Showing 336001 words to 339000 words out of 355604 words
kuma, sun koma saman table dan cin abincin dare.
💖💖TRIPLETS💖💖
dedicated to AISHA BAITA JIDDAH 💘 (MUMMO RIMSHA)
E89-90💖
Jin abin da ya ce yasa ta ɗago kanta daga kirjin nasa tare da gyara zamanta ta haɗe fuskokinsu waje guda. "Yaya Imran ni fa matarka ce, me yasa zaka tambaye ni dan zaka yi mani abin da ya kasance halak ɗin ka?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe ba tare da ya yi magana ba ya haɗe bakinsu waje guda ya fara bata hot kiss, shiru ta natsu tana karɓar saƙon da yake aika mata da shi, while a can cikin gida kuma, sun koma saman table dan cin abincin dare.
Akil ba kunya ya rinƙa bawa Umaisha abinci a baki kamar yadda suka saba, yau sai wani yauki Umaishar take yi mashi kamar mace mai karamin ciki, Hjy Batula ta lura da hakan, shiyasa ma ta zage take ta faman turawa Umaishar duk abin da take buƙata, har da tambayarta ko akwai wani abin kwaɗayi da take buƙata, kamar an ce mata cike Umaisha ke da shi, Abbi ma dai ba'a barshi a baya ba, tsab ya gano ƴar tasa kamar akwai ajiya a jikinta, shiyasa shima yau yake bata kulawa ta musamman, oga Akil kuwa ya san komai domin ko wani motsi na matarsa tsab ya san komai, sai dai wani sain nuna mata yake yi kamar bai san komai ɗin ba, dan su cigaba da zaman lafiya, dama kuma haka ya dace namiji ya kasance, ba komai ne zaka rinƙa nunawa mace ka sani ba, domin mata ba su son ka rinƙa nuna masu kamar kai ka san komai ɗin kana fariya, idan hakan tana kasancewa to da wuya a rinƙa samun jituwa a tsakaninku.
Akila kuwa duk ta susuce ta zama wata sukuku da ita, tunanin abin da masoyin ɓoye ya ce mata ne gabaɗaya ya birkita mata kwakwalwa, ta zama kamar ba ita ba, Irfan ya yi rarrashin duniyar nan akan ta gaya mashi mene ne yake damun ta, amma ina taki gaya mashi, ba dan ya so ba ya kyaleta.
A ɓangaren gidan Lion kuwa. Lokacin da Areef ya farka daga barcinsa, ya farka ne yafiya lou kamar babu wani abin da ya faru, sai dai fa ya farka da ciwon jiki, gabaɗaya zafi jikinsa yake yi mashi, wayarsa ya ɗauka dake a saman bedside drawer ya duba time, 6:40 pm dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali kafin ya fara duba cikin wayar tasa, miss calls ɗin daddynsu ne da Aseef a cike a ciki, gobe Musharraf zai ta so shiyasa Aseef yake ta kiran shi a waya dan ya ji jirgin ina zai bi domin da jirgin kasuwa zai zo, ya bi jirgin Spain ne ko yaya.
Layin Imran ya fara kira akan ya aiko mashi Rimsha ta É—ebo mashi drinks a freezer dake a kitchen, na cikin bedroom nasa sun kare, tun É—azun ya so cewa a kawo mashi, amma bai sami dama ba, Saboda lokaci jikinsa na ya mashi ciwo sosai.
Number Imran bata shiga hakan yasa ya ce bari ya kira Lion, bai kai ga kiran Lion É—in ba kiran Aseef ta shigo, É—aukar kiran ya yi video call ne, dan Aseef bai cika kiransu normal call ba, sai dai video call dan ya gansu su gan shi.
Har lokacin bawan Allah murmushi ne akan face nasa, ya fito ne daga gym yana nufar cikin gida, iya singlet da shot ne kawai a jikinsa, sai haÉ—a zufa yake yi, kewar É—an uwan nasa ne ta takura mashi ya sanya shi ya kira shi dan suga juna ko ya É—an ji daÉ—i.
Areef bai san time da murmushi ta subce mashi ba ganin É—an uwan nasa yana murmushi. "Aseef daga ganin face naka akwai wata a kasa, so what is this?".
Kara faɗaɗa murmushin sa ya yi kafin ya ce "Ina murna ne na ɗan iya kalmomi almost 10 a cikin yaren Hosa (Hausa)" kunsan harshen nasa ne a lanƙwashe take akan yaren Hausa, shiyasa bai iya kiran Hausar ba.
Girgiza kai Areef ya yi yana mamakin yau Aseef ne da karya, to fa babbar magana, abin da bai taɓa kwatantawa ba, za su iya rantsewa da Allah koda a bayan Aseef ɗin ne, zasu iya bugan kirji suce bai taɓa yin karya ba, haka yake duk abin zai fito daga bakinsa to gaskiya ce, hakan yasa duk gidan bayan Lion idan ya yi magana babu mai musa maganar tasa, domin kuwa idan sun musa ma kansu suka yi wa, shi dai gaskiya ya faɗa.
Sosai Areef ya zuba mashi idanu dan ya karanci me a fuskar tasa da ya yi mashi karya akanta yau, abin ya É—an É—aure mashi kai.
Ganin Areef yana ta kallon shi ne yasa ya É—an kawar da wayar daga saitin face nasa yana faÉ—in "Why are you looking at me like this? What are you looking for?".
Murmushi Areef ya saki domin ya kuma ganowa karara akwai abin da Aseef ya ɓoye mashi, da alama kuma damuwa ce domin wannan murmushi da take kan face ɗin nasa ta dole ce, ba kamar murmushin da ya saba yi masu bane, idan baku manta ba shima Lion lokacin da Aseef ɗin ya kirashi da kallo ɗaya ya yi mashi ya ce to me Aseef kuma ya jajuɓo masu, kunga kenan akwai dai wani abin a kasa kamar dai yadda suke tunani, amma ya kafe akan lallai shi bashi da damuwar komai, amma kuma da alama Lion ya san da damuwar shiyasa ma bai tambayi dalilin shigarta ba.
"Aseef where is uncle Musharraf?" Cikin sauri ya dawo da wayar saitin face nasa yana faÉ—in "Uncle yana cikin gida yana karisa shirye shiryensa dan kaga jirgin safe zai bi ai". Ya yi maganar tamkar zai yi kuka, jinjina kai Areef ya yi domin ya gano me matsalar dama kuma ya yi mashi tambayar ne dan ya bugi cikinsa ya gano me ainahin damuwar, sai dai kuma koma yaya ba zai iya barin Musharraf a Usa ba tun da basu nan, yasan halin Æ´an uwansa sarai, ko daddy idan ya san Musharraf musulmi ne yana iya kashe shi da kansa, gara idan da suna nan ma, ko Lion ba zai bari ayi mashi wanin abin ba tun da ya kasance musulmi.
Sun jima suna hira Areef yana kara karfafa mashi gwiwa akan ya gama exams ya zo ya same su, tare kuma da kwantar mashi da hankali akan kada ya damu da tafiyar Musharraf, shi dai kawai ya tsaya ya yi karatu, da haka suka sha hira na ƴan uwa masu masifar kaunar junansu kafin su yi sallama Areef ya kira Lion bai ɗauka ba, hakan yasa ya yi kokarin ya miƙe da kansa yana jan kafa ya fito Palo, shi kuma Aseef toilet ya wuce dan yin wanka bayan ya ɗaura wayar a saman bed nasa kenan.
Babu kowa a palon da Areef ya fito, a hankali yake jan kafarsa da yake a kirji akayi mashi aikin, shiyasa ma yake iya takawa a hankali, da kyar ya haura sama ya nufi É—akin da yake zaton ita ce ta Lion É—in, Sakamakon kamshin perfume nasa da ya yi yawa a É—akin.
Babu kowa a cikin É—akin sai saukar ruwa dake tashi daga toilet alamar yana wanka kenan.
Saman gado Areef ya haye ya kwanta yana sauke numfashi ya kawo da kyar.
Idan muka koma gidan Abbi kuwa, IMRAN & JELLY sosai ya yi kissing nata son ranshi, bata hana shi ba, kuma bata yi mashi kuka ba domin bata a hayyacinta, ya gama kashe mata jiki dukka, tuni ya sanya ta ta lula duniyar sama jannati, ba ta ma san time daya zura hannunsa a cikin rigarta ba, sai dai ta ji wani irin yanayi mai wuyar misiltawa ya kara ninkuwa mata a jikinta, kankame shi ta yi tana sakar mashi wani irin numfashi wadda ke kara rikitar da shi.
Hakan yasa ya kara birkice mata yana aika mata saƙonni babu wasa, daga karshe ma kwantar da ita ya yi a saman kujerar ya yi mata rumfa da kirjinsa tare da ɗage rigarta sama ya capco nipple nata ya fara tsotsa kamar sweet.
A wannan lokacin ne kuma ta samu damar sakar mashi kuka domin nipples É—in sun fara yi mata zafi, ya murjesu sosai sannan kuma ya zo yana tsotsa mata.
Can kasa kasa ya fara jiyo kukan nata, da kaÉ—an da kaÉ—an har ya jiyo sautin tata da kyau, idanunsa a rufe, da kyar ya koma gefenta ya zauna tare da jingina kansa da jikin headboard na kujerar yana sauke wani zazzafar numfashi.
Ita kuwa cigaba da kuka ta yi duk da ya kyaleta É—in ma, ba ita ta yi shiru ba har sai da ya rarrasheta sannan ta yi shiru, amma fa ya sha fama wajen rarrashin nan nata kafin ya samu ta yi shiru.
Rumgumeta ya yi suka yi shiru, ban da saukar numfashin su dake tashi a hankali babu wani abin da zaka ji a wajen.
A cikin gida kuwa, sun kammala cin abinci lafiya lou, Akil ya ce su za su koma gida sai jibi za su zo, kiransa gefe guda Hjy Batula ta yi dan su yi magana, da yake yanzu da ya yi aure ya yi sauki sosai sai ya bi goggon tasa, da a baya kafin ya yi aure ne kuwa da ba zai je ba sai dai ta yi maganar tata a nan.
Sun É—auki minti talatin suna magana kafin ya dawo cikin palon, sallama suka yi wa su Abbi, sannan ya rungumo matarsa a gaban kowa, ba kunya haka suka nufi waje.
Ba su kai ga fita ba muryar Ommu ta katse su da cewa "Umaisha zo mu je É—aki ina da magana dake". Gaba É—aya palon zuba mata idanu suka yi, mamaki ne ya kama su dama tana cikin gidan nan, Hjy Batula kuwa mamaki ne ya kamata dama Hadiza yar kawarta matar yayanta ne ko yaya abin yake ne bata gane ba.
Abbi kuwa ɓata rai ya yi ya ce maza su wuce su tafi dare ya yi, meyasa tun da safe da suka zo bata fito sun yi maganar ba sai yanzu? Haka ba dan ta so ba tana ji tana gani Umaisha suka wuce da mijinta, sai dai kuma ta ci alwashin dole ta nemi number Umaisha ko ta halin yaya ne ma, ta waya ma abin zai fi tafiya mata daidai a cewarta.
Salati Hjy batula ta sanya, dan sai yanzu ta gane wace ce Hajiya Hadiza, tun tana amrya amrya tun da ta haifi Irfan yana jariri rabon da su sake haÉ—uwa sai yanzu, shiyasa ma bata gane ta ba, shekaru wajen 27 ai ba wasa ba, dole zata canza.
Har wajen mota yau ma suka raka su AKil, ya bar Akila a nan ta kwana dan ta nace lallai da Jelly zata kwana yau, ga shi kuma basu isa suce Akila su tafi da Jelly É—in su je gida su kwana ba, saboda Ammie ba zata yarda ba, shiyasa kawai suka barta su kwana da Jelly'n a nan shi ya san me zai gayawa Ammie idan ta tambayi ina Akilar.
Akil dai bai samu damar sallama da Imran ba, domin Imran baya nan duniyar, yana can sama jannati, haka ya ja mota suka wuce shi da matarsa su Abbi kuma suka koma cikin palo.
Imran dai bai dawo da jelly ba sai wuraren karfe 10 na dare, sannan ya dawo da ita cikin gida, lokacin babu kowa a palo, daddyn Jelly ya wuce part nasa shi da Aylarsa, shi ma Irfan ya wuce part nasa bayan ya yi ya yi akan Akila ta gaya mashi menene yake damunta taki ya, haka ya hakura damuwa cike fal ransa ya wuce part nasa ya kwanta kawai, amma dai barci ta gagara zuwa mashi, sai tunanin heartbeat yake yi, yayin da ita kuma take tunanin wani na da ban.
---
Saman table Imran ya haye tare da zuba masu abinci shi da amaryarsa, shima dai kamar Akil, a baki ya rin ƙa bata tana ci tana zuba mashi shagwaɓa, idan da sabo ya saba bata abinci a baki tun bata kai haka ba, kullun idan ya je Kano daddy ya huta, shi ne mai bata abincin, hakan yasa suka saba sosai.
Su kuwa su Rimsha suna É—akin Hanan, da ita Rimsnan da Akila sai Hanan da kuma Hjy Batula dake ta yi masu karin lectures, Aunty kuwa ta shige ciki ita da mijinta abinta, dan yau Hjy Hadiza ta kyale mata abin, da alama akwai abin da take shiryawa ne Shiyasa bata bi ta kan Abbin ba.
A takaice dai Imran sai karfe 11 suka baro gidan Abbi shi da Rimsna bayan ya yi wa Jelly alkawarin gobe zai zo da Rimsha ya haÉ—a su suje wajen lalle da gyaran gashi, dan dama tun kwana biyu da suka wuce Rimsha take damunsa akan tana son ayi mata kunshi.
Abin da ya sanya Imran bai tafi da Jelly ba shi ne ba'a gidansa yake ba, ba zai iya bari a kaita gidansu kuma baya nan ba, saboda yasan irin kiyayyar da Ammie take yi wa familyn Abbansu, wannan dalili ya sa ya ce da daddy a barta a nan zuwa next week, daddy bai musa mashi ba domin shima dai har cikin zuciyarsa baya son yar tasa É—aya tilo a duniya ta yi nisa da shi bayan rabuwarsu na Æ´an watanni, abin akwai wahala amma ya zai yi, ya zama dole wata rana hakan ta faru.
Da haka dai suka yi sallama ya É—auki Rimsha suka koma gida, amma sai da Æ´an sandan kan hanya masu kamen dare suka tare su suna tambayarsu daga ina suka fito, ina Imran zai kai karamar yarinya kamar Rimsha a cikin daren nan, domin babu alamar kamanni a fuskokinsu bare ace Æ´an uwa sa ce.
Ba musu ya gaya masu, barinsu suka yi suka wuce bayan sun gama ƴan dube dubansu a cikin motar dan tabbatar da babu wani abu na cutarwa da Imran ɗin ya ɗauko, sai da suka tabbatar babun ne sannan suka basu iznin wucewa, lokacin da suka dawo gida, Lion na tsaye a balcony bedroom nasa, bai yi barci ba, yana riƙe da cup mai shegen kyau a hannunsa, da alama coffee yake sha, kun san kuma coffee tana ɗaya daga cikin abin da yake sha idan yana cikin farinciki, to wannan ma haka ne da alama daren yau dai yana cikin farinciki, sai dai kamar kullun ba'a ganewa, kuma da alama farinciki tasa tana da alaƙa da samun nasara akan aikin Areef da yake yi.
Kallo É—aya ya yi wa su Imran ya mai da kallonsa kan wayar dake a hannunsa, bathrobe milk color ce a jikinsa, ya É—aure dark black curly hair nan nasa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin, kamar dai kullun sai tashin fitinannen kamshi perfume É—in nan nasa yake yi, da yake dare ta yi sosai ga kuma blue light a wajen, sai fuskarsa ta kara wani irin haske saboda ba hasken rana mai disashe hasken duk wata haske.
Cikin gida su Imran suka wuto sai kallon saman Rimshan take yi tana kallonsa, duk da ba wani kallon face nasa da kyau take yi ba.
A palon sama suka rabu da Imran, kowa ya wuce bedroom nasa dan yin wanka ayi shirin barci. Haka kuwa akayi kusan a tare suka yi wanka suka shirya cikin kayan barci.
Rimsha ta kwanta bayan ta sanya kayan barci riga da wando launin navy blue, shi kuma Imran launin purple ya sanya, ita Rimsha ta kwanta tare da É—aukar wayarta tana dubawa, uban miss call na A'A ne turun wadda za su kai miss call 66 mamaki ne ya kamata, ita yau kwata kwata ma ta mance da wata waya, shere miss call É—in ta yi ta shiga hotuna, kamar kullun sai da ta kalli gabaÉ—aya hotunan Lion sannan ta ajiye wayar tare da yin addu'ar barci ta kwanta.
Shi kuma Imran sai da ya kira layin daddy suka zuba soyayya da jelly har 1 sannan ya ce su yi barci bayan ya sha shagwaɓa iya son ranta sannan ta kyale shi, bawan Allah rungume da pillow yana murmushi ya yi barci.
Washegari bayan sun karya kamar yadda ya faÉ—a haka ya ce Rimsha ta shirya su je sayayya daga nan ayi mata kunshe sai gyaran gashi ita da kanta baya kitsuwa saboda tsantsi, to ta amsa da shi sannan ta shirya.
Kafin su fita sai da suka fara shiga wajen Areef duk da a tsorace suke da shi, amma Imran ya yi imanin ba wata matsala domin Lion ko zai mutu ba zai taɓa barin ɗan uwansa a cikin matsala ba, yana bala'in kaunarsu fiye da kansa, sune komai nasa, idan ya ga fuskokinsu ma musamman Aseef har wani daɗi yake ji da yake dai ba'a gane mashi ne kawai, kuma a zahirin gaskiya Lion ya fi kaunar Areef akan Aseef, abin da yasa jama'a suke ganin kamar ya fi son Aseef saboda Aseef a mai rauni sosai ya taso, ya tashi da wannan ciwo wadda yasa gaba ɗaya familyn William jacop suka ja shi a jiki sosai, hakan yasa shima Lion ɗin ya fi kusanci sosai da Aseef ɗin akan Areef, amma ko da yanayin yadda suke mu'amala ya ci ace mai hankali yasan cewa ya fi son Areef, saboda Areef na farko ma ya fi su saurin shiga ran mutane, duk da dukkansu akwai bala'in farinjini, amma shi Areef sauƙin kansa da rashin ja da manya ga son mutane yasa ya fi shiga rai, shi kuma Aseef kunsa yadda dai yake a baya idan ba Lion ba, ba wanda ya isa ya bashi umarnin akan abu, ko Areef sai dai ya lallaɓa shi su rabu lafiya, sannan kaifin ƙwaƙwalwa da basira yasa Lion ya fi kaunar Areef dan yana son mutane masu brain sosai, to Areef fa akwai ƙwaƙwalwa kamar dai Lion ɗin, ku da kun gani, mara ƙwaƙwalwa ba zai iya kwatanta abu ɗaya a cikin waƴan da Areef ya yi ba.
Da sallama É—auke a bakinsu suka shiga cikin É—akin, yana zaune a saman bed nasa, yau ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan bed É—in.
Ya ilahi ya lillahi Rimsha ta ruÉ—e da kanin kafafunsa, musamman yatsunsa ga kunba (farce) kafar tasa sai wani kyalli suke yi farere tas kamar madara, Allah