Showing 42001 words to 45000 words out of 355604 words
fa a yan kwana kin nan sai kun kara hakuri da shi, dan zai birkice mu ku fiye da a baya, amma daga nan zamu yi nasara". Jin abin lion ya ke tamkar a mafarki, dan sun kwashe shekaru suna neman wa Michael magani, sun je hospital kala-kala, amma ba su yi nasara ba, dan ko wani likita cewa yake a haka a ka haife shi, dan haka babu wani magani, sun tambayi daddy sun lokacin da suka yi wayo, menene asalin abun da ya faru da Michael daddy ya ki faɗa musu sai dai ya ce musu shima bai sani ba.
To yau Allah ya yi Michael zai samu sauki, farinciki ya hana lion magana,. Kasan cewar shi baka taɓa gane farincikin sa ko bakin cikin sa, hakan yasa ba wanda ya gane cewa lion ya yi farinciki da samun saukin Michael.
Yau saboda murna lion ya jima sosai a hospital ɗin kafin ya koma gida. Yana zuwa gida, ya isko daddy a falo, nan fa daddy ya tsayar da shi, tare da sa masa kuka a kan ya har yanzu Michael bai dawo daga white house ba, kuma yana kiran layin James baya shiga. Da kyar lion ya samu ya lallaɓa daddy tare da yi masa alkawarin gobe Michael zai dawo, da kyar daddy ya yarda sannan ya wuce bedroom nasa.
Kai tsaye bedroom na James lion ya wuce, dan ya je ya yi wasu binciken na shi. Ya jima a ɗakin James yana yan bincike-binciken shi, kafin nan ya fito ya koma part nasa.
A gaban mirrorsa ya tsaya yana kallon fusataccen fuskarsa, sosai ya zubawa kansa ido kamar mai son gano wani abun, a hankali ya kai hannun sa yana shafa kyakkyawan fuskar sa, tunani yake sosai a kan James, tabbas James na bukatar taimako. Kamar wanda a ka tsikara ya ciro wayar sa daga aljihun sa tare da fitowa da sauri ya shige ɗakin binciken sa.
Ɗaki ne mai girman gaske, kasan ɗaki wani irin tiles ne mai kamar glass kana iya ganin fuskar ka jikin tiles ɗin, ga shi tsab tiles ɗin yake kamar kafa bai taɓa takawa ba. Bangon jikin ɗakin ta gabas, ma'ana ta wajen mahangar garin, glass ne a wajen maimakon gini kana tsaye daga cikin kana hangen cikin birnin Washington DC. Gaba ɗaya cikin ɗakin kewaye yake da haɗaɗɗun drawers masu kyau, wanda a ka ɗaura Manya-manyan na'urorin da kuma manya-manyan desktop computer a kansu, wadanda da ka gan su ka san ba aikin wasa ake da su ba, ga kuma wasu haɗaɗun chairs masu kyau da tsada, a kalla chairs ɗin nan za su kai 20 a cikin ɗakin, dan gaban kowani na'ura ko kuma desktop computer akoi wannan kyakkyawan chair ɗin a wajen. Komai na dakin a share a gyare tsaf kamar sababbin kaya a ka zuba, su kan su computers ɗin ba za ka taɓa cewa hannu ya taɓa taɓa su ba, saboda hasken da suke da shi ba datti ko kaɗan, wani daddaɗar kamshin tare da sanyin AC ke tashi a ɗakin wadda zai baka tabbacin mamallakin ɗakin nan mutunne mai mugun bala'i tsabta tare da son kamshi, dan komai nasa wani hadaɗɗe. Kamshi yake yi.
Um Masha Allah lion na mu duniyar tsabta da kamshi, kai dai in dai kamshi da tsabta ne to kai ne number 1 amma kar aje ta ɓangaren tausayi da horar da masu laifi dan a komai kai number 1 ne ba'a magana!!.
Saman wani haɗaɗen chair lion ya zauna, da kaga chair ka san na musamman ne, kamar yadda mamallakin ta yake na musamman, ɗaya tamkar da billion. Zama ya yi yana fuskantar wani makekiyar desktop computer mai bala'i kyau da tsada, mai girma sosai. Kunna computer ya yi, ya sanya hannun sa a kan screen ɗinta ya fara aiki.
Number James ya shiga cikin computer dan ya binciko a daidai ina aka soke layin James, kuma bayan an soke layin ya aka yi da ita.
Sosai ya nutsa cikin bincike ba ji ba gani, aiki yake tukuru babu kama hannun yaro. Duk da daddaɗar sanyin AC dake tashi a ɗakin, hakan bai hana zufa karyo masa daga gefe da gefen kunnensa ba, lokaci guda ya birkice kamar ba shi ba.
Zaro idon nan nasa ya yi yana kallon cikin computer, kamar wanda alluran sojansa ta motsa, nan take idon nan nasa suka canza launi zuwa ja, wasu siraran jijiyo ne suka bayyana daga goshinsa har zuwa wuyansa, sai huci yake fitarwa.
Ya jima a haka kafin nan ya furzar da iska mai bala'in zafi daga bakinsa tare da jan dogon numfashi ya sauƙe a hankali. Ci gaba da bincikensa ya yi na tsawon lokaci, duk yanayinsa ya canza, kamar ba shi ba, ya fito a asalin lion ɗinsa, duk wanda ya yi gigin tinkarar shi a yanzu za a iya ce masa mai kararren kwana, don halin da yake ciki a yanzu tsaf zai iya hallaka duk wanda ya tinkare shi, ganin shi a yanayin da yake ciki yanzu zai iya sanya mutun ya mutu ba tare da shiri ba.
Dakatawa ya yi da binciken nasa, ya miƙe a zafafe ya nufi bangrensa. Yana shiga bedroom nasa ya wuce toilet. Ruwa mai bala'in sanyi ya zuba wa kansa, don ya samu sauƙi, ya samu zuciyarsa ta ɗan sauka, ya huce, saboda ba ya son ya yi aiki cikin fishi da ɓacin rai, shi yasa ya yi hakan.
Bayan ya zuba ruwa ya fito ne, ya wuce dressing room ya shirya cikin pajama launin fara, sannan ya dawo saman lallausan gadonsa ya kwanta, ya jawo system nasa zai kunna hasken screen ɗin, sai kuma ya fasa, saboda har lokacin zuciyarsa na masa zafi, ba ya son yin aiki cikin ɓacin rai, don haka sai ya mayar da system ɗin saman bedside drawer ya kwanta tare da lumshe dara-daran idonsa yana tunanin James har barci ya yi awon gaba da shi.
After some day's, a yanzu Musharraf ya samu lafiya sosai, don yana iya taka kafarsa a hankali ya fito falon kasa, haka zalika shi ma, Michael ya samu sauƙin ciwokan da ya ji a sanadiyar hatsarin da ya yi, sai dai matsalar kwakwalwarsa ce, har yanzu da saura.
_Ni ma na tattare kayana na yi nan wannan dirama ba a nan ba._
Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
💞💞TRIPLET'S💞💞
🌹🌹Episode 15-16🌹🌹
After some day's, a yanzu Musharraf ya samu lafiya sosai, don yana iya taka kafarsa a hankali ya fito falon kasa, haka zalika shi ma Michael, ya samu sauƙin ciwukan da ya ji a sanadiyar accident ɗin da ya yi, sai dai matsalar kwakwalwarsa ce, har yanzu da saura ba ta warke ba.
Yau tun safe sosai helicopters ke shawagi a sararin samaniya, daga cikin Washington DC zuwa wajenta, kamar masu duba wani abin. Tun da daddy ya ji shawaginsu ya yi yawa ya san Romeo zai bar kasar ke nan, don da ma in dai ba fitar sirri zai yi ba kafin ya fita kasar sai an tashi helicopters sun yi ta kewaye cikin Washington DC, don tabbatar da tsaro, sai sun duba ko'ina. Idan sun tabbatar normal sannan private jet ɗin Romeo ya ɗaga, amma kafin ya ɗaga sai manya-manyan jiragen sojoji na kota-kwana biyu sun yi gaba, sannan nasa jet ɗin ya bi bayansu, sai wasu jiragen biyu su saka jet ɗinsa a tsakiya sai jirgin yaki ɗaya a bayan jet ɗin, don tabbatar da sun ba wa The General Of The Army kuma jika ga His excellency tsaro mai kyau, don ran Romeo daidai yake da ran zaratan sojoji 100 a cewarsu, don za a tara sojoji 100 ba za su iya aikin da shi kaɗai yake yi ba, kasancewar shi ba komai yake saka wa karfin dantse ba, akwai shi da aiki da kwakwalwa kamar agogo, manyan kasashe na duniya idan abin ya shige musu duhu sai sun nemi taimako daga wajensa, sannan kuma His Excellency yana bala'in kaunar sa fiye da tunanin mai tunani, duk cikin jikokinsa ya fi son lion, daga shi sai Michael yana matukar son su sosai. Ran Romeo babban abu ne mai matukar mahimmanci ba ga iya USA ba, har wajenta. Matukar Romeo zai fita Washington DC to fa sai an bincike ko'ina, har kasar da zai je, kafin ya dira cikin kasar sai helicopters sun tashi a cikin kasar ma, sun duba ko'ina da kyau.
Cikin taku irin na jaruman maza masu jini a jika, ya fito daga ɓangarensa, jikinsa na sanye da blue jeans mai bala'in kyau, sai Round neck T-shirt black color mai ratsin blue, a saman kayan nasa ya ɗora wannan jacket ɗin nasu, wato Puffer Jacket, ita ma black color, kalar rigarsa, kyawawan fararen kafafunsa na sanye da Hermes Birkenstock sandal, hannayensa na sanye cikin hand gloves baka, yayin da fuskarsa ke sanye da face mask baki, ya ɗaure dark black curly hair sa nan a baya, ya bar na gaban goshin kamar kullun. A yau fusatacciyar fuskar nan tasa ta fi ta koyaushe razana mai rai, domin yau fuskar tasa a ɗaure take tamau kamar wani hadari, har wani siraran jijiyo ne suka bayyana masa a goshinsa saboda ɗaure fuska sosai da ya yi, girarsa sun haɗe waje guda, saboda ɗaure fuska da ya yi, da ma gashin girar nasa ya kusa haɗewa saboda yawa, shi yasa da ya ɗaure fuska sai girar tasa ta haɗe, kwarjininsa ya kara bayyana sosai, tamkar wani zakin da ya yi shekara babu abinci, kallo ɗaya za ka masa ka san yau a fusace ya ke ainun.
Yana sako kafarsa ta saman benen zai sauƙo kasa, shi ma Musharraf yana sako tasa kafar zai hauro, bawan Allah bai san da cewa idan lion na saman staircase to ba wanda ya isa ya hau ba, har sai ya sauka, shi bai ma san waye lion ɗin ba, sunansa kawai yake ji.
Ga shi yau ran lion a matukar ɓace yake, don shi kaɗai ma sai wani huci yake, kamar ba lafiya ba, yana tafiya yana wani bubbuɗe kirjinsa, da ma kuma ga kirjin nasa a bubbuɗe.
A daidai tsakiyar staircase ɗin suka yi karo da Musharraf yana ɗan jan kafar sa a hankali yana ɗingisawa.
Wani mahaukacin mari lion ya sauƙe wa Musharraf a fuskarsa, wadda ya sanya shi yanke jiki ya zube kasa sumamme, kasancewar bene ne, hakan yasa ya gangara a sume ya sauka kasa, tsallakawa ta kansa lion ya yi, ya nufi hanyar fita daga cikin falon, don ma yana sauri ne shi yasa ya yi wa Musharraf mari ɗaya ya wuce.
"My lion where are you going?" Cewar daddy da ya fito daga ɗakin magungunansa da yake kasan benen, a hankali lion ya juyo da kallon sa kan daddy. Ganin fusatacciyar fuskarsa ba karamin razana daddy ya yi ba, ya sha jinin jikinsa don ya san halin ɗan nasa, kun san halin daddy da saurin birkicewa nan take ya ruɗe ya fara haɗa wa lion words yana in-ina. "My lion what is going on? What is happening? What is wrong with you?". Sai jero tambaya yake yi yana haɗe words, kuma ya yi maganar cike da tashin hankali.
Furzar da iska mai matikar zafi daga bakinsa lion ya yi, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakinsa ya ce, "Zan je Spain ne dad, I need your prayer." Yana kai karshen maganar bai tsaya ya jira amsar da dad zai ba shi ba ya fice da sauri, don ba abin da zai hana shi dira cikin Spain yau, kuma bai son ganin tashin hankali da dad zai shiga, don ya san ba karamin tashin hankali zai shiga ba, ya san halinsa sarai, musamman ma Michael ba ya nan James ba ya nan, halin da zai shiga ba zai yi kyan gani ba, kuma ba tafiyar sirri zai yi ba ya zama dole daddy ya sani, ko bai faɗa masa ba, dole zai sani ko don jiragen dake shawagi a sama, shi yasa ma bai ɓoye masa ba, ya sanar da shi ga in da zai je kawai.
Yana fita daga falon ya nufi jerin gwanon motocinsa dake jere kamar kullun suna jiran tafiya kawai. Gidan nasu yau ya cika da zaratan sojoji sosai ta ko'ina, saboda sun san da tafiyar tasa, gabaɗaya sun jeru layi kamar wadanda za su tafi fareti, tun daga farkon kofar falon har zuwa, babban gate na gidan, Jibga-jibgan zaratan sojoji ne. Tun da ya fito suke ta faman ɗaga hannu suna sara masa tare da buga kafafunsu ɗaya a kasa.
Ko kallon in da suke bai yi ba, ya wuce ya nufi motoncin nasu, yau saɓanin kullun ne, don an kara yawan motoncin nasu, saboda kowa ya san da tafiyar tasa, don karin tsaro zuwa airport, shi yasa aka karo manya-manyan motocin sojoji masu numfashi.
Motarsa da ya saba shiga nan wannan Baturen ya buɗe masa kofar motar, ya shiga ya zauna. Yana zama Tga ya fito hannunsa riƙe da system da wayar lion, shi ma Tga yau sanye yake cikin kaki. Zuwa ya yi, ya miƙa wa lion system ɗin sannan ya ɗaga hannu ɗaya ya sara masa, karɓar system da wayar kawai lion ya yi ba tare da ya kalli Tga ɗin ba.
Runtse dara-daran idanunsa ya yi, har cikin ransa yake jiyo sautin kukan Brady, don yasa su Tga sun kulle Brady a ɗaki, saboda ba zai tafi da shi ba, kun san Turawa yadda suke da dabbobinsu, lion ya fi jin zafin rabuwa da Brady a kan su Tga, har ga Allah yana jin ciwon kukan da Brady ke yi, shi ma kuma Brady sai haushi yake dakawa da karfi, don Romeo ya ji shi ya dawo ya ɗauke shi, amma ina Romeo na jin shi, sai dai ba zai yiwu ya tafi da shi ba ne kawai.
Zuba masa ido sojan da zai tuka motarsa ya yi wato direbansa na yanzu tun da ya tura Tyrone gadon asibiti, da ma Tyrone shi ne asalin direbnsa, Tga kuma na hannun damarsa, kuma uncle nasa, ɗan autansu daddy. To har yanzu Tyrone na asibiti tun dukan da ya masa a kan watch.
Yau tun daga cikin gida suka saki jiniya mai tashin kai, tamkar fillin daga za su tafi, jiniyar yau ma ta daban suka saki, wadda da ka ji ka san manya-manyan jiga-jigan kasar ne za su fita.
Da gudun gaske motoncin suka tashi, don sun saka alamar danja a gaban motoncinsu, duk da cewa ko ba su saka alamar danja ba ma, babu wani abin hawa da ke hawa titin da suke kai har sai sun wuce, to amma yau da yake za su yi gudun wuce ka'ida sai suka sanya alamar danja don bin doka, kada su zama suna matsayin masu doka kuma suna karya doka da kansu.
Tun kafin su iso bakin gate security sun wangale musu katafaren gate ɗin gidan, a guje suka danna hancin motocinsu waje.
Ko'ina jiniya ta kareɗe cikin unguwar, da ma tuni jama'a sun san da tafiyar tasa don sun gani a labarai sai dai babu wanda ya san abin da zai kai shi Spain, sannan ba kowa ma ya san ina zai je ba, kawai dai sun san The General of The Army zai fita cikin Washington DC yau.
Tsabar gudun da suke shararawa a kan titin nan, gudu na wuce ka'ida, hakan yasa suka isa *Dulles International Airport* cikin ƙankanin lokaci.
Ko'ina a cikin airport ɗin cike yake makil da manya-manyan sojoji da kuma jiga-jigan masu faɗa a ji a faɗin kasar, ga kuma manya-manyan gidajen TV wato ƴan jarida ta ko'ina, da ƴansanda ma ba a bar su a baya ba. Idan na ce zan tsaya zayyana muku jama'ar da suka halarci wannan airport ɗin to sai mu kwana mu wuni ba mu gama ba, kawai ku kwatanta a ranku, don fa waje airport ya cika iya cika, saboda lion bai yarda da su zo yi masa rakiya daga gida ba. Idan ba ku manta ba kun san family William Jacop gabaɗayansu ba sa yarda da mutane, ba wai kuma dan tsoro ko wani abu ba, haka suke ba sa son bako kuma ba sa yarda da mutun, kila suna da nasu dalilin na yin haka ba mu sani ba, shi yasa jama'a suka zo yi masa sallama a airport.
Suna danna hancin motocin su cikin airport ɗin, jerin gwanon motocin His Excellency Mr President ya danno hanci cikin airport ɗin, shi ma ya zo yi wa jikansa sallama.
Kusan a tare lion da His Excellency suka fito daga cikin motocinsu, dukansu manya-manyan jiga-jigan sojojin ne suka take musu baya. Rungume lion His Excellency ya zo ya yi, yayin da shi ma lion ya sanya hannayensa duka biyu ya rungumo kakan nasa sosai. Sai hotuna ƴan jarida ke ɗaukar su, don ba halin su matso kusa da su, ga shi kuma suna son jin me zai kai lion Spain, suna son tambayar shi amma ba dama, don ko lion shi kaɗai ya fito babu ɗan jarida mai karfin gwiwar iya tinkarar sa, ya ce zai masa tambayoyi, ballantana yau ga jiga-jigan dubban sojoji ta ko'ina, ai ko kusa ma ba su kawo a ransu za su samu damar ganin shi da ido ba ma, don ba tafiyar yara yake ba, taku yake irin na jaruman sadaukan yaki, da ya fito daga motarsa kafin su farga ya shige cikin jet ɗinsa. Amma Allah ya taimake su sun sa mu damar ganin shi albarkacin His Excellency, don ya tsaya su yi sallama.
Kiss His extcellency ya manna masa a kumatu tare da ɗan raba jikinsu yana masa fatan alkhari. Saboda face mask dake fuskarsa yasa bai sa mu damar yi wa His Excellency kiss ba, don ba zai cire face mask ɗin nan a gaban ƴan jarida ba, hakan yasa ya wuce ya nufi cikin jet nasa His Excellency na ɗaga masa hannu tare da fatan alheri.
Gabaɗaya sojojin dake wajen suka ɗaga manya-manyan bindigun su sama, suka saki harbi, ji kake ratatata ruwan wuta.
Wucewa yayi ya shiga cikin jet na sa, jibga-jibgan sojojin shida ne suka take masa baya zuwa cikin jet ɗin, su ka tsaitsaya a kansa, riƙe da manya-manyan jiga-jigan bindigogi masu numfashi, masu kai sako direct in da aka aika su. Zama yayi saman wani haɗaɗen sofa wadda da ka gan