Showing 228001 words to 231000 words out of 355604 words

Chapter 77 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2746

da su da zane, yau sosai ta kura mashi ido tana kare wa kyakkyawar face nasa kallo, hancin nan nasa ba'a magana, bai yi dogo irin zut ɗin nan ba, a'a wani irin ne nashi akwai kara amma ba irin wannan kara mara kyan gani ba, soft skin ɗin nan nasa ba'a magana har wani sheki yake yi, hasken sa ya kafara fitowa, jikinsa kamar madara, cikin kwanciyar hankali yake sauƙe numfashi, da alama yana jin daɗin barcin da yake yi.

Almost 30mins tana kallonsa kafin Imran ya fice daga cikin ɗakin.

Sai bayan ya fita ne ya juyo da camerar kan fuskarsa, ɗan sunnar da kanta kasa ta yi tana yan kame-kame.

"Our first lady, fatan dai ana karatu sosai? Kada ki zo tunanin Saif ya hana min ke karatu, gara ki zage dan Saif baya son mutumin da bai yi karatu ba". Ɗan motsa kyawawan laɓɓanta ta yi, nan take dimple ɗin ta suka lotsa dukka biyu, hakan ba karamin kara fito da kyan fuskarta ya yi ba.

"Yaya Imran ina karatu sosai ma" jinjina kai ya yi kafin ya ce "Heartbeat bata dawo ba ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e.

"Okey idan ta dawo ki ce mata na ce ta bawa dolly abinci tunda ke kina tsoro, sannan yayan ku Akil zai taho da wata kanwar mu Aafia, za ku kwana da ita, gobe zai wuce da ita da Umaisha gidansa, fatan ba zata takura maki ba?" Da fara'a akan face nata ta ce "E yaya Imran, yaushe zata zo?".

Shiru ya ɗan yi kafin da bisani ya ce "E to yanzu ma zaki iya ganin su, bata da lafiya ne, ku kula mana da ita sosai" To ta amsa mashi da shi, sannan ya mata fatan alkhari akan Lion kamar yadda suka saba, daga nan suka yi sallama.

Ajiye wayar ta yi a gefenta ta cigaba da duba takardun nata.

A ɓangaren su Aafia kuwa, kwana ɗaya da wuni ɗaya ta yi kafin ta farfaɗo, ita kuma Hanan dama bata suma ba, hakan yasa jikinta ya yi kyau sosai, dan ta sami kulawar likitoci, da farko Akil daya farfaɗo ya dawo cikin hayyacinsa ya yi yunkurin korin Hanan ɗin, dan ya ɗauka ita ma tana daga cikin kawayen Aafia, daddyn Jelly ne ya dakatar da shi, ya ce mashi koma kawar Aafia ɗin ce su yi hakuri su karisa aikin da suka fara domin su sami ladan gaba ɗaya, ya bari ta sami lafiya tukun nan, dan a yadda suke ganin tan nan a cewar su idan ya koreta a yanzu ba zata iya gane gida ba, saboda bata gama dawowa daidai ba, ba don ya so ba ya hakura suka zuba ido suna jiran tashin Aafia.

Baiwar Allah lokacin da ta farfaɗo da kukan azaba ta tashi, tana ihu kamar zautatciya tana surutai akan bata so ya rabu da ita, kada ya cutar da ita, yaya Irfan zai kasheta, yaya Akil zai kasheta, ita bata so ya kyaleta, idan yana so ya sa bindiga ya harbeta, amma kada ya keta mata haddinta, sosai take kuka tana sambatu.

A wannan gaba har Irfan sai da ya zubar mata da kwalla, shi kuwa Akil sosai idonsa suka ciko da kwallar amma bai bari sun zuba ba, idanun nan nasa sun yi jawur kamar wuta, bawan Allah sai sara mashi kansa ke yi, ya rasa meke yi mashi daɗi a duniyar nan, shi kam daddyn Jelly ai ya jima ma da fara nashi kukan, tunma bata farfaɗo ba, da ta farfaɗo tana wannan sambatun kuma, sai abin ya kara taɓa mashi zuciya.

A wannan rana dai sun sha kuka, sai rarraahinta suke yi, har shi kansa Akil ɗin yau rarrashinta yake yi, dan duk wani mai Imani ya ga halin da take a ciki, sai ya zubar mata da kwalla.

Bayan komai ya lafa ta dawo daidai ne, can yamma kusan mangariba.

Bayan sun sha rarrashinta da kyar suka samu ta hakura ta fawwalawa Allah komai.

Misalin karfe 8 na dare gaba ɗayan su suna zaune har da Abbi da Aunty, Ayla da Kuma Hajiya Hadizatu wato Ommu, duk sun zo dubata dan Akil ya kira su ya gaya masu yan Kidnaping ɗin sun yi mata duka sosai sun ji mata ciwo tana asibiti, bai gaya masu cewa sun yi mata fyaɗe ba, sun rufe abin iya su AKIL DADDY'N JELLY, IRFAN, AAFIA ƊIN SAI HANAN iya su kawai suka san da zancen, su Abbi sun zo ne gaba ɗaya dubata, sai kukan munafurci Hajiya Hadizatu take yi, har da jan hanci, ita adole yarta ta sha wuya, bayan kuma tun da ta dawo Nigeria bata nemi ƴaƴan nata ba, amma yanzu ta zo tana cikawa mutane kunne da kuka, ko da ta zo asibitin ma kuma ita Aafia ɗin bata ko yi mata wani kallo sosai ba, dan magana ta gaskiya ba su wani son ta, domin tun asali bata ja su ajiki ba, bata wani kulawa da su, hasalima idan Abbi ya yi mata wani laifi ce mashi take a gabansu ta yi nadamar haihuwa tare da shi, kuma akan su take sauke haushin laifin da ya yi mata, ta yi ta yi masu masifa tana zaginsu, wata sain ma har da duka, abin da ya fara haɗa su faɗa sosai da Abbi har ta kai ga zage-zahe ma shine, lokaci da ta sa mi cikin Umaisha ta ce sai ta zubar, ba zata haifi wannan ciki ba, dan ta ga ji da haihuwa cikin talauci, sun sha faɗa sosai tsakaninsu, kuma duk da haka bata fasa yunkurin zubar da cikin ba, sai dai da yake Allah ya ƙaddara sai Umaisha ta zo duniya sai da ta zo, duk wani maganin zubar da ciki da ta sha a banza ta shashi, haka ba dan ta so ba ta raini cikin, Aafia da Irfan sun ci bakar wuya a hannunta, duka, zagi yayan matsiyaci kamar ba ƴaƴan ta ba, haka ta rinƙa azabtar da su da laifin babansu wadda shima ba laifin sa bane dan ya sami karayar arziki ne, kuma abin da ya jawo hankan ta fara faruwa, tun lokacin da ya sami karayar arziki ta ce ya saketa, shi kuma ya ki yarda, shine ta fara azabtar da shi, da shi da ƴaƴan nasa dukka, idan daddyn Jelly ya yi magana ta ce za su yi dambe, alokacin shima bai wuce 18 years to 19 ba, bayan ta haifi Umaisha kuma, ta ki yarda ta shayar da ita nono, ba yadda Abbi bai yi ba, amma ta ki yarda, daga karshe Umaisha dai madara ta sha, kuma tana da shekara uku Ommu ɗin ta bar masu gidan, wai ta ga ji da talauci.

A lokacin gaba ɗaya yan uwan Abbi suna da kuɗi sosai, shima karayar arziki ya samu ba dan haka ba yana da kuɗi sosai, shiyasama ai ta yarda ta zauna har ta haifi su Irfan ɗin, dan yana da kuɗi sosai da farko, a lokacin dukka yan uwansa sun ki bashi kuɗi ya farfaɗo da kansa ne saboda Hajizan, dan ita ya sa suka ki taimaka Mashi, dan sun san ko da sun ba shi ruwa zai sake koma, kaso 80 cikin ɗari na karayar arziki da ya samu ma suna zargin ita ce sila, dan alokacin da yake da kuɗin ba shi da aiki sai kai ta kasashen ketare ita da yan uwanta, ta tafi yawon buɗe ido, ta barshi da yara a gida, yana wahalar raino, hakan yasa su Abba suka ki taimaka Mashi har sai da ta bar gidan, lokacin shima daddyn Jelly yana da makudan kuɗaɗe na gadonsu, sai dai yana makaranta kuɗin suna wajen Abba, shi ya so bawa Abbi kuɗin dukka, saboda shi yasan halin da Abbi yake a ciki, dan gida ɗaya suke, Abbansu Imran ne ya hana shi, haka suka zuba wa Abbi ido kawai, haka kuwa suka yi, bayan tafiyar Ommun ne Abba ya bashi jari, lokacin kuma daddyn jelly ya bar Kaduna saboda bala'in Hadiza, yana ji yana gani tana azabtar da su Irfan da kuma yayan sa, ga shi ba halin ya yi magana, ta yi abinci ta hana Abbi, ga shi ba kuɗi ke gare shi ba, Hajiya Umaiya bata son su bare ya je gidan Abba ya ci abinci, domin farkon auren Hajiya Umaiya tana girki sosai, komai tsab-tsab, kuma ta iya girki, sai bayan ta Haifi Akila ne abin ya fara juye mata kwakwalwa, da farkon auren su, tana bala'in son yan uwan mijinta, dan sun mata komai, sun so ta sosai, daga bayane kamar ba lafiya ba, ta riƙiɗe ta koma wata iriya da ita. NA SAN KO BAKU SAMI DOGON BAYANI BA, KUN FAHIMCI IN DA LABARIN YA DOSA, KUN FAHIMCI WASU ABUBUWA DA SUKA FARU A BAYA A GIDAN ABBI, TO IN SHA ALLAH MUNA TAFIYA ZAN WARWARE MAKU KOMAI.

Daga Kano daddyn Jelly ya aikowa da Abbi kuɗi, haka suka haɗa shi da Abba suka ɗan farfaɗo da Abbin, da Hosain ya tashi shine ya yi mai kankat ya zubawa Abbi ruwan kuɗi, wannan ya sa Abbi ya farfaɗo, haka ya cigaba da rainon ƴaƴansa har Allah ya raya mashi su, bai yi aure ba har sai kwanakin can da ya auri aunty, shima kusan kamar daddyn Jelly ne, ya shafi shekara kusan sha biyar ba mata tun bayan tafiyar Ommu, kafin daga bisani ya auri aunty, lokacin da Umaisha ta girma ma a yan tsakanin nan Abbi ya sake gamuwa da karayar arziki ta yan damfara wadda har ta kai ga yana ƙoƙarin sayar da kamfanin sa, sai da ɗan uwansu Husain ya taimaka Mashi idan baku mance time ɗin ba, a takaice kenan Abin da ya sanya su Aafia basu damu da Ommu ba.

Story.

Har da wani rungume Aafia Ommu ta yi tana kukan munafurci, daga Aafia har su daddyn Jelly sun yi mamakin ganin Hajiya Hadiza na kuka akan su Aafia, Irfan kam sake baki ya yi yana mamaki, yana ganin ikon god.

Sai da Abbi ya rinƙa rarrashin Ommun sannan ta yi shiru tana wani faɗi kamar zakanya.

Bayan wasu mintuna komai ya lafane, Akil ya tambayi Aafia wace ce kuma Hanan, kawar ta ce ko waye.

Allah sarki Aafia da kyar Muryar ta yake fitowa, haka ta fara basu labarin yadda suka haɗu da Hanan ɗin, da kashe mata mahaifiya da yan bandits suka yi dukka ta basu labarin komai.

Daddyn Jelly ya fi kowa tausaya mata, da yake shi zuciyarsa a kusa take, yanzu yake iya kuka akan abu, haka zalika yanzu zaka mashi abu ƙarami ya ɓata mashi rai, sai dai da yake bawan Allah ne yana ƙoƙarin a ko da yaushe yana ɓoye ɓacin ransa, ba zaka taɓa sanin ya ɓata rai ba, amma da ga ta ciki shi yasan me yake ji, suna yi mashi kallon mai hakuri sosai, hakan yasa ma idan ya fito da ɓacin ran sa fili suke mamaki, har su ce e lallai abin da aka yi mashi, abune nai girma, kuma daɗin daɗawa baya shiga harkar kowa.

Abbi ne ya dubi Hanan dake kwance saman bed nata tana kuka, Aafia ta tuna mata da mamanta, a nutse ya fara tambayarta yar ina ce ita, tana kuka ta fara basu labarin gidansu, da irin halin babanta, da komai bata rage wani abu ɗaya ba, hakan yasa suka kara tausaya mata sosai da sosai, Abbi ya ce to idan ta samu lafiya ta huta, za su rakata har zuwa gida Katsina sai su gayawa babanta abin da ya faru, sannan su ruke shi alfarman ya basu ita su dawo da ita gida, Abbin ya ce zai riƙeta kamar yarsa, cikkin sauri Ommu ta katse shi da cewa "Ba dai kamar yarka ba Abbi, sai dai ka riƙeta dai, amma ƴaƴan ka sun wuce ka haɗa su da wata bare, ai yan gida daban ne".

Duk cikin ɗakin ba wanda ya tanka mata, da ido kawai suka bi ta da shi, bata wani damu ba, dan tasan ba son ta suke yi ba dama.

Bayan an sallame su Akil ne ya wuce da Aafia gida, ya je ya ɗauki Umaisha, basu ma kwana ba a daren suka wuce gidansa wadda yake a ta anguwar da Lion yake, ba su da nisa sosai, nan ya mai da su, su biyu a cikin gidan kawai, Akila ta ji daɗi sosai, kuma ta yi kukan dan kafin ta je gidan Akil sai ya kwana biyu, saɓanin da da suke tare da Umaisha kullun, da farko Ammie ta ki yarda ya ɗauki Umaisha ɗin, sai da ya ce mata ai gidansu zai mai data, ta zauna a can, shine ta yarda, da yake ba fita take ba, sai bai wani damu ba, dan yasan ba zata je gidan sa ba, ita kuma bata kawo cewa zai yi mata karya ba, domin bata taɓa kama shi ya yi mata ba ko da sunan wasa.

A ɓangaren ita kuma Hanan, gida su Abbi suka wuce da ita, Aunty sarkin tausayi, tuni ta riƙeta kamar kanwa, Abbi ya ce narar Saturday za su je Katsina wajen iyayen Hanan ɗin, da wannan zancen suka rufe maganar. A hanyar asibiti kafin su dawo gida daddyn Jelly ya sayi waya mai kyau, dama kuma already yana da sim card nasa da ya cire a wancan wayar tasa da ta lalace.

Washegari tun safe daddyn Jelly yana kwance a ɗakinsa bai fitoba, ko da Irfan ya kawo musu breakfast ya kasa fitowa ya ci, yana kwance, da alama yana cikin wata damuwar ne.

Misalin karfe 3:30 na rana, Aunty, Hanan, Ayla, suna zaune a palon kasa, Ayla da Hanan sun zama kamar yan uwan juna, sun haɗa kai sosai, sai hira Hanan da Aunty suke yi, ita kuma Ayla sai bin su da uhm, hmm kawai take yi, da alama ita ma akwai abin da yake damunta. Dukkansu kaya color ɗaya suka sanya, Hanan ta saka blue abaya na Aafia, dan ta girmi Ayla, kayan Ayla sun yi mata kaɗan, sai ta sanya wadda Aafia ta bari, ita kuma Ayla abayar da suka sawo a shopping ita da daddy'nta, mai shegen kyau blue color ta sanya a jikinta tare da yafa mayafin abayar.

Aunty da ta lura da hakan sai ta ce "Yau tun safe ban ga yaya Maik ba, ko lafiya?" Cikin sauri Ayla ta amsa ta da cewa "E nima tun ɗazun na ke son tambayar ina ya tafi".

Dariya sosai Aunty ta yi kafin ta ce "Dama na tsokalo zancen Yaya Maik ne dan na gane meke damunki, to dai yanzu na gane, wato dai kewar mijin naki kike yi, shine muna magana kina yi mana shiru ko? Eyeee dole Abbi ya zo gobe a ɗaura auren nan, wlh dole na zuga shi, ina na isa, tun ba'a je ko'ina ba har kin fara kewa ko?".

Kifa kai ta yi a bayan Hanan tana murmushi kasa-kasa, ita kuma Hanan da kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin matsanancin damuwa sosai, kawai daurewa take yi tana hiran da su, kuma dama Aunty da gangan take kara jawota da hira, dan saboda ta mance da damuwar da take a ciki.

"To amarya ta ango jeki part nasu ki duba mana ko lafiya bai leƙo mu ba yau, amma fa kada ki daɗe". Cewar Aunty kenan.

Da sauri ta miƙe ta nufi kofar palo, har zata fita kuma, sai ta fasa, ta dawo ta haura sama, jim kaɗan ta fito sanye da hijabinta har kasa launin blue, kalar abayar jikinta, sai murmushi take yi, an sami abin da ake so, za'a je duba masoyi.

Kai tsaye part na Irfan ta nufa, da sallama ɗauke a bakinta ta shigo Palon, babu kowa, dan haka sai ta nufi ɗakin daddyn nata kawai.

A bakin kofa ta yi sallama, yana daga kwance ya amsa mata, yana ƙoƙarin ce mata yana zuwa da yake baya son ta shigo ɗakin, saboda ba wani kayan kirki bane a jikinsa, daga shi sai Short da singlet.

Bai kai ga ce mata yana zuwa ba kawai ta shigo mashi ɗakin, da yake yana kwance, kuma ya ɗan ja bargo zuwa kugunsa dan akwai ɗan sanyi garin, hakan yasa bata gane cewa short ne kawai a jikinsa ba.

Kusa da gadon ta zo ta tsugunna tare da faɗin "Ina wuni daddy".

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da miƙewa zaune yana kallonta, while ita kuma tana kallon kasa.

"Lafiya lou baby, yau tun safe ban ganki ba, kewarki ta dame ni, kuma na kasa fita, yanzu ma kuma na kasa ce maki kije Palo dan ina son ganin face naki sosai". Ya kai karshen maganar yana ɗan leƙo fuskarta.

"Daddy to lafiya yau baka fito ba?" Ta faɗa a sanyaye. Nisawa ya yi kafin ya ce "Yau Jelly take cika shekara 16 daidai, yanzu haka shekaran ta sha shida da awa bakwai da suka ɗauru a kai, da safe aka haifa mani ita, ina kewar ta sosai, ɓatar ta ya dawo mani sabo, ban taɓa rabu da jalila daidai da rana ɗaya ba, sai ranar da ta ɓata, shekara sha 16 muna tare, ba dare ba rana, kin ga ai dole yau daddy ba zai iya fita ba". Ya kai karshen maganar cikin raunataciyar murya kamar zai yi kuka.

Allah ya gani bawan Allah yana bala'in kaunar jelly fiye da kansa, Allah kaɗai ya san me yake ji a cikin zuciyarsa, musamman yanzu da ya ga halin da Aafia ta faɗa, ya kara tayar mashi da hankali sosai da sosai, jiya kwana ya yi yana Sallah yana rokan Allah akan duk in da jelly take Allah ya tsare mashi ita, zuciyarsa ba zata iya jure makamanciyar abin da ya faru da Aafia ya faru da Jelly'n sa ba, idan hakan ta faru ya san shikenan tasa ta zo karshe, mutuwa zai yi, wannan dalili yasa ya kwana yin Sallah jiya, yana sallah yana kuka yana gayawa Allah bukatunsu, bayan ya gama ya yi karatun Al Qur'ani mai girma har sai da lokacin yin sallar asuba ta yi, sannan ya yi sallah ya ɗan kwanta, karfe takwas daidai ya farka, dan ya sa alam ta tashe sa takwas daidai.

Shiru Ayla ta yi tana tunanin zan tukan Aunty na yadda take gaya mata yadda ake yi wa miji idan yana cikin damuwa.

(Aunty kin yi kuskure da baki gaya mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login