Showing 24001 words to 27000 words out of 355604 words

Chapter 9 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2743

ta kwashe da shi tana tafa hannu

kallon sama da kasa a cikin duhu Kausar tawa Ayla kafin tace "Ke ma a mahaukaciya kika ɗauke ni kenan?" Girgiza kai Ayla tayi kafin ta tsagaita dariyar tace "Haba Our Aunty yar lukuta, ni na isa in ɗauke ki a mahaukaciya? A'a bamu isa ba ai, kawai abun ne abun dariya, ke daga kinji cikin ki ya ɗauka yayi nauyi shikenan baki da wani case sai ki hau zuba zance mara kan gado, yanzu da kike wannan magana ma, uban wa zai bamu kuɗi, mu samu mu samu kuɗin mota mu koma wajen iyayen mu ma, tukun nan mana, kafin mu fara tunanin zuwa wani waje" shiru Kausar tayi bata sake yi musu magana ba dan gani take su duka basu hangi abun da take hango musu na kuɗin da zasu samu idan sukaje wajen GAR ba, amma ita dai koma ne tasawa ranta, sai taje wajen GAR.

"Ayla ya akayi kika fita daga daukar mutuwa?" Cewar Rimsha, Ayla za tayi magana, wani matashi ya shigo da irin Mp manyan nan, kiɗa na tashi na wakan yarbawa, ana wakar omomo maryamo ashokine lule ashokine lule.

Kamar wadda aka tsikara haka Kausar ta miƙe ta fara dikar rawa, irin nasu na yarbawa tana biye wakar, abun ku da yarba, shima matashin ajiye mp yayi suka shiga tika rawa tare da Kausar, yau Rimsha taga ikon Allah daman haka Kausar take, tirkashi, ita kam Ayla kwana biyu da tayi a nan ta saba ganin fiye da haka ma, mace da namiji suna rawa suna rungume juna haɗuwar titi rabuwar gate.

Sai wani kasa suke suna sama, Kausar da matashin nan, kamar wasu zabbi, kan kace me matar sarki ta fito daga nata ɗakin, tana karkaɗa jiki kamar kaza na karkaɗa fuka fukin ta, abun ma dariya ya bawa Ayla, yadda yau kuma matar sarki ta fito da wani sabon salon rawa na daban

Rimsha da Ayla sun shagala da kallon wannan chasun na su matar sarki, basu ankara ba sai ganin Kausar sukayi ta riƙo hannun Ayla tana faɗin "Taso ki taka mana" ba musu Ayla ta tashi dan wani lokaci idan matar sarki tana rawa, tana riƙo hannun ta suyi tare, a kwana biyun da tayi tare da su, shiyasa yanzu ta fara sabawa da rawan nasu.

Jawo Rimsha ma Kausar tayi suka riƙe hannu suna biyewa Kausar tana ta wani jijjiga su, ita kam Rimsha duk ta in da Kausar ta ja ta, bin ta kawai take kamar wani igiya, babu wani action ba komai, zololo zololo take bin ta dan bata saba ba.

Sun ɗauki 45 mins suna chashewa kafin nan, su zube kasa a wajen suna mai da numfashi, matar sarki kam bata yi rawa sosai ba, bata fi 20mins ba ta tafi ta basu wajen. Bayan sun zauna ne, matashin ya kashe kiɗan yana kallon su a cikin duhu, duk da cewa akoi hasken wata, amma ba sosai ba

"Alay yaushe mukayi baki?" Cewar matashin, yayi maganan da broken English, Ayla zatayi magana Kausar ta rigata cikin harshen yarbanci tace "Sunan ta Ayla ba Alay ba" murmushi tayo yayi kafin yace "Ba zan iya faɗa hakan ba, shiyasa nake ce mata Alay" shiru Kausar ta ɗan yi kafin tace "Okey boder daga nan zuwa ilorin akoi nisa?" Yayi mamakin jin yadda Kausar ke yarbarnci reras, dan haka sai ya kunna wutar mp sa mai bala'i haske dan yaga fuskar ta da kyau.

Sai dai kunna wutar da yayi ta ja mashi matsala, domin kuwa yana haske su, yaji duk duniya ya samu mata, tun da idon sa ya sauƙa a kan Rimsha shikenan, sai dai kuma ko da ya haska mata wutar a ido, tsawa ta daka masa da karfi wadda sai da gaba ɗayan su suka tsorata. Da sauri Ayla ta dafa ta tana faɗin "Rimsha lafiya?" Ture hannun Ayla tayi, cikin tsawa tace "Kada ku sake haska min haske a ido" Kausar ta tsorata sosai domin wanna ba muryan Rimsha bane kwata kwata, cikin sauri Kausar tayi baya, yayin da shima matashin ya kashe hasken mp nasa yana faɗin Sorry, shi da yake bai san kalar muryan Rimsha ba, sai yayi tunanin ko dai haka muryan ta yake, su kuma su Ayla already sun san yadda voice nata yake, shiyasa suka tsorata dan sunji wannan murya da tayi magana da shi yanzu dai ba muryan ta bane.

Tirkashi meyake shirin faruwa kenan, anya Rimshan gaske ce a wajen, idan ba Rimshan gaske bace, ina ta gasken take, meke faruwa da wayan nan yan matan ne? ya akayi Ayla ta riga su zuwa kauyen nan? Ya akayi ta kuɓuta daga hannun su Barbushi? Hmmm akoi cakwakiya mu dai je zuwa dan muga yadda zata kaya, tsakanin wayan nan yan mata.


💞💞TRIPLET'S💞💞





💔💔Episode 7-8💔💔


Ɗan baya kaɗan itama Ayla tayi dan ta tsorata jin yadda muryan Rimsha ta sauya lokaci guda, kallo juna suke cikin duhu, tayo kuma da bai san meke faruwa ba, sai ya washe baki yace "Alay wayan nan bakin naki da alama suna da faɗa" shiru Ayla ta masa, dan tsoron magana ma take, kada tayi wani magana kuma ya zama faɗa tsakanin ta da Rimsha.

Kausar ce tace "Boder baka bani amsa taba?" "Amsar me fa?" Ya tambaya yana kokarin tashi daga wajen "Amsar daga nan zuwa ilorin akoi nisa" hanyar fita daga gidan ya nufa yana faɗin "Babu nisa, daga nan zuwa cikin lasoju naira 200 ne daga lasoju zuwa eyankorin shima 200 ne daga eyankorin zuwa cikin Ilorin wato gari alimi 150 ne kuɗin transport kinga kuwa ai ba nisa" cikin sauri tace "A'a mu ba cikin Ilorin bama zamu shiga, a eyankorin zamu tsaya, a nan gidan mu yake" dai dai zai fita gidan yace "Naira 400 zai kai ki can ai" sosai Kausar taji daɗi, sun kusa isa gidan su.

Ita kuwa Ayla tunani take sosai a kan Rimsha menene ya sauyawa Rimsha muryan ta cikin kankanin lokaci haka, matsowa Kausar tayi ta dafa Rimsha tana faɗin "Meesha kin ji mun kusa isa gida ko?" A hankali kasa kasa Rimsha tace "Ke dai kin kusa isa gida, ni kam da saura na sosai" jin Rimsha tayi magana da normal muryan ta ne yasa Ayla matsowa kusa da ita tana faɗin "Meesha muje mu kwanta ko? Dare nayi sosai" suna kokarin miƙewa babban ɗan sarkin ya shigo cikin gidan yana wani tafiya yana bonshin wando na faɗu wa ya riƙe gefe.

Kai tsaye kitchen ya nufa yaje ya ɗauko abincin sa wanda Kausar ta ɗauka ta fara ci.

A inda tayo ya tashi a nan shima olohunwa wato ɗan sarkin yaje ya zauna tare da buɗe kulan abincin, ya zurma hannu ciki ya fara kai loma, babu ko wanke hannu.

Sosai Ayla tayi godiya ga Ubangiji da Allah yasa olohunwa ban gane cewa Kausar taci masa abinci ba. Lallaɓawa sukayi suka miƙe suka nufi wani ɗaki wanda ya kasan ce shine ma saukin su.

Babu komai a cikin ɗakin sai tabarman mai ɗan girma, da pillow guda ɗaya, sai godiya ga Allah suke, dan hakan ma ba karamin daɗi suka ji ba, domin a daular mutuwa ko taburman ma basu samu ba.

Addu'ar barci sukayi tare da kwanciya suka saka Rimsha a tsakiyar su, kasan cewar ita ce karama, dan a shekaru dukan su Ayla zata girme musu, dan ita zatayi 15 years, ita kuma Kausar 14 to 15, Rimsha ce karama mai 13 years, sai dai duk cikin su babau wacce ta fara period har yanzu, amma dukan su, sun fara kirgan dangi, Ayla kam ma har ta fara zama yan mata.

"Ayla baki faɗa mana ya akayi kika bar daular mutuwa ba" cewar Rimsha, shiru Ayla bata amsa musu ba, sake mai-mai ta tambayar Rimsha tayi, nan ma shiru Ayla bata amsa ba, hannu Rimsha tasa ta ɗan bubbuga Ayla tana faɗin "Me haka Ayla? Ki bani amsa na mana, sai magana nake, amma kinyi banza dani" shiru Ayla ba tayi magana ba, haurar da hannun ta sama Rimsha tayi tana laluɓar fuskar Ayla dan taji idon ta arufe ne ko abuɗe ne, dai-dai cikin Ayla taji wani abu kamar dutse gashi da girma kulu lu, a sukwane ta miƙe zaune tana faɗin "Ayla me a cikin ki?" Shiru Ayla ba tayi magana ba, gashi ɗakin da duhu, cike da tsoro Rimsha tace "Kausar ki taɓa cikin Ayala kiji wani abu kamar dutse" ita ma Kausar ɗin shiru batayi magana ba, hannu Rimsha ta sake kaiwa saman cikin Ayla, sai taji wayam babu komai, wannan dutsen ya ɓace, jijjiga Ayla ta fara yi da karfi tana kiran sunan ta "Ayla!! Ayla!! Ayla" cike da ruɗu da tashin hankali, dan a tunanin ta Ayla mutuwa tayi, tun da yanzu suka kwanta ba jimawa, amma ace Ayla tayi shiru kamar wadda ta mutu.

Ta kai 5mins tana jijjiga Ayla da karfi tana kuka, ga kuma Kausar ita ma kwance bata jin su, kuma bata motsi, ganin sunki tashi ne yasa ta miƙe da gudu zatayi waje, kamar a mafarki taji Ayla na cewa "Rimsha ya naji kamar kina magana?" Tashin hankali "What!!? Rimsha ta faɗa a tsorace, miƙewa zaune Ayla tayi za tayi magana, matar sarki ta shigo ɗakin hannun ta riƙe da ɗan ƙaramin fitilla irin mai amfani da battery remote ɗin nan, tazo ta ajiyewa Ayla a in da ta saba ajiye mata tana faɗin "Ya ke kuma kike tsaye" tayi maganar cikin harshen yarbanci, kasan cewar ita Rimsha bata jin yarbanci sai tayi shiru bata amsa ba, kamar a mafarki Kausar da Rimsha ke ta kira tun ɗazun tace cikin harshen yarbanci "Meesha bata jin yarbanci" shafa kan Rismha matar sarkin tayi tace "Fine girl" sannan ta wuce ta fice daga ɗakin.

Dawowa Rimsha tayi ta zauna kusa da Ayla tayi shiru tana mamaki, me yasa duk lokacin da ta tambayi Ayla ya akayi ta fita daular mutuwa sai wani abun ya gipta, kuma da alama Ayla bata son sanar da su ta yadda ta fito daga daular mutuwan, dan da farko da suka tambaye ta, tace musu sai sun huta, na biyu kuma tayo yazo, yanzu kuma gashi ta sake tambayar ta daga ita Ayla ɗin har Kausar duk sunyi kamar sun suma, basa jin komai, anya ba wani abu kuwa.

To masu karatu me kuke tunani game da Ayla, Kausar, da kuma Rimsha? Mu haɗu a comments section.

A takaice dai a wannan dare Ayla bata samu damar sanar da su ya akayi ta fita daga daular mutuwa ba, haka zalika ita kuma Rimsha bata dai na tunanin yadda akayi Ayla ta fito daga daular mutuwa ba kuma ya akayi ta kasa faɗa musu ta yadda ta fito.

Kasa barci Rimsha tayi tana tunani, su kuwa Kausar da Ayla tuni sunyi barcin su abun su, sai can tsakiya dare sannan barci ɓarawo ya ɗauki Rimsha tunani cike fal ranta.

A ɓangaren Jelly kuwa, yau gidan babu kowa, Hajiya ta tafi super market yi musu shopping, Nawid yana Katsina gidan kakanni sa, shi kuma Abbo bai dawo ba, ita ka ɗai ce zaune a palon Hajiya, tayi zaman yan bori, ta baje abun ta, kafa ɗaya can ɗaya nan, tayi ɗai-ɗai, ta tasa abubuwa a gaban ta, irin su chocolate, Ice cream, yogurt, soyayyen naman kaza, sweet da sauran su,

Gaba ɗaya ta damalmale wannan ɗan bakin nata da ice cream, har gemun ta, duk sai da ya samu ice cream sai taunan naman kaza take, ga wani cinyar kaza a hannun ta, tana ci tana kaɗa kai tare da lumshe idanun ta irin santi na ɗeban ta. Jikin ta na sanye da wandon jeans pink color da yar riga mai karamin hannu white color, ta sanya turban cap pink mai shegen kyau a kan ta.

Da sallama Abbo ya shigo palon, bata san ma ya shigo ba, dan da alama sai an mata weji, idan ba haka ba zata iya kwacewa, nama yayi daɗi baji ba gani, shi kuwa wani sanyi yaji ya ziyarci zuciyar sa, lokacin da ya ɗaura idon sa a kan ta, kasan cewar yasan Hajiya bata nan, hakan yasa ya kariso cikin palon da sauri

Kusa da ita ya zauna, a kasa kenan, har lokacin Jelly bata san da shigowar saba, hannu yasa ya ɗauki nama ɗaya zai kai bakin sa, cikin sauri ta riƙo hannun sa, ba tare da ta kalle shi ba, tana ta faman kaɗa kai alamar santi idon ta a lumshe tace "Ajiye shi" yar murmushi yayi kafin yace "Baby nine fa" "Kai waye? Nace ka ajiye shi kawai" ta faɗa, har lokacin bata buɗe ido ta kalle shi ba, "Abbon kine fa" sai lokacin ta buɗe ta kalle shi, sakin hannun nasa tayi tana faɗin "Cemin zakayi old man" zaro ido yayi yace "Daga ina yau kuma kika jiyo old man?"

Roban wani Ice cream ɗin ta ɗauko ta buɗe ta fara dumbutsan ice cream ɗin da hannu tana kaiwa bakin ta, har gemun ta duka yana shafa, cike da santi tana kaɗa kai tace "A Tv naji, wai idan mutun ya tsufa old man ake ce masa, dan haka daga yau sunan ka kenan" murmushi yayi ya sanya hannun sa yana shafo wuyar ta, yana faɗin "Idan dai kece zaki cemin old man ɗin ina so ai" a sukwane ta miƙe tsaye tana faɗin "Kwarto jama'a Kwarto" zabura shima yayi ya miƙe tsaye yana faɗin "Ina kwarton yake?!!" Da hannu ta nuna shi tana faɗin "Ga ka nan, wayyo Kwarto" tsawa ya daka mata ganin tana kokarin tara masa jama'a "Ke waye yace miki ni Kwarto ne? Tukun nan ma aina kika ji sunan Kwarto?" Turo baki tayi kafin tace "A Tv naji mana, nagani wata mata da wani mutun yazo zai taɓa ta shine tayi ihu tace kwarto ne, mai neman mata, shine jama'a suka kama shi suka masa duka, kai ma yanzu kazo zaka taɓa ni dan haka kai kwarto ne, wayyo jama'a kwarto nima kuzo ku taimake ni ku kama shi ku masa ɗan iskan duka!!" Da karfi tayi ihu, ganin da gaske take, kuma yasan halin ta, idan duniyar nan duka zai bata, bazata taɓa yin shiru ba sai lokacin da taga dama, dan haka sai ya kwasa a guje yayi cikin bedroom na shi ya banko kofa, yana mai dana sanin barin ta da suke tana kallo, yarinya sai kaifin ƙwaƙwalwan bala'i, kome ta gani a Tv ta riƙe a kwakwalwan ta, amma kuma idan aikin arziki ake koya mata bata ɗaukan komai.

Duk da ya gudu Jelly bata dai'na ihun kwarto kwarto ba, har su maman Afnan suka shigo ihu kwarto take, sai tambayar ta ina kwarton yake suke, amma Jelly taki kula su, dan Hajiya tace kada tayiwa kowa na gidan magana, shiyasa bata kula suba, ihun ta kawai take tana bubbuga kafa a kasa tana yarfe hannu.

Da dai sukaga Jelly fa kamar ta haukace sai suka kama kan su, dan daman suna zargin Jelly da taɓin hankali, to yau dai sun tabbatar, sai tsaki maman Afnan take jelly ta ɓata mata rai, yarinya ita kaɗai a ɗaki ta kama ihun kwarto kamar ba lafiya ba a cewar su.

Ita kuwa Jelly sai da tayi ihun kwarton ta mai isar ta sannan ta koma ta zauna ta ci-gaba da ɗure ɗuren abubuwan da take, idan ka ganta sai ka rantse da Allah ba itace tayi wannan ihu yanzu ba.

30mins da faruwar Abun Hajiya Turai ta dawo cikin gidan daga shopping, har lokacin Jelly na wajen da take zaune tana baje abun ta, shi kuma Abbo yana bedroom na sa kwance saman gado yana tunanin yadda zai yi, dan son Jelly na neman yi masa illa, ta ɗayan gefen zuciyar sa kuma, yana dana sanin fara yunkurin taɓa Jelly da yayi, dan yasan halin ta sai ta faɗa wa hajiya.

Haka kuwa akayi, Hajiya na shigowa ta miƙe ta nufeta da gudu, tana faɗin "Ummi kwarto ya taɓa Ni" jin haka yasa Abbo miƙewa a razane, ya diro kasa daga saman gadon nasa, yazo bakin kofar bedroom ɗin ya laɓe, ya kasa kunne yana jiran yaji me Hajiya zata ce.

"Waye kuma kwarto baby?" Hajiya ta tambaya tana ajiye niƙi niƙin kayan dake hannun ta, "Abbo mana, shine yazo yana taɓa min wuya" zaro ido Hajiya tayi, cikin sauri tace "Wani Abbo kuma?" "Abbon Nawid mana" Jelly ta faɗa tana turo baki "Abbon ya dawo ne?" Cewar Hajiya, eh Jelly ta bata amsa, miƙewa Hajiya tayi ta nufi bedroom ɗin Abbo tana faɗin "Ina zuwa ki jirani"

Nima na tattara kayana nace ina zuwa bari naje na gaida Josephine a New York sai na dawo, bye sai mun haɗu gobe.

Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .



💞💞TRIPLET'S💞💞





💔💔Episode 9-10💔💔



"Waye kuma kwarto baby?" Hajiya ta tambaya tana ajiye niƙi niƙin kayan dake hannun ta, "Abbo mana, shine yazo yana taɓa min wuya" zaro ido Hajiya tayi, cikin sauri tace "Wani Abbo kuma?" "Abbon Nawid mana" Jelly ta faɗa tana turo baki "Abbon ya dawo ne?" Cewar Hajiya, eh Jelly ta bata amsa, miƙewa Hajiya tayi ta nufi bedroom ɗin Abbo tana faɗin "Ina zuwa ki jirani"

Abbo na jin Hajiya ta nufo bedroom na sa, sai yayi sauri ya haye saman gadon sa, ya kwanta tare da lumshe ido kamar mai yin barci, har da wani yin mumfashi irin na mai barci za

Da sallama ɗauke a bakinta Hajiya ta shigo cikin bedroom ɗin, shiru Abbo yayi bai amsa mata ba, kamar mai barci, saman gadon ta haye ta zauna tana faɗin "Abbon Nawid har kayi barci ne?" Shiru ya mata bai yi magana ba, ganin haka yasa tayi tunanin ko barci yake, dan haka sai ta sauƙa ƙasa, ta fito daga cikin bedroom ɗin.

Tana dawowa palo ta tarar da Jelly ta mata aika-aika, ta zazzage mata duk wayan nan niki-nikin kayan da ta shigo da su a jaka, ta haɗe su waje guda, sai faman bubbuɗe kwalayen take, tana fitar da duk wasu abubuwa dake ciki.

"Baby me


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login