Showing 345001 words to 348000 words out of 355604 words

Chapter 116 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2825

kuma?" Nisawa ta yi kafin ta ce "Me yasa kaki ka bayyana mani kanka? Me yasa kake bawa zuciyarta wahala? Haba mana bugun zuciyata why kake azabtar da ni kuma kake ikirarin cewa sona kake yi?".

Ɗan dafe kansa ya yi yana faɗin "Nayi kuskure matata amma ki yi mani afuwa kin ji ko? Ba zan sake ba, kuma zan tura maki hotona yanzu, amma me yasa kike da tsoro haka ne? Ni mutun ne ba aljani ba kawai jiya na yi maki zolaya ne na tsakanin masoya, amma tuba nake yi Gimbiyata".

Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "To shikenan Heartbeat ɗi na, komai ya wuce amma dai ina matukar son na ganka, ka turo mani pic naka please".

"Zan turo maki amma ki yi mani murmushi tukun nan ko my pleasure?". Wani kayatatcen murmushi ne ya subce mata tare da sanya hannunta ta rufe face nata tana faɗin "Uhm Uhm yanzu dai sai da ka saka ni Murmushi ko?".

Wani irin shagwaɓe murya ya yi cikin salo mai jan hankali tare da kwarewa a iya shagwaɓa ya ce "Uhm uhm ba dole na sanya bugun zuciyata murmushi ba, kin san yadda nake ji a cikin zuciyarta idan kika yi murmushi kuwa?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a tamkar tana gaban shi.

"My heartbeat idan ki ka yi murmushi ji nake yi duniya ta tsaya mani cak, ji nake yi tamkar bana a duniyar nan, wani irin baƙon yanayi ne ke ratsa zuciyarta har izuwa gabaɗaya sassan da jini ke gudana a jikin nawa, ina tsintar kaina a cikin wani irin farinci wadda ba zai misaltu a gare ni ba, ina jin kamar an yi mani albishir ne da gidan aljanna, please my bugun zuciya keep smile kin ji ko matar Heartbeat ɗin ta".

Wani irin daɗi ta ji a cikin zuciyarta, har wani irin sanyi kamar an zuba mata kankara take ji yana ratsata, jinta take yi a sabuwar duniya, kara narke mashi ta yi suka cigaba da zubawa juna kalaman soyayya da Kauna, gabaɗaya ya sanya ta ta mance da zancen hoto, dama kuma da gangan ya yi hakan domin baya son tura mata hoton nasa a yanzu, yana tura mata zata gane shi, shi kuma ba haka yake so ba, yana so ne sai ta kamu da son shi wadda ba zata iya rabuwa da shi ba, sannan sai ya kawo mata kansa har gida su ga juna, kuma yana so ne ta so shi tsakani da Allah ba tare da ta san waye shi ba.

Ya kware wajen iya shagwaɓa da soyayya, hakan yasa yau har kukan daɗi Akila ta yi mashi, domin ya fita iya soyayya da komai nesa ba kusa ba, hawaye babbiyu yau ta yi mashi kuka, cikin sigar shagwaɓa kuma ya rarrashi kayarsa, yana bala'i kaunarta fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma akwai shi da zuciya da kishi tare da neman magana, da gangan wani lokaci yake tsorata domin yana jin daɗin yin hakan, yana jin daɗin yaga yana tsoratata tana zuba mashi kukan shagwaɓa, hakan ba karamin daɗi yake yi mashi ba.

Sai misalin karfe 1 na dare sannan ya ce ta kwanta shiru kada ta yi magana, duk abin da zai faɗa bai ce ta bashi amsa ba, ta dai yi shiru har barci ya ɗauketa, amma ta bar mashi wayarta a kunnnenta yana makale domin ta saurari abin da zai na gaya mata ɗin har ta yi barci, okey ta amsa mashi da shi sannan ta yi abin da ya faɗa ɗin dukka tare da kara jawo bargo ta shige.

Wasu shegun zafafan kalamai ya fara faɗa mata a kunnenta, yana yi yana haɗa mata da shagwaɓa, sai murmushi take yi har barci ya ɗauketa fuska ɗauke da murmushi, shiru ya yi yana sauraran yadda numfashinta ke sauƙa a hankali hankali har karfe biyu na dare, sannan ne ya kace kiran cike da begenta, bai gaji da jin muryarta ba, haka zalika wannan shagwaɓar tata baya isarsa, baya gajiya kwata kwata, ita ma ta iya soyayya sai dai ko rabin shi bata kai ba, tana bashi kulawa iya iyawarta.

Cike da kewarta shima ya kwanta tare da jawo lallausan bargo ya shige ciki, ya rufe har kansa.

A ɓangaren su Jelly da yaya Imran ma dai an sha waya har karfe 1 sannan shima ya ce ta kwanta ta yi barci dan saboda tashin asuba, yasan halinta sarai bata tashin asuba ta daɗi idan ana tashinta, amma fa shi a nashi ɓangaren da rungumar pillow ta barshi ya kwana, ta zuba mashi shagwaɓa da soyayya son ranta, ta bar bawan Allah da matse pillow domin ta jefa shi cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa.

A ɓangaren Rimsha kuwa, ba ita ta farka ba sai karfe 8 na dare, baiwar Allah ta tashi lafiya Lou sai dai ciwo da jininta yake ɗan yi mata. A hankali ta sauƙo kasa ta nufi toilet.

Wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallar mangariba da kuma isha, sannan ta shirya cikin wando da kuma riga kamar yadda ta sa ba, yau garin akwai iska da hadari da alama ruwan sama za'ayi, hakan yasa ta ɗauki jacket data ɗauko a ɗakin Imran ta sanya a jikinta ta fito palo dan ta yi magana da yaya Imran.

Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin nasa, baya nan hakan yasa ta wuce kasa dan tasan yanan tare da Areef a ɗakinsa kenan.

Sallama ta yi masu a bakin kofar, har suna haɗa baki wajen amsa mata sallamar tata tare da bata izinin shigowa, cikin natsuwa ta shigo cikin ɗakin.

Areef na zaune saman gado da gabaɗaya jikinsa, shi kuma Imsan yana zaune ne a bakin gadon, Areef ya jingina kansa da jikin headboard na gadon yana fuskartar Imran ɗin, shigowarta tasa gabaɗaya suka zuba mata idanu cike da tausayinta fal ransu.

Gaishesu ta zo ta yi kafin Areef ya yi mata alama akan ta zo kusa da shi ta zauna, shima dai Areef kallon ƴar baby yake yi wa Rimsha kamar Imran ɗin, kuma gaskiya ce yarinya ce 14 years da ƴan hayaniya ne fa ke gare ta.

Ba musu ta koma gefensa ta zauna domin tun da ta ga daddynta ya yarda da su, sai ita ma ta kara yarda da su dama can already ta yarda da su, karawa kawai ta yi a yanzu.

Ɗan kwantar mata da kanta ya yi a jikinsa Imran yana hana shi kada ya fama ciwonsa amma ina bai damu ba, shi dai burinsa kada ta shiga damuwa tunda Imran ɗin ya gaya mashi halin da take ciki na rashin lafiya na abinda Dr ya ce, shiyasa shima baya son barinta ta shiga damuwa.

Wayarsa ya ɗauko ya fara kiran layin da Aseef ya sai wa Musharraf jiya kafin ya baro Usa, bugu ɗaya daddyn ya ɗauka domin shima ya ƙagu ya yi magana da Rimshan kuma ya kira layin Areef ɗin bata shiga.

Juya kiran Areef ya yi ta koma video call, bawan Allah yana cikin jirgi ba su sauƙa ba, murmushi Areef ya sakar mashi kafin ya ce "Uncle please promise me akan ba zaka shiga damuwa ba? Na maka alkawari sai in da karfi na ya kare, amma tabbas zan bawa sister kulawa sosai".

Jinjina kai daddy ya yi yana faɗin "James in dai Rimsha a hannunku take kai da Imran, to ba zan taɓa shiga damuwa ba". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Uncle just call me Areef not James, ni musulmi ne, amma kada ka bari kowa ya sani a gida, a baya ma abin da ya sa ban gaya maka ba, ina tunanin zaka iya gaya wa wani ne, ciki kuma har da Aseef a lokacin, zan gaya maka dalilin da yasa bana so a san ni musulmi ne, amma ba yanzu ba, yanzu ka yi magana da gimbiyar TRIPLETS tukunnan".

Daddy bai kawo komai a ransa na sunan da Areef ya kira Rimsha da shi na gimbiya TRIPLETS ba, ya ɗauka kawai dan hankalinsa ya kwanta ne yasa ya ce hakan, dan haka sai bai wani damu ba, shi kuma Areef ya juya wayar zuwa kan fuskar Rimsha da ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa ta gefen kirjinsa ya yi.

Ganin daddynta yasa ta miƙe cikin sauri tana faɗin "Daddy daddy please ka dawo ka ji? Daddy idan baka dawo ba zan iya mutu wa, babu JEHAN babu MUMMY babu GWAGGO, ni kaɗai na saura daddy, dan Allah ka dawo mu nemo ina suke" tana magana tana hawaye.

Katse kiran Areef ya yi ba tare da ya bar daddy ya yi magana ba, rai a ɗan ɓace ya fara magana "Rimsha me yake damun ki ne? Me yasa kike son tayarwa da uncle hankali ne? Ki sani uncle yana bukatar kwanciyar hankali fiye da ke, ko so kike ki saka mana shi a cikin damuwa ne? Ki ja wani ciwon ya kama mana shi ko? To zamu ɓata dake in dai zaki rinƙa yi wa Uncle kuka, kuma ba zan sake haɗa ku a waya ba".

Hakuri ta fara bashi akan ba zata kara ba, ta tuba. "Okey ki yi mani alkawarin ba zaki sake cewa uncle wani abin da zai tayar mashi da hankali ba? Ki yi mani alkawarin farinciki zaki rinƙa sanya shi kullum?". Da sauri ta fara gyaɗa mashi kai akan ta yi alkawarin farinciki zata rinƙa sanya daddyn.

"Good to jeki ki kawo mani wayarki, sai ki dawo ku yi magana da uncle ɗin kin ji?". Okey ta amsa mashi da shi sannan ta miƙe da sauri ta fice daga ɗakin, shi dai Imran ya kasa magana domin kuwa ba ƙaramin daɗin yadda Areef yake kaunar Rimsha ya ji ba, shima a yanzu kauna na daban yake yi mata bayan jin cewa ƴar uwarsa ce, kun san Imran dama yana bala'in kaunar ƴan uwansa sosai da sosai.

Da sallama ta dawo cikin ɗakin lokacin kuma Areef ya sake kiran daddy dan su cigaba da magana da ita. A in da ta tashi a nan ta koma ta zauna, cikin girmamawa ta miƙa mashi wayar tata shi ma ya miƙo mata nasa dan su cigaba da magana da daddy, karɓa ta yi tare da kawo wa saitin fuskarta, ai kuwa zancen Areef gaskiya ce, ta ɗagawa daddy hankali har kwallah sai da ya yi, ga idanunsa nan akwai alamar kwallah a ciki.

Hakuri ta fara bawa daddyn tare da ƙoƙarin nuna mashi ta hakura zata zauna da ƴan uwanta, kamar dai yadda suka yi da Areef haka ta yi ƙoƙarin nunawa daddy cewa tana farinciki.

Shi kuma Areef ba tare da ta gaya mashi password na wayar ba, da kansa ya buɗe wayar ya shiga cikin domin ya sanya mata number daddynta, ganin uban miss call na number da aka rubuta Yaya Ahmad ne yasa ya ɗago ya kalli Imran tare da tambayarsa waye kuma Yaya Ahmad a cikin familynsu.

Sai da gaban Imran ya faɗi domin yasan halin Areef sosai da sosai, zai iya sanyawa a ɗaure A'A akan Rimsha, komai kuɗin dangin su A'A kuwa, duk da cewa kusan suke da mulkin NIGERIA a yanzu, tsab Areef zai iya ɗaure gabaɗaya familynsu, abin da su Areef ɗin sune ke juya kasar Nigeria koma ace Africa baki ɗaya, yah gwamnatin kasar su ke mulkar Nigeria da sunan an bamu ƴanci, to waye gwamnatin kuma? Ai kunga sune gwamnatin tun da kakansu ne akan mulki, to kunga a gwamnatan ce za su ɗaure A'A ɗaurin da ba zai iya fitowa ba ma kuwa.

Cikin sigar da Areef zai fahimtar Imran ya gaya mashi waye A'A me kuma ya haɗa shi da Rimsha sannan da abin da yake so a wajen ta, da yake Areef akwai kwakwalwa sosai sai bai tuhumi Rimsha akan me yasa take kula shi ba, ya yi amfani da abin da ya gani na ganin yawan miss call nasa a wayarta, which means kenan Rimsha bata ɗaukar kiransa, idan bata ɗaukar kiransa kuma ai bata damu da shi ba, idan kuma bata damu da shi ba babu so kenan.

Number A'A ɗin ya kira tare da sanya wayar a hand-free, bugu ɗaya Ahmad ya ɗauka murya can kasa kasa ya ce "Rimsha sai yau kika tuna da ni ko? Wai me na yi maki ne kike neman kashe Ni? Kin manta alkawari da ki ka yi mani ko?" Cikin yaren Hausa ya yi maganar so Areef bai fahimci me yake faɗa ba, dan haka sai ya fara magana cikin yaren English. "Hyyy man that's is not Rimsha, kanin mijijta yake magana ko kuma in ce maka yayanta zaka fi fahimta, bana son ka sake kiran wannan number a rayuwarka, ka mance da wace ce Rimsha a rayuwarka, zai fi zama maka alkhari if not zaka yi regretting zuwanka duniya".

Ita kuwa Rimsha ko a jikinta, a lokacin kuma ta gama magana da daddynta sai wani murmushi take yi, dama kunsan ba son A'A take yi ba, shiyasa bata wani damu ba dan Areef ya karta mashi warning,

Shiru A'A ya ɗan yi kafin ya ce "To ai Rimsha bata da wani yaya idan ba Imran ba, cos ba zan daina kiranta ba domin ita nake burin na aura". Yana kai karshen maganar diff ya katse kiran. Tab an ce rashin sani ya fi dare duhu, A'A ya yi abu a duhu kuwa, bai san da waye yake magana ba.

A'A yana katse kiran kuma sai ga shi ya kira number Imran, ba musu Imran ya ɗauki kiran, cikin yaren Hausa suka fara magana a in da Imran ɗin yake gaya mashi waye ne ya kira shi da number Rismha yanzun nan, wani irin mahaukacin razana A'A ya yi, jikinsa har kerma yake yi, lokaci guda ya dibirbirce ya fita hayyacinsa, sai faman haɗa words yake yi wajen magana, da kyar ya iya tambayar ya akayi wayar Rismha ta shiga hannun ɗaya daga cikin familyn William jacop, a nan ne Imran ya gaya mashi me yake gudana sai dai ya ɓoye mashi cewa Areef kawai ke son Romshan ban da Lion, ce mashi ma ya yi Lion ne yake sonta da kansa, kuma shi ya ajiyeta a gidan, tuni A'A ya yi wurgi da soyayyar Rimsha domin ya sani ba shi da yadda zai yi ya iya tunkarar Lion ba, ba zai iya ba, ubansa ya yi kaɗan, hakan yasa shi ma ya hakura da ita ya fawalawa Allah kawai, da haka suka yi sallama sannan A'A ya rubuta sakon ban hakuri na Long page ya tura ta layin Rimsha dan Areef ya gani.

Har lokacin wayar na hannun Areef yana tunanin kalar bakin hukuncin da zai yi wa A'A sai ya ga sakon ban hakuri tare da yin alkawarin ya fita harkar Rimsha har abada, guntun tsaki ya ja kafin ya goge saƙon bayan ya karanta kenan.

(OH LION YANA ZAUNE ANA TA YI MASHI KARYAR WAI SHI YA AJIYE RIMSHA A GIDAN, IMRAN ƊAN DUNIYA NE YASEEN🤣 BARI WATARANA YA JI LABARI YA DAMKESU ZA SU YI BAYANI)

Imran yana gama magana da A'A kiran Lion ya shigo wayar tasa akan ya sanya Rimsha ta kawo mashi abinci ɗaki sannan idan ya gama ta je ta gyarawa su Mark ɗakinsu aikinta ya fara daga yanzu. Cikin tashin hankali Imran ya kalli Areef in da yake gaya mashi abin da Lion ya ce kenan.

Jinjina kai Areef ya yi kafin ya ce "Ta je ta yi, a yadda Lion yake a yanzu ba wanda zai iya shawo kansa, kasan yau ne ranar da abin ya faru, ba zan iya tinkararsa ba nima, amma bari a kwana biyu, zan gwada shawo kansa akan ya hakura ya kyalata ta yi iya aikinsa kawai ban da na su Mark, ba zan yarda tana shiga ɗakin wasu ba, a matsayina na wadda aka bawa amanarta dole na kula da ita fiye da kaina, uncle ya yarda da ni ne yasa ya bani amanarta, to nima ba zan zuba mashi kasa a ido ba, yanzu dai ta je ta yi duk abin da ya ce mata, Rimsha ki je kitchen ki ɗauki abincinsa ki kai mashi, idan ya ci sai ki kwashe kayan abincin ki mayar kitchen ɗin, sannan ki je ki gyarawa su Mark ɗakinsu ko?".

A lokacin ta gama magana da daddy kenan saƙon ya iso mata, Allah ya tsare daddy bai ji ba, da zuciyarsa zata fashe idan ya ji da gaske aiki zata yi kuma harda kartin nan su Mark zata yi wa aiki.

Jiki ba kwari ta miƙe ta fito ta nufi kitchen, already abincin a shirye yake, Mark ya shirya mashi komai, sai sheki kayan da aka zuba abincin yake yi, tamkar yanzu aka fito da su daga ledarsu.

Da kyar ta iya ɗaukar abincin saboda tray ɗin ya yi girma sosai, a lokacin kuma karfe 10 ta yi.

Kirjinta sai dukan uku uku yake yi, ba ƙaramin razana ta yi ba, sai ambato sunan Allah take yi a cikin zuciyarta, aiki a karkashin irin su Lion sai da ambato sunan Allah domin a samu kwarin gwiwa.

Faɗuwar gabanta tare da bugawar zuciyarta kara ninkuwa ya yi lokacin data nufi kofar ɗakinsa, sosai ta tsananta ambatar sunan Allah da take yi.

Muryarta sai kerma yake yi yana wani sarkewa ta yi sallama a bakin kofar, shiru bai amsa ba kuma yana zaune a bakin bed nasa, jikinsa na sanye da kayan barci masu shegen kyau launin sky blue mai haske, sai latsa laptop yake yi ya ɗaure gashin kannan nasa, wannan fitinannen kamshi perfume ɗin nasa ne ya kauraye gaba ɗaya cikin ɗakin, ya yi kyau sosai tamkar shi ya yi kansa.

Ta ɗauki almost 30 mins tana tsaye tana yi mashi sallama amma kamar babu shi a cikin ɗakin, sai da ta ji zata iya faɗuwa saboda gajiya, sannan ta daure ta kutsa cikin ɗakin cike da tsoron me zai biyo baya da ta shiga babu izininsa.

Saura kaɗan ta saki tray ɗin abincin ganin shi da ta yi, a hakan ma ba fuskarsa kai tsaye ta gani ba, a'a yana duke yana kallon laptop nasa, kawai dai jikinsa ta gani ya razana ta duk da yana cikin kayan barci, ba ainahin surar jikinsa ta gani ba, kamshin perfume nasa kuma ba ƙaramin kwantar mata da hankali ya yi ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login