Showing 306001 words to 309000 words out of 355604 words
ɗan ciza laɓɓansa na kasa ya yi kafin nan ya zauna a saman bed ɗin nasa tare da yi wa Imran massage akan ya kawo mashi kanwar nan tasa nan yanzu. TOH FA BABBAR MAGANA.
Ai kuwa Imran ba dan ya so ba ya tasheta daga barci, jin ance Lion na kiranta ne yasa ta fara karanta duk wata addu'a da ta zo mata a bakinta, ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba.
Sauƙowa kasa daga saman gadon ta yi jikinta sai kerma yake yi da haka ta ɗauki hijabi har kasa ta zumbula ta bi bayan Imran tana ta jero addua'o'i a ranta dan ta san abin da ya aikata Mashi.
Suna shiga cikin ɗakin tun basu kariso ba Lion ya dakatar da su tare da faɗin "Ka miƙa wa Mark ita". Kallon shi da kyau Imran ya yi yana zaro ido kafin ya dawo da kallonsa kan Rimshar wadda take tsaye bata ma gane nufin Lion ɗin ba.
"Rimsha me kika aikata bayan bamu nan?" Cewar Imran, "Prof" Lion ya ambaci sunansa can kasa kasa da wannan sanyayyar muryar tasa yayin kuma da yake rubuta saƙo a wayarsa, Imran ya gane nufinsa wato su fita mashi a ɗaki baya son wata magana.
Salati Imran yasa tare da riƙo hannunta suka fito waje, suna fita a tsakiyar palon ya tsaya ya fara tambayarta me ta aikata.
Cikin rawar murya ta fara gaya mashi komai na abin da ta yi, bata ɓoye mashi komai ba.... Ai kuwa bai bari ta karisa gaya mashi maganar ba ya tsinketa da wani wawan mari, ji kake tas.
Cikin sauri ta dafe kuncinta, rai a matukar ɓace ya fara magana "Me yasa bakya jin magana? Me yasa duk abin da na gaya maki baki amfani da shi? Yanzu kin san me nufin Saif kuwa? To cewa ya yi na miƙaki wajen tsinannen kafurin sojan nan wadda hukuncinsa gara mutuwa, kin san waye Saif kuwa? Da zaki shiga ɗakinsa ki yi mashi wannan shirmen kuma ki yi tunanin ba zai gane ba? Hankalinki ɗaya kuwa? To wlh bari ki ji abin da baki sani ba, Saif baya magana kuma ya sauya, idan kikaga yau baki karɓi hukunci daga hannun wancan kafurinba to wlh sai dai idan mutuwa Saif ya yi dan ina mai tabbatar maki idan duniyar nan dukka gatanki ne basu isa su tankwara Saif kuma ya tankwaru ba, baki taɓa ɓata mani rai irin na yau ba Rimsha, so kike yi zuciyata ta buga na mutu ki huta ko? Da wanne zan ji fisabillilahi? Naji da ɓatar Jelly ce ko kuma na ji da wannan bala'in da kika jefa kan ki a ciki?"
Zubewa kasa ta yi akan gwiwowinta tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tana kuka tana bashi hakuri. Bashi da zaɓi dole ya hakura ya duƙa ya rungumota tare da fara rarrashinta yana bata baki.
Duk abin da suke yi Lion yana jinsu domin a palon sama suke, kuma a kusa da bakin kofar ɗakin nasa suke, sai dai ko kaɗan bai ji cewa zai iya sauya magana ya dakatar da Mark daga bata hukunci ba, dole ta karɓi hukunci, dan ma ta yi sa'a shima yana cikin yanayi mara daɗi ne ga abubuwa sun sha mashi kai da shi zai bata horon da sai ta gwammaci muguwa, gobe ko da kuɗi aka bata ba zata yi gigin tinkarar ɗakinsa ba.
Haka Imran ya ja hannunta zuwa Palon kasa, ya san cewa Lion ya tsani kalmar sorry, akan cewa sorry ma zai iya harbe Rimshar kowa ma ya huta, shiyasa Imran ɗin bai yi gigin yunkurin ce mashi ya yi hakuri ba, kuma yasan ko ma ya faɗa ɓata bakinsa zai yi dan dai Lion ba zai canza magana ba, hakan yasa kawai ya hakura ya miƙawa Mark ita.
Already dama Mark ya sami massage ɗin Lion akan ya bata horon tsallen kwaɗo mai kyau, ta ɗauki good 3 hours tana tsallen kwaɗo tana kewaye gidan duk girmansa kuwa, kada ya kyaleta har sai ta kasa tafiya da kafafunta.
Ai kuwa haka Mark ya sanyata yin tsallen kwaɗo, Imran ya kasa jurewa sai ya koma cikin gida ya nufi ɗakin Areef yana matsa mata kwalla, Mark kuwa da yake ya saba bawa katti ma horo bare ita, sai ya zama ko a jikinsa, sai ma kara nishaɗi da yake idan yana basu horo.
Ko minti 20 Rimsha bata yi tana wannan frog jump ɗin ba ta faɗi kasa, ciro belt Mark ya yi akan zai zaneta, ga belt ɗin nasu nan ba sai na gaya maku ba, shegen azabar zafi ke gare shi kamar me.
Yana ƙoƙarin zaneta sai yaga fa bata numfashin, duƙawa ya yi a gabanta tare da sanya hannunsa a bakin kofofin hancin ta, ai kuwa bata numfashin, guntun tsaki ya ja tare da miƙewa ya nufi cikin gida.
Jim kaɗan ya fito da ruwar roba a hannunsa ya zo ya zuba mata, a razane ta farfaɗo tana sambatu, tsawa ya daka mata tare da bata umarni akan ta cigaba da yin tsallen kwaɗon.
Haka tana kuka ta cigaba da yi, duk kafafunta sun kunbura.
Imran kuwa yana shiga ɗakin Areef ya gaya mashi abin da yake faruwa, rai a ɓace Areef ya ce "Prof dafa mani bari na tashi ka gani, me za'a hukunta a jikin yarinyar nan fisabillilahi, muje wajen Mark ɗin dan kaniyarsa".
A tsorace Imran ya ce "No Areef bana son ku sami matsala da Saif akan Rimsha, pls ka yi hakuri kawai mu jire". ƴar tsawa ya dakawa Imran ɗin da ɗan karfi "Prof kana da hankali kuwa?! Kasan me kake faɗe kuwa? Mu kyaleta fa kace? Kasan waye Mark kuwa? To ina son ka sani Lion yanzu haka ma ya mance da ita, shi haka yake idan ya ce a bawa mutane horo to rufe babinsu yake yi domin yasan sojojin sa zasu hora wadda ya ce a bawa horon da kyau, ba za su ɗaga mashi kafa ba, dan haka kada ka damu muje na karɓeta a hannun Mark ɗin Lion ba zai gane ba".
To Imran ya amsa da shi sannan ya dafa mashi ya miƙe da kyar. A hankali Areef yake taka kafar tasa tare da dafa kafaɗar Imran ɗin, yana jin zafi sosai bawan Allah amma haka ya daure, abun ku da babban jami'in, idan da wani ne ya ji raunukan da Areef ya ji to da sai ya fi wata uku baya iya motsawa sai dai a kwantar a tayar, amma da yake shi ya sami horo mai kyau jarumin sadaukin namiji ne sai yake daurewa yana takawa, ko da zafin haka yake jurewa.
Sun jima suna tafiya kafin su fita palon, a kalla za su ɗauki 7 mins kafin su fito waje saboda a hankali Areef yake tafiya.
Yana fita ya ɗaure fuska sosai cike da bada umarni da izza ya ce wa Mark ɗin ina Rimsha. Cikin girmamawa Mark ya nuna mashi akan tana ta baya wajen garden ta zaga da frog jump zata zago.
Wucewa Areef ya yi yana cigaba da ɗingisa ƙafarsa har ya isa wajen, da hannu ya yi mata alama akan ta tashi ta zo, kasa tashi ta yi saboda kafarta sun kumbura suntum sun yi ja, tana ma zaune ne a wajen dan ta kasa cigaba da yi, shine ta zauna tana jiran Mark ɗin idan ya ji ta shiru sai ya zo ya kasheta kawai dan ta ga ji ba zata iya ba.
Areef yana ƙoƙarin yi mata magana idanunsa suka sauƙa akan ƴan kwacen waya dake kwance plat suna kallon rana, bayin Allah kullun cikin horarwar Mark suke.
Da mamaki Areef ya tambayi waɗan nan fa, nan fa Imran ya gaya mashi su waye ne, shima kuma Imran ɗin ya sha mamaki domin bai taɓa tunanin cewa har yanzu suna gidan ba, abin da basu sani ba shine Lion ma kwata kwata ya mance da batunsu a gidan, shiyasa bai sallamesu ba, tun da ya miƙa su hannun Mark ya mance da su.
Umarni Areef ya yi masu akan su tashi su tafi, da Imran ya tambaye shi akan me zai ce su tafi bayan kuma Lion ne ya basu wannan aiki, nan ma dai sake jaddada mashi Areef ya yi akan cewa yana da tabbacin Lion ya rufe babinsu ya mance da su, idan za'a shekara ana ajiyesu a gidan to in dai ba wata rana Allah ya kaddara suka yi ido biyu da Lion ɗin ba ya ce a sallamesu to har su mutu suna nan.
Jinjina kai Imran ya yi yana mamaki shi dai yasan tabbas ba wata mantawa da Lion ya yi da su, dan yasan halinsa sarai, amma da yake ɗan uwansa ne ya faɗin hakan sai ya ja bakinsa ya yi shiru kawai.
"Prof sake ni ka kira mani Mark" cewar Areef. "Zaka iya tsayuwa kuwa Areef?" Jinjina mashi kai ya yi alamar e zai iya, to Imran ya amsa mashi da shi sannan ya wuce ya nufi wajen Mark ɗin.
Zuba mata idanu Areef ya yi yana kallon yadda take ruwan hawaye Baiwar Allah, abin ba ƙaramin konawa Areef rai ya yi ba.
Suna a haka har Mark da Imran suka dawo wajen. Gaban Areef Mark ya tsaya cikin girmamawa ya ce ga shi nan. Ɗan kame jiminsa Areef ya yi ya tsaya da kyau tare da dagewa ya ɗauke Mark ɗin da wani bahaguwar mari domin shi dai Areef bahagone, da left hand yake aiki.
Har wani jiri Mark ya gani na lokacin guda, ji ya yi tamkar Lion ne ya mareshi, ya ji hannun maza, cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa suka yi jawur kamar jini.
Rai a ɓace Areef ya ce da Mark ɗin maza ya ɗauki Rimsha ya kai mashi ita ɗakinta, cikin girmamawa ya amsa da to sannan ya wuce ya nufeta, dan yasan ba'a yi wa TRIPLETS gardama, idan Areef ya yi magana to tamkar Lion ne ya yi, a haka Lion ya gina gaba ɗaya sojojinsa akan lallai su rinƙa jin maganar TRIPLETS nasa tamkar yadda za su ji nasa maganar.
Girgiza kai ta fara yi alamar bata son Mark ya taɓa ta, ganin haka yasa Areef ya dakatar Mark ɗin daga ɗaukar tata, kallon Imran ya yi yana jiran karin bayani akan me yasa Rimsha bata son Mark ya ɗauke ta, nan fa Imran ya gaya mashi addini ya yi hani da hakan kuma mu a al'adar mu ma ba'a yarda da hakan ba.
Jinjina kai Areef ya yi yana mai kara yabawa Nigeria, koba komai Nigerians suna tsare mutuncinsu, addini, da kuma al'ada, duk da suna aikata laifuka amma mafi yawanci a ɓoye suke yi, ba su fitowa ɓaro ɓaro su yi abu tsaɓanin kasashen turawa.
"Prof ka ɗauketa to ka kaita ɗaki sai ka zo ka dafa mani in koma ciki na gaji, kuma kaga yau za'ayi mani aiki Drs sun kusa diro Naija, bai kamata na jijjiga jinin jikina sosai ba".
To Imran ya amsa da shi kafin ya nufeta, sosai take kuka bai tsaya rarrashinta ba saboda yana tausayin Areef sosai, yasan cewa ya ga ji da tsayuwa ga alama nan har haɗa zufa yake yi.
Imran yana ɗaukar Rimsha suka bar wajen shi kuma Areef ya umarni Mark daya ɗauki waƴan nan ƴan kwacen wayar ya fitar da su zuwa waje ya sasu a abin hawa a kai su gida. Shima dai Mark ɗin to ya amsa da shi kafin ya wuce ya fara aiwatar da umarnin na Areef.
Saman bed nata Imran ya kwantar da ita sannan ya dawo ya tallafawa Areef suka koma cikin ɗaki.
Bayan sun koma ne Areef ya ce ya je ya rarrashin masa matar ɗan uwansa ya bata hakuri komai ya wuce wata rana In Sha Allah zata zama ita ce mai controlling na zuciyar Lion ɗin baki ɗaya, zata zama sai abin da take so, for now dai ta yi hakuri duk da bai san laifin da ta yi da ta cancanci wannan hukunci daga wajen Lion ɗin ba.
Imran na ƙoƙarin gaya mashi laifin da ta yi, ya dakatar da shi ya ce baya buƙatar ji, shi dai kawai ya je ya rarrasheta ta yi shiru ta yi hakuri. To Iman ya amsa mashi da shi tare da yi mashi godiya suka yi sallama.
Yana shiga ɗakin nata ya iskota har ta yi barcin wahala, ruwan zafi ya ɗebo a toilet tare da ɗauko ɗan ƙaramin towel ya zo ya fara gaza mata kafafun nata.
Jin ana taɓa ta yasa ta farka, cool murmushi Imran ya sakar mata tare da faɗin Sorry sister, ita ma murmushi ta ƙaƙalo tana kara bashi hakuri, ba komai ya ce mata sannan ya cigaba da gasa mata kafafun nata har sai da suka ɗan rage mata zogin da suke yi mata.
Bayan ya kammala ne ya kara yi mata faɗa sosai tare da ja mata kunne akan ta kiyaye Lion, alkawari ta yi mashi akan zata kiyaye daga haka suka yi sallama ya wuce bedroom nasa dan ya je ya yi wanka.
Misalin karfe 6 na yamma Drs suka iso, kuma a wannan yamman suka fara aikinsu dan Lion ba shi da wata buƙata da ta wuce ɗan uwansa ya tashi, yana son Areef ya tashi dan su yi aiki a tare, yana son mayar da Areef soja tun da ya cire shi a C.I.A kuma Areef ya sami horo na bugawa ajarida wadda zai iya bugawa da manya manyan sojiji na kasa da kasa, kuma yana da ƙwaƙwalwa ta Family'n William jacop.
Misalin karfe 8:30 bayan sun yi sallar isha Imran ya sawo masu abin ci shi da Rimsha suka ci suka ƙoshi sannan suka yi sallama akan sai da safe, yanzu kafafun nata sun ɗan saki amma ba dukka ba dan har yanzu bata iya takasu kuma hakan ya ja mata zazzaɓi har sai da Imran ɗin ya saya mata magani.
Bayan sunyi sallama ne ta shiga toilet ta yi wanka tare da yin shirin barci ta kwanta, shi ma Imran ya wuce ya je ya yi wanka ya yi shirin barci sannan ya wuce izuwa ɗakin Lion, daidai lokacin shima Lion ya yi wanka ya shirya karfe tara da rabi a lokaci.
Hayewa saman bed Imran ya yi yana karewa Lion kallo, ba ƙaramin kyau kayan barcin suka yi mashi ba, launin ash color mai haske ne, shi dai yana son abu mai haske sosai, haka kamshi ma ba sai na kara gaya maku ba, mayen son kamshi ne na bugawa a zarida.
Zama ya yi a gefen bed ɗin tare da jawo laptop nasa sannan ya gayawa Imran an turo mashi in da Jelly take amma yanzu zai bincika ya tabbbatar da gaske ita ɗin ce domin ba wani ganin ƙoƙarin su Tyrone yake yi ba a fagen iya bincike, kawai ma dan abubuwa sun sha kansa sosai ne yasa ya ce Tyrone ya yi aikin.
TOM KUN JI ABIN DA YA FARU A GIDAN LION BAYAN DAWOWARSU, YANZU MU KOMA CIKIN LABARI.
Jin ringing na wayarsa ya sa Imran ya ɗan miƙe daga kishingiɗar da ya yi yana ƙoƙarin ɗauko wayar a in da ya ɗaurata saman bedside drawer, shi kuma Lion ganin Nawid yana kira da number Ummi ne ya sa ya bibiyi waye yake kira, idan baku mance ba ya datsi wayar baki ɗaya.
Ganin Nawid ne yasa Imran ya ɗauki call ɗin yana faɗin "Dr lafiya kira da daren nan haka?".
A hanzace Nawid ya ce "Prof wani taimako nake son ka yi Mani" duk abin da suke faɗe Lion yana jinsu dan ya gano cewa Imran Nawid ya kira, abin kuma ya ba shi mamaki ganin Imran ya san Nawid amma kuma bai san cewa yarinyar da yake nema tana tare da Nawid ɗin ba, zuba masu ido Lion ya yi dan ya ji karshen zance, yana son ganewa shin da gangan su Nawid suka saceta ne ko yaya, idan da ganganne to yana da kyau a hukunta su.
"Dr wace iriyar taimako ne? Ka faɗa ina jinka". "Prof wata matsala muka samu a gida, yanzu dai na kawo maka kanwata da zan aura please ka fito ina ƙofar gida, ka zo ka karɓeta ka haɗata da Heartbeat su kwana zuwa da safe idan mun gama settle na problem na gida sai in zo in ɗauketa".
Ɗan dafe kai Imran ya yi yana faɗin "Kash Dr wlh bana gida kuma Akil ma baya gida, amma ka kaita wajen ƴan uwan Abbo ko Ummi mana". Shima Nawid ɗin dafe kai ya yi yana faɗin tom shikenan, da haka suka yi sallama.
Imran na ajiye wayar ya juyo da kallonsa zuwa kan Lion dan ya tambaye shi ko Jelly'n ne aka gane, wani irin razana ya yi sakamakon idanunsa da suka sauƙa cikin dara daran blue eyes ɗin Lion, idanun Lion sun tsorata shi sosai, bai yi tunanin Lion na ganinsa ba, kuma abun da yasa ya kara tsorata Lion ya tsare sa ne da idanun nasa alamar kamar yana karantarsa, ya kuma ɗan zaro idanun nasa, kuma kunsan idanun Lion da daddare suna kyalli, shiya kara tsorata Imran.
"Prof kwata kwata brain naka sai a hankali". Shine abin da Lion ya faɗa, juya idanu Imran ya yi yana sauƙe ajiyar zuciya dan ya tsorata ainun.
Mai da kallonsa kan laptop nasa Lion ya yi, almost 5mins sannan gently ya ce "Ka sake kiran wannan friend ɗin naka da kuka yi waya yanzu ka ce ya kawo maka yarinyar nan ta kwana".
Tun da Imram ya ji Lion ya faɗi haka jikinsa ya bashi Jelly ce, wani irin zabura ya yi bawan Allah jikinsa har kerma yake yi wajen ɗaukar wayarsa ya fara kiran layin Ummin, sai dai ina wayar bata shiga, ba network, kamar zai yi hauka ya diro kasa daga saman gadon zai nufi waje, dakatar da shi Lion ya yi tare da ce mashi ya sake kiran layin.
Sauri sauri ya sake kira, kira ta farko number ta shiga, ringin biyu ta yi Nawid ya ɗauka, tsabar sauri Imran har haɗe words yake yi wajen gaya mashi unguwar da zai zo ya same shi ya kawo yarinyar, to Nawid ya amsa mashi da shi sannan suka yi sallama.
Zarya ya fara yi a cikin ɗakin yana haɗa zufa, girgiza kai Lion ya yi yana yiwa Imran kallon mara hankali mara sanin ciwon kai, daga haka ya kashe laptop ɗin tare da karisa hayewa saman bed ɗin ya kwanta ya bi lafiyar