Showing 282001 words to 285000 words out of 355604 words

Chapter 95 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2819

ya gado dukka biyu, Abban su Imran ya fi kowa zuciya a cikinsu, yana da zafi idan ka taɓo shi, shine ya fi gadan kakansu da kuma babansu, sanadiyar auren Ammie ya zama haka, wadda Allah ne kaɗai yasan sanadiyar sauyawarsa lokaci guda haka, amma idan kuka cigaba da bin alkalamin princess Teema zaku ji komai har ma da tarihin Abba, a nan ne zaku gane yafi kowa zuciya a cikinsu, daga Abba a zuciya sai Hosain, wadda shima yana da bala'in zuciya sosai, laifi suka yi mashi yasa ya tafi ya bar masu gidan ya yi zuciya bai sake waiwayarsu ba, bayan shi kuma sai Abbi, Abbi ma akwai zafi idan ka taɓa shi, daddyn Jelly ne kawai mai ɗan sanyi a cikinsu, amma Hajiya Batula ma ba baya ba wajen zuciya, shiyasa yaranma suke da zuciya sosai, Akil shine ya ɗauki rabi daga zafin zuciyar Abba, shi kuma Imran irin daddyn Jelly ne, Irfan kuma irin Abbinsa.

"Wai ma tsaya shin wannan ɗin wanene?" Ommu ta tambaya tana kallon Akil da yake zaune a gaban motarsa yana jiran su Aafia su shiga ya wuce abinsa.

A fusace Abbi ya ce "Mijin Umaisha ne ko kina da magana ne? Mijinta ne kuma ƴaƴanta".

Rai a matukar ɓace Ommu ta juya ta koma cikin gida, domin taga Abbi ya hasala, ransa ya ɓaci, kuma ta san halinsa sarai idan ransa ya ɓaci tsab zai yi mata wankin babban bargo ya kuma koreta daga gidan, ta san shima ba baya ba wajen iya faɗa da masifa, hakan yasa ta shafawa kanta lafiya ta nufi cikin gida dan ta sami damar zama daram a cikin gida, yanzu ba zata yi sa in sa da shiba har sai ta gama mallake shi a tafin hannunta sannan ta fara juya shi kamar abaya.

Akil kuwa rai a ɓace ya tada motar Aafia tana ɗagawa Hanan hannu suka yi sallama, Aunty kuwa tun da aka fara wannan rigima ta wuce ɗaki abinta, saboda bata son ganin faɗar tasu.

Sai da Abbi ya ga tafiyarsu sannan ya juya tare da riƙo hannun Hanan suka wuce izuwa cikin gida.

Suna shiga palo ya sake hannun nata yana faɗin "Jeki ɗakin ku ki kwanta abinki".

Ya kai karshen maganar tare da wucewa ɗakin Aunty, yau ransa ya ɓaci sosai, Ommu na san kure hakurinsa.

A ɓangaren Irfan kuwa, sai bayan ya ji tashin motar Akil sun bar gidan sannan ya jawo wayarsa ya kira layin Akila.

Ringin ɗaya ta sanya hannu zata ɗauka, abin mamaki sai taga wayar ta ki yin picking, ta yi ta yi abin ya ci tura, daga karshe ma sai ta ga an yi rejected na call ɗin, abin ya ɗaure mata kai.

Tana tsaka da mamaki sai ga saƙo a cikin wayarta, ko bata duba ba tasan baƙon masoyinta ne wato ɓoyayyen masoyi.

Cikin sauri jikinta har kerma yake yi dan ta duba saƙon sa, a yanzu haka kawai take tsintar kanta da bala'in dakon jiran saƙonsa ko kiransa, tana matukar son jin voice nasa, musamman idan yana cewa heartbeat tamu, abin ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, tamkar dan bakinsa akayi sunan heartbeat, ya iya kira sosai.

"Sorry my angel ba zan iya bari ki ɗauki waya a yanzu ba, ki yi hakuri sai kin je gida kin ji ko? Idan anje gida sai ayi hira da yaya Irfan ɗin". Shine abin da wanann saƙo na ɓoyayyen masoyin nata ya ƙuntsa.

A hankali ta tsinci kanta da furta "To ai kaima ina son jin voice naka!". Ta yi maganar tana turɓune fuska irin na shagwaɓa tare da turo baki.

Da haka suka isa gida, bai sake yi mata saƙo ba kuma bai kira ta ba.

A kofar gida Akil ya sauƙeta tare da tsayawa yana kallonta har sai da ta shiga cikin gida sannan ya juya kan motarsa zuwa gidansa.

Ita kuma tana shiga cikin gida kai tsaye ɗakin Ammie ta wuce, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin ɗakin, Ammie na kwance saman bed nata.

Jin sallamar ƴar tata ɗaya tilo a mata yasa ta miƙe zaune tana faɗin "Akila ya naga kin dawo? Ba Akil ya ce Abuja kuka tafi ba? kuma kwana zaku yi".

Gigiza kai Akila ta yi tare da tafiya da gudu ta faɗa jikinta tana dariya.

"Lafiya dai ko Akila?" Ta kasa magana dariya kawai take yi, haka kawai idan ta tuna yaya Irfan ko saƙonnin baƙon masoyinta sai ta fara murmushi, a zahirin gaskiya kuma a ganinta Yaya Irfan take so, shi kuma baƙon masoyi yana burgeta ne kawai, kuma voice nasa yana yi mata daɗi, sannan kuma a matsayin aboki kawai ta ajiye shi duk da bata san waye shi ba.

Yar hira kaɗan suka yi da Ammie sannan ta wuce ɗakinta, wanka ta fara yi tare da shirin kwanciya sannan ta haye saman bed nata bayan ta yi alwalar barci kenan.

Tana kwanciya ta jawo wayarta ta fara kiran layin Irfan.

Bugu ɗaya ya katse ya kirata, jujjuya fararen idanunta ta yi tamkar tana a gabansa.

"Matar Mijinta kun isa gida lafiya?" Ya yi maganar da murya tamkar mai jin barci.

Nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "Lafiya lou mijin matarsa, daga ɗan dawowa na har na fara kewarka mijina".

Shima nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Heartbeat wato dai a waya za'ayi mani hira har da kirana da miji amma a fili sai ayi ta rufe mani fuska ko?".

Ƴar dariya ta yi irin na soyayya mai cike da salo na jan hankali, cikin shagwaɓa ta ce "Kai ko yaya Irfan ka fara kenan?".

"Ba wani zancen na fara kenan, gaskiya ce na gaya maki ai, tukun nan ma ba wannan ba me yasa tun ɗazun ina kiran wayar ki bata shiga?".

Mamaki ne ya bayyana akan face nata, to me yasa zai ce wayarta bata shiga bayan kuma ita a kunne wayar tata take, kuma akwai Network. Nan take kalaman baƙon masoyinta ya fara yi mata yawo akunne na cewa gaba ɗayanta tana karkashin sarrafawarsa da kuma kulawar shi ne, ba iya wayarta ne kawai yake a ƙarƙashin kulawar shi ba, har ita kanta, kenan babu wanda ya isa ya kira wayarta har sai idan baƙon masoyinta ya so? Kenan idan baya son ta yi magana da mutun zai iya hana wa? To wai ma waye shi? Wannan ko a aljanunma ya cika tantiri. BABBAR MAGANA HEARTBEAT ALLAH YA KUƁUTAR DAKE.

Jin ta yi shiru ne yasa Irfan ya ce "Heartbeat ya kika yi shiru?" Nisawa ta yi kafin ta ce "Sorry yaya Irfan ina kallon wani abinne ya ɗauke mani hankali".

Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce "Tom Shikenan, amma banso kuka koma gida a yau ba, na so gobe da safe na fara yin karin kumallon safe da kyakkyawar face ɗin matata".

Cool murmushi ta saki kafin ta ce "To amma zaka zo gobe ai na ganka ko?".
E ya amsa mata da shi sannan suka cigaba da zuba kalaman soyayya son ransu, sai faman birkita bawan Allah take da salon soyayya da kuma shagwaɓarta, duk ya susuce mata sai zuba mata kalaman da shi kanshi bai ma san ta ya suke fita daga bakinsa ba, bai san yaushe ya iya su ba.

Misalin karfe 10 daidai wayar tasu ta katse kit kamar an ɗauke wutar nepa, mamaki ne ya kamata suna tsaka da macewa juna suna zuba love amma waya ta katse, ƙoƙarin sake kiran shi ta yi, amma ina wayar a kashe yake nuna mata, shima ya yi ƙoƙarin sake kiranta, shima abin da yake nuna mata shi yake nuna mashi, wato dai wayoyinsu a kashe.

Jin wayarta a kashe ne yasa ya ajiye wayar tasa ba dan ya so ba ya jawo bargo ya rufu ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.

A ɓangaren ta kuwa tana jawo bargo wayar tata ta fara kara.

Daga ta cikin bargon ta zuro hannunta wajen saman bedside drawer ta ɗauki wayar, ba tare da ta kalli number ba ta yi picking call ɗin.

Sexy voice nasa ta ji yana cewa "Ayi barci my angel, hirar ta isa haka, yaya Irfan ɗin nan naki yana bani tausayi, ni ma dai ina bama kaina tausayi, so good night". Yana kai karshen maganar ɗif ya kashe wayan ba tare da ya jira amsar ta ba, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da zuro hannunta ta maida wayar saman bedside drawer ta ajiye tare da lumshe idanuwanta tana tunanin duniya.

A ɓangaren daddyn Jelly da Ayla kuwa, tun da ta kai mashi abinci baya nan sai ta cire hijabin jininta ta zauna saman bed tana jiran shi.

Bai dawo gidan ba har sai 10 na dare, lokacin da ya dawo already ta yi barci, kuma bata haura saman bed ɗin ba, sai ta kwanta a baki bakin gadon, da alama ba da niyar barci ta kwanta ba, barcin ne kawai ya sawwareta.

Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa gefa tare da ajiye kayan dake hannunsa a kusa da kayan abincin da ta kawo masu, wani irin mugun tausayin tane ya dira mashi a ransa, nan take idanunsa suka sauya launi.

Kayan jikinsa ya fara ragewa kafin ya wuce toilet dan yin wanka.

Wanka ya yi ya fito ya shirya cikin kayan barcinsa masu kyau da tsada, sai tashin fitinannen kamshi yake yi, ya yi wani fresh da shi, a daren nan face nasa ta yi wani fayau haka kamar bashi da lafiya, ƙara gudun Ac ya yi tare da feshe ɗakin da air freshener.

Bayan ya kammala komai ya kariso kusa da ita ya zauna ta gefenta tare da jawo ledojin da ya shigo da su.

Ɗayar ledar wadda ta kasance karama daga ciki, ita ya fara buɗe wa, kyakkyawar waya ce kirar Iphone 15 a cikinta, ciro wayar ya yi daga cikin kwalinta sai ɗaukar ido take yi.

A nutse ya miƙe ya je ya sanyata a charji sannan ya kashe wutar ɗakin tare da kunna hasken wayarsa.

Hannu yasa a hankali yana tashinta daga barcin, cikin natsuwa yake kiran sunanta, da alama gaba ɗaya jikinsa a mace yake yau. Da yake ta sanya a ranta shi take ji, sai ta yi saurin tashi, jawota jikinsa ya yi yana mata magana kasa kasa a kunne.

Bai kyaleta ba har sai da ya tabbatar ta fita daga magagin barci idanunta sun buɗe, sannan ya kyaleta tare da bata umarnin akan ta sauƙo suci abinci.

Ba musu ta sauƙo, da kansa ya zuba masu abinci ya kuma ciyar da ita sai da ta ƙoshi sannan shima ya ci kaɗan.

Bayan sun kammala ne, ya ɗauko leda guda ɗaya daga cikin wayan da ya shigo da su ya miƙa mata yana faɗin "Ga sadakinki baby, ban so baki kuɗi ba, akwai abin da naso baki a matsayin sadaki, amma dole tasa na baki kuɗi, but ban fasa baki wannan abin da nayi niyar ba, amma sai mun koma Kano".

Kamar dai kullum da to ta amsa da shi tare da buɗe ledar, sababbin kuɗaɗe ne rafa rafa 500k ne cif cif, da yake ita bata san kuɗi dayawa haka ba, sai bata iya gane naira nawa bane ciki, dan haka sai ta mai da kuɗin cikin kedar kawai tare da miƙa mashi ta ce babu abin da zata yi da shi ta bashi kyauta bata so.

Murmushi kawai ya yi tare da karɓa ya ajiye a gefe sannan ya jawota cikinsa suka miƙe suka hau gado bayan ya tattare wajen da kansa kenan.

Suna kwanciya cikin salo ya fara wasa da ita kamar yadda suka saba, kamar dai kullum duk abin da ya yi mata sai ta mai da mashi da martani, ba ƙaramin kara haukata shi take yi ba.

Sun ɗan jima suna romancing na juna kafin daga bisani ya yi addu'ar saduwa ya shigeta a hankali, kuka ta fara yi mashi tare da kankameshi tana faɗin zafi take ji, dan Allah ya kyaleta, shi kanshi sai da ya yi mata hawaye, saboda ya san waye shi, ta yi kuka kuma shima ya yi, idan baku mance ba yana da saurin kuka ga tausayi, Musamman kuma yanzu da ya kasance da abar kaunarsa ce take a wannan hali dole ya yi mata kuka.

Duk iya ƙoƙarin da ya yi wajen ganin ya yi mata a hankali sai da ya gaza, ya kasa jurewa ya daure ya yi mata a hankali saboda wani irin ni'ima dake a gareta, hakan yasa ta ci bakar wahala a hannunsa har da suma, kuka kuwa ba'a magana, kafin ta suma ta yi kuka har voice nata ya daina fita, haka zalika shima ya yi mata kukan da bai san yaushe ya fara ba.

Yana bala'in kaunarta kuma har ga Allah bai so kawar mata da budurcinta a yanzu ba, kawai dai ya bi maganar Abbi ne, ba dan haka ba da ba zai yi ba har sai ta kai 18 years da ya faɗa.

Sai bayan ya sami natsuwa ne ya sauƙa daga kanta tare da kwanciya a gefenta, yana kwanciya kuma wani mugun zazzaɓi mai zafin gaske ta rufe su gaba ɗayansu lokaci guda, ita tana sume ma amma jikinta ya yi zafin zazzaɓi kamar wuta.

Da kyar ya iya jan bargo ya rufe su, sai rawan sanyi yake yi, abin ya ɗaure mashi kai sosai, zazzaɓi lokaci guda haka, wani irin azababben ciwon kai ne ta dira mashi lokaci guda, sunan Allah ya fara ambata a zuciyarsa, ya yin da jikinsa ke kara tsananta zafi sosai, ita kuwa da yake tana sume ba zaga fahimci ya karfin zazzaɓin tata yake ba.

TO ME YAKE SHIRIN FARUWA DA SU CIWO LOKACI GUDA HAKA? KUMA CIWO MA MAI TSANANIN GASKE HAKA. TO NI DAI NA AJIYE ALKALAMI NA SAI MUN HAƊU GOBE IDAN MAI DUKKA YA KAIMU...

💖💖TRIPLETS💖💖




E75-76💖


Da kyar ya iya jan bargo ya rufe su, sai rawan sanyi yake yi, abin ya ɗaure mashi kai sosai, zazzaɓi lokaci guda haka, wani irin azababben ciwon kai ne ta dira mashi lokaci guda, sunan Allah ya fara ambata a cikin zuciyarsa, ya yin da jikinsa ke kara tsananta zafi sosai, ita kuwa da yake tana sume ba zaga fahimci ya karfin zazzaɓin tata yake ba.

Da kyar ya iya samu barcin wahala ta ɗauke shi, ba shi ya farka ba sai da hasken rana ta sauƙa mashi akan face nasa, bawan Allah ko sallah bai yi ba, abin ya ɗaure mashi kai, tamkar a mafarki ya ji abin, tunani ya fara yi wannan wace iriyar barci ne ta ɗauke shi haka, tamkar ya bar duniyar baki ɗaya, kuma duk abin da ya faru jiya da daddare ji yake yi tamkar mafarki ne.

Da kyar ya iya waro dara daran idanuwansa wadda har lokacin suke ja sosai, kai tsaya kan face nata ta sauƙe idanun nasa.

Har wani hasken wahala ta kara yi, ta yi wani fayau da ita, abin ya bashi mamaki yadda face nata ya yi tamkar ba ita ba.

Lallaɓawa ya yi ya maiƙe zaune tare da jan bargon jikin nasu kasa, kawar da kallonsa gefe guda ya yi cikin sauri lokacin da idanunsa suka sauƙa akan aika aikan da ya yi mata.

Jininta ya zuba sosai baiwar Allah, ɗan ciza laɓɓansa ya yi tare da yarfar da hannunsa gefe yana lumshe idanunsa alamar sam bai ji daɗin abin da ya aikata ba.

Da kyar ya iya furta "Am so so sorryyyyyyyyyy my baby" ko motsi bata yi, har lokacin tana sume.

A hankali ya zuro kafafunsa kasa ya miƙe tsaye ya nufi toilet. Good 1 hour ya ɗauka yana zubawa jikinsa ruwa mai zafi ko zai zami sassaucin abin da yake ji a jikin nasa.

Bayan ya gama ya yi wankar tsarki tare da ɗauro alwala, Alhamdulila ya ɗan sami kwarin jikinsa, ya warware, ko da ya fito bai je in da ta ke ba, jallabiya ya zura a jikinsa tare da shumfuɗa dadduma ya tada Sallah.

Bayan ya idarne ya miƙe ya iso gare ta, tsayawa ya yi ya zuba mata idanu na ɗan lokaci kafin ya wuce izuwa cikin toilet ɗin.

Jim kaɗan ya fito ya zo ya ɗauketa cak kamar ƴar baby ya nufi toilet ɗin da ita, gaba ɗaya bed sheet nasu ya ɓaci da jini.

Cikin makeken baf ɗin wanka dake a cike da ruwan zafi ya tsundumata, ruwan akwai zafi dai dan gasa jiki.

Yana sumdumata ta farfaɗo, ta kuma farka mashi da sabon kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, rarrashinta ya fara yi yana bata hakuri, ina da alama ma bata sauraron shi, kuka kawai take yi.

Da ya ga haka sai ya kyaleta ya shiga buɗa mata kafafunta ruwan zafin na ratsata, ƙanƙame shi kawai ta yi tana kuka tare da zuba mashi sambatu wadda bata ma san me take faɗe ba.

Haka ya gasa mata jikinta sosai da sosai kafin ya naɗo kayarsa a towel suka dawo cikin ɗaki, saman carpet ya kwantar da ita, sannan ya cire bed sheet dake a gadon tare da ɗauko wani ya shimfuɗa sannan ya kwantar da ita a saman bed ɗin.

Har lokacin kuka take yi mashi, sai dai kuma muryar tata baya fita sosai, muryar ta dashe sosai da sosai saboda kukan da ta sha daren jiya.

Duƙufa ya yi akan rarrashinta babu kama hannun yaro, idanunta a runtse taki buɗewa, hakan kuma da ta yi ya fi mashi, domin kuwa shima baya son ya haɗa idanu da ita, wani irin kunyarta yake ji shima.

Sun kwashi good 30mins a haka, sai rarrashinta yake yi, da kyar ya samu ta iya hakura ta yi shiru.

Haka ya rinƙa lallaɓata kamar wata baby.

Yana ƙoƙarin kiran Abbi a waya dan ya sanya Hanan ta kawo mashi kayan tea sai kawai ya ji sallamar Hanan ɗin a Palo.

Ajiye wayar ya yi tare da miƙewa ya nufi Palon, tsaye take a tsakiyar palon ga kayan abinci jere a saman katon tray dake a hannunta.

Gaishe shi ta yi ya amsa da kalma ɗaya sannan ya karɓi kayan abincin ya wuce ciki da sauri, ita kuma ta juya ta koma part nasu.

Saman carpet ya ajiye tray ɗin tare da ɗaukar tray ɗin jiya ya fitar da shi palon, already Hanan ta rigata ta tafi a lokacin, saman table dake a palon ya ajiye sannan ya koma ciki.

Tea mai zafi ya haɗawa babyn tasa sannan ya haye saman bed ɗin, saman bedside drawer ya ɗaura cup ɗin tea ɗin tare da ɗagota ya mannata da kirjinsa kafin ya ɗauko tea ɗin yana faɗin "Babyn daddy ki yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login