Showing 111001 words to 114000 words out of 355604 words
har wani harbawa take yi da karfi karfi. Akila na kawo ruwa Abba ya karɓa ya buɗe ya miƙa masa, ba musu ya karɓa ya fara sha, domin ya fi bukatar ruwar sama da komai a yanzu.
"Aafia me kuka yi wa yayan naku?" Abba ne ya tambaya yana dawo da kallonsa kan su. Sai kuka suke da kyar da kyar, sun kasa magana, Akil duk ya fashe musu jikin su, domin mahaukacin duka ya musu, wadda idan ana irin shi ko ina ake sauƙewa mutun bulala shine mahaukacin duka.
Sun jima a haka sun kasa magana, ita kam Rufee ma kwanciya ta yi plat a kasa domin ta samu ta rinƙa kwakwalo numfashin ɗan numfashi da ya rage mata yake fita da kyar.
Kamar daga sama suka ji muryan sa cikin tsawa yana faɗin "Aafia ki gaya mini gaskiya, idan kika kuskura kika yimini karya, na yi bincike na gane abin da kika gaya mini karya ce wlh da hannuna zan kashe ki!!!". Ihu Akila ta kurma jin abin da Akil yake faɗe shi kansa Abba ba shiri ya ja baya kaɗan dan ya samu damar ganin shin da gaske Akil ɗin ne ko ba shi ba, ita kan ta Umaisha da take matarsa sai da ta kara waro idanuwanta dan ta tabbatar shin shi ɗin ne ko dai an yi mata canjin shi.
"A'afia kin taɓa sanin namiji a rayuwar ki?!!" Jin tambayar suka yi tamkar saukar aradu, domin babu wanda ya san dalilin da ya sanya ya yi musu wannan ɗan iskan duka haka.
Girgiza kai ta fara yi ta kasa magana, wata uwar tsawa ya daka mata wadda ya sanya ta buɗe baki ba shiri "Zaki buɗe baki ki yi mini magana ne ko sai na taka wuyarki a nan?!!!".
Jikinta sai kerma yake yi, hannunta ya kasa tsayawa waje guda, da kyar ta iya buɗe baki murya na rawa ta ce "A'a ban ta ɓa ba"
Abba ne ya ce "Akila ke da Umaisha ku wuce ɗaki" cikin sauri ya dakatar da su "No Abba ka kyalesu a nan, gara su ga komai da idanuwansu domin duk wanda ta yi gigin kamanta abin da Wannan tsinanniya ta yi to tabbas ni da kai na zan yankata, zuciyata ba zata iya jurar ganin ɗaya daga cikin nawa ya aikata zina ba" ya kai karshen maganar yana nuna Rufee.
Abba dai kansa ya kullu, su ma su Akila kan su ya ɗaure, suna bukatar sanin mekefaruwa a nan wajen.
"Akil ka gaya mana wai me yake faruwa ne" Abba ne ya tambaya yana kara tsaresa da ido.
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Akwai wata rana dana je Abuja, na sauƙa a hotel, ina kwance cikin ɗaki na naji ana knocking, na gaji sosai amma haka na daure na ta shi naje ya buɗe kofarnan, ina buɗewa idanuwana suka yi mini arba da wannan shaiɗaniyar yarinya, tana cikin maye, ta sha giya ta bugu ta fita hayyacin ta, sai layi take yi, ina kokarin yi mata magana sai wani matashin a ɗakin kusa da ni ya fito yazo ya ja hannunta yana faɗin "Baby sai da nace miki kada ki sha kayan nan yau zan mai daki gidanku, amma kin zo kin ɗebi kaya, kayar ma dayawa, ga shi sun bugar dake sosai, yanzu a haka zaki koma gida? Zama ki iya shiga gidan kuwa? Koda na sauke ki a kofar gida? Na san mama basu da matsala dan kin koma a buge Matsalar dai shine ki iya karisawa cikin gidar, ga shi nan da ɗaki na ma kin kasa ganewa kinzo kina buga wa mutun kofa" ya kai karshen maganar tare da jan hannunta ya rungumeta yana bani hakuri suka shiga ɗakin su dake kusa da nawa, tana buge lokacin shiyasa bata iya gane fuskata ba, shine yanzu ta zo har tana yi wa matata sharri"
Wani irin sanyi Akila ta ji lokacin da Akil ya ce sharri Rufee ta yi wa Umaisha, Allah sarki ya san halin matarsa farin sani, ya san abin da zata yi da wanda ba zata yi ba, kuma ba wanda ya isa ya zo ya ce masa matarsa ta yi kaza ya ɗauka, yana da dogon nazari da tunan a kan abu, ba da kai yake yin abuba, baya karɓar jita jita, sai dai idan ya ji da kunnensa ya kuma gani da idonsa
(To da Akil ba mai tunani bane da mekuke tunanin zai ɗauki Umaisha?)
Jin abin da Akil ya ce ya sa Abba a fusace ya ce "Ka taka ta har sai ta gaya maka gaskiya, domin abokin ɓarawo ɓarawo ne, dole sai hali ya zo ɗaya ake abota, wannan mummunar abin a family'n mu, a'a wlh ba zata sakuba, ka mata duk abin da zaka yi mata har sai ta faɗi tsakaninta da Allah" yana kai karshen maganar ya wuce ransa a matukar ɓace.
Har ya kai kofar fita sai kuma ya juyo ya ce "Ka je ka sanar da Deen ina daka masa warning a kan kula da yarannan, hauka yake yi ne ace kawayen ƴaƴansa ire-iren wayan nan, aikin me yake yi da ba zai bincika dawa suke tare ba? Kullun ranar Wednesday sai na shirya naje makarantar su Akila ba tare da sanin ta ba, haka kawai zan je in zauna a office na detector, dan naga suwa ye kawayen ta da sukawaye take tare, duk wanda na gansu tare sai na yi bincike a kan yanayin tarbiyar gidan su, amma daga kai har Imran ba wanda ya san da hakan bare kuma ita Akilar, dan haka ka ce da Deen na ce ya shiga hankalinsa ya dawo cikin hayyacinsa da kyau, ya san abin da yake yi, neman kuɗi ba hauka bace, dan nasan yanzu bai wuce ya ce yana fita baya zama ba, to idan ma haka ne ka ce ina ba shi umarni da ya auro musu wata uwar da zata kula da su tun da wancan ta watsar da su".
"Abba ai bappa yana da mata ya yi aure" "ya yi aure?" Abba ya furta da mamaki a kan fuskarsa.
"E Abba ya yi aure" shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Me matar tasa take yi da bazata kula da yaran nan ba? Yanzu ma ai Aafia ita kaɗai ta rage, me yasa ba zata kula da ita ba? Ko dan ba ita ta haifeta ba ne?" shiru Akil ya yi dan ba shi da amsa.
Sai da ya ji Abba ya fara faɗa sosai yana zagin Aunty sai ya ce "Abba kayi hakuri, matar da bappa ya aura yarinya ce sa'ar su Aafia ɗin, kaga kuwa ba zai yiwu ta basu kulawa kamar babbar mace ba, domin za su rinƙa ganin ai kan su ɗaya da ita, dan haka ni zan yi magana da bappa zan ɗauki Aafia ta dawo nan domin na bata tarbiya da ta rasa a baya, amma kafin nan sai na yi bincike dan na tabbatar da gaskiyar abin da ta gaya mini" Albarka Abba ya sanya masa sannan ya wuce ya fice daga ɗakin.
Dawo da kallonsa kan Rufee ya yi cikin tsawa ya ce "Idan kika sake yi wa Aafia magana sai na take wuyarki kowa ya huta, ba ke babu yar uwata, ke ma Aafia ki buɗe kunnanki da kyau ki saurare ni, zan canza miki makaranta zuwa school ɗin su Akila, amma kafin nan zaki cigaba da zuwa school zuwa next week mu samu transfer later, wlh idan ki ka kuskura kika bari na samu labarin kin sake yiwa wannan shegiyar magana sai na lahira ya fiki jin daɗi, yau a gidan nan zaki kwana gobe da safe ki shirya ki wuce school tun da naga kun buɗe, idan kun tashi ki wuce gida zan zo na yi magana da Bappa, ke kuma kafin na shiga ɗaki na fito, ki tashi ki bar gidan nan idan ba haka ba kika bari na fito to zan tattaka miki wuya!!" yana kai karshen maganar yana nuna Rufee da hannu.
Da kyar ta iya miƙewa ta ɗauki jakarta dake saman sofa ta fice daga palon bakinta sai jini yake yi, shi kuma Akil ya koma cikin bedroom nasu dan ya canza kayan jikinsa, dan duk ya nannaɗe wajen dukansu.
Yana shiga ɗaki Akila ta lallaɓa Aafia suka wuce ɗakinta, ita kam Umaisha ta kasa motsawa daga in da take tsaye, abin duniya sun taru mata, mamaki take yi daman haka halin Rufee yake, tun da jimawa take ta ce wa Aafia ta fita harkar Rufee amma taki yarda to ai yau ga shi ta ji asalin wace ce Rufee, har Abuja take zuwa bin maza, wa iya zubillah.
Tana tsaye tana tunani har Akil ya fito ya same ta, bata ji fitowarsa ba, sai jin hannunsa ta yi ya shafa mata fuska yana janyota jikinsa.
"My baby tunanin me kike yi? Kada fa ki je ki saka wa kanki tunani ki jamin rashin morewa yau". Da yake ya saba yi mata magana a dunkule ba wani gane wa take yi ba, sai tayi murmushi kawai ta ce "Me haɗin tunanina da jin daɗin ka kuma?".
Matso da bakinsa ya yi daidai sai tin kunnenta kamar wani na part ɗin zai ji su, kasa-kasa ya ce "Idan kina cikin damuwa ruwan daɗi ba zai zo ba" rufe fuska ta yi tana murmushi, shima murmushin kawai yake yi. Bawan Allah yana matikar son Umaisha duk ɓacin ran da ya shiga yana ganin fuskarta yake shiga cikin farinciki.
Rungume a kirjinsa take suka fita daga palon bayan ya ɗauki wayarsa da laptop da ya ajiye, haka suka wuce zuwa cikin motar sa, sai bayan sun shiga motar da kan shi ya ɗaura mata nikaf ɗin a fuskarta sannan ya tada motar suka bar gidan zuwa restaurant.
(Gaskiya aiki ya ganku, kullun sayan abinci, kai Umaisha a dage a koyi girki, idan ba haka ba irin su Rufee suna nan a duniya masu kwace maza🤣🤣 ni dai na haɗa kaya na zuwa gidan daddy gidan comedy wato Washington DC dan muji ya ake ciki)
💖💖 Washington DC💖💖
Misalin karfe 4:30 na asuba Musharraf ya tashi ya nufi kitchen a palon kasa kenan, da kansa ya haɗa tea mai kauri sannan ya dawo part ɗin su.
Saman dining table dake palon part ɗin, ya ɗaura tea ɗin nasa, sannan ya wuce bedroom na Michael.
Yana baje a saman bed nasa, ya rungume pillow a kirjinsa, sannan ya sanya wani pillow a tsakanin kafafunsa, kyakkyawar fuskar nan tasa sai kyalli take yi, tamkar wadda ya shafa baby oil, soft skin ɗin nan nasa kamar bai taɓa taka kasa ba, kyakkyawar brown curly hair sannan ya bazu masa har saman idonsa, da yake shi yana rage tsawon gashin nasa, baya barinta ta kai na lion da James tsawo, ya ce takura masa yake yi, shiyasa yake yankewa ya bari iya goshinsa, ta baya kuma iya bayar wuyarsa.
Ɗakinsa sai ta shin daddaɗar kamshin air freshener irin na ɗakin Lion ta ke yi, shi kan shi tashin haɗaɗen kamshin perfume nasa yake yi, yana sanye da dogon wando da riga mai dogon hannu na barci, kayan suna da laushi kuma basu da nauyi, yan shara-shara ne, launin Ash color.
Barcinsa yake yi cikin kwanciyar hankali, yana sauƙe numfashin nan nasa a hankali-hankali.
Musharraf ya ɗan jima yana karemasa kallo, hutu iya hutu suna da shi, dukkansu Triplets suna da bala'i farin jini ga shegen shiga rai kamar me, duk da cewa basu kula kowa, sannan da James da Lion sun fi Michael kwarjini, shi ma James Lion ya fishi sosai, shi Lion abin da ya sanya wasu ma suke tsoron haɗa ido da shi, idanun nasa sun kasance tamkar ya sanya musu kwalli, ga shi dai kwayar idon nasa blue ne, sannan farin ciki kuma farine tas, amma kasar idanun nasa tamkar ya zana musu kwalli, wajen baƙi ne, sai kuma ya haɗe da dark black zara-zaran eyelashes nasa masu tsawon gaske, hakan ba karamin karawa idanuwansa kwarjini suke yi ba, akwai wasu sirrika na musamman a tattare da idanunsa, wadda sai wanda ya iya kallon cikin idanun nasa zai gane hakan, sai dai har yau ba'a samu mai karfin zuciyar iya kallon cikin kwayar idanun nasa ba, sai dai gefe-gefe.
Shi kuma James design na idanuwansa ɗaya ne da Lion, sai dai na Lion ya fi nashi girma, sannan nasa bai yi kamar an sanya kwalli ba, normal ida ne nasa, shi kuma Michael ba in da design na idanuwansa suka baro na uncle T da ya rena.
A hankali Musharraf ya haye saman bed ɗin, fuskar sa ya fara shafawa yana kiran sunan sa a hankali-hankali "Michael, wake up" ina ai Michael baya duniyar mutane yana can hanyar Englan.
Sai da Musharraf ya masa kira uku sannan ya ɗan motsa, a kunne Musharraf ya raɗa masa ya tashi lokacin sahur ya yi, kamar zai yi kuka ya turo baki tare da tuɓune fuska, cikin magagin barci ya ce "Please uncle leave me alone". Ba yadda Musharraf bai yi ba, amma ya ki tashi, haka ya hakura ya kyalesa ya wuce ya nufi waje.
Tea ɗin sa ya ɗauka ya sha sannan ya koma ɗakin sa dan ya je ya yi alwala ya yi sallar raƙatainil fajir dan asuba ta kusa.
Da safe kamar kullun misalin karfe 6 Tga ya zo ya tashi Michael, dan tun da suka sha punishment suka dai na goyawa Michael baya, da wuri suke tashin sa ya je ya fara gym nasa.
Yana turo baki yana yi har sai Romeo ya fito, yanzu ya fara sabawa da gym ɗin.
Bayan ya gama gym ɗin ya yi wanka ne ya wuce wajen Musharraf.
Kwance ya isko sa samar gadonsa yana askar da kansa ba tare da littafi ba. Kusa da shi yazo ya zauna yana faɗin "Uncle ɗin James barka da hutawa".
Miƙewa zaune a tsakiyar gadon ya yi yana kallonsa "Michael me yasa na yi ta tashinka kayi sahur ka ki ta shi?" Nisawa ya yi ya ce "Uncle ai ba dole sai anyi abin da ka ce ɗin ba ake iya ɗaukan azumi, na sani ai saboda pastor ya gaya mana". Murmushi Musharraf ya yi yana faɗin "Eh ba dole sai an yi sahur ba, amma yana da kyau ne ayi ɗin"
Jinjina kai ya yi kafin ya ce "To shikenan ni haka zan yi babu sahur ɗin, amma ina da tambaya?" Tattara hankalinsa waje ɗaya ya yi ya zuba masa ido yana faɗin "Ina jin ka mece ce tambayar taka?"
"Idan ina azumi zan iya shiga toilet? Sannan zan iya yin wanka?" Gyaɗa masa kai Musharraf ya yi sannan ya shiga rabe masa abin da aka halaktawa mai azumi da kuma wanda aka haramta masa.
Sosai ya gamsu ya kuma yi alkawarin zai kiyaye. Haka suka cigaba da hirarsu har zuwa karfe 11 a nan wajen barci ya yi awon gaba da Michael, yana yin barci Musharraf ya fara tofa masa addua'o'i kamar yadda ya saba.
💖After some hours 👌
Misalin karfe biyu na rana Michael ya fara yi wa Musharraf kuka da hawaye a kan yinwa yake ji, shi gaskiya ba zai iya wannan azumi ba, idan Musharraf ya ce masa to ya karya ya ci abinci, sai kuma ya sake saka wani sabon kukan yana faɗin, idan ya karya azumin ai shikenan basu yi dayawa ba James ba zai dawo ba, abin har mamaki yake bawa Musharraf kuma ya fara tsorata kada Romeo ya ji halin da Michael yake ciki, ga shi kuma shi Micheal baya karya, a na tambayar shi, zai faɗa cewa Musharraf ya sanya shi yin azumi, dan su roƙi Allah James ya dawo gida da wuri, idan su Tga suka ji wannan maganar za su gane cewa Musharraf musulmi ne, kuma yana neman musuluntar da Michael, daga nan kuma ya shiga uku a hannunsu, ga shi zaman shekara huɗu zai yi da su, ba halin ya ce zai bar gidan, ba zai yi wu ba, zama da su ya zama dole, kuma ukuba ya zama dole ya karɓa, ko yana so ko baya so, dolema ya so domin punishment ɗin Tga yana maka kuma kana dariya, ba halin ka ɗaure fuska.
Bawan Allah duk ya kiɗime ya shiga tashin hankali, cike da ruɗu ya rinƙa rokar Michael a kan ya karya azumin dan Allah, har da yi mashi alkawarin zai haɗa masa tea da kansa, amma ina Michael ya murje ido ya ce ba zai karya ba, kuma yaki dai na yin kukan ƴunwa.
(Babbar magana Musharraf kana tsaka mai wuya, kai sarkin shisshigi ba)
Da kyar Musharraf ya samu Michael ya sake yin barci, sai rokon Allah yake yi Allah yasa kada Michael ya tashi sai mangariba, idan ba haka ba, yana tsaka mai wuya. Bawan Allah ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai zarya yake yi a cikin ɗakin, ga yunwar azumi, da zarar ya ga Michael ya yi motsi zai yi maza ya je ya duba ya gani ko ya tashi ne.
Sai Misalin karfe 4 daidai Michael ya farka, ya farka kuma da sabon kukan ƴunwa, yau ɗaya har ya rame, sai kwala-kwalan brown eyes zaka gani, sai rarrashin shi Musharraf yake yi amma ya ki yin shiru.
A wannan hali Tga ya zo ya same su, bedroom ɗin Michael ya fara shiga baya nan, ya zo zai fice sai ya ji magana a ɗayar ɗakin shine ya shigo.
Cikin tsawa ya ce "Michael what brought this man in to your part...?!!" Bai gama rufe baki ba, idanuwansa suka sauƙa kan hawayen dake fuskar Michael ɗin, a zafafe ya kariso wajen yana faɗin "What happened Michael?" Shiru Michael bai yi magana ba, sai kukansa yake yi.
Wani wawan damka Tga ya yi wa wuyar Musharraf, har sai da Musharraf ya ji kamshin lahira, wani irin mahaukacin tsawa ya daka masa "Me ka yi wa Michael yake kuka?!!" Musharraf ya kasa magana dan ba damkar wasa Tga ya yi wa wuyarsa ba, sai zaro idanuwansa waje yake yi.
A fusace Tga ya ɗaga hannu zai wanka masa mari, cikin sauri Michael ya shiga tsakaninsu marin ta sauƙa a kan fuskarsa, ji kake yi tas, ihu Michael ya saki mai ɗan sauti, domin ƴunwar da yake ji, tasa sautin sa bata fita sosai.
A sukwane Tga ya saki Musharraf ya fara shafa kumatun Michael ɗin yana bashi hakuri, kuka kawai Michael yake yi ya kasa magana.
Tga ya