Showing 66001 words to 69000 words out of 355604 words

Chapter 23 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2770

bata da kwarin gwiwa iya kallon cikin idonsa ko da a mafarkin ne.

Tirƙashi babban magana, yau a ke yin ta🤔

A zafafe ta miƙe zaune a tsakiyar gadon Kausar, sai zufa take haɗawa saboda mafarkin Lion da ta yi, addu'a ta yi sosai, dan neman tsari daga wajen Allah, kullun tana yawan mafarkinsa sosai, amma bata taɓa yin irin na yau ba, kullun sai dai ta yi mafarkinsa yana zaune gefenta suna ɗan hira kuma da face mask, bai taɓa taɓa ta ba ko da sunan wasa sai mafarkin yau, abin ya bata tsoro da kuma mamaki, duk ta firgice ta yi wiki-waki da ita, dark black curly hair tan nan ya watse ya bazun mata har ta gaban fuskar ta, da kyar take iya jan numfashi.
Idan ta tuna yadda taga fuskarsa a mafarki yadda ya juyo da ita suka haɗa ido da wayan nan dara-daran kyawawan blue eyes ɗin nasa, sai ta haɗiyi wani wahalallen yawo mai wuyar wucewa. Tana kokarin sauƙa daga saman gadon ne ta ji jikinta a jike, dubawa da zata yi ashe fitsari ta yi a wando, tashin hankali ganin kyakyawar fuskar Lion a mafarki ya saka Rimsha fitsarin kwance

(Niko nace to Rimsha dama ba za ki iya ba kika fara, kallon fuskar Lion a cikin mafarki ma kawai ya saki fitsari a wando, to ina ga kuma a zahiri? Ga shi kuma Kausar ta ce ku tara kuɗi ku je wajen sa, Babbar magana, hmmm anayi muna jin daɗi🤣🤣🤣 amma dai i pity you my Meesha 🥺)

kara tsorata ta yi cikin sauri ta diro kasa daga gadon ta nufi wajen kayan Kausar, wani dogon riga ta ɗauka ta fito ta shige toilet.

A gurguje ta watsa ruwa, daga cikin toilet ɗin ta sanya kayan Kausar ta fito falo, nan ta isko su Ayla har sun ci abincin safe sun zauna suna kallo.

Zama ta yi sama sofa kusa da Ayla ta ɗauko remote ta canza tasha zuwa news dan taga meke faruwa a duniya, ta ko yi Sa'a tana shiga News dara-daran sleeping eyes nata suka mata arba da hotunan Lion a Airport zai tafi Spain lokacin, sai tattaunawa manya-manyan gidan Tv suke yi a kan hakan, kara tsorata da shi tayi dan yadda taga fuskar sa a Airport ɗin lokacin yana sallama da His excellency, dama kuma kun san ranar ya fita cikin ɓacin rai a fusace, runtse ido ta yi, alamar bata son kallon fusataccen fuskar sa,

Sai dai kuma me tana runtse ido a sukwane ta buɗe domin kuwa tana runtse idon fuskar sa ta gani yana kokarin yi mata kiss lokacin a mafarki. Ihu ta saki tare da miƙe wa tsaye, daidai lokacin gidan Tv suka ɗaura wani shot video sa in da yake magana da president ɗin Spain lokacin da zai bar gidan ya koma hotel, kun san lokacin a fusace ya yi maganar, ganin haka yasa Rimsha ta watsa a guje zuwa cikin bedroom na su tana dafe kanta dake mata barazanar tarwatsewa saboda ciwo, ga shi Lion na neman haukatata, ko in ce tana neman haukata kanta, domin Lion kam bai ma san tana yi ba, bai san da zamanta a duniya ba ma. Tashin hankali wanna shine Babbar cakwakiya.

Da sauri su Ayla suka bi bayanta. Saman gado kusa da in da ta yi fitsari suka iskota, ta dafe kanta tana hawaye, baiwar Allah idan ta rufe ido ba abinda take kallo fa ce fuskar lion yana ƙoƙarin yi mata kiss, ga shi bala'i tsoron ganin fuskar tasa take, kwarjininsa yana haukatata, idan kuma ta buɗe ido fusataccen fuskarsa da ta gani a Tv yanzu take gani, Allah sarki ta ko ina ba sauki, duk ta ruɗe ta zama kamar zararriya abin tausayi, lokaci guda ta canza ta rasa ina zata sanya rayuwar ta ta ji daɗi, ta rasa nitsuwar ta. Wanna abu yana azabtar da ita, a zahirin gaskiya ko daga nesa idan taga fuskarsa cikin face mask sai gabanta ya faɗi kuma a haka zuciyarta ta kamu da bala'i kaunar shi, a yan wanna kananun shekarun nata, zuciya baki wa Rimsha adalci ba ko kaɗan. Sosai take hawaye ta rasa madafa, kuma a haka ma a cikin farinciki Lion ya mata magana a cikin mafarkin tata, wanna da a ce tsawa ya mata ai ina ga Rimsha sai mutuwa.

Kusa da ita Ayla tazo ta zauna tana faɗin "Rimsha lafiya ki ke kuka?" Shiru ta kasa magana, haka ita ma Kausar tazo ta tambaye ta, nan ma shiru bata amsa su ba, sai kuka kawai take baiwar Allah.

(Why Lion zaka yi mana haka, ai ya kamata a ce da akwai amana, ko kwarjinin ka zai firgita kowa bai kamata ka bari ya firgita mana Rimshan mu ba, dan ta ɗebi tsawon shekaru da dama tana dakon sonka🥺.)

Su Ayla sun jima zaune suna ta rarrashinta, kafin su samu ta daina kuka amma taki yin magana, saboda bata san me zata ce musu ba.

Sun shafe 1 hour a haka kafin Rimsha ta iya samu abin ya sake ta, ta miƙe zaune. Kasa kasa kamar mai raɗa ta ce "Ina Iya kausar?" "Iya ta fita unguwa" Kausar ta bata amsa, matsowa Ayala ta yi ta rungumeta tana faɗin "Rimsha dan Allah ki faɗa mini me ya sanya ki kuka?" Kakalo murmushi dole ta yi tana faɗin "Ayla a yanzu ba ni da wanda ta fi ku, dan haka zan faɗa miki amma ba yanzu ba" shiru Ayla ta yi kamar mai nazarin wani abin, ita kuma Kausar wucewa tayi ta nufi waje tana faɗin "Bari na je gidansu waliya ina zuwa, Iya ta ce na karɓo mata abin ɗebar ruwanta da suka ara" to kawai su Ayla suka bita da shi, juyawa ta yi ta fice daga ɗakin.

Kausar na fita Rimsha ta Matso kusa da Ayla sosai tare da riƙo hannunta ta fara bata labarin abin da ke faruwa da ita a kan Lion, daga karshe ta rufe da cewa "Bana son Kausar ta sani ne saboda banson matsala" kasa kasa Ayla ta ce "Matsalar me kuma Rimsha?" Kara kasa da murya Rimsha ta yi kafin ta ce "Ke dai Ayla ki riƙe amana amma ita Kausar ba ta da amana ita da Iya akwai abin da suke shirya mana, shiyasa yanzu na ja baya da su, jiya na shiga ɗakin Iya na samesu suna magana kasa kasa suna gani na suka yi shiru kuma tun kafin na shigo na ji suna magana, sannna kuma ki yi taka tsantsan da wayan nan boda Jami'u wlh yan iskane dan dana fita yin alwala da asuba na haɗu da ɗaya daga cikinsu ban gane wanene bane ya yi kokarin taɓa min kirji na kauce na gudu na dawo ɗaki" a hankali Ayla ta ce "Haka ne kam nima ɗazun sai da ɗayan bansan sunan shi ba sai da ya taɓa min kirji, kin san munrigaki ta shi barci, kuma Iya ta fita ta bar mu da su, ina ga da gangan ya aiki Kausar shagon wajen nan, tana fita ya kama mini breast na, shi kuma ɗayan lokacin yana wanka, ɗayan kuma yana ɗakin su, dana ja da baya zan ta shi ya yi saurin riƙeni ya ce idan nayi wani magana sai ya yanka ni, shine na yi shiru, ya ci gaba da taɓani, yana cikin taɓa ni Kausar ta dawo sai ya yi saurin ya sake ni" ta kai karshen maganar tana hawaye, goge mata hawayen nata Rimsha ta yi a kule ta ce "Wlh kada ki sake bari ya taɓa ki, idan ya sake yin gigin hakan ki masa ihu, ba gara mu bar musu gidansu ba da su taɓa mana mutuncin mu, ko yatsana ba wanda zan bari ya taɓa, banzaye wayan da basu san ciwon kansu ba kazamai kawai" ta kai karshen maganar cikin fishi, dan har ga Allah abin da suka wa Ayla ya ɓata mata rai dan tana barci ne da bazata bari hakan ta faru ba, Allah sarki Iya ita ma bata nan ne da ba zata yarda da Jami'u ya taɓa ko ɗaya daga cikinsu ba, kuma har ga Allah Iya bata san halin Jami'u kenan ba shi yasa, bai taɓa nuna musu hakan a filli ba, kullum a mutumin kirki Iya ta ɗauke shi shiyasa ma ta yarda da neman auren Kausar da yake yi, bata san ɗan iskane mai lasisi ba, ga bin mata ga shaye-shaye.

Tirƙashi su Rimsha kuna cikin tsaka mai wuya, ba abin da zamu ce sai dai Allah ya shiga lamarin ku.

Duk wannan magana da Ayla da Rimsha keyi kaf a kunnen Kausar suka yi shi, domin kuwa ba wani gidan su waliya da ta tafi tana fita ta laɓe musu a bakin kofa tana sauraren su, daman kuma da gangan ta ce musu Iya ta aiketa, dan ta lura Rimsha bata son yin magana a gaban tane, shiyasa ta musu hakan, dan su tattauna.

To meke shirin faruwa ne? Mu je dai zuwa.

Bayan ta gama sauraren tattaunawan nasu ne, ta lallaɓa ta fice daga falon ta nufi waje tana riƙe da haɓa tana girgiza kai, a zuciyar ta tana faɗin "Ku zauna a gidan mu, muyi mu ku komai, ci, sha, sutura, amma ku rasa waye zaku yi wa sharri sai yayana kuma mijin da zan aura, wlh ba zata sakuba". Tana ta zancen zuci har ta isa gidan su Waliya

Su kuwa ba su kawo cewa Kausar zata musu laɓe ba dan hakan yasa suka saki jiki wajen yin hirar su, a hakan ma kasa kasa suka yi dan kada wani ya ji yo su, suna gudun matsala.

Allah sarki bayin Allah, Allah dai ya fitar da ku daga cikin wannan ukubar rayuwa. Bari mu leƙo Daular mutuwa mu dawo

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu, Much kauna 🥰

💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 20-21🌹


Su kuwa ba su kawo cewa Kausar zata musu laɓe ba dan hakan yasa suka saki jiki wajen yin hirar su, a hakan ma kasa kasa suka yi dan kada wani ya jiyosu. Allah sarki bayin Allah Allah dai ya fitar da ku daga cikin wannan ukubar rayuwa.

Bari mu leƙo Daular mutuwa mu dawo.

☠️☠️Ɗaular Mutuwa☠️☠️

Guguwa ne mai karfin gaske ta kewaye ko ina, wani masifaffen duhune ya lulluɓe gidan gaba ɗaya, daga cikin guguwar wasu sautika ne ke tashi kala-kala na muryoyin sheɗanun aljanu daban-daban, masu magana da yaren da ɗan adam baya ji, idan ba kana da karfin imani ba baka iya zama a wajen, gaba ɗaya gidan ansawa yake yana bada wani irin amo mai sautin gaske, gaba ɗaya wayan da ke cikin gidan, kowa ya yi ta kan shi, ma'ana sun shige cikin ɗakunan su.

Wannan nasifaffen guguwa ya jima yana yi kafin haske ya karaɗe gidan, amma ita guguwar bata dakataba. Gingima-gingiman jiga-jigan matsafane suka fara fitowa ta sassa daban-daban daga cikin gidan, munin halittar su ma kawai ya isa ya sa ɗan Adam suma. Gaba ɗaya matsafa dake gidan sai da suka fito yau, sun jeru layi a cikin part ɗin su Baba da Mustapha, duk girma irin na part ɗin nan sai da suka cika shi tab da yawansu, dan suna da yawa sosai ba wasa ba, munanane gaba ɗayan su, basu da kyan gani ko kaɗan, tsayawa zayyana muku bala'i munin su ma ba zai yi wu ba, domin zai cinyemin ɗan fillin dake gareni, dan haka ku ayyana su a ranku kawai, suna da kattin kai da katon hancin ga idon nan nasu jawur kamar jini, kamar kuma zai faɗo kasa saboda girma.

Sun tsaitsaya kamar wasu gumaka, numfashinsu kamar na saniya, sai dai a cikin su babu duna, baya wajen. Ko ina suka kai shi oho.

Daga ta bayan su wani sauti mai bala'i karfi ya fara fitowa, ji kake dip-dip-dip, ƙasa na amsawa, wannan sauti kuma ba komai bane face sautin takun Queen oga kwata-kwata kenan.

Wannan sauti ya ɗan jima yana yi, alamar daga nesa take kenan, sautin na kara matsowa alamar tana tunkaro wajen.

Lokacin da ta iso wajen, sautin ya kara karfin amon da yake yi ne sosai, gaban su tazo ta tsaya.

Kai-kai-kai, ya subhanallah, Queen mummuna ce ajin farko, tana da tsawo sosai ga kuma ƙiba, da kallo ɗaya zaka mata ka san ƙabilar Ebo ce, gaba ɗaya Daular Mutuwa mallakin kabilar Ebo ne. Queen tana da katon hanci kamar tukunya, ga hancin nata a baje a kumatunta, alamar ta kara girma shi da tsafinta, haka zalika bakinta wargajeje gari guda, sannan tana da manya-manyan hakwara guda biyu ta gaban hakwaranta na sama, wayan nan hakwaran nata guda biyu, suna da tsini kamar kifiya, sannan suna da tsawo wadda ko ta rufe baki su basa shiga cikin bakin nata saboda tsawon su, wayan nan hakwara nata masu kama da na zamisa tsab za su iya tsinke jijiya mafi karfi na jikin ɗan Adam, shiyasa ita bata yanka mutun da wuka wayan nan mayun hakwaran nata take damke makogoron mutun ta ɓalle shi ta tsinke jijiyoyin shike nan mutun ya mutu, sannan daga tsakiyar goshinta akwai wani tsagu wadda yazo mata har gemunta, ya yi kamar ya raba kanta gida biyu, ga kan nata ba'a magana girman shi ba zai faɗu a baki ba.

(Tashin hankali ke Queen naki bala'i ya wuci tunanin mai tunani😳)

Fitowar ta sai da ya sanya gaba ɗaya Daular Mutuwa ya girgiza, gaba ɗaya yan adam dake gidan sai da suka suma, baba da Mustapha ne kawai ba su suma ba, amma sun tsorata ainun suma, saboda munin Queen ba kowa zai iya ganin ta bai sume ba, idon nan nata gula-gula jawur da su kamar jini kamar zasu faɗo kasa, gashin kanta kuwa ba'a magana, idan ka gan shi kai ka ce jijiyoyin bishiyoyi ne, a tsaitsaye suke kamar ba lafiya, ga su da bala'i datti kamar me, tsayawa zayyana muku munin Queen zai cinye mana ɗan sauran filin dake gare mu, ku ayyana muninta a ran ku.

Ko da ta tsaya a gaban su, jijjiga jikinta ta yi da karfi kamar wata giwa, sannan ta waje wannan mummunar wagegen bakin nan nata wadda hayaki ke fitowa daga cikinsa, kamar an hura wuta a cikin nata. Da karfin gaske ta kurma wani mahaukacin ihu wadda bala'i sautin sa sai da ya sanya dakarun nata da kansu suka toshe kunnuwan su, ihun nata kuma ya karawa guguwan dake tashi karfin gudu, haka zalika muryoyin dake fitowa ta cikin guguwar suma sun kara sautin muryoyin nasu.

Good 2mins ta ɗauka tana kurma wannan balaƴaƴƴen ihun, kafin ta tsagaita, ta sake girgiza jikinta, gaba ɗaya dakarun nata tsugunnawa kasa suka yi a gabanta alamar girmamawa.

Cikin yaren su na matsafa ne ta basu Umarni a kan duk in da su Rimsha suke, su tabbatar sun nemo su cikin kankanin lokaci sun dawo da su sun mata ferfesun su, idan ba haka ba ransu zai yi mummunar ɓaci, domin dole ne su Rimsha su karɓi hukunci saboda sun karya mata record na gidan ta, ba'a shiga a fito da rai, su sun shiga sun fito, abin da ba'a taɓa yi ba wai ɗan adam ya shiga kuma ya fito a raye, ina sai a kan su Rimsha.

Sosai dakarun nata suka rinƙa bata hakuri tare da yi mata alkawarin ko ina su Rimsha suke sai sun dawo da su cikin gidan nan, yanzu za su fita gari, su shiga cikin al'umma, za su saje da su su nemo su. Wucewa kawai Queen ta yi bata sake yin wata magana ba, tana taku kasa na ansawa, haka ta wuce cikin fadarta, dakarun dake tsaron fadarta ne suka rufa mata baya.

Da haka taro ya watse, dakaru goma ne suka shirya suka rikiɗe zuwa siffar kyawawan matasan samari sannan suka wuce izuwa cikin gari, cikin jama'a dan neman su Rimsha.

Su kuma sauran kowa ya koma bakin aikinsa.

A cikin Daular Mutuwa dakaru basa amfani da kaya irin namu na mutane, saboda ba zai shigesu ba, wani irin tamfol suke using mai matikar karfi da tauri kamar fatar shanu, kuma basa ɗinka shi kamar yadda mutane ke yi, no ɗaɗɗaura tampol ɗin kawai suke a jikin su, sannan gaba ɗaya Daular Mutuwa iya maza ne kawai matsafar dake ciki, Queen ita kaɗai ce mace, kuma mai jagorantar su, Asali gidan na kakantane chigozie, shi ya wallafa Daular tun shekaru 40 baya, dukkansu kuma kabilar Ebo ne, sai dai basa magana da yaren Ebo a gidan, da wani yare nasu na matsafa suke amfani, sannan kuma basa da yawan magana, duk gidan duna ne kawai mai magana da mutane, su Barbushi sai dai yanka da shan jini, manya-manyan gidan matsafa daga sassa daban-daban a faɗin kasa da wajen ta suna zuwa wajen Queen domin sayan wasu sassa na jikin ɗan adam domin yin tsafinsu, shiyasa idan suka kasa shan jinin mutum sai su ajiye shi zuwa lokacin da wasu gidan matsafar zasu bukaci wani sassa daga jikinsa, sai su yanka shi su sayar, amma sai dai duk wani gidan tsafi dake son sassar jikin mutun, akwai wani waje na daban da suke haɗuwa dan yin taron, ba a cikin Daular Mutuwa wajen yake ba, yana daga gefe.

Baba da Mustapha bayin Allah, suna zaune shiru a cikin ɗakin, a cikin zuciyoyinsu suna yi wa su Rimsha addu'ar Allah yasa kada Queen ta yi nasarar gane in da suke, Allah yasa sun tsira kenan, shi baba haka kawai yake jin matukar kaunar Rimsha a cikin ransa, baya son ganin ta cikin wahala, gara masa shi ya mutu da wani abin ya same ta.

Allah sarki baba bai san cewa Rimsha jikarsa bace.

(Wayyo duna ko ya suka yi da shi oho, muje dai zuwa mu gani kila gaba mu sani, bari mu leƙo lion mu gani.)


💓💓Washington DC💓💓

Wunin yau zumbur Jay yana wannan aiki, ya jigata, duk wanda ya gan shi sai ya matsa masa kwalla, ga shi kuma da alama Lion ya mance da shi. (To fa Babbar magana.)

Sai can gari ya fara sanyi irin bayan la'asar kenan, His Excellency yazo gidan dan yi wa jikansa sannu da dawowa, a palon kasa ya zauna, masu ba shi tsaro kuma daga wajen sojojin bakin gate suka tsaya, dan tsarin Lion ne babu wani jami'in doka da ya isa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login