Showing 288001 words to 291000 words out of 355604 words
yana da jacket, ita bata da shi ko guda ɗaya, basu saya ba, da ta shiga kuma, sai ta yi karo da wannan jacket ɗin mai kamshin perfume ɗin Lion, perfume ɗin da ta fi kauna a rayuwarta, hakan yasa ta ɗauki jacket ɗin ta tsaya a tsakiyar ɗakin tana surutu ita kaɗai, shiyasa Lion da ya zo wucewa ya ji ana magana kasa kasa a cikin ɗakin.
Tana fitowa daga ita sai wasu shegun kayan barci masu shegen kyau launin sky blue riga da wando, kayan sun zauna ajikinta sosai, kana iya ganin ainahin shape na jikinta, ɗakinta ta koma tare da sanya jacket ɗin a jikinta.
Har gwiwarta jacket ɗin ya kai mata, hakan ya bata tabbacin cewa ba jacket na Imran bane, domin tsawon Imran da kaɗan ya fi tata, tunani ta fara yi anya ba jacket ɗin Lion bane, tuna haka yasa wani irin kayatatcen murmushi ya kubce mata.
A fili ta furta "Ko yanzu na mutu Allah ya cika mani burina ɗaya, yau na saka rigar GAR" wayarta ta ɗauko ta fara ɗaukar hoton a cikin wannan dare.
Sai da ta yi hotuna kala 15 sannan ta haye gadon zuciyarta cike da farinciki mara misaltuwa. Da haka barci ya kwanshe ta.
Misalin karfe ɗaya na dare, duniya dukka suna barci shi kuma Lion yana tsaye saman dadduma jikinsa na sanye da farar jallabiya tas, sai ta shin kamshi yake yi.
Sallah yake yi yana karanta manya manyan surori irin su Bakara Ali Imran nisai, yana karatun idanunsa sunyi ja sosai da sosai, babu abin da yake sanya idanun Lion suyi ja haka sai karatun Al Qur'ani mai girma wadda duk zuciyar mumini idan ta karantata kuma ta san ma'anar ta, to dole ta zubar da kwallah, domin kuwa Al Qur'ani mai girma ita ce ke nunawa bawa ainahin girman Ubangijin mu, dole duk wani bawan da zai ji girman Allah da kuma abubuwa na Ni'ima da Allah yake yi wa bayin sa, wasu su butulce, wasu kuma su sanya kafa su dake, wasu su yi amfani da shi wajen gaya wa wasu su kuma ba zasu yi amfani da shi ba, wasu kuma zasu ɗauka ne kawai su ajiye a ƙwaƙwalwarsu ba tare da sun yi amfani da koda aya guda ɗaya ba, suje su yi ta sha'anin su kamar ba su san me zai faru a gaba ba, su mance akwai tashin alkiyama, akwai lahira, kafin lahira akwai kwanciyar kabari wadda babu wanda ya san shekaru nawa za'ayi a cikinta, idan ka yi aiki mai kyau duk shekarun da zakayi a kabari kana cikin ni'imar Allah subhanahu wata'ala, idan kuma kayi aiki mara kyau duk shekarun da za'ayi kana cikin bakar azaba mara misaltuwa ne daga hannun Mala'iku, babu mai citonka, babu mai jinka, kai kaɗai zaka kasance cikin wannan duhu da bakar azabar, bayan kabari mai duhu da firgitar da bawa za'ayi busan kawo na fitowa daga kabarin wadda a nan ne ake cewa zafsi zafsi takai takai uwa zata mance da ɗanta ƴa ta mance da uwarta, lahira ba wasa bane, Allah zai sauƙo mana da rana daidai saitin kawunanmu, waƴan da suka yi aikin Alkhari sune kawai zasu shiga ƙarƙashin inuwar alarshin Ubangiji mai girma, bayan nan fa akwai gadar siraɗi wadda take shinfiɗe a samar wutar dajannama, kaifi tafi reza siranta kamar gashin kai, a haka zamu bi ta kanta mu wuce, bakar duhune a wajen wadda baka iya ganin koda ɗan yatsarka, aikin Alkhari da muka yi shine zai zo ya haska mana hanya mu wuce, idan ka yi kuskure faɗawa cikin wuta zaka yi, jama'a me zamu nema a duniya da har zai sanya mu manta waƴan nan dukka? Mulki? Kuɗi? Koko Duniya? Ko kuma me? Idan mulkine to a wannan rana ta tashin alkima Allah zai tara mutane duniya baki ɗaya waje guda ya yi mana tambayar da babu wadda ya isa ya motsa bare ya bada amsa WAYE SARKI A YAU shine tambayar da Allah zai yi mana, ina mulkin take a nan? Sarakuna shuwagabanni dukka babu wanda ya isa ya yi motsi ko kaɗan, Allah da kanshi yake sake cewa shine mai mulki a yau, babu wani sai ki sai shi, idan kuɗi ko duniya yake saka mance lahira, to dukka a nan zamu tafi mu barsu kamar yadda bamu san lokacin da zamu zo duniya ba, haka ba zamu san lokacin tafiya lahira ba, ƴan uwana ya kamata ku sani, Allah baya kama bawa akan laifin da bai sani ba, amma mutun ya sani ya take sani babbar haɗari ne, irin shi mummunar kamu Ubangijin yake yi mashi, da kuma malaman da za su karantar amma su ba zasu yi amfani da abin da suke karantarwa ba, waƴan nan idan ba su tuba ba, wlh Ubangiji ba zai yi masu kamu mai kyau ba, waƴan da suke sanin Allah ya ce, sai dai su gayawa bayi Allah ya ce ayi kaza ayi kaza su kuma ba zasu taɓa kwatanta yin hakan ba, ku ji tsoron Allah kada ku gyara wa wasu goben su ku kuma taku ta taɓarɓare, sai anyi magana sai kuce ai bature ya ce do what I say don't do what I do, wlh ku kiyayi wannan kalma idan ba haka ba zata kai ku ta baro ku, Allah ka kiyashe mu ka kuma rabamu da sharrin zuciya, amma dai zuciya bata da ƙashi, duk abin da zaku yi, ku tabbatar tsakani da Allah kuke yin shi, kada ku yi abu dan a yaba maku, zaku tashi a ranar gobe kiyama kun baro duniya da aikin lada sosai kun je lahira babu ko ɗaya, domin ba domin Allah kuka yi ba, dan haka mu kula dan Allah, ayi koma saboda Allah.
Ya jima yana Sallah tare ka karatu, idan ya yi raka'a biyu ya yi sallama sai ya zauna kusan minti 20 yana rera karatun Al Qur'ani mai girma da wannan zazzakar murya tasa.
Sai Misalin karfe 2:30 bayan ya sallame daga sallar ne ya tashi ya fito Palo, can kasa kasa ya fara jiyo kamar ana magana.
Juyo waƴan nan dara daran blue eyes ɗin nasa ya yi izuwa kofar ɗakinta domin daga nan maganar take fitowa.
Kamar zai sauƙa kasa, sai kuma ya fasa ya ce bari ya gani waye mai maganar nan, domin ɗazun ya ji magana kasa kasa yanzu ma haka, Kuma yanzu dare ta tsala sosai waye mai magana haka.
Ya yi Sa'a kofar ɗakin tata a buɗe, tura kofar ya yi ta yadda zata buɗe mashi dukkan saboda ya sami damar ganin cikin ɗakin gaba ɗaya ba tare da ya shiga ba.
Zaune take a saman dadduma ita ma tana karatun Al Qur'ani mai girma bayan ta idar da Sallah, ta bawa kofar shigowa baya tana fuskantar gabas, kallo ɗaya ya yi wa cikin ɗakin ya juya ya bar wajen, dama buƙatarsa ya ji maganar me ake yi kasa kasa tun ɗazun, sannan kuma waye mai yin maganar, tun da ya ga sallah ake yi to Shikenan baya bukatar wani abin kuma, dan haka sai ya juya ya nufi kasa.
Kai tsaye ɗakin Areef ya nufa, yau kwata kwata ya kasa samin kwanciyar hankali, sai tunanin Areef ɗin yake yi, abin ya tsaya mashi a rai sosai, haka kawai yake jin kamar wani abin na shirin faruwa.
Kasa kasa ya yi sallama a bakin kofar ɗakin tare da shigowa ciki.
Kwance yake a saman bed ɗin nasa, sai zuba barcinsa yake yi hankali kwance, cikin natsuwa yake sauke numfashinsa, kai daga gani kasan wannan barcin na musamman yake yi, amma kuma babban abin da ya sanya Lion ya kasa runtsawa yake jin tamkar akwai abin dake shirin faru ko kuma ma yake faruwa shine jikinsa yana yi mashi wani irin yanayi kamar ana azabtar da ɗaya daga cikin Triplets nasa, idan baku mance ba abaya na gaya maku, duk abin da ya sami ɗaya, to dukkansu suna iya jin yanayi makamanciyar wannan a jikinsu, hakan yasa ya kasa runtsawa.
A ɓangaren Aseef ma haka ne, bawan Allah ya kasa runtsawa, daya ga ji sai ya tashi ya ɗauro alkawala ya fara gabatar da sallah ko zai sami sassauci, shi ma Musharraf yana a saman dadduma suna sallar dare tun da barci yaki zuwa.
Lion ya jima tsaye tare da kunna wutar ɗakin yana karewa Areef kallo, daga karshe sai ya kariso bakin bed ɗin tare da zama kusa da ɗan uwan nasa yana mai cigaba da kallon face ɗin ɗan uwan nasa.
Bai taɓa zubawa abu ido yana kallonsa haka ba sai akan Areef, ko lokacin da suke tare gaba ɗayansu, da kallo ɗaya yake yasu ya gane idan suna cikin damuwa ko makamancinsa, amma bai san me yasa yau ya zubawa Areef idanu sosai yana kallonsa har haka ba.
Ko motsawa irin wadda masu barci suke yi shi Areef baya yi, tamkar wadda babu ruhi a jikinsa, ba dan numfashin dake futa daga gare shi ba, to da zaa iya cewa babu ruhi a tattare da shi.
A hankali Lion ya fara tufa mashi addu'a, yana karatu yana tofa mashi, shiru har lokacin baya wani motsawa bayan numfashin, Lion bai wani damu ba ya cigaba da tofa mashi addu'a, daga karshe dai ya yi addu'a mai tsawo kafin ya tofa a hannunsa sannan ya shafa wa Areef ɗin a face nasa.
Wani dogon numfashi Areef ɗin ya ja tare da saukewa a hankali, nan take numfashinsa ta sauya, nan take ya koma ainahin yadda yake barci before. Abin da yasa Lion ya yi mashi addu'a, ya lura da cewa gangar jikinsa ne kawai a nan, sai numfashin da suka bar mashi domin su kawar da hankalin mutane, amma zance ta gaskiya Areef baya a Nigeria kwata kwata, sun ɗauke shi suna can suna azabtar da shi, daga kungiyar G.M.A kenan.
Bawan Allah yana dawowa daidai kuma ya cigaba da barcinsa kamar yadda kowa yake yi, fuskar nan tasa ta kara haske sosai, miƙewa Lion ya yi tare da karanto addu'a sosai ya kara tofa mashi sannan ya fice daga cikin ɗakin.
Yana fita ya nufi sama, daidai zai shiga ɗakinsa kuma, sai ya ji alamar motsi a ɗakin Imran, ƴar mamaki ya yi akan me yake damun ƴan gidan nan ne, yau kowa bai yi barci ba, kasan cewar yana bala'in kaunar Imran sosai sai ya shiga bedroom ɗin nasa.
Kasa kasa ya yi sallama, Imran yana zaune a tsakiyar bed nasa, idanunsa biyu kuma bai amsa sallamar ba, abin ya ɗan bawa Lion mamaki.
Prof ya ambaci sunansa a hankali, ɗago kai Imran ya yi yana kallonsa, da yake blue light ne a cikin ɗakunan gidan gaba ɗaya, kuma mafiyawancin lokaci basu kashe wutar ɗakin sai hasken wutar ta saje da kwayar idanunsa.
Juyawa ya yi ya nufi waje, bin bayansa da kallo Imran ya yi, har zai fita ba tare da ya juyo ba ya ce "Kazo ɗaki mu yi magana". Ya kai karshen tare da ficewa abinsa.
Nauyayyar ajiyar zuciya Imran ya sauke tare da dirowa kasa daga saman bed ɗin, jikinsa na sanya da kayan barci masu kyau launin black color, bayan Lion ɗin ya bi yana sauƙe ajiyar zuciya.
Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, Lion na tsaye a tsakiyar ɗakin jikinsa na sanye da kayan barci riga da wando, ya cire jallabiyar jikinsa yana ruƙe da waya yana latsawa.
Saman bed nasa Imran ya haye ya kishingiɗa yana mai faɗin "Saif me kake yi har yanzu baka yi barci ba?".
Shiru ya yi na ƴan mintoci kafin ya ce "What is wrong with you Prof?". Shiru Imran ya ɗan yi yana tunanin ya faɗa mashi ne ko kada ya faɗa mashi, ya san halinsa sarai, na farko idan ya gaya mashi idan dai ya aminta to tabbas matsalar a cikin kwana ɗaya zata warware da izinin Allah, na biyu kuma idan ya gaya mashi bai Aminta da zancen ba tofa sai dai ma ya yi mashi faɗa akan zancen, babban abin da yasa Imran yake ɗari ɗarin gaya mashi kuma, saboda ya taɓa cewa zai shiga case ɗin daddyn Jelly ya ki bada number, ya kuma san halinsa sarai idan har ya ce ba zai yi abu ba, to fa ya rufe babin wannan abin.
Shiru Lion ya yi yana jiran amsa daga bakin Imran ɗin, almost 5mins ya ji Imran shiru bai bashi amsa ba, hakan yasa ya juyo tare da juyo da kallonsa izuwa kan Imran ɗin.
Wani irin wahalallen yawu Imran ha haɗiye domin har ga Allah ko shi kwarjinin Lion yana matukar razana shi, musamman idan ya zuba maka wayan nan dara daran idanun nasa masu rikitar da mai kallonsu.
Ai Imran bai san time da ya gaya mashi cewa yana damuwa ne akan ɓatar matarsa ba, maganar gaskiya ba wannan ce ta sanya shi a damuwa ba, maganar daddyn Jelly na videonsa dake a hannun baban Muneer shi yake sanya shi tunani, ya rasa ina zai sa ransa akan wannan abin, idan wannan video ta fita da wani ido ma'aikata a banki za su kalli Abbansa? Da wani ido jama'a zasu kalli family'nsu? Wannan ne babban abin da yake damunsa, amma ya rasa me yasa da Lion ya zuba mashi idanu ku sai ya rikice ya gaya mashi ɓatar Jelly ya sanya shi damuwa sosai acikin wannan dare har haka, tabbas ya shiga damuwa sosai ɓatar jelly, to amma ɓatar tata ta riga da ta zame Mashi jiki.
Kawar da kallonasa jefe Lion ya yi, ya ɗan ɗauki mintuna kafin ya ce "A ina ta ɓata kuma a yaushe? Shekarunta da kuma yanayinta".
"A Kano state ta ɓata irin wata uku zuwa biyar haka baya, she is 16 years old, kyakkyawar gaske ce..." Maganar ce ta makale sakamakon juyo da idanunsa da Lion ya yi izuwa kansa.
"Wata uku zuwa biyar kuma har yau ba'a iya gane ina take ba?" Lion ya tambaya yana kara tsare shi da idanun.
Tabbatar mashi da hakan Imran ya yi, jinjina kansa ya yi yana mai kara ganin laifukar da shuwagabannin ya kamata su gyara masawar suna son cigaba a rayuwar kasarsu.
Gyara kwanciya Imran ya yi yana faɗin "Ina kewarta, serious ranar da ta dawo a ranar za'a ɗaura mana aure, ba zan iya sake hakura ba, na sha bakar wahala a ɓatarta, ban taɓa tunanin zan yi rai in kawo har yanzu ba tare da an gane ta ba, ban taɓa tunanin a yanzu bata zama mallakina ba".
Juyo da kallonsa Lion ya yi kan Imran ɗin, kasa kasa ya ce "Ban san da kai da Areef waye ya fi wani jaraba ba". Hararar wasa Imran ya yi mashi kafin ya ce "Ga ka nan kuwa, kai ai inaga duk duniya ba wanda zai fika, daɗin abin dai ɗaya shine da Allah yasa bakasan da abin ba, baka ma san soyayyarba da wlh ƴar mutane ta shiga uku, ina ga sai gawarta, kai daga ganin wannan idanun naka kai kanka idan zaka gayawa kanka gaskiya kasan da hakan, ni ina mamakin ka ma wlh, mutum kamar wani dutse ko karfe, kwata kwata baka da wani shauki sai na harbi da bindiga".
Yau da alama ƴan mutuncin Lion suna kusa tun da har ya tsaya Imran yake wannan hirar da shi, ko da yake yana bala'in kaunar Imran ɗin over, basu hira har haka, magana ɗaya biyu idan ta yi yawa uku ce kawai take haɗa su, ba Imran kawai ba, bai taɓa yin magana da wani ta wuce magana uku ba sai akan wannan case ɗin na Areef, a nan ne ya ke iya zama yana ɗan magana mai tsawo da Areef ɗin wadda take iya kai har tambayoyi kala huɗu ko biyar yake yi mashi.
"Prof seriously i will make you regret". Ya kai karshen maganar tare da nufar Imran ɗin.
A guje Imran ya miƙe ya rungume shi yana dariya yana faɗin "Ni ai haka zaka yi hakuri ka kyaleni, kuma ai gaskiya na faɗa, wlh serious ba wasa bane ni ba yadda kuke tunani bane, ni fa kawai ina son ta ne amma duk kun saka mani idanu, Allah ni ba wani abin da zan mata, sister ta ce fa".
Rungume shi shima Lion ɗin ya yi yana faɗin "Yana da kyau kayi hankali da waƴan nan halittun, mata ba abin yarda bane, even mazan ma all ban cire maka kowa ba, don't believe everyone to come closer, prophet Muhammad SAW was said ba wace ta kai uwa son ƴaƴanta, amma kuma a duniyar yau uwa ita ta cuci ƴaƴan nata, idan har uwa zata yi hakan waye kake tunanin a waƴan nan halitu na mata zasu ruke maka amana?".
Shiru Imran ya yi yana tunani, raba jikinsu Lion ya yi yana kallon face ɗin sa, gently jiki a mace domin yau daga maganar Lion ya fahimci abin da ya daɗe yana zarginsu na cewa basa son mum ɗin su.
"A gaskiya idar har uwa ta cutar da ƴaƴanta da kanta kuma da saninta da gangan to tabbas babu da wanda wannan zuciya zata sake yarda a duniya, ba mace ba har maza ba zaka sake yarda da kowa ba, domin uwa ta wuci komai da ake tunani a duniya, ita ce take bada rayuwarta domin ƴaƴanta su rayu, amma a duniyar yanzu son abin duniya yana jefa iyaye cikin bala'i tare da danasani daga baya mara amfani, uwa a zamanin yanzu sai wadda Allah ya so ta da rahma, amma iyayen yanzu sa....." Bai karisar da maganar ba Lion ya ɗaga mashi hannu yana faɗin.
"Is okey, uwa ita ce karshe soyayya a duniya na ɗan adam, so idan ta yi breaking heard na ƴaƴanta they can't trust anyone again, so na dai gaya maka be careful akan waƴan nan halittu, ni ba zan hana yin aure ba, saboda Sunnah ce, but yana da kyau kasan me kake yi ka ajiye batun cewa sister kace, uwa ta fi sister ita ma ta ci amana bare kuma sister, you have to be very very careful".
Jinjina mashi kai Imran ya yi alamar to "Zan tura maka wata number ka turawa wannan number pic na yarinyar zai ɗaura hotonta a system ya yi searching na irin face nata a gaba ɗaya fuskokin dake a Nigeria, amma zai ɗauki ɗan lokaci domin kuna da yawa a kasar, dan ma dai gudun system ɗin yafi gudun jirgin sama ne,