Showing 141001 words to 144000 words out of 355604 words
Yana ragewa tun bai ajiye remote ɗin ba Ac ta sake kure gudun da kanta, a sukawane ya zaro idanuwansa waje yana kallon samar.
Da karfi-karfi Ac ke futa har kamar zata tarwatsa kanta, banda sunan Allah ba bu abin da yake iya faɗi a cikin zuciyarsa, ya tsorata sosai, wutar ɗakin ne ya fara rawa ya kawo ya ɗauke kamar spark na wutar nepa, bai ankaraba ya ga samar ɗakin nasa yana ƙoƙarin faɗo mashi a kansa, runtse idanuwansa ya yi yana ihu tare da furta sunan Allah a cikin ihun nasa, ya aza hannun bisa kayinsa yana jiran faɗowar ɗakin kawai a kansa.
Tsawon minti ɗaya ya ji shiru, ba wani abin da ya faɗo mashi, cikin sanɗa da dabara ya yi kokarin buɗe idanuwansa. Ai kuwa yana buɗe wa ya yi arba da wata iriyar halitta mai bala'in munin gaske, yar karama kamar mage, ga idanunta kamar na mutun, sake runtse idanunsa ya yi ya kurma wata razananiyar ihu da karfi!! Wadda da ka jita kasan ba ta lafiya bace.
Yana tsaka da ihun sai ya ji an taɓa shi, a zabure ya buɗe idanuwansa, a zuciyarsa yana ayyana yanzu kuma dame zai yi arba.
Tga ne tsaye a kansa, ga su John a gefe. Wata uwar tsawa Tga ya daka mashi wadda ta sanya shi haɗiyar wata bakar wahalalliyar yawu mai wuyar wuce maƙogoro, "Why are you shouting for us here?". Tsuru-tsuru ya yi da idanu ya kasa ko motsi bare kuma magana.
Ganin ya ki magana ya sa ran Tga ya kara hasala sosai, wato Musharraf ya raina shi, cikin fushi ya ɗaga hannu zai mare shi, da sauri Michael da ya shigo yanzu ya yi maza ya riƙe hannun nasa yana faɗin "Sorry uncle T, uncle ɗin James whapped kake ihu haka?".
Bin ɗakin da kallo Musharraf ya yi, komai ya koma yadda yake, wannan halittar ma ta ɓace, ga kuma Ac ya koma normal gudun da yake yi, cikin sauri ya kai kallonsa saman ɗakin dan ya ga shin shima saman ya komane ko dai ya faɗo, gaba ɗayan su da suke ɗakin suma ɗaga ido sama suka yi dan suga me yake kallon.
Sakin hannun Tga Michael ya yi, ya koma kusa da uncle ɗin James, ya zauna yana faɗin "Uncle lafiya me yake faruwa ne?" Kasa magana Musharraf ya yi, dan bai san me zai ce musu ya gani ba, wannan wace iriyar musifa ce ya faɗa a zuciyarsa.
Wucewa Tga ya yi rai a matukar ɓace ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "Zan turo sojoji su ɗauki mutumin nan zuwa gidan mahaukata". A zabure Michael ya miƙe tsaye,
"Uncle T uncle ɗin James ba haukaci bane, dan haka ba bu wanda zai fita da shi daga gidan nan, ai ni a gani nama ya fi ku hankali.....". Kai daga jin yadda Michael ya yi maganar kasan a matukar tsorace yake, sai wani haɗe words yake yi.
A sukawane Tga ya juyo jin yadda Michael ɗin ke ta faman haɗe masa words ɗin kamar ba lafiya ba "Michael are you okey kuwa?" Gyaɗa musu kai ya yi alamar yana lafiya, shi ma John kallon tuhuma yake bin Michael ɗin da shi, domin sun ga canji sosai a tattare da shi, sannan yanzu baya shiga cikinsu suyi hira, baya zama a palo, kuma ga yawan fita da yake yi, saɓanin da a baya da baya fita, daga school sai white house, kuma babban abin da ya kara basu mamaki kuma ya ɗaure musu kai shine, na farko da ka taɓa Musharraf gara shi ka yi masa dukan tsiya, na biyu kuma jiya da kansa ya samu Lion da maganar zai koma school, abu na uku idan yana magana kamar pastor su, a cewar su, dan pastor kawai suke yi wa ganin yana magana kamar malami, to yanzu haka Michael yake yi musu magana, cike da ilimi, babu shirme kuma babu shagwaɓa sosai, duk da cewa shagwaɓar ta bishi, amma dai ya ragu sosai, yanzu idan kaga yana yin shagwaɓar ma sai idan yana bukatar wani abin daga wajen su, shine sai ya yi ta musu magana cikin shagwaɓa dan su bashi, sannan yanzu ga bala'i kaunar yan uwansa da yake yi, idan sun yi abin da ba daidai ba sai ya zauna yana ce musu hakan da suka yi babu kyau su tuba, abaya suna ɗauka cewa karatun pastor ne ya fara shiga kanshi, sai daga jiya zuwa yau sai suka fahimci ilimin Michael ya wuci na pastor, hakan yasa suka fara zargin shi, ga shi kuma idan sun tambaye shi waye ya koya mashi hakan, sai ya ce musu kawai a bakinsa ya ji ta zo masa, daga sama take zuwa.
(Dama ilimi na zuwa daga sama ne? Gaskiya Michael ka iya rainin hankali)
Amma fa duk wannan abin da Michael yake yi, Musharraf ya yi nasarar rufe bakinsa ne ta hanyar addu'a da kyakkyawar niya, hakan yasa Allah ya taimake shi ya rufe mashi bakin Michael ɗin, baya iya gayawa su Tga ga mai koya mashi abubuwa, a yan kwanaki biyun nan ya iya abubuwa sosai dan gane da addinin musulunci, ga ƙwaƙwalwar tasa sai kara buɗuwa take yi, da angaya mashi abu zai haddace, hakan ma yasa ya ce zai koma school ya ci-gaba da karatu.
"Michael you are not okey!!" Tga ya faɗa tare da dawowa cikin ɗakin, "Uncle T like how am not okey? I didn't understand" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna.
Zuba musu ido Tga ya yi shi da Musharraf ɗin, yana yi musu kallon tuhuma tare da rashin yarda da su. "Where are you coming from?" Ya yi tambayar yana kallon Musharraf.
Cikin sauri Michael ya ce "he is from england" ɗaure fuska sosai Tga ya yi alamar babu wasa a tattare da shi, cike da izza da bada umarni na uncle da yaronsa ya fara magana. "Michael i don't want to hear your mouth again, hey man i said where are you coming from?". "I'm from England". Musharraf ya ba shi amsa daidai da abin da Michael ɗin ya faɗa, sai dai ya yi maganar a cikin wani irin yana yi na matsananciyar tsoro da fargaba, gabansa sai faɗuwa yake yi, dan ya san basu da imani da tausayi ko kaɗan, idan suka san shi musulmi ne ba karamin azabtar da rayuwarsa za su yi ba.
Furzar da iska mai zafi Tga ya yi daga bakinsa kafin ya ce "impossible!!" Satar kallon Michael Musharraf ɗin ya yi, daidai lokacin da ya miƙe yana faɗin "Uncle T please mana ka kyale shi ka ji? Shi ba mugu bane, kuma ba shida komai a ziciyarsa sai alkhari". Wucewa Tga ya yi ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake yin magana ba, hakan da ya yi kuma ba karamin jefasu cikin ruɗani ya yi ba, musamman shi Michael dan yasan uncle T ɗin nasa da bakar zuciya kamar me, yasan ba zai yi wu ya kyale Musharraf haka kawai ba, wannan shirun da ya yi dole akwai abin da ya ayyana a ransa.
Wucewa shima John ya yi ya bi bayan Tga, shi kuma Michael zama ya yi gefen Musharraf yana bashi hakuri, akan kada ya damu, haka yan uwansa suke, basu son baƙo ko kaɗan, amma kada ya damu ya kyalesu suyi su gama, ba komai Musharraf ya ce masa, shi ba ma su Tga ne a gaban sa ba, babban abin da yake damunsa shin wanene ke razanar da shi? Wanene zai iya kasancewa matsafi a cikin family William jacop? Domin wannan abin da suke yi tsafice, to waye ne zai yi hakan? Me yasa suka takurawa Michael shi kaɗai? Ko dan sauran basa magana ne? Me yasa tun ranar da ya musuluntar da Michael abubuwa suke ta faruwa da shi marasa kyau? Sannan meyasa kullun mace ce ke aiwatar da hakan? Hakan na nufin zancen James gaskiya ne, mum ɗin su tana da alaƙa da magicians? Ko kuma ita ke yin tsafin da kanta? To me yasa take tsafin akan ƴaƴanta na cikinta? Sannan kuma tana ikirarin tana bala'in kaunar su? Ko dai a nata haukan hakan yana nufin tana basu kariya ne?.
Wayan nan tunanin su suka cikawa Musharraf ƙwaƙwalwar kansa, wadda kuma ko kusa ko alama bashi da amsoshin su.
Idan muka koma ɓangaren Lion kuwa.
💖Bayan wasu ƴan awanni.💖
Ruwan sama ne ke zuba kamar da bakin kwarya, ga shi ruwan zuba yake yi babu iska ba tsawa, kawai shaaaa yake zuba.
Tsaye yake a balcony bedroom nasa, yana kallon yadda ruwan saman nan ke zuba Kamar da bakin kwarya, kasan cewar wutar dake a wajen blue light ne, ga kuma wajen ya yi duhun hadari, da kuma duhun dare, sai abin ya kara kyau da kawatuwa, hasken wutar yadda take haska shi abin ba'a magana, ta saje da kwayar idanuwansa da suka kara haske a yanzu saboda dare.
Sanye yake da bathrobe fara kal a jikinsa, rigar bata karisa isa mashi gwiwarsa ba, ya ɗaure dark black curly hair san nan a bayan wuyarsa, ya bar na gaban goshin, yau fuskarsa har wani kyalli take yi, ya kara kyau sosai, da alama yau yana cikin farinciki, daya ke shi baka gane farincikin da bakin cikin shi, saboda kullun fuska a ɗaure, hakan yasa ba wanda ya iya fahimtar yana cikin farincikin, fari kuma kyakkyawar hannunsa riƙe take da wani kyakkyawar cup mai ɗauke da hot coffe sai tiriri yake yi. Bai cika shan coffee sosai ba, a cewar Triplets nasa wato James da Michael idan kaga Lion na shan coffee to yana cikin farinciki kenan, shi daga abincin da yake ci suke iya gane cewa yana cikin farinciki ko bakin ciki, haka zalika daga abin cin da yake ci suke iya gane bashi da lafiya ko yana da lafiya, wani irin murɗaɗen mutun ne wadda duk duniya ba wanda yake iya gane gaban sa bare bayan sa, ba zaka taɓa gane ina ya dosa ba, kullun a siffa ɗaya yake, komai abin farincikin da ya same shi, fuskar nan tamkar hadari take ako da yaushe.
A hankali yake kai cup ɗin sai tin ɗan bakinsa yana kurɓar coffee ɗin, kai daga ganin yadda yake yau kasan yana cikin yanayi na musamman.
(Amma me kuke tunanin ya sanya shi shiga cikin yanayin nan? Bayan kuma James baya nan? To ko dai ya yi nasarar gano ainahin in da aka kai James ɗin ne? Kun san dai kwana biyu da suka wuce ya ce ya gano ma'anar A.E.A ko? Sannan ya ce James yana ɗaya daga cikin A.E.A to ko dai mun samu damar sanin asalin takamaimai location ɗin ne? Muje dai zuwa?)
Tun da Tga ya shigo cikin ɗakin ya tsaya daga ɗan nesa ya zuba mashi ido yana kallon yadda yake kallon zubar ruwan saman nan, yasan ba haka kawai ba akwai dai wata a kasa, sai dai matsalar ko ya tambaya ba zai samu amsa ba.
Ya jima tsaye a wajen har ya ga ji, da alama shi kuma Lion zai iya kara tsayuwar awa biyar a wajen ma bai gaji ba, ganin haka ya sa ya kariso wajen yana faɗin "Well-done sir". Kamar ba mutun a wajen, ko motsi bai yi ba bare ka yi tunanin ya ji shigowar Tga ɗin, haka zalika bai amsa sannun ba.
Gefen sa Tga ya tsaya yana faɗin "Lion gaskiya ina zargin wannan mutumi da James ya kawo gidan nan, so ina son yin bincike akan shi ka bani dama!!".
Cikin natsuwa ya sake kai cup ɗin saitin ɗan bakinsa ya kurɓi coffee ɗin, yau jin duniyar yake yi tana mashi mugun daɗi, sai dai ko alamar hakan babu akan fuskar tasa.
"Lion sai magana ta biyu da ta kawo ni, akan yarancan da su Tyrone suka kama, masu yi wa kananan yara fyaɗe nan, wani hukunci zan yi musu?".
Good 30mins ya ɗauka har lokacin bai karisa shan coffee ɗin ba, kuma bai yi magana ba, daya sha iya yadda ya ishe shi, sai ya riƙe cup ɗin kawai ya dakata da sha yana kallon ruwan sama, Tga kuma sai satar kallon shi yake yi, dan yau ya kara kyau sosai, har wani kyalli soft skin nasa take yi.
"Wayan da su Tyrone suka kama ka musu kachiya part two is okey, shi kuma mutunmin zan yi bincike akan shi, but not now, saboda saura kwana uku in yi tafiya so i don't have enough time da zan yi bincike akan shi, sai na dawo kawai" ya yi maganar gently kuma in a cool voice nasa, idan kaga yadda yake maganar ba zaka taɓa cewa yana motsa laɓɓansa ba, saboda cike da class yake maganar, a hankali yake fitar da ko wace words ta yadda lips nasa basu wani motsawa sosai. Ba irin Maganar su Tga ɗin yake yi ba, cike da salo na jan hankali mai kallonsa da class maganar take fita.
(Lion Masha Allah komai ya haɗa🥰)
Tga ya kasa tafiya duk da cewa an bashi amsar abin da ya zo nema, ya tsaya sai satar kallon Lion ɗin yake yi, saboda kyan da ya yi mashi, shi kuma Lion sai kallon ruwa yake yi a cikin zuciyarsa yana tunanin ya kamata kafin ya yi tafiyar nan ya binciki Michael, mum nasu, da kuma John and Jay, domin idan ya yi tafiyar nan zai ɗan ɗauki lokacin kaɗan bai dawo ba, zai iya kai 1 week ko 2, so gara ya duba wani hali suke ciki kafin ya tafi.
Sun jima tsaye a haka, da Tga ya gaji sai ya yi mashi sallama ya wuce dan ba zai iya jure tsayuwar nan ba, domin training ɗin General ba ɗaya bane da The General of The Army, ko da gwajima ba haɗi, basu haɗa hanya ba, abin da Lion zai yi ko rabin shi ba za su iya ba.
Sai da ruwan samar nan ta ɗauke sannan ya ajiye cup dake hannunsa saman glass table dake a wajen ya dawo cikin ɗakinsa.
A gaban Mirror ya tsaya yana kallon fusataccen fuskarsa, a hankali ya kai hannunsa yana shafa lallausan dark black curly gashin dake kwance a gefen lallausan kumatunsa, shi kansa fuskarsa burge shi take yi, kyau fuskarsa take yi mashi. Slowly ya dawo da kallonsa saman kyakkyawar wuyarsa, kallon kashin da ya bayyana masa a wuyar tasa yake yi, wadda take nuna alamar ya rame, rashin James ya sanya shi rama.
Ya jima a haka, can kuma ko me ya tuna a zafafe ya juya zuwa cikin dressing nasa. Jimkaɗan ya fito hannunsa ɗauke da wannan akwatin na mum ɗin su, a gefen bed nasa ya zauna tare da buɗe wa, wannan sarkar ya fitar kallonsu yake yi, haka kawai ya ji yana son saka sarkar a wuyarsa. Ɗaya daga cikin sarkar tana da design of heart a jikinta, kuma heart ɗin tana da ɗan girma kaɗan, saura biyun kuma akwai design of heart ɗin sai dai su rabi rabin heart ɗin ne ba full heart kamar ta farkon ba, zubawa sarkar idanu ya yi na ɗan lokacin. Can kuma sai ya ɗauki kayin sarkar guda biyu masu rabi rabin heart ɗin ya yi kokarin haɗesu su fita full heart, amma sai suka ki zama alamar ba nasu bane, ɗaya ma ya fi ɗaya girma, ajiye su ya yi ya miƙe zuwa dressing room ɗin.
Jim kaɗan ya fito riƙe da wani hoto, a in da ya tashi a nan ya koma ya zauna, zubawa hoton ido ya yi yana kallon sarkar dake wuyar Josephine ɗin lokacin bata kai haka shekaruba. Tabbas wannan sarka mai full heart ɗin shine a wuyarta, shiru ya yi yana tunanin ina ragowar gefe da gefen heart ɗin can kuma suke. Lokacin guda wani tunani ya faɗo mashi a zuciyarsa, a nutse ya ajiye hoton ya ɗauko wannan sarka na wuyar Josephine wadda ta sanya musu cikin akwatin yanzu, cikin hikima da dabara ya raba heart ɗin biyu, da yake kana iya raba su, shiyasa sauran suke rabi rabi, abin da yasa kuma bai taɓa damuwa ya nemi ina rabin su yake ba kenan, dan yana tunanin wata ƙila a hargitsi ne suka rabe suka faɗi, shiyasa bai nema ba, amma yana son nemansu domin ya haɗesu su yi full heart ya bawa su Michael su sanya a wuyarsu, sai dai bai sami lokacin yin hakan ba.
Bayan ya rabe heart ɗin sai ya yi kokarin gwadawa ko zai iya rufe ɗaya daga cikin masu rabi rabin nan, amma ina ko wanne da nashi, ba mai rufe na ɗan uwa, hakan yasa ya mai da jikin wanda ya ciro kawai, sai ya ɗauki babban cikin ya ɗaura a wuyarsa, da yake su basu damuba maza suna saka sarka sosai, su kuma biyun sai ya ɗauke su ya mai da guda ɗaya cikin akwai tin, ɗayar kuma ya ajiye saman bedside drawer da niyar idan Michael ya zo ya bashi ya sanya a wuyarsa, duk da basu son mahaifiyar tasu, suna kokarin ganin basu mance da ita ba, kuma yanzu shi Lion ya fara jin wani abu a zuciyarsa dan gane da ita, a yan kwanakin nan kullun zuciyarsa na yawan gaya mashi cewa daddy ne bai yi mata adalci ba, sai dai aikin da yake yi a kan James ya hana shi binciko gaskiya lamari akan faɗar daddy da mummy ɗin.
(Tofa a ganin ku waye mai laifi a cikin su kenan?)
Sosai sarkar ta yi mashi bala'i kyau, dama kuma already akwai wani ɗan siririn sarka a wuyarsa, mai bala'i kyau da tsada, sai ya haɗe su. Bayan ya sanya sai ya tattare komai harda hoton mum ɗin tasu ya maida ma'ajiyar su, sannan ya dawo ya haye bed ya kwanta tare da jan wannan bargon nasa mai bala'i laushi ya rufe jikinsa zuwa wuyarsa, ga sarkar Michael kuma ya ajiye mashi a saman bedside drawer duk time da shigo sai ya ba shi.
Yan da ya lume a lallausan bed ɗin nan nasa abin ba'a magana, ga black curly hair nan nasa ya zubo mashi har fuskarsa, sai wani lumshe idanuwansa yake yi kamar mai jin barci, ga yanayin garin gwanin burgewa saboda ruwan saman da akayi, iskan mai sanyin daɗi na kaɗawa, iskar yanayin garin tafi ta Ac daɗi. Ya ɗan jima cikin wannan yana yi mai daɗin kafin nan ya