Showing 45001 words to 48000 words out of 355604 words
shi kasan na musamman ne, duk da cewa gaba ɗaya, luntsuma-luntsumar sofar dake cikin jet ɗin, sofa ne masu numfashi wanda idan ka gansu, kai kace a fadan shugaban ƙasa kake, saboda haɗuwar su, ga su da laushi sosai, ko wani sofa akoi wani kyakkyawan glass table a gaban shi, wanda za a ɗaura maka drinks ko wani abin. Kasan cewar mamallakin Jet ɗin sarkin son kamshi ne hakan yasa cikin Jet ɗin ke tashin wani fitinannen daddaɗar kamshi turare mai kwantar da hankalin mai shaƙa, ga kuma daddaɗar sanyin Ac dake tashi, abun gwanin burgewa, Jet ɗin nan ya haɗu iya haɗuwa, dan haɗuwar sa ma ba zai faɗu a baki ba, ɗauke yake da tambarin sunan Romeo kamar haka *The General of the Army Romeo, da manyan baki*.
Jingina kai ya yi da jikin sofar da yake zaune, ya lumshe dara-daran kyakkyawan idon sa, ya yin da jibga jibgan sojojin sa ke ta faman kallon gefe-gefen sa dan bashi tsaro, amma basu isa su kalle shi direct ba dan bai son yawan kallo, sai dai su kalli gefe-gefe da shi, dan su tabbatar ba wani motsi ko wani na'uran nesa dake ɗaukan shi, don yanzu daga nesa za'a iya dasa maka na'ura ta ɗauko ka duk halin da kake ciki, har makiya su iya farmakar ka, sai dai a na iya gane na'uran a jikin mutum idan a ka dasa maka, hakan yasa suke yawan kallon in da yake, don su tabbatar ogan su yana kalau yana cikin tsaro.
Manyan jiragen sojoji biyu ne suka fara tashi kamar da mintuna goma sannan jet ɗin lion ya tashi, sai wasu manya-manyan jiragen biyu saka tashi, suka saka jet ɗin a tsakiyarsu, sai na yaki ɗaya a baya. Haka suka nufi Spain.
A ɓangaren daddy kuwa, Romeo na fita, ya zauna saman sofa yana dafe kirjinsa da ke masa bala'i ciwo kamar zai fashe. Already da ma lion ya san hakan za ta faru shi yasa ya ce da Tga ya zauna a gida kada ya bi shi, ya kula da daddy kawai, time to time su rinƙa yi masa alluran barci zuwa gobe zai dawo, shi ma kuma Michael gobe za'a dawo da shi gida, dan ya samu sauƙi ba laifi.
Sai faman dafe kirji daddy yake, a wannan halin Tga ya dawo cikin falon ya same shi, bayan ya kaiwa Romeo system da wayar ke nan.
Cikin sauri ya kariso cikin palon yana faɗin "What happened daddy?" Shiru daddy ya yi ya kasa magana saboda zafin da kirjinsa ke yi masa, dan a tunanin sa yaki lion zai tafi, shiyasa ya shiga damuwa, ga shi kuma lion ya ce Spain zai tafi, kuma daddy yasan da cewa James na can, tsoro yake kar dai wani abin ne ya faru a can Spain ɗin, dan yadda ya ga fuskar lion yau ba'a magana, abin sai dai mu ce Alhadulillah.
Ganin daddy ya ki yin magana yana ta faman dafe kirjinsa ne yasa Tga ya ɗauke sa cak kamar ƙaramin yaro, kai tsaye word room ya wuce da shi. Yazo zai haura saman benen ne yaci karo da Musharraf sume a kasa yana kwance magashian. Mamaki Tga ya yi na me ya kawo Musharraf nan, har ya suma haka.
Ransa cike da tunani ya wuce word room ɗauke da daddy. Bayan ya kai daddy ya masa alluran hutu ne, ya dawo ya ɗauki Musharraf dan ya mai da shi word room, amma kuma ya yi hakan ne dan James da Romeo ba wai dan yana son Musharraf ba, kawai don dai ya san akwai camera a palon ne, kome ya yi James ko Romeo za su gani, shi yasa ya yi hakan, ba dan haka ba, kun dai san Tga baya kaunar Musharraf ko kaɗan.
Word room ya mai da Musharraf ya kwantar da shi saman bed nasa, ya fito ya nufi nashi bangaren don ya je ya yi wanka ya canza kakin jikinsa.
To mu leƙo Nigeria kafin mu dawo wata kila lion ɗin mu ya isa Spain sai mu bi shi muga ne ya je yi a can
Ilorin, Kwara State💞💞
Sai misalin karfe 6 na yamma Rimsha ta farka daga barcin wahala da ya ɗauke ta, jikin ta duk zafi yake mata, kamar an mata duka da itace haka ta ke ji. Meƙewa zaune a tsakiyar gadon ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon, wanka da tayi a ruwan saman nan ya ja mata ciwon kai sosai, ga shi tazo ta sha kuka rasuwar daddynta, abin sai ya haɗu ya mata yawa. Da kyar ta iya miƙewa ta nufi drawer kayan Kausar. Mayafi ta ɗauko tare da ɗaukan 1k daga cikin ragowar canjin da ya rage.
Falo ta fito, babu kowa, Kausar da Ayla ba sa nan, tasha mamakin ina kuma suka je, da kamar za ta wuce ta fita, sai kuma ta fasa ta juyo ta dawo ta nufi wajen Iya. Kamar yadda ta bar Iya ɗazun haka ta dawo ta same ta tana kwance saman gado. Sallama ta mata, daga kwance Iya ta amsa sannan tare da mata izinin shigowa.
Shiga cikin ta yi, wajen da ta tsaya ɗazun a nan ta tsaya yanzu ma. A nutse ta ce "Iya ina Kausar da Ayla." "Sun tafi tallar kifi." Iya ta ba ta amsa, mamaki ne ya kama ta, tallar kifi kuma ta faɗa a ranta, ita dai a nata tunanin sai talakawa ne kawai ke yin talla, amma me yasa su Kausar, za su je talla bayan su suna da rufin asiri, bata san yarabawa da neman kuɗi bane, basa zaman banza, fita suke su nemi halak ɗinsu, matansu da mazansu, basa wasa da neman kuɗi.
Kamar za ta sake yiwa Iya wata maganar, amma sai ta fasa ta fito ta nufi waje.
Kai tsaye shagon Sadudin ta nufa, dan yanzu ta san hanya zuwa shagon nasa. Makilin da brush na goge baki ta saya, brush guda biyu ta saya, makilin kuma guda ɗaya. Ta ba shi 1k ya bata canjin 400, har ta karɓi canjin za ta tafi sai kuma ta sake ba shi canjin ta ce ya bata cardboard paper and pencil, Allah ya sa yana da shi, ya karɓi kuɗin ya ɗauko ya bata tare da canjin 180, color na zane ta sake saya da ragowar canjin.
Bayan ta gama sayyan zata wuce Sadudin ya fara tambayar ta daga ina take, ya suke da Kausar, tana jin abin da ya ce, dan da broken English ya yi magana, saboda ya san ba bayarabiya bace.
Saboda tsiya irin na Rimsha sai ta nuna masa ita bata jin English ma kwata-kwata, shi kuma ya dage sai ya ji gulma, sai ya fara yi mata yar kurma-kurma da hannu, nan ma ta ce masa bata gane komai ba. Saboda gulma irin na shi har da fitowa waje daga cikin shagon yana mata kwatancen ta in da arewa yake ya na faɗi daga can take. Hannu ta ɗaga sama ta ce masa daga duniyar wata take, nan fa ya gane raina masa wayo tayi ashe tana jin sa, ta bar shi sai yin yar kurma-kurma yake kamar mahaukaci ya zage sai kwatance yake.
Kafin ya gama tunanin da yake Rimsha ta sa kai ta wuce abinta, ciza laɓɓa ya yi alamar bai ji daɗi ba, yaso ya ji daga ina take, ya so ta saki jiki da shi, amma ina bai samu dama ba, dan ita ma Rimsha ba kanwar lasa ba ce, ta iya tsiya, amma sai idan ka taɓota take tsiyar nata.
A nutse take tafiya har ta isa gida. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin palon, wani matashi ta yi arba da shi zaune cikin palon saman sofa yana cin abinci, kamannin sa ɗaya da Kausar, sai dai shi baki ne Kausar kuma tana da ɗan haske. Cikin girmamawa ta gai da shi cikin harshen turanci dan tasan da wuya idan baya jin turanci, fuskarsa ɗauke da fara'a ya amsa tare da tambayar ta wa take nema, dan a tunaninsa Rimsha yar garin ce, tazo neman Kausar ce ko Iya, shiru ta masa ta rasa amsar da zata ba shi.
Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce "Wajen Kausar ki ka zo ne?" Ya yi maganar cikin harshen Hausa dan ya lura kamar Rimsha bahaushiya ce ba bayarabiya ba ce, cikin sauri ta gyaɗa masa kai alamar eh wajen Kausar ta zo. Girgiza kai ya yi yana faɗin "Eyya sorry ba ki san Kausar ta ɓata da su ka je Kd da Iya ba ko?" Shiru Rimsha ta masa, ta rasa ta ya zata masa baya ni, tunani take ko dai ta ce masa, ita ma yanzu yar gidan ce. Ci-gaba da cin abincin sa ya yi tun da ya ga taki yi masa magana, ita ma shiru ta tsaya, tana son wucewa cikin ɗakin Kausar ta je ta jiye mu su brush nasu ita da Ayla, sannan ta fara aikin zanen fuskar GAR, amma kuma tana tsoron wuce wa kada wannan matashin ya yi tunanin ko wani abu ta zo ɗauka musu.
Ta jima tsaye a wajen kafin Iya ta fito daga cikin ɗakin ta tana faɗin "Wasiu idan ka gama cin abinci ka sayo mana kifi da ɓomo, dan zan ɗaura abincin dare" ta yi maganar cikin harshen yarabanci. Da alamar shi ma Wasiu irin Kausar ne fagen cin abinci, dan ga shi nan Iya tana masa magana bai tanka ba, sai kai loma kawai take hannu baka hannu kwarya.
Wani nauyayyar ajiyar zuciya Rimsha ta sauƙe lokacin da Iya ta shigo palon kamar wadda aka tsare a prison yanzu kuma anzo fitar da ita, haka ta ji a ranta.
"Rimsha me ya tsai da ke a nan?". Cewar Iya, kasa da kai Rimsha ta yi tana ɗan satar kallon bodar Wasiu. Ganin haka ya sa Iya ta gane me Rimsha take yi wa kame-kame. "To wuce ciki abinki, wannan yayanku ne, yayan Kausar na biyu ne." sai lokacin ya da kata da cin abincin, ya dawo da kallonsa kan Rimsha. "Iya daga ina kuma ku ka samo wannan yarinya mai bala'i kyau haka?" Yar dariya Iya ta yi kafin ta ce "Tare suka zo da Kausar" a zabure ya miƙe tsaye yana faɗin "Me ki ke ce Iya? Kausar fa, to ina Kausar ɗin ta ke? Yau she ta dawo? Ai na a ka gane ta?" Ya yi maganar yana zaro ido waje.
"Oh sorry ban faɗa ma ka Kausar ta dawo ba ko?". Cewar Iya. Jin sun kamo wani topic na hira ne yasa Rimsha ta lallaɓa ta wuce da Sauri abinta ta shige ɗakin Kausar tana sauƙe ajiyar zuciya, ta baro su nan suna zance.
Tana shiga ta ajiye brush da makilin ɗin da ta sayo musu ita da Ayla, a saman ɗan karamin drawer dake ɗakin, sannan ta haye saman gado, tare da shinfiɗe cardboard paper ta ɗauki pencil ta fara zanen fuskar GAR kamar yadda ta saba. Kasan cewar ta kware a zanen na shi ne yasa ta yin saurin gamawa, dan in da sabo ta saba, yanzu yanzu zata zana shi, kuma ya fita ras, kamar ki kira shi ya amsa.
Yau zanen sa da ta yi ma, na daban ne da kullun, dan yau ta zana shi a babba da face mask, sai kuma ta zana wani karamin hoton na shi, a kasan babban, shi kuma wannan karamin ba bu face mask ta zana shi, duk da cewa bata taɓa ganin shi ido da ido ba, ma'ana bata taɓa ganin asalin fuskarsa babu face mask ba, tana iya kawata yadda kyansa zai kasance a zahiri, sai ta zana shi ita yana yin yadda fahimtar kyansa da ta yi.
"Rimsha rubutun mene wannan a kirjin ki?" Kamar daga sama ta ji muryan Malika, ko a ce muryarta, don ba abin da ya raba muryarta da ta Malika. Cikin sauri ta ɗago kai tana kallon Malika. Tsaye take a bakin kofar shigowa ɗakin, ta goya hannu a kirji tana murmushi, kamar kullun dogon riga ne har kasa purple color a jikinta, ta yafa mayafin rigar a kanta.
Murmushi ita ma Rimsha ta yi tana faɗin "Ina ki ke tafi ɗazun?". Karisowa cikin ɗakin Malika ta yi tare da zama kusa da ita tana kallon zanen sunan GAR dake kirjin Rimsha. "Baki faɗa min zane me a kirjin ki ba". Cewar Malika ta yi maganar tana kai hannun ta saman kirjin Rimsha.
Kasan cewar Rimsha ta fara kirgan dangin sai abin ya bata kunya ta ɗan ja baya bata bari Malika ta taɓa mata kirji ba, kuma azahirin gaskiya tun da tayi zanen sunan Romeo take rufe wa bata son kowa ya gani yanzu ma da Malika ta gani, bata sani ba, ta duƙa tana zane ne wuyar rigarta ya ɗan zazzago rubutun ya bayyana.
Kara faɗaɗa murmushita Malika ta yi kafin ta ce "Rimsha ki na da kamala da kamewa, ina miki fatan ki kasan ce haka har karshen rayuwarki, ki zama mai tsare mutuncin kan ki dan mutunci madara ne idan ya zube ba zata taɓa kwasuwa ba, naji daɗin yadda kika janye jikin ki baya, amma ina son ki sani ni ba zan taɓa cutar da ke ba, sai dai ma nayi iya kan bakin kokari na wajen ganin na taya ki tsare mutuncin ki". Ajiyar zuciya Rimsha ta sauƙe sannan ta ce "Ina godiya sosai Malika, amma dai kina ba ni tsoro da kuma mamaki" "Mamakin me Nake baki Rimsha?" Cewar Malika tayi maganar tana ɗan zaro ido.
"Me yasa wani lokaci mutane basa kallon ki sai ni kaɗai? Sannan kuma me yasa da Ayla ta gan ki ta suma? Ya aka yi kika shigo gidan nan yanzu? Me yasa idan muna magana da ke ba wanda yake ji me muke faɗe?". Zuba mata ido Malika ta yi, har sai da ta kammala jero tambayoyin nata, sannan ta saki haɗaɗɗen murmushi tana faɗin "Rimsha ki na da abin dariya, to amma kina da gaskiya dole zaki ji tsoro dan baki saba ba, ni ba mutun ba ce kamar yadda kika ɗauka, ni aljana ce" a zabure Rimsha ta ja baya tare da miƙa wa tsaye tana zaro dara daran sleeping eyes nata,
"Menene Rimsha? Kada ki ji tsoro na mana". Runtse ido Rimsha tayi tare da kurma wani razananiyar ihu, wadda ya sanya Malika ɓace wa ba shiri.
Da gudu Iya da boda Wasiyu suka shigo cikin ɗakin Iya tana faɗin "Rimsha lafiya ki ke kurma ihu haka?". Idon ta a Runtse saboda tsoro ta kasa magana kuma ta kasa buɗe ido, dan tana ganin idan ta buɗe idon ta mutuwa za ta yi, Malika aljana za ta kashe ta.
Da kyar Iya ta samu ta lallaɓata tayi shiru tare da komawa ta zauna tana tunanin ita kuma daga ina ta samo aljanna, ganin ta yi shiru yasa su Iya suka koma palo.
Shiru ta zaune a wajen tana tunani har su Kausar suka dawo ƙarfe 6:30pm daidai su ka shigo cikin gidan daga tallan kifi.
Da sauri Rimsha ta miƙe ta rungumo Ayla tana son faɗa mata cewa Malika aljana ce, sai kuma ta kasa, ga dai maganar a bakin ta, amma ta kasa faɗe. Haka ta hakura suka yi alwala dan lokacin sallar mangariba ya yi.
Sai bayan sun yi sallah mangariba da issha ne suka zauna a palo suna hira. Miƙe wa Rimsha ta yi ta shiga kitchen wajen Iya, dan taya ta girki.
Yau tuwon semo da miyar Egusi Iya da Rimsha suka yi. Sai karfe 9 na dare suka kammala girkin suka dawo palo suka baje, suka fara cin abinci, suna ci suna hira, ita kuma Kausar tana ci tana haɗa zufa, don ba ta magana kam sai dai kai loma.
Suna tsaka da cin abincin ne boda Jami'u da boda Kabiru suka dawo. Da gudu Kausar ta tashi ta nufe su, tana ta washe baki. Tsalle tayi ta haye jikin boda Jami'u, ɗaga ta ya yi sama kamar yar baby, duk wannan kiba na Kausar bai hana shi ya iya ɗaga ta ba, dan Jami'u irin mazan nan masu tsawo da ƙiba, ga shi da kiran karfi.
Ihu ne ya kaure a gidan, na karti wato boda Jamiyu da boda Kabiru, don ba su san kanwarsu kuma yar autarsu ta dawo ba. Shi boda Jamiyu ɗa ne ga yayan baban Kausar kuma shi yake son Kausar ɗin ma'ana saurayinta ke nan. Ihu suke kamar ba lafiya ba, wai a haka murna suke nunawa, miƙewa Iya ta yi ta fara taya su. Bayin Allah Rimsha da Ayla suna ganin ikon Allah iya ganin idonsu a kasar Yarabawa, wani lokaci ma har tunani suke anya Iya ba ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba kuwa mata ce wani lokaci bata da setti ko kaɗan.
Haka suka yi ta ihun nuna murnarsu na wani lokaci kafin nan su tsagaita, Jami'u ya sauƙe Kausar kasa daga jikin sa, sai dariya suke.
Daga Jami'u har Kabiru sun yi shocked da ganin su Rimsha, sai kallon Rimsha suke, dan akwai wutar nepa, haske ya karaɗe palon gabaɗaya hakan ya sa suka samu daman ganin Ayla da Rimsha sosai.
Jami'u ya kasa hakuri har sai da ya tambayi daga ina Rimsha take, nan fa Kausar ta fara basu labarin irin wahalar da suka sha tun shigar su daular Mutuwa har fitowar su. Sosai su Jami'u suka tausaya musu. Hannu ya kai zai shafi kan Rimsha, cikin sauri ta ɗan ja baya, yar dariya ya yi kafin ya ce "As from today you are my sister, so kada ki damu, na san halin ku Hausawa baku son a rinƙa taɓaku sai ku rinƙa avoiding na mutane, kamar ba ku da gaskiya." cikin harshen Turanci ya yi maganar. Shiru Rimsha ta masa, dan ita gaba ɗaya ma haushi suka bata, jibi yadda yake wani rungume Kausar dan iskanci kuma yasan akwai aure a tsakanin su. A ɓangaren Ayla ma ba karamin haushin abin ta ji ba, wasu karti da su ba kyan gani, ga shi dukansu sun wani saka gajeren wando zuwa guiwa da riga mai karamin hannu.
Shi kam Kabiru sai kallon Rimsha yake ya kasa dai'na wa, haka shi ma Jamiyu, sai dai shi Jamiyu satar kallon ta yake dan kada Iya ko Kausar su gane yana kallon nata.
Yanzu su ma a nan gidan za