimsha ke yi wa Lion ba, ya ɗauka iya ball da ya yi da tray ɗin abincine ya sanya ta suma, a ɗazun kuma da ta suma lokacin da ta kawo mashi ruwa, ya tauka ta razana da ganin face nasa ne, wadda hakan ba wani bakon abu bane, domin dayawa daga cikin mata matsorata suna suma idan suka yi ido huɗu da shi, to shi Imran ya zaci ita Rimsha tana daga cikin su ne, shiyasa bai wani damu ba.

Sosai ya rinƙa rarrashinta, da kyar ya samu ta dawo daidai, da kansa ya tasata a gaba suka nufi Palo, a nan ta isko su Akila sun yi wanka sun dawo suna jiran ta zo su ci abinci, ai kuwa abincin da bata ci ba kenan baiwar Allah, daren ranar dai da yunwa ta kwana, haka zalika daren ranar bata yi barci ba sai wajen karfe 2 na dare sannan ne barci ya ɗauke ta, sai ajiyar zuciya take sauƙewa cikin barci.

Babban abin bakincikin kuma shine, tana fara barci ta fara mafarkin shi. Wai tana zaune a palo ita kaɗai, ta yi shiru ga kamshi da sanyin Ac na tashi, su Imran basu nan sun fita, ita ka ɗai ce a cikin palon, jikinta na sanye da wando da riga sun kamata sosai, tana rungume da pillow ta shagala da kallon Tv dake a gabanta, bata ankaraba sai ta ji hannun mutun a saman wuyarta, bata wani razana ba domin kamshin perfume nasa ya isar mata da sakon ko wanene, hannu tasa ta fara shafo nasa hannun, kwanto da kansa ya yi a saman kafaɗarta yana sauƙe mata numfashinsa a hankali hankali, sai faman lumshe idanu suke yi duk kan su biyu.

Sun ɗan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login