Showing 267001 words to 270000 words out of 355604 words
wlh bata isa ta fitar da mu cikin matsala da damuwa ba idan muka shiga, so ka yi abu saboda Allah, domin Allah shi kaɗai ne mai cetan bawa daga wata wahala ko bala'in, haka zalika idan ka yi addinin musulunci saboda Allah zaka shiga gidan aljanna, gidan da babu mai iya kwatanta maka makamancin ni'ima da daɗin dake a cikinta, so duk time da ka ji cewa yes saboda Allah kuma saboda addinin ya cancanta a so shi a kuma shige shi to muna maraba da baƙoncin ka, ka natsu ka duba cancanta, ni a gaban kowa zan iya bugar kirji na ce wlh duk wanda ya fahimci addinin musulunci to yasan dole ta cancanta a shigeta kuma ayita saboda Allah, sai dai mutane marasa son gaskiya kuma ɓatattu ne za su ce bata cancanta ba".
Shiru Musharraf ya yi yana mamakin kai fin ƙwaƙwalwa irin na Michael, da ace ya jima da shiga addinin Musulunci da a yanzu ya zama babban malami, ƴaran William akwai kaifin ƙwaƙwalwa sosai gifted su.
KUYI HAKURI DA KIRAN SU DA JAMES DA MICHAEL DA NAKE YI WATA SAIN, SABODA HAR YANZU AKWAI WAYAN DA IDAN NA KIRA SUNAN SU NA MUSULUNCI BASA GANE AKAN WAYE MUKE YIN MAGANA, SHIYASA NAKE SHIGO DA SUNAN SU NA KAFIRCI, AMMA A HANKALI HANKALI ZAMU ZAME SUNAN KAFIRCI MU BAR NA MUSULUNCI IDAN JAMA'A SUN SABA DA NA MUSULUNCI FATAN KUN FAHIMCE NI!!!.
"Ɗaya daga cikin sojojin ne ya sake cewa "Sir ni na yarda har ga Allah wannan addini yana da kyau, domin yau shekarata 8 ina tare da ku, na san da cewa duk abin da kuke yi mai kyau ne, baku kula abin da babu kyau, so ina da kyakkyawar yaƙinin cewa tun da ka shiga wannan addinin to tabbas shine addinin ƙwarai, dan haka nima zan shiga..."
Da sauri Robertson ya tari numfashin sa da cewa "Sir nima zan shiga saboda Allah ɗin".
Sosai Michael (Aseef) ya shiga matsanancin farincikin, da sauri ya karisa wajen da suke ya rungumosu yana faɗin "Alhadulillah Alhadulillah Allah ya kuɓutar da ku daga duhu zuwa haske, Allah ya nufe ku da rahma, na yi maku murna sosai, uncle Musharraf ka basu kalamar shahada".
To Musharraf ya amsa da shi tare da matsowa in da suke, su kuma saura biyun sai nazari suke yi akan hakan, da alama ba su yarda ba, amma kuma sun sha mamakin ganin yau Aseef (Michael) ya rungumi sojoji biyun nan, suna jin suma kamar su karɓi Addinin amma sai kuma sheɗan yana zuga su.
Ɗaga kai Aseef ya yi ya dubi cameran dake a cikin kitchen ɗin ya ce "My Lion mun sami karuwa a addinin Musulunci, Allah Alhamdulila" ya kai karshen maganar tare da juyowa ya kalli biyun da basu karɓi musulcin ba. Ba kyama ba cutarwa dan ba su musulta ba, cikin mutunta juna ya ce "Tese zo ka nuna mani yadda ake kunna gas ɗin nan, kai kuma Iron ka kawo mani pot bari na ɗaurawa uncle ruwa, dan na ji ya ce da ruwa ake dafa shinkafar, am very happy yau zan ci African food".Ya kai karshen maganar yana murmushi.
Sun kasa motsawa sun tsaya tare da sunkuyar da kansu kasa suna mamakin abin. Cikin sauri Aseef ya matso kusa da su tare da riƙo hannayensu yana faɗin "Iron lafiya? Me ya faru kuma na ga kun tsaya kuna sunkuyar da kan ku ƙasa?".
Cikin girmamawa Iron ya ce "Sir all my though zaka bamu punishment ne, zaka tsane mu dan mun ki karɓar addinin da ka kawo mana, a tunani na zaka sanya a...." Bai kai karshen maganar ba Aseef ya ɗaura ya tsaya ɗaya a saman ɗan ƙaramin bakinsa yana faɗin
"Shiiiiiiiiiii ya isa haka, me yasa zan wahalar da ku? Addinin musulunci addini ne mai sauƙi, addini ne wadda bai hana kowa ya yi addininsa ba, bai takurawa kowa ba, hasalima addinin musulunci ne kawai ya bawa kowa dama ya yi abin da yake son yi dan gane da addininsa matuƙar ba zai ci zarafin wata addini ba ko kuma abin da suke amfani da shi wajen yin addininsu, ni ba zan ki ku ba, ba kuma zan baku wahala ba, domin na san shiriya ta Allah ne, kuma addinina mai sauƙi ne tare da kamala, addinina ya bani dama na kyautatawa makwabcina ko da kuwa kafuri ne, so banga dalilin da zai sa na ki ƙu dan kun ƙi addini na ba, yanzu dai ku kawo mani abin da na ce maku, kada ku damu ina kaunar ku kamar koda yaushe".
Hawaye Iron ya fara yi yana faɗin ya yarda zai karɓi musulcin saboda Allah kuma saboda kyawun addinin, farinciki a wajen Michael da Musharraf ba'a magana, a tare suka basu kalmar shahada suka karɓa suna masu yaƙini mai kyau da kuma yi wa addinin kyakkyawar za to.
Suna tsaka da wannan farinciki uncle Herry ya faɗo cikin kitchen ɗin a ruɗe yana faɗin "Michael where are you? Naje ɗakin ka baka nan, na zo zan wuce na hangoka a nan, what are you doing here?".
Hankali kwance Aseef ya ce "Uncle what is happening? Na ganka a ruɗe" "Michael since yesterday Tyson (TGA) bai dawo ba, mun kira number sa a kashe".
Jinjina kai Aseef ya yi yana faɗin "Okey uncle go into your room zan kira Lion a kan hakan".
To uncle Herry ya amsa da shi tare da ficewa daga ɗakin, hankalinsa a tashe kwata-kwata bai ma lura da wayan da suke a cikin kitchen ɗin ba ya fita kawai.
aikin gabansa kawai Aseef ya cigaba da yi yana ƙoƙarin ɗaura ruwa a pot, dan Robert ya kunna mashi gas ɗin.
Ganin hakan ya sa Musharraf ya ce mashi ya je ya kira Lion ɗin mana, girgiza kai ya yi yana faɗin "I can't go anywhere uncle, kyalesu ina da tabbacin koma a ina yake Lion ya sani, Allah yasa ma shine yasa aka ɗauke shi zuwa headquarter aba shi jikinsa da wahala da kyau".
NI KUMA NA HAƊA KAYANA TARE DA AJIYE ALKALAMI NA SAI ALLAH YA KAI MU GOBE!!.
💖💖TRIPLETS💖💖
E 71-72
Ganin hakan ya sa Musharraf ya ce mashi ya je ya kira Lion ɗin mana, girgiza kai ya yi yana faɗin "I can't go anywhere uncle, kyalesu ina da tabbacin koma a ina yake Lion ya sani, Allah yasa ma shine yasa aka ɗauke shi zuwa headquarter aba shi jikinsa da wahala da kyau".
Shiru Musharraf ya yi suka cigaba da aikin da suke yi, su Iron sun tsaya suna kallon ikon Allah, har yanzu mamaki bai sake suba, yau ɗaya daga cikin TRIPLETS ne a Kitchen, kai abin ya yi mugun basu mamaki wadda ba za su taɓa mancewa ba.
Aseef ne ya ce masu su zo su haɗu su yi aiki a tare mana, tunda yanzu sun zama friends, har suna haɗa baki wajen maimaita sunan friends, ɗaga masu kai kawai ya yi alamar e friends, da sauri suka matso suka sanya hannu su ka fara aiki a tare.
Kasa jurewa Aseef ya yi, baya son warin abubuwan da Musharraf ke zubawa a girkin, ji yake yi tamkar zai yi amai, bai taba zama a wajen da ake yin girki ba, ga shi kuma baya son Musharraf ya fahimci cewa yana kyamar abincinsa, da kyar yake jan numfashi, har wani canza launi idanuwansa suka yi saboda bakar wahalar da yake sha ta sanadiyar rashin jan numfashi da yake samu.
Cikin dakiya ya ce "Uncle who teach you how to cook?".
Musharraf yana ƙoƙarin juya kayan miyar dake soyuwa ya ce "Na yi makaranta ai, a school na koyi duk wayan nan abubuwa".
Kasa sake yin magana ya yi saboda wani irin amai da ya zo mashi, da sauri ya nufi waje har yana yaɗawa da gudu, kai tsaye bedroom nasa ya nufa, yana shiga ya wuce toilet, amai ya fara shararawa kamar ba gobe, yana yi yana dafe cikinsa saboda yadda take murɗa mashi ba kaɗan ba, nan take zufa ta fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa.
Shi kuma Musharraf bai ma lura da lokacin da ya fita ba, sai juyawa kawai ya yi yaga baya nan, bai kawo komai a ransa ba, sai ya ci-gaba da aikinsa kawai.
Sosai ya yi aman nan har sai da ya sami sauƙi sannan ya sakarwa kansa shower dan ya yi wanka kila ya ɗan sami sassaucin abin da yake ji a cikin zuciyarsa da kuma jikinsa baki ɗaya.
Bayan ya yi wankar ne ya fito ya shirya cikin wando three quarter baki da yar riga mara nauyi, mayukansa ya shafa tare da perfume nasa sannan ya nufo waje.
Yana fita ya wuce ya sanar da sojijin dake gyara masu bedroom nasu akan suje su wanke mashi toilet nasa tare da gyara bedroom ɗin, cikin girmamawa suka amsa da okey sir, sannan ya wuce izuwa ɗakin daddy, yana son komawa kitchen ɗin amma ya kasa dan saboda ba zai iya sake jin wannan wari na su kayan miya da sauransu ba.
Kwance ya isko daddy har lokacin hira suke yi da Areef, daddy ya yi ya yi akan su yi video call amma Areef ya ki yarda saboda yasa cewa idan daddy ya ganshi hankalinsa ba ƙaramin tashi zai yi ba, zai iya ja ma ciwonsa ta tashi, ga shi kuma basu kusa.
Saman bed ɗin ya haye tare da kwanto da kansa saman cinyar daddyn yana kallon Tv, a hankali daddy ya fara shafa kyakkyawar brown hair sa tare da gangarawa har izuwa bayansa, sai faman lumshe idanu yake yi tamkar mai jin barci, a ɓangaren daddy kuwa yana matukar jin kaunar ƴaƴan nasa kamar ransa.
Sun kwashi 1 hour bayan shigowa Aseef ɗin kenan suna waya da Areef, daga karshe suka yi sallama daddy ya miƙawa Aseef wayar, karɓa ya yi tare da gyara kwanciyarsa a jikin daddyn nasa ya kara wayar a kunne suka fara hira da Areef ɗin.
Suma sun jima suna hira kafin ya ce anjima zai kira shi yanzu zai je ya ci abinci ne, da haka suka yi sallama ya miƙe daga kwanciyar da ya yi yana faɗin "My daddy am coming".
Yana ƙoƙarin sauƙa daga gadon daddy ya riƙoshi tare da manna mashi kiss a goshi yana faɗin "I really love you my son" kayatatcen murmushi ya saki kafin shima ya yi wa daddy kiss a kumatu sannan ya diro kasa daga saman gadon ya fito waje.
Kai tsaye palon kasa ya nufa, wani irin fitinannen kamshi air freshener ne ke tashi a palon, da alama Musharraf ya kammala girkin da yake yi kenan, domin dama haka dokar gidansu yake, idan an kammala girki sojijin nan za su tattare ko'ina sannan su feshe ko'ina da turaren da ya dace da shi, su mai da komai mazauninsa, na wankewa su wanke na gogewa su goge, shiyasa a koda yaushe komai na gidansu yake kasan cewa tamkar ba'a taɓa taɓa su ba, kai ka ce sabbine daga ledarsu aka fito dasu saboda tsabar gyara da kula da suke samu.
Ba kowa a palon da alama Musharraf ya wuce part nasu dan dama bai cika zama a palonba, saboda takurawar da Tga yake yi mashi.
Juyawa ya yi izuwa part nasu, da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin palon nasu.
Saman table ya hango Musharraf yana zaune yana cin abinci, ya yi wanka ya canza kaya, ba ƙaramin kyau ya yi ba abinsa.
Karisawa saman table ɗin ya yi ya zauna yana faɗin "Uncle sorry na barka kai kaɗai ko?" Murmushin ya yi kafin ya ce "My Aseef don't worry".
Hannu ya kai ya karɓi spoon dake a hannun Musharraf ɗin tare da ɗibar abincin ya kai bakinsa, wani irin yanayi ya ji tare da danasanin kwatantawan da ya yi, ba tare da ya tauna abincin ba ya haɗiye tare da ajiye spoon ɗin ya yi maza ya ɗauki glass cup dake cike da ruwa dake a gaban Musharraf ɗin.
A zafafe ya kafa cup ɗin a bakinsa yana shan ruwan, sai sorry Musharraf yake ce mashi, to kawai yake amsawa da shi, jiki ba kwari ya miƙe ya nufi saman sofa ya kwanta yana faɗin "Uncle get ready fa on Monday zaka tafi Nigeria wajen JAMES".
A zafafe Musharraf ya ɗago yana kallon shi. "Aseef an gane James ne?" Jinjina mashi kai ya yi alamar e an gane shi, ajiye spoon dake a hannunsa ya yi tare da miƙewa ya sauƙa daga saman table ɗin ya tsunguna ya yi wa Allah sujudur shukur, dan nuna godiya da farincikinsa ga Allah subhanahu wata'ala.
Bayan ya ɗago sosai ya yi wa Areef addu'a tare da fatan Allah ya tsare shi a duk in da yake, sai amsawa da Amin amin Aseef yake yi.
Bayan ya kammala ya koma saman table ya cigaba da cin abincinsa yana ayyanawa a ransa ya zama mashi dole idan ya je Nigeria ya koma wajen ƴan uwansa, idan ba haka ba zai shiga matsala babba.
While shi kuma Aseef kewa kawai yake yi wa tunani, zasu barshi shi kaɗai bawan Allah. Bari mu koma Nigeria dan jin wani hali suke a ciki
GIDAN LION💖
Ya jima yana tunanin yadda zaayi ya iya kashe mahaifiyarsa da kansa, da abaya lokacin da yake kristar ne, to da sab zai iya kasheta, amma yanzu ya san mahimmancin iyaye, addinin musulunci ya gaya mashi waye iyaye, sanadiyar hakan nema har ya fara tunani a ransa zai iya yafewa mummy ɗin tasu, amma yanzu kuma ta yi laifin da idan ya tabbata hakan ne, da gangan ta aikata hakan, ba kuskure ko wani abu makamancin haka bane, to dole ne akasheta kamar yadda za'a kashe kowa dake a cikin kungiyar, babban matsalar shine yau ita ce rana ta farko da ya fara shiga damuwa dan yayi tunanin zai kashe wata, abin yasa shi ya ji kwata-kwata bashi da wata kuzari, amma kuma abin mamakin duk da wannan laifi da Josephine ta aikata, ta fi daddy samun waje a zuciyar Triplets, why basa son daddy? Daurewa kawai suke yi suke bashi kulawa kamar yadda addinin musulunci ya koyar da su, amma ba wai dan suna jin kaunarsa a cikin zuciyoyinsu ba.
Kyawawan fararen kafafunsa ya fara zurowa kasa kafin ya muƙe zaune yana kallon ɗakin, har lokacin idanunsa ba su koma daidai ba, sun yi jawur da su, tunani yake yi me yasa komai zai faru sai dai ya faru da Areef ko Aseef? Me yasa shi basu tunkararsa da ire-iren hakan? To menene banbancinsa da su Areef ɗin? Bayan kuma tare suka zo duniya, ɗan gara Aseef ma ace gaba ɗaya rayuwarsa ya yi tane tamkar ba mutunba, saboda ciwonsa, amma Areef fa? Abaya tare suke yin komai, lokacin da suke zuwa school tare suke komai, kaya iri ɗaya, karatu tare suke yi, abin da ya karanta shi Areef ya karanta, karatun addini tare suka yi, bincike akan addinan gaba ɗaya har suka fitar da na gaskiya a tare ne, to me yasa shi duk ka irin wannan abin ake tsoron tunkararsa da shi?.
Ya jima a hakan kafin ya miƙe ya nufi toilet dan ya yi wanka da ruwa mai zafi sosai ko zai sami kwarin jikinsa.
Bayan ya yi wanka ya fito sake shiri ya yi cikin pajama sky blue a wannan karon kam ya ɗaure gashin kansa ya bar wannan guntu na gaban goshin kawai.
Yana kammala shiri ya fito ya nufi kasa wajen Areef, kwance ya isko shi yana latsa wayar tasa.
Gefensa saman bed ɗin ya zauna tare da ɗan janye lallausan bargon da ya rufe jikinsa zuwa wuyarsa da shi, zubawa kirjinsa wajen ciwon nan nasa wayan nan dara-dara blue eyes ɗin nasa ya yi, shima Areef ɗin zuba mashi Ash eyes nasa na ƴan mintoci ya yi kafin ya ce "What is wrong with my blood?".
Kallon gefen ido Lion ya mashi kasa kasa a nutse ya ce "Au zaka gwada mani aiki ne?" Ƴar murmushi Areef ya yi kafin ya ce "Ni na isa in gwada maka aiki ne? Kawai dai naga kana cikin damuwa ne yasa na tambaya, amma ai ba batun na gwada maka aiki, ban kai nan ba".
Shiru Lion ya yi mashi na ƴan mintoci kafin gently ya ce "What is G.M.A?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya fara magana.
"G.M.A lokacin da na fara cin karo da ɗaya daga cikin members na kungiyar, a lokacin na kashe shi, yadda kuma akayi na gane, wani aiki naje to bayan na gashe waƴan da zan kashe zan bar wajen kenan sai a ka harbo mani bullet ɗin nesa, da alama suna kallona daga nesa, Allah ya tsare bullet ɗin bata same ni ba sai ta sami mutumin ɗin a kafa, ya faɗi kasa yana kuka, da sauri na karisa wajen sa, a maimaƙon naga jini na zuba daga wajen da aka harbe shi, sai naga wani farin ruwa ne yake zuba, abin ya ɗaure mani kai, sake harbin bullet da akayi ne yasa na ƙira hukumarmu akan su harbi koma waye ke mana harbin nesan nan, haka kuwa akayi suka harbesa, kasan CIA ko bata je waje ba muddin ɗaya daga cikin ma'aikatan ta za su je waje to tabbas kamar suna wajen ne, suna iya ganin komai. Bayan sun harbi mutumin nan ni kuma na fara binciken sauri akan waddake a gabana, daga karshe dai na ɗaukesa muka je cikin daji na yi bincike akan ya akayi farin ruwa yake fita a jikinsa a maimakon jini, a nan ne na gane cewa member ne daga cikin G.M.A abin ya ɗaure mani kai, ban ɓata lokaci ba waje kashe shi a wajen na tafi na bar gawar, daga nan sai na fara bincike akan suwaye su, a ina kuma suke? Me suke aikatawa? A nan ne na gane kungiya ce ta shan jini wadda ke a cikin New York, sai dai har yanzu na kasa gane a ina ɗaya taka maimai kungiyar take".
Shiru ya ɗan yi yana mai da numfashi. Jinjina kai Lion ya yi tare da ɗaukar wata ƴar karamar na'ura ya dasawa Areef ɗin a kirjinsa daidai wajen ciwon nasa, ƴar kara Areef ɗin ya yi saboda azaba.
Miƙe wa Lion ɗin ya yi ya fara haɗa abubuwan da zai buƙata, da yake Lion in dai fagen aikin likitoci ne to ba baya ba, ya kware sosai kamar babban likita, domin zance ma kusan ya karanci