Showing 258001 words to 261000 words out of 355604 words
karfi ta ce "Rimsha ki ɗan yi nisa da Ayla dan kada wannan bala'in ya taɓa ki" a razane Rimsha ta zaro ido tana kallon ta.
Malika ta gane cewa karin bayani Rimsha ke so, dan haka sai ta ce "E abin da kika ji haka ne, akwai wadda ta bawa wani boka aiki shi kuma ya sanya aljanu yan uwa na yin wannan aiki, ba za su iya taɓa wadda aka ce ayi wa aikin ba, yana da riƙo da askar masu karfi, dan haka kan Ayla za su sauke wannan aikin nasu, bana son ki yi kusa da ita dan zata iya mutuwa akowani lokaci k.....
Sai mun haɗu Monday idan mai dukka ya kai mu
💖💖TRIPLETS💖💖
E 69-70
Malika ta gane cewa karin bayani Rimsha ke so, dan haka sai ta ce "E abin da kika ji haka ne, akwai wadda ta bawa wani boka aiki shi kuma ya sanya aljanu yan uwa na yin wannan aiki, ba za su iya taɓa wadda aka ce ayi wa aikin ba, yana da riƙo da askar masu karfi, dan haka kan Ayla za su sauke wannan aikin nasu, kuma kinsan a cikin aikin ma har da wadda duk macen da ta raɓe shi da sunan soyayya zata mutu, bana son ki yi kusa da ita dan zata iya mutuwa akowani lokaci, ko kuma wani mummunar abin ya sameta". Nan take Rimsha fara hawaye abin ya taba ta sosai da sosai, da yake sun jima suna kewar juna sai kowa ya yi tunanin kukan ɗaɗin haɗuwa da yar uwar tata take yi. Ita kuma tana son tambayar Malika amma tana tsoron yin magana kada su yaya Imran su yi mata kallon mahaukaciya tun da ba kowa ke kallon Malika ɗin ba.
Ganin tana kuka ne yasa Imran ya sanya hannu ya raba ta da jikin Ayla ɗin, sai murmushi Ayla ke yi bakinta yaki rufuwa, ita kuma Rimsha wannan murmushi da Ayla ke yi, yana kara tayar mata da hankali ba kaɗan ba.
Gaba ɗaya family suna haɗe a Palon, mazan sun yi shigar mayan kaya matan kuma abayas, Abbi, daddy'n jelly, Aunty, Irfan, Akil, Akila, Umaisha, Aafia, Ayla amarya, a gaba ɗaya ƴan gidan, Hajiya Khadijat ne da kuma Hanan sune basu a waje, ita Hajiya Khadijat ma bata gidan, ta tafi gidan Ummin Nawid wuni, ita kuma Hanan tana wanka.
Akila ce ta taso ta rungumeta tana rarrashinta, a haka suka karisa cikin palon suka zauna, saman sofa ɗaya Ayla da Rimsha suka zauna, while daddyn Jelly na gefensu, Aafia baiwar Allah da yake tana samun kulawa sosai wajen Akil har kumatu ta yi, saɓanin a gidan nasu da bata gaba bata baya, kullun a yadda take, ba cigaba, amma yanzu Akil na kula da ita sosai, hakan yasa kaso 70 cikin 100 na damuwar da take a ciki na rabata da budurcinta da aka yi ta ragu mata, a yanzu dai ta dai'na yawan tunanin sosai, ta fawwalawa Allah komai, ta dukufa da karatun dake a gabanta, Amarya Umaisha kam ba'a magana, dan ƙibar da ta yi ma a yan kwanakin nan ba kaɗan bane, kumatun nan sun ciko sosai, da yake dama tafi Aafia diri da kuma kiɓa, ita kuma Aafia ta fita tsawo, Umaisha akwai hips da breast sosai kamar Rimsha da Akila, su ukun nan shape nasu kusan ɗaya, sai dai wadda ta fi ƙiba a ciki afi yawan ganin nata.
Sai hira suke yi cike da annashuwa da farinciki, suna ta gaggaisawa da juna, ita kuma Hanan tana wanka, bata fito ba. Daddy'n Jelly bawan Allah tunanin Jellyn sa kawai yake yi, ga ƴan uwanta sun haɗu amma bata nan, abin sam bai yi mashi daɗi ba, ya jefa shi cikin tunani.
Kasa hakuri Rimsha ta yi dan tana son yin magana da Malika, dan haka sai ta miƙe tana faɗin "Yaya Imran ina zuwa zan je wajen mota na dawo". Bata jira amsar shi ba ta fice da sauri abinta.
Tana fita Aunty ta fara tambayar a ina Imran ya samo yarinya kyakkyawa haka, wato magana suke akan Rimsha, bai ɓoye masu ba, ya gaya masu gaskiya yar Nawazudden ce, nan fa daga Abbi har daddyn Jelly suka fara godiya ga Allah da ya kawo masu ƴar Nawazudden har cikin gida, ashe da rabon su ramawa Nawazudden abubuwan alkhari da ya yi masu, ba ɓoye ɓoye da yake bappanun sune, hakan Imran ya fara basu labarin irin wahalar da Rimsha da Ayla suka sha kamar yadda Rimsha ta gaya mashi.
Duk cikin palon ba wanda bai matsa masu kwallaba, nan fa daddyn Jelly ya kara ɗaura ɗamarar kula da amaryarsa sosai, dan tasha wahalar rayuwa ba kaɗan ba.
Ita kuwa Rimsha tana fita waje ta fara ƴan waige waige tana neman Malika, can jikin motar Imran ta hangota tana tsaye ta harɗe hannu a kirji tana ɗan murmushi kamar kullun.
Da sauri Rimsha ta karisa wajen ta. Cike da tashin hankali ta fara magana "Malika menene yake faruwa? Dan Allah ki gaya Mani, wlh idan Ayla ta mutu zan iya shiga tashin hankali da zai iya zama sanadiyar rayuwata, kin dai ga nima bani da lafiya ko? To dan Allah ki tausaya Mani, yanzu haka da karfi karfi zuciyata ke bugawa, kirjina ciwo yake yi mani, dan Allah ki ji tausayin mu Malika". Tana magana idanuwanta cike tap da kwallah.
Matsowa Malika ta yi ta dafata tana faɗin "Rimsha bana son ganin ki cikin damuwa, bana son abin da zai taɓa ki, amma abin da na gaya maki akan Ayla gaskiya ce, ina son ki sani ba laifi na bane, kuma kema ba laifin ki bane, dan haka kiyi hakuri kamar yadda kika saba karɓar kaddarori da jarabobi to a wannan karon ma dagewa zaki yi ki karɓi mutuwar Ayla.
Tashin hankali, wani irin duhu Rimsha ta fara gani yana gilma mata ta cikin idanunta, jiri ta fara gani mai karfi yana ɗebanta, wani irin juyi duniyar yake yi mata, nan take ta fara ƙoƙarin zubewa kasa a wajen.
Cikin sauri Malika ta tareta tana faɗin "Rimsha kada ki faɗi, wai baki ji abin da Dr ya ce bane? Ko kin mance ne? Idan fa kika cigaba da sanya damuwa a ranki har kina yawan faɗuwa ki suma zaki sami paralyse, to dan haka ya kamata ki kula, ki zama mai karɓar kaddara a duk yadda ta zo maki, kuma ai ba ce maki na yi aikin ya kamata ba, bai kai ga kamata ba, a takaice ma bokan bai kai ga kammala aikin ba, so kinga akwai damar da za'a iya kuɓutar da ita, kin san fa wadda ta bada aikin cewa ta yi amata aikin da duk macen da ta raɓe shi da sunan soyayya to ta mutu, sannan kuma shi a sanya mashi son ta ita wadda ta bada aikin kenan, ita kaɗai zai so, to kinga aikin ba zai kama shi ba, ita kuma Ayla abin da yasa zai kamata ta mutu, saboda ta raɓe shi da sunan soyayya ne, dole aikin ya faɗi akanta.
Cikin sauri har tana haɗe words ta ce "Yanzu dai Malika ki gaya mani taya ya Ayla yar uwata zata kuɓuta daga hannun wayan nan azzaluman?"
A takaice Malika ta ce "E kuna da hanya biyu koma in ce ɗaya, domin ɗayar ba lallai ta yi amfani ba, bari na fara gaya maki wadda ba lallai ta yi amfani ba, askar, yin addua da zama da alwala shine hanya ta farko kuma shine ba zai yi amfani ba, abin da ya sa na ce ba lallai ta yi amfani ba, saboda Ayla ba zata iya ba, ba zata juri yi kullun ba, saboda bata saba ba, acikin askars da muke da su ma kwata-kwata guda uku Ayla ta iya, so yanzu ko kin ce mata ta rinƙa yi ba zata iya yin shi kullun ba, zata rinƙa mancewa, kuma Kinga bokan yana kan yin aikin, zai iya kammalawa ko wani time daga yanzu, wannan shine hanya ta farko, wadda ba zata yi wani amfani ba, hanya ta biyu wadda zata yi amfani kuma shine the best solution da kuke da shi a yanzu, domin daga yanzu zuwa ko wani lokaci bokan nan za su iya kammala wannan aiki, ina kara jaddada maki, wannan hanya dai ba wata bace fa ce a sami haɗuwa tsakanin Ayla da AbdulMalik, jininsu ya haɗu, ta haka ne za'a iya samin nasara, amma shima fa idan ba'a yi yadda ya dace ba ana iya samun matsala".
Kwata kwata Rimsha bata gane irin haɗuwar da Malika take nufi ba, dan haka sai ta ce "Ai yanzu ma suna haɗe gida ɗaya, baki gani suna tare a palo bane? Ko dai ba AbdulMalik ɗin a cikinsu ne? Ko ba su bane ƴan uwan Ayla ɗin?".
Nisawa Malika ta yi kafin ta fara bata labarin yadda akayi Ayla ta zo gidan da kuma wanene AbdulMalik sannan ta yi mata karin haske akan irin haɗuwar da take magana akai. Babbar magana shiru Rimsha ta yi tana tunanin ya za'ayi ta gayawa Ayla ga abin da Malika ta ce, kai ina hakan ma ba zai yi wu ba, to waye ya dace ta gaya mawa?.
Ganin haka yasa Malika ta saketa tana faɗin "Kiyi tunani mai kyau, ki nutsar da brain naki, ki ceci kawar ki ƴar uwan ki, na barki lafiya zan je gida, amma zuwa gobe zan dawo". Tana kai karshen maganar ta ɓace ɓat, hakan kuma ya yi daidai da fitowar Imran, dan ya ji ta shiru, ita da ta ce tana zuwa yanzu, amma shine ta je ta jima haka, shine ya fito duba ta, bayan shima ya gama gayawa su Abbi wacece ita ɗin.
Ganin ta wani sukuku ya sa ya tambayeta ko lafiya, me ya tsayar da ita a wajen nan?.
Ta kasa magana sai dai ta yi gaba ya bi bayanta, ta rasa waye zata fara tunkara da wannan maganar, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan ba magana ce da zata faɗu ga kowa ba, ta ya za'ayi ta fara tunkarar wani ta ce mashi me to? Ta ce tana son daddy'n jelly da Ayla su yi kwanciyar aure ne ko kuma dai me? Wannan magana tafi karfin ƙwaƙwalwarta, Malika ta kai ta ta barota a wannan fannin kam.
Suna shiga palo daddy'n jelly da Abbi har suna haɗa baki wajen cewa "Zo nan Rimsha" abin ya bata mamaki, ya akayi suke mata wannan kira haka har suna haɗa baki, bayan kuma ɗazun da ta shigo banda mirmishi da suke yi mata, ba su wani kulata sosai ba.
Kusa da Abbi ta je ta zauna ta kasa wani motsin kirki kirjin ta sai dukan uku uku yake yi, wannan magana tafi karfinta, waye zata sanarwar? Ko Imran ɗin ta sanar wa ba zai iya tunkarar daddyn Jelly da maganar ba, magana ce wace girmanta ya fi karfin katon dutse, har gara ɗaukar katon dutse akan furta ta, ko abokan juna yana da wuyar furtawa a tsakanin su bare kuma ace ta gaya wa Imran shi kuma ya gayawa bappansa, to ta ina ma zaa fara? Su ce mashi ya kwanta da Ayla ne ko dai yaya?. Wanann shi babbar magana.
Su kuwa banda mirmishi ba wani abin da suke yi, sai hira ake zubawa, cikin dabara Irfan ya kira Akila akan ta zo ta raka shi waje, suna fita su Imran suka fara gulmarsu suna dariya.
Aunty ce ta ce kowa ya zo su haye saman dining table aci abinci, Akil ba kunya ya ce shi a kasa zai zauna ya ciyar da babynsa a baki, a saman table ɗin nan ba zai ji daɗin bata abaki da kyau ba, salati Aunty ta yi tana tafa hannu, hararar ta daddyn Jelly ya yi yana faɗin "To zaki fara saka wa mutane ido ko? To wlh ki fita tun wuri, yau gabaɗayansu ma a nan za su kwana".
Abbi ne ya caɓe zancen da cewa "Maik ina rabaka da shiga harkar matata! Ka kiyaye ni tom, idan ba ka yi wa Halima biyayya ba zaka shiga wuta!".
Gaba ɗaya palon suka sa dariya, Aunty kuwa har da kara bubbuɗe hanci ita a dole matar yaya babba ce.
"Yaya Deen da gaske Sadiya ƴar sa ido ce, yanzu ba ga shi daga zuwan su Akil har zata saka masu ido ba".
Hararar shi Abbi ya yi yana faɗin "Ina Hanan ɗina ne? Naga kowa ban ganta ba".
Aunty ne ta ce "Hanan tana ɗaki tana wanka" jinjina kai Abbi ya yi yana faɗin "Gobe za mu je gidansu In sha Allah, idan muka dawo kuma kinga na haɗa yara uku kenan". Ɗan zaro ido Aunty ta yi yana faɗin "Ƴara uku kuma? Waye da waye?"
Da hannu ya nuna mata Rimsha yana faɗin "Da Rimsha da Hanan ɗin da kuma Aliya". Cikin sauri daddy'n jelly ya ce "A'a yaya Deen ni zan ɗauki Rimsha gaskiya, ka bari ni zan riƙe ta, a waje na zata zauna kafin mu nemo su mummynta da ƴar uwarta, idan ya so kai sai ka riƙe ƴar uwar tata".
Girgiza Abbi ya yi kafin ya ce "A'a kai da a yanzu baka da gida, kai ma fa riƙon ka nake yi tukun nan".
Dariya Aunty ta yi tana ƙoƙarin yin magana Akil ya rigata da cewa "Aunty wai ina abin cin ne? My wife tana jin yunwa".
Miƙewa Aunty ta yi ta nufi saman table tana faɗin "Bari naje na kawo wata kila baby ne ke jin yunwa ba wife ba, karna yi wa ɗan jikana rowa".
Rimsha kam miƙewa ta yi tare da riƙo hannun Ayla ta ce "Ayla ina ne ɗakin ki? Ina so ne in je ban ɗaki".
Satar kallon daddyn Jelly ta yi kafin ta ce "Muje na kai ki" ta kai karshen maganar tare da miƙe wa suka nufi sama.
"Baby ina zaki je ba tare da kin nemi izinin mijinki ba?" Cewar daddyn Jelly, da sauri ta juyo tana ƙoƙarin dawowa.
Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa "A'a raka mana first ladyn mu" kasa Rimsha ta yi da kai, ba abin da yake yi mata yawo a ƙwaƙwalwarta face zancen Malika, ga shi kuma shine kawai hanyar da za su bi wajen tseratar da Ayla.
Suna shiga ɗakin ta rungume Aylar tare da fashewa da kuka, sosai ita ma Ayla ta rungumeta tana hawaye, ita duk a tunaninta kukan sun jima basu haɗu bane Rimsha take yi.
Sun ɗan jima a haka kafin su raba jikinsu su koma bakin gado suka zauna. "Rimsha ki je toilet ɗin mana?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce "Ayla babu wani toilet da nake son zuwa, keɓewa kawai nake son mu yi, mu samu dama mu yi hira".
Sake rungumeta Ayla ta yi suna masu matuƙar jin kaunar juna.
A palo kuwa, sai hira suke yi, Akil babu kunya a gaban kowa da Aunty ta kawo mashi abin cin ya fara bawa Umaisha a baki, ita ma Umaisha ɗin da yake ta saba, yanzu ya koya mata, sai bata ji kunyar Abbi ba, sai cin abincin su suke yi, shi dai Imran daya ga haka sai ya miƙe ya fice waje bawan Allah.
Yana fita ya hango Akila da Irfan can wajen flowers suna hira, jikin motarsa ya koma ya tsaya yana hawaye, soyayyar Jelly ce ta dawo mashi sabuwa, Akil ya tuna mashi da lokacin baya idan ya je Kano, a baki yake bawa Jelly abinci, tana ci tana zuba mashi shagwaɓa, yanzu kuma da ya fito ya sake cin karo da su Irfan, sai ya sake tuna idan ya zo dawowa Kaduna yadda Jelly ke biyoshi waje tana yi mashi kukan shagwaɓa akan kada ya tafi ya kwana, hakan yasa shi hawaye, wani irin azababben son tane ke kara taso mashi, ji yake yi kamar zai mutu, zuciyarsa na mashi zafi sosai.
Yana tsaye a wajen bai ga lokacin da daddyn Jelly ya fito ba sai jin muryarsa ya yi yana faɗin "Dama nasan kuka ka fito yi Imran, tun da naga irin kallon da ka yi wa su Akil nasan sai ka tuna Jelly, saboda abin da kuka saba yi da ita kenan, ni kaina ina ganin Akil ya fara bawa Umaisha abinci kai da Jelly ne kuka faɗo mani a raina, kayi hakuri komai zai wuce In Sha Allah, idan har Jalila tana raye ina da kyakkyawar yaƙinin zata dawo gare mu, idan matar kace, to ba makawa sai ka aureta".
A zafafe Imran ya ɗago kai jin yau daddyn Jelly ya kira Jelly da sunanta kai tsaye wato Jalila, baya kiran sunan domin sunan wadda ta haifi mummyn Jelly ɗin kenan, saboda ta yi mashi kara, ta yi mashi abubuwa da dama shiyasa ya yi mata takwara, familyn mummy'n Jelly basa son aurensa da Hajiya Umaima wato mummyn Jelly amma haka mamanta ta dage sai da akayi aure, wannan dalili yasa ya yi mata takwara kuma yake girmama sunan, harta mahaifin mummyn Jelly baya son auren, kuma kafin ya yarda ayi auren sai da ya kafa wa mummyn Jelly sharaɗin akan idan ta fita gidan shi ta fita kenan, kada ya sake ganin kafarta, haka saboda son da take yi wa daddyn Jelly ta ce ta amince, ta yarda, wannan shine dalilin da yasa daddyn Jelly baya zuwa gidan sirikansa, kuma hakan yasa ma yaki yarda ko hutu Jelly ta je gidan, domin yasan basu sonta, kakanta mace kawai ke sonta, sai kuma kawunta Ahmad wato A'A.
Goge hawayen fuskarsa ya yi kafin ya ce "Ba komai daddy ina hakuri ai, kuma ya zama dole na yi hakuri, amma dai idan na tuna ta dole zan yi kuka, ban taɓa son wani abu a rayuwata kamar yadda nake son jelly ba, tun tana ƴar shekara 2 zuwa 3 Allah ya zarabceni da sonta, na tabbatar mawuyacin abune na so wani abin kwatan makamancin son da nake mata, kullun sai na yi mafarkinta daddy, kullun na kwanta, daurewa kawai nake yi ina shiga cikin mutane mu yi hira da dariya, amma ni kaɗai na san me nake ji a cikin zuciyata, Allah ya gani ina kaunar jelly fiye da raina, ya Allah ya dawo mani da ita".
Yana magana wasu hawayen suna biyo kuncinsa. Tunani daddyn Jelly ya fara yi da ace ya aura mata Muneer da ba makawa Imran mutuwa zai yi, irin wannan kauna da yake yi mata tun