Showing 171001 words to 174000 words out of 355604 words
zo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa kawai yake aikatawa.
Kowa ya fara magana yana faɗan arbarkacin bakinsa akan kuɗin da za'a fitar dan kera manya-manyan makamai wadda karfinsu zai iya tashin state guda, ko uppan bai ce da su ba, kowa sai magana yake yi, shi hasalima ciwon kai suke sanya mashi wannan surutu da suke yi, ji yake yi tamkar ya bar wajen amma bai yi hakan ba, saboda akwai abin da yake son fahimtar a tattare da su.
An samu bambance bambancen ra'ayoyi dan gane da fitar da wannan kuɗin, wasu sun ce yes a fitar wa su kuma sun ce a'a kada za'a fitar yana da kyau a karawa yan kasa abun yi ne, ma'ana marasa aikin yi domin a ragewa kasa talauci, tun da suna da makamai sosai kawai a buɗe masana'antu companys da dama a ɗebi ma'aikata talakawa da ba su da abin yi domin kasar su ta sake tsabtatuwa daga cutar talauci, shi dai Tga ya tsaya akan gara a sayo kayan haɗa makamai domin sun fi mashi talakawan nan mahimmanci, shi kuma His Excellency hankalinsa ya fi rajaa akan gara a buɗe masana'antu saboda ba shi da burin da ya wuce kasarsa ta cigaba da zama super pawer ta duniya, ya fi son ya ga ya fi kowacce kasa komai.
Ganin sun dame shi da surutune yasa ya miƙe ba tare da ya ce komai ba ya nufi waje, bai kai ga fita ba His Excellency ya ce ina zai je ba su gama zama ba, shiru ya yi bai yi magana ba har sai da ya kai kofar fita sannan kasa kasa ya ce "Uncle please idan kasan irin wannan zama za ku yi kada ka sake kirana". Cikin sauri His Excellency ya ce "To yanzu dai gaya mani naka shawarar mu ji". A takaice ya ce a gina masana'antu, sannan ya wuce ya nufi waje abinsa, gaba ɗaya wajen tsit suka yi, domin sun san koda sun yi magana ma abanza ne tun da Lion ya ce masana'antu za'a gina tofa abin da za'a yi kenan, a ɓangaren His Excellency kuwa tuni ya yanke hukuncin abin da Lion ya faɗa shi za'a yi har ya fara shirye-shiryen rubutawa majalisa takarda dan a samu a saki kuɗaɗen da wuri a fara gabatar da aiki domin kawar wa da kasa talauci.
*Allah sarki manyan kasashen kenan kullun burinsu ta ya za'ayi kasar su ta ci gaba, burinsu a kullun kasarsu ta kasance ta farko a duniya wadda zata mulki ko wace kasa kuma ta juya su yadda take so, kuma sun san cewa kasarsu ba zata taɓa ci gaba ba, har sai sun raba yan kasa da talauci da mutuwar zuciya, da hanya ɗaya kawai zasu iya yin hakan, shine su rinƙa gina masana'antu suna bawa yan kasa talakawa aiki ana sarrafa abubuwa daga masana'antun ana fitarwa kasashen duniya ana sayarwa, su ci riba kuma sun raba matasansu da zaman banza zaman kashe zuciya, ya Allah ka sanya shuwagabannin muma su farka irin haka, Allah kasa su zama irin haka, ba wai bukatarmu a ɗauki kuɗi a bamu ba, a'a a gina mana abun da zamu rinƙa zuwa muna aiki a ciki muna samun halak ɗin mu ko ya yake, ya dai kasance kullun zamu je mu yi aikin mu samu, amma idan kuɗi za'a bamu kwana biyu kuɗin sun ƙare an koma gidan jiya😭 wani kuɗin ma idan aka baka abin ko karamar buƙatarka ba zai biya maka ba, please aikin yi muke so ba kuɗin da bai taka kara ya karya ba🥺😭🙏*
Lion yana fita gida ya koma ya yi wanka ya kwanta yana tunanin yadda tafiyarsa zata kaya, sai karfe 2 ya ci abinci Bawan Allah nan.
A ɓangaren su Musharraf kuwa, Michael na toilet yana wanka shi kuma ya fara haɗa tea ɗin sa don ya sha, domin bashi da wani abincin da ya wuci tea, bawan Allah, yana tsoron cin abincin gidan tun da ba musulmai bane kada ya je ya ci abin da Allah ya haramta mashi ci, hakan yasa ya kikaye kansa daga tea sai fruits kawai yake laptawa cikinsa.
Bayan ya zuba duk wani abin da zai bukata a cikin cup, sai ya ɗauki flaks ɗin ruwan tea ɗin, ya buɗe ya fara zubawa a cikin cup ɗin, sai zuba ruwan yake yi, amma cup ɗin taki cika, na cikin flaks ɗin kuma yaki karewa, idan ya cire flaks ɗin daga bakin cup ɗin zai ajiye sai yaga cikin cup ɗin babu komai, alamar ruwan tea ɗin bai zuba a ciki ba kenan, idan kuma ya sake mai da flaks ɗin yana zuba ruwan, tofa sai dai ya yi ta zubawa amma ba zai ga komai a cikin cup ɗin ba, abin ya ɗaure mashi kai, ya kuma tsorata shi sosai, yana tsaka da zubawa sai yaga ruwan tea ɗin ya canza kala daga brown zuwa jawur kamar jini, har wani yaukin jini yake yi, ihu ya kurma tare da sakin flaks ɗin ya yi baya zai faɗi, cikin sauri Michael da ya fito yanzu ɗaure da towel a kugunsa, ya yi maza ya riƙosa yana faɗin
"Uncle ɗin james lafiya kuwa?". Kasa magana Musharraf ya yi sai sunan Allah da yake iya kira a cikin zuciyarsa, amma ya kasa iya furtawa a bakinsa, ganin hakan yasa Michael ya zaunar da shi a saman ɗaya daga cikin chair ɗin table ɗin yana faɗin "Uncle ni bansan meke damunka this two days ba, sai ka rinƙa yi mana ihu yanzu kasa ni fitowa ba shiri" ya kai karshen maganar tare da komawa cikin bedroom nasa domin shiryawa, Allah sarki Musharraf shi ya ga abin da ya gani, a hankali ya ɗaga idanuwansa ya sauke su saman table ɗin, abin mamakin sai yaga komai ya koma yadda yake, duk wasu madara da ya zuba a cikin cup ɗin duk sun koma cikin robarsu, sai lokacin kuma ya samu damar kiran sunan Allah, yana kira kuma ya samu kwarin gwiwa ya tashi ya haɗa tea dinsa ya ɗauka ya nufi cikin bedroom ɗin, yana shiga ya samu Michael naɗe saman bed ya shige cikin bargo.
Da mamaki ya ce "Asif ya na ganka kana kwance? Ba wajen Lion zaka je ba ne?". Can kasa-kasa ya ce "Uncle dan Allah ka kyakeni sai da safe zan je wajen Lion ɗin, now I'm feeling sleeping over" Ya kai karshen maganar tare da janyo barkon ya rufe har kansa, abin ya kara ɗaurewa Musharraf kai, yanzu fa Michael ya fito lafiya Lou baya jin barci, amma daga shigowarsa ɗaki ba'a fi two mins ba wai barci yake ji, anya babu lauje a cikin naɗi kuwa,? Ya yi wa kansa tambayar da bashi da amsarta, ganin ba shi da amsa kuma ya sa ya ce "Asif abinci fa?" Shiru Michael bai amsa ba, da alama ya yi barci ne. Jin haka yasa ya miƙe ya koma saman sofa ya zauna.
Tas ya shanye tea ɗin sa, ya mai da cup ɗin palo, ya dawo shima ya yi wanka tare da shirin barci ya kwanta a bedroom nasa. Asuba ta gari.
Shima dai Lion kamar kullum wanka ya yi ya kwanta ransa fes sai tunainin James nasa yake yi, shima time to time ne dan yanzu tun da ya gano A.E.A bai sa wata damuwa sosai akan ɓatar James ɗin, jima yake yi tamkar ya dawo da James ɗin. Barci mai daɗi suka yi yau, mai cike da annashuwa, ga shi wuraren karfe 1 dare an tapka ruwan sama sosai, sai barcin ta kara armashi.
A NIGERIA KUWA.
Kamar kullum Rimsha na tashi karfe 6 na safe, ta zo ta gyare ko'ina tsab, daga bedroom nata har palo, sanna ta ɗaura masu abinci, yau Akila tana da glass karfe 10 tun karfe 7 ta zo suka fara aikin girki a tare, shima Akil ya bar Umaisha a kan ta zo ta rinƙa koyan girkin, dan ya ji daɗin abincin jiya sosai.
Kamar jiya yauma a tare suka yi girkin, bayan sun kammala, kamar yadda suka saba suka jere a Palo, ko wacce ta wuce ɗakinta dan ta je ta yi wanka.
Bayan sun yi wanka sun shirya ne suka sake dawowa suka haɗu a Palo, Imran ne ya kira Akil a waya ya zo suka haɗu suka yi breakfast a tare, Akila ta tambayi Imran ko dai su rinƙa sakawa Ammi da Abba abinci ne, e ya amsa masu da shi tare da zuba masu ruwan albarka, sai murna suke yi suna amsawa da Amin.
Bayan sun kammala Rimsha ta ce Akil ya kara mata karatu shafi biyu, to ya ce mata sannan ta kara karanto mashi na jiya, sosai ya ji daɗi yadda take son karatu kuma take mai da hankalinta sosai a kan hakan.
Shafi biyu ya kara mata sannan ya miƙe ya fice daga palon yana sa mata albarka, har cikin zuciyarta Umaisha ta ji wani irin bakin ciki, ta ji ba daɗi ganin yadda Akil yake yawan sakawa Rimsha Albarka, abin ya sosa mata zuciya, Akila ta lura da hakan sai addu'a take yi a zuciyarta Allah yasa kada hakan ya jawo masu matsala a tsakanin su.
"Rimsha yau ku kunna kaba ɗaya fridge ɗin gidan nan, anjima za'a shigo da wasu kayan drinks ku shirya komai yadda ya kamata, ku gyara koina, saboda ina da babban bako, Saif zai zo yau". Cewar Imran, to suka amsa mashi da shi sannan ya miƙe yana sanya masu Albarka ya fice daga palon zuwa bedroom nasa, dan ya je ya yi wanka ya shirya zuwa gidan su Irfan.
Su kuma ɗakin Rimsha suka wuce, ita kuma Umaisha ta ki binsu domin ta fara jin tsanar Rimsha a cikin zuciyarta, saboda Akil yana kula ta yana saka mata albarka.
(Toh fah kishi kumallon mata Umaisha manya)
Hira sosai yau Akila da Rimsha suka sha, sai karfe 10 Akila ta wuce school ita kuma Rimsha ta fito palo dan yin aikin da Imran ya ce su yi, wato gyaran gida da kunna su fridges da sauransu.
💖💖A WASHINGTON DC KUWA💖💖
Misalin karfe 8 na safe yana tsaye a gaban mirror ɗakisa, yana duba wasu takardun da suke a wajen, ya yi shirinsa tsab na tafiya, sai tashin kamshi yake yi, ya saki wannan dark black curly hair nan nasa bai ɗaure ba, wannan guntu na gaban yana nan shima, sanye yake da wando jeans mai bala'in kyau Black colar sai high neck t-shirt fari tas, ya yi wa kayan kyau sosai da sosai, kamar kullum fuskarsa sanye da face mask black color kyawawan fararen kafafunsa na sanye da black sos cikin white Boot mai bala'in kyau da tsada, a takaice dai yau wankan Black and white ya yi, tsabar kyau kamar shi ya yi kansa.
Baki ɗauke da excuse Micheal ya shigo cikin ɗakin, ta cikin mirror gabansa ya kare mashi kallo, shima dai Michael ɗin kallonsa yake yi, ganin haka yasa Lion ya juyo suna kallon juna da kyau, ya zubawa Michael wayan nan rikitattun idanun nasa masu rikitar da ƙwaƙwalwar wadda ya kalla, ya rasa natsuwarsa, sosai yake kare mashi kallo kamar mai tuhumar shi, cikin sauri Michael ya kariso Wajen ya rungume shi yana sauƙe nauyayyar ajiyar, hannu bibbiyu Lion yasa ya riƙe shi da kyau yana mai jin matukar kaunar Triplets nasa a cikin ransa. Wani nishaɗi na musamman suke ji dukkansu biyu. Allah sarki jini ba wasa ba, dole ku ji daɗi.
Sun ɗan jima a haka ba wanda ya ce da ɗan uwansa kala, daga bisani suka raba jikinsu, Michael ya koma bakin gado ya zauna yana faɗin "My Lion please i need money" a cikin natsuwa Lion ya tako zuwa wajen bedside drawer ya sanya hannunsa ya buɗe drawer ya ɗauki sarkar nan da ya ajiye mashi ya miƙa mashi, karɓa Michael ɗin ya yi tare da sanya a wuyarsa ba tare da ya tambaya daga ina ta fito ba.
Sake turo ɗan bakin nan nasa ya yi murya a shagwaɓe ya ce "Lion please money" Shiru kamar kurma haka Lion ya yi mashi, daga karshe ya ɗauki wayarsa da laptop ya nufi waje, cikin sauri Michael ya miƙe zai bi bayansa, bai kai ga fita ba ya ji alert wadda ko bai duba ba yasan kuɗin da ya buƙata ne Lion ya tura mashi, wani daɗi ya ji, cike da murna ya fara ayyana irin business ɗin da zai buɗewa Aryan da kuɗin a cikin zuciyarsa.
Shi kuma Lion kai tsaye palon kasa ya nufa, wani irin taku yake yi wadda duk in ya taka kasa sai dark black curlysa nan ya girgiza, ya watse daga bisani kuma ya sake haɗewa, kai ka ce hura gashin iska ake yi, amma ko ɗaya kawai dai yana yin tafiyar da yake yi ne, da alama yana sauri sosai, babu kowa a palon kasan sai wayan nan jibga-jibgan bodyguards ɗin da suke a wajen dining table, su daddy a lokacin duk suna ɗakin su, basu kai ga fitowa yin breakfast ba tukunnan.
Kai tsaye wata kofa dake ta kusa da Kitchen ya nufa a maimakon kofar fita palon, yana buɗe kofar ta sada shi da wajen dawakansa, ta nan ya ratsa izuwa wani ɓangare daga ta cikin gidan, tafiya kaɗan ya yi ya shiga ta lambun daddy ya fito ta kofar sirri dake a wajen, yana fita gidan Tga da Tyrone suna tsaye da mota a wajen sun gama shirya mashi gaba ɗaya kayan sawarsa dama tun jiya da daddare a cikin bayan motar, yana fitowa ba ɓata lokaci Tyrone ya buɗe mashi gidan gaba na motar ya shiga suka bar wajen, kai tsaye airport su nufa.
Ko da suka je airport ɗin bai fito daga motar ba sai da ya sanya wata dankareriyar long coat mai bala'in kyau da tsada Black colar a jikinsa, coat ɗin ta haɗu sosai, a iya gwuiwa ta tsaya mashi, wani rawani irin nasu na turawa ya ɗauko mai jikin mage ya ɗaura a wuyarsa saboda sanyi da ake yi, cikin wannan natsuwa tasa da class ɗin ya fito, already su Tga sun gama shirya mashi komai, a Airport ɗin ba kowa ne ya iya gane shi ba, kai tsaye cikin jet nasa ya je ya shiga, ba ɓata lokaci suka daga suka lula sararin samani. Sai da su Tga suka ga tashin shi sannan suka shiga mota suka juya zuwa gida, sai tunanin yadda za su kare da Brady Tga ya ke yi, dan karen baya yarda da kowa sai Lion, idan ya ga Lion baya nan ne sai kaga ya ɗan saki jiki da Michael, tunani cike fal ransu suka koma gida.
Nikuma na haɗa kayana zuwa Gida NIGERIA kasarmu da gado.
Misalin karfe 6:40 Imran ya shigo ɗakin Rimsha bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya iskota ita da Akila suna shirin zuwa garden dan su kaiwa Akil haddarsu ya kara masu wani, yau bai dawo gidan da wuri bane shiyasa ba su fara karatu da wuri ba.
"Rimaha ki kawo wa Saif ruwa mai sanyi da maltina, ya yi azumi kuma lokacin shan ruwa ya yi, mai sanyi sosai za ki kawo mashi kin ji? Yana ɗaki na" gyaɗa mashi kai ta yi alamar ta ji sannan ta ya fice, miƙe wa Akila ta yi ta nufi waje tana faɗin "Ki same ni a garden idan kin gama, ba zan jira ki ba dan kar yaya Akil ya ji mu gaba ɗayan mu shiru ya zo ya hukunta mu" ta kai karshen maganar tare sa ficewa daga ɗakin.
Ita kuma Rimsha bayan ta gama shirinta tsab, sai ta ɗauki zumbulelen hijabinta har kasa ta zura a jikinta sannan ta yo waje.
Kai tsaye Kitchen ta nufa, hijabin nata ya rufe koina a jikinta, baka iya ganin komai nata sai hannunta da ta fitar ta cikin hannun hijabin domin ɗaukar plate ɗin ruwa da kuma glass cup, sai drinks kala biyu da ta ɗaura a saman plate ɗin ɗaya maltina ne ɗayar kuma coca colar.
Sai sauri take yi ta ɗauki plate ɗin ta fito waje, ta ƙosa ta kai musu ta wuce wajen Akila suna jiranta, karfe 7 daidai Akil ya ce zai karɓi haddar kafin ya wuce masallaci, idan ya dawo sai ya kara masu, yanzu kuma karfe 6:50 bata wani biya haddar sosai ba, tana saurin ta kai masu ta zo ta sake biya haddar da kyau dan kada Akila ta fita kokari.
Sai sauri take zubawa ga hijabi zumbulele har kasa kamar matar liman, ta doso kofar ɗakin kenan, ba shiri ta ja wani irin birki, lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata wani irin daɗaɗan murya da bata taɓa jin irin shi ba, a nutse wannan murya yake tashi yana bada wani irin sauti mai ratsa dukkan ilahirin ganganjikin ɗan adam mai sauraro, kira'ar Alqur'ani mai girma yake rerawa cikin suratul An'Am, kai daga jin wannan murya kasan mamallakinta karshe ne wajen natsuwa da kamala da kyau, da iya rera karatu, domin yadda yake fito da ayoyin nan ɗaya bayan ɗaya, a nutse ko wannan yake fita ba tare da kaucewa wata wasaliba, kai da ga ji kasan ya kware a kira'ar Alqur'ani mai girma.
Ta jima a tsaye a bakin kofar tana sauraran wannan daɗaɗar muryar da bata taɓa jin irin shi ba, tabbas mai wannan murya ba bahaushe bane, domin yadda yake yin karatun tamkar irin limaman larabawan nan ne, babu baki na hausa ko ɗigo a wannan murya.
Almost 10mins tana tsaye, bata iya motsawa ba har sai da ta ji ya kai aya, ma'ana ya kai karshen surar. Cikin natsuwa ta fara takawa dan ta shiga cikin ɗakin, zuciyarta ta ƙosa taga wanene mamallakin wannan sexy kuma cool voice ɗin.
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo, Imran yana zaune saman bed nasa ta baki baki, yana riƙe da wata yar karamar roba kamar na maganin ciwon kunne, sai juya robar yake yi yana yan dube-dube a jikinta, kamar yana leman wani abin.
Nan take wani murmushi ya bayyana a fuskarta sakamakon murmushin da ya sakar mata, bata yi magana ba shi ma kuma bai yi magana ba, hannu ya sa ya nuna mata gefe ɗaga cikin ɗakin, wajen da yake Sallah, sai lokacin ya ce "Ga wanda zaki kai wa ruwan, amma akwai sanyi sosai ko? Dan kin ga azumi ya yi kuma kin san su da sabo da sanyi".
Fuska