Showing 339001 words to 342000 words out of 355604 words

Chapter 114 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2747

ya yi masu halitta wadda ina da tabbacin ko su aka ce su yi halittar kansu ba za su yi ya wuce hakan ba, saboda sun hallitu kyau iya kyau, kuma Allah da ikonsa dukkansu TRIPLETS ɗin halittar kafarsu iri ɗaya haka zali hannunsu har yatsun hannayen nasu iri ɗaya.

Sai kallon kafafun nasa take yi, ganin haka yasa cikin zolaya ya ce "Kafar Lion ya fi nawa kyau fa". Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi. Zuba mata idanu ya yi sai kallonta yake yi kafin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya sannan ya ce "Rimsha you are so very very beautiful, gaskiya ina matukar son ki da ɗan uwana, I don't know the reason why nake jin kin kwanta mani a raina, you are very lucky gaskiya, ban taba expecting cewa akwai wata rana da zan bawa mace goyon baya akan abu ba, and also my brother he is very lucky idan har ya same ki, cos na san ba zaki bani kunya ba, and then ba zaki taɓa ɓatawa ɗan uwana zuciyarsa ba, daga ni har su muna da bukatar mu sami soyayya wadda zata goge mana memory mu ta baya, mu iya soyayyar daddynmu kawai muka sani, yana da kyau yanzu mu san wani, am very sure ɗan uwana zai samu irin wannan soyayya a tattare dake, na san zaki yi mamakin faɗa da nake yi akan ɗan uwana ba akan kai na ba ko?" duk da na zayyano kyawawan zaton da nake yi maki, nasan zaku yi mamakin me yasa ni ban ce ina sonki ba sai dai in ce ina sonki da Lion, to kada ki yi mamaki, ki sani ɗan uwana ya yi mana abun da ba zamu iya biyan shi ba, sai dai mu yi mashi addu'a, yana kaunar mu fiye da kansa, kullun cikin yi mana abin da muke bala'in so yake yi, bamu taɓa ce mashi muna son abu ya ce mana a'a ba, idan kuma kika ga ya ce mana a'a to tabbas wannan abun ya bincika ba Alkhari bane a gare mu, idan muna cikin damuwa baya iya barci har sai ya fitar da mu, ɗazun na ce maki soyayyar daddy kawai muka sani ne domin ban yi niyar jan magana dake ba, amma a zahirin gaskiya soyayar da Lion yake yi mana tafi ta daddy, so kin ga kuwa yana da kyau muma duk abin da muka san zai zama na Alkhari a gare shi, to ya kama mu tsaya sosai wajen ganin mun sama mashi shi, sannan bugu da kari shi mutun ne mai wuyar sha'anin, shawo kansa akwai bakar wahala, idan muka samu ya yarda dake shikenan, amma yardar ne wahalar domin zuciyarsa ta fi cutuwa akan abin da mace ta yi mana sama da tamu zuciyar, bai iya gaba ba kamar yadda bai iya so ba, abubuwa biyun nan duk wanda yake yi to fa yana yi ne da gaske babu wasa, idan ya so ka to da gaske ne kuma zaka ji matukar daɗi, haka idan ya kika ba zai taba yi wuya ya sake son ka ba, mawuyacin abune ya waiga ya kalli mace, kai ina da wuya ma hakan ta kasan ce, amma muna sa ran hakan a tattare dake, shi wani irin bahagon mutun ne wadda duk yadda kuke ba zaki taɓa gane ina ya dosa ba, so na san abubu da dama akan shi, shi ne ma dalilin da yasa na tsaya akan ki, domin kina ɗaya daga cikin irin mutanen da yake so, na farko kina da tarayya mai kyau da kuma kyakkyawar zuciya, na biyu hankali, kina da hankali sosai, na uku ilimi, na huɗu son addini da kuma aiki da abin da addini ya koyar da mu, na biyar iya soyayya." Ya yi magana ta karshe na iya soyayya yana ɗaga mata gera ɗaya.

Ɓoye fuska ta yi a jikin Imran tana murmushi. "Kina mamakin yadda aka yi na san abubuwa akan ki ko?". Cikin sauri ta ɗago da kan nata tare da gyaɗa mashi kai alamar e tana mamaki.

"Zan gaya maki amma ba yanzu ba, sai dai kuma ki sani babu abin da ban sani ba a kan ki wadda Prof ya sani, sai dai prof ya ɓoye mani cewa ke ba kanwarsa bace, ni kuma na gano hakan ne ta wata hanya da shima sai nan gaba zan gaya maki, yanzu dai ina zaku je?".

A wannan karon Imran ne ya bashi amsar in da za su je ɗin, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Okey amma dai ya kamata mrs Saif ta dai'na fita gaskiya, cos tun da gyara za ku je tom ayi gyara sosai zan sanya Lion ya biya kuɗin gyaran ta hanyar da bai yi zato ba, kai dai prof idan ka ga kuɗi a account naka kada ka kira shi ma bare ka tambaya har ya gane plan na ne, Rimsha kada ki kuskura na ji ko na gani kin kula wani ko kin kalli wani, dan nima ina da bala'i kishi kamar ɗan uwana, to amma yau Monday me ya hana ki zuwa school?".

Imran ne ya amsa mashi da shi ya hanata zuwa dan za su je shopping da sauran su, sosai Areef ya ɓata rai in da ya yi wa Imran ɗin faɗa sosai akan kada ya kuskura ya sake wannan gangancin dan za su fita ya hanata zuwa school, ba za su hakura da fitar sai ta dawo ba, ita ma faɗa ya yi mata sosai akan kada ya sake jin ta yi hakan.

To ta amsa da shi sannan suka yi sallama, da kyar Areef ɗin ya miƙe dan ya rakasu, Imran yana ce mashi ya bari ya bari shi kuma ya ce a'a gara ya rinƙa takawa a hankali hankali zai fi mashi.

Haka dai ya rakasu har harabar gidan sannan ya dawo ya zauna a palon kasa dan ya ɗan huta, har cikin zuciyarsa ya rasa dalilin da ya sanya yake kaunar Rimsha, har mamaki abin yake ba shi, ta shiga zuciyarsa farat ɗaya, amma dai ba wa kansa yake yi wa kaunar tata ba, ɗan uwansa yake yi wa, dan shima Lion ɗin ya samu farinciki a rayuwarsa, su kuma kullun Lion ɗin yana cikin sanya su farinciki, shi ne dai bashi da mai sanya shi sai dai su ɗin, to yana da kyau ya samu gaskiya, duk da abune mai matukar wuya, amma Areef yana sa ran tabbas da izinin Allah za su yi nasara, tun da har Aseef ma ya sa baki za su yi nasara, yanzu dai fatan ya samu lafiya kawai yake yi.

Imran kuwa gidan Abbi ya wuce ya ɗauki Jelly, Hanan da kuma Akila suka wuce.

Wajen gyaran jiki suka fara zuwa aka yi masu su dulka da sauransu. Yaran nan sun dawo kamar wasu taurari, daga nan sai kunshi da aka zana masu mai shegen kyau, Rimsha kamar wata tauraruwa haka ta zama, ga wannan curly hair nata ya sha gyara sai santin shi su Akila suke yi, da haka suka wuce shopping in da ya saya masu atamfofi da laces dan baya son irin shigar da Rimsha take yi a gidan nan nasu, saboda ya lura sojojin nan sun fara saka mata ido, ga shi kuma wani lokaci suna fita su barta a gidan ita kaɗai, kada wata rana su fita sojojin su cutar da ita, kuma idan suka cutar da ita ko da Lion ya hukunta su ko kashe su ma ya yi sun riga da dai sun cuceta dai, abin da ya wuce ba zai dawo ba, to maganin bari kada a fara, kuma ya duba gaba ɗaya kayanta dukka kanana ne, abayas ɗin ma basu da yawa sosai, wannan dalili yasa ya saya masu atamfofi da laces dan ayi mata ɗinkin hausawa ta rinƙa dressing mai kyau tana rufe jikinta dan gudun matsala.

Daga wajen shopping ɗin suka wuce wajen ɗinki dan su bada kayan ɗinki. Da suka je Imran yaki yarda taila ya gwada su, shi da kansa ya karɓa ya gwadasu sannan ya gayawa tailan size nasu ya rubuta, sosai Rimsha ta ji daɗi da Imran ya yi hakan, domin dama a cikin zuciyarta ba yarda zata yi tailor ya taɓa ta ba.

Tailor ya faɗi kuɗinsa Imran ya yi mashi transfer sannan suka wuce suka nufi gida.

Sai misalin karfe 4 na yamma Imran suka dawo gidan Lion bayan ya mayar da su jelly da niki nikin kayan da suka saya gidan Abbi, ansha yawo ansha shopping da gyara, sun yi kyau fiye da tunanin mai tunani bare ma Rimsha kam ba'a magana, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigawa ya kalleta.

Suna shiga cikin palo kamar yadda suka saba ɗakin Areef suka fara shiga, baya nan, da mamaki suka fita suka haura sama.

A Palon sama suka isko shi yana zaune saman sofa yana shan coffee. Kusa da shi Imran ya je ya zauna ita kuma Rimsha ta nufi bedroom nata dan ta ajiye niki nikin kayan hannunta bayan ta gaishe shi kenan.

"Wannan murna da faricnikin fa na menene?" Cewar Imran, yana tambayar Areef ɗin. Fuska ɗauke da murmushi Areef ya ce "Daga yanzu zuwa ko yaushe zaka iya ganin uncle Musharraf da nake gaya maka, baka ga babu motar Lion a waje bane? Ai ɗauko mani shi Mark ya je yi a airport".

Murmushi shima Imran ɗin ya yi zai yi magana kenan suka ji sallama a bakin kofar palon, a tare suka kai kallonsu wajen, Musharraf ne da Mark dake a bayansa ya yi mashi jagora ne zuwa cikin gida, sun je ɗakin Areef ɗin baya nan shi ne suka bi yo shi nan sama.

Sai murmushi Areef yake yi tare da yi masu iso, shi kuma Imran a razane ya miƙe tsaye yana faɗin "Yallaɓoi dama kai ne uncle Musharraf ɗin?". Sai lokacin Musharraf ya lura da Imran dake wajen, jinjina mashi kai ya yi alamar e shi ne.

Cike da murna ne ko tashin hankali ne Imran ya kasa gane wa, da karfi ya kwalawa Rimsha kira yana faɗin "Rimsha ki zo ga daddynki" ya yi maganar da turanci da yake yanzu ba su cika yin magana da hausa ba saboda su Areef ɗin da basaji, yaren, so sai turancin kawai ya bi bakinsu suma.

Wani irin miƙewa Areef ya yi yana mamaki daddyn Rimsha kuma? Allah sarki shine dalilin da ya sanya Areef yake kaunarta kenan.

Ita kuma jin abin da Imran ya ce ne yasa ta fito da gudu yayin da shima Musharraf ɗin ba shi da burin da ya wuce ya ganta ɗin, domin a nasa tunanin dukka family'n sa sun mutu basu raye, shiyasa time da ya dawo Nigeria ya ga gidansa a rufe da kwaɗo sai kawai ya zaɓi da ya bar kasar baki ɗaya tun da ba wanda ya rage mashi a cikin su mummy, kuma dama a tunaninsa yasan da wuya ƴan adawa su kyale mashi family'n sa tun da shima sun yi yunkurin kashe shi Allah ya tseratar da shi, wannan dalili yasa ya bar kasar gabaɗaya da nufin kuma ya barta kenan ba zai kara dawowa ba.

Ganin tabbas da gaske daddyn tane yasa ta kwansa a guje ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, shi dai Areef ya kasa magana, sai ma murmushi da yake yi domin yanzu ya kara samun karfin gwiwa wajen taimakawa Rimsha akan abin sonta, tun da ta kasance ƴar cikin Musharraf to halin kirkinta ma ya wuci hakan domin duk abin da Musharraf ya rinƙa yi wa Aseef suna sane da shi, shi kuma Areef Allah ne kawai ya jarrabe shi da kaunar Musharraf ɗin ba ma wai dai abubuwan da ya yi masu ba.

Rimsha an sha kuka kamar ba gobe, shima Musharraf sai da ya yi kwalla, Areef da Imran ne suka rinƙa rarrashinsu, da kyar suka yi shiru, duk fa wannan abin da suke yi Lion yana bedroom nasa yana jinsu, sai aikin latsa waya yake yi kamar babu shi a gidan.

Bayan sun yi shiru komai ya lafa ne daddy yake tambayarta ina su mummy, nan take gaya mashi ita ma bata sani ba, ita kaɗai ta rage, daga nan ne sama sama ta shiga bashi labarin abubuwan da suka faru har izuwa yau, ya sha kuka kamar ƙaramin yaro. Akan siyasa aka tarwatsa mashi farincikinsa, wannan bala'i dame ta yi kama, kowa duniya kawai ya sa a gaba.

Shi dai Mark yana tsaye ne kawai yana binsu da ido dan ba jin me suke faɗe yake yi ba, shi dai kawai ya ga ana magana ana kuka, shima dai Areef kukan kawai yake ganin ake yi, bayan haka baya gane komai tun da ba yaren yake ji ba, amma dai ya fahimci labari Rimsha take bayarwa, sai daga baya bayan komai ya lafane an sha kuka an koshi sannan Imran yake mayarwa da Areef abubuwan da suka faru, sosai Areef ya jinjina kai tare kuma da yi wa kansa alkawarin idan ya samu lafiya dole ya bankaɗo gaskiya, dole ya yi bincike akan suwa ye suka yi wa Uncle nasa hakan, a cikin rayuwar Areef idan ka cire TRIPLETS nasa to Musharraf shine mutun na biyu da yake kauna, haka Allah ya jarabce shi, hakan kuma yasa ya yi alkawarin biwa uncle ɗin nasa hakkinsa, ba zai bar Nigeria ba sai ya yi wannan aiki koda kuwa ita zata zama aikinsa ta karshe a duniya ko a hukumance.

Shiru suka ɗan yi na ɗan lokacin, sai shesshekar kuka Rimsha take yi ta lafe a jikin daddynta, zama daddy ya yi ta zauna a saman cinyarsa tare da kwantar da kanta a kirjinsa idanunta sun yi jawur saboda kuka, suma su Imran komawa kowa ya yi ya zauna, Areef dai abin ya yi mashi daɗi sosai da Rimsha ya kasance ƴar Musharraf.

Katse masu shirun daddy wato Musharraf ya yi da tambayar a ina Rimsha take zama yanzu, wannan karon da turanci suke maganar. Nan Imran ya ba shi labari yadda ake ciki, ai kuwa daddy ya ji babu daɗi, cike da jin haushi kuma cikin yaren turanci dan ma Areef ya ji ba sai an fassara mashi ba, ya fara magana "Ba zai yi wu Rimsha ta zauna cikin zaratan maza haka ba, ba zan yarda da hakan ba, dan haka ta kwashe kayanta mu je na mai data gidana na nan Kd, ban yarda ta zauna a nan ba, maza tashi ki kwaso kayan ki mu tafi". Ya kai karshen maganar tasa cikin izza da nuna isa akan ya isa da ita.

Ita kuwa cikin zumuɗin ganin daddynta yasa ta miƙe ta shige ciki dan ta haɗo kayanta, sai faɗa daddy yake yi akan me Imran bai kai ta gidansu ba ko kuma gidan Abbi da zai kawo ta nan cikin maza, ga Areef bashi da lafiya kuma yasan halin turawan nan sarai wasu basu da hankali idan sojojin nan suka yi mata wani abin fa, idan baku manta ba Musharraf suna da kwantaciya a kasa tsakaninsa da Lion na marinsa da Lion ya taɓa yi, hakan yasa Musharraf ɗin baya son Rimshan ta zauna a nan dan sanin bakin halin irin na Lion.

Shi dai Areef sai ƙoƙarin dannan daddyn yake yi domin Lion na gida, shi kuma Lion idan yana waje ba wanda ya isa ya nuna yana da izza ko kuma ya nuna yana da iko da wani matukar yana waje, idan yana wajen to shine sarki, shi ne zai yi iko da kowa, idan ka yi gigin kin hakan to fa ka shirya kukan da mutuwa ta fi maka sauki, hmmm kuma ga shi a cikin gidan Lion ɗin daddy ke nuna izza yana magana son ransa har da nuna isa, ai da wuya daddy ya wanye lafiya da Lion ɗin.

Ai kuwa Rimsha tana fito da trolley ta akan su tafi Lion ya fito daga cikin ɗakin daidai lokacin kuma da daddy ya miƙe akan su tafi.

Tsare Musharraf ɗin da waƴan nan idanun nasa masu rikitar da ɗan adam ya yi, sannan gently in a cool voice ya fara magana "Ke wuce ki koma ciki, kai kuma wuce a mayarda kai in da ka fito, magana kake yi akan tana zaune a cikin maza ko? To kasani daga yau ta zama ƴar aikina, even gyaran bedroom ita zata yi, abinci komai dare idan ban ci ba to bazata yi barci ba dole sai ta kawo mani, kuma ta jira na ci sannan ta yi barci idan na bata izini, kamar dai yadda ka ga bodyguards na gida haka zata zama mana ƴar aiki, turawa basu da hankali ka ce ba? zan gwada maka kuwa, zaka ga karshen zama a cikin maza".

Cikin sauri Areef ya ce "No Lion please ka kyale shi ya zauna to, idan ya so sai su zauna da yarinyar tasa, you know fa ina kaunarsa....".

Wani kallo ya wurgawa Areef ɗin wanda ya sanya shi haɗiye maganar tasa ba tare da ya karisa ba. Tsawa ya daka masu akan ya gama magana Musharraf ya wuce a mai da shi Airport ya koma Washington DC, daga yau ya mashi hannu riga da Rimsha tun da har da nuna masu izza a cikin gidansa, to ya rabasu ya ga karshen tsiya, kuma dole ta zauna a cikin maza ta yi masu aiki domin ba shi kaɗai zata yi wa aiki ba, harda su Areef da su Mark sai ya ga karshe rashin kunyar Musharraf, zama cikin maza yanzu ta fara karo wasu sojoji ma zai yi su kara yawa a gidan su kai ko su 12 ta yadda zai tabbata yes a cikin zaratan mazan take zaune ita kaɗai mace bakinciki ya kashe Musharraf ɗin su gani.

Ba yadda Areef bai yi ƙoƙarin fahimtar da shi ba akan ya yi hakuri ya kyaye Musharraf, amma ina baya magana biyu, sai ma tsawa da ya kara daga masu wadda ta sanya Rimsha kwasowa a guje tare da sakin trolley ɗin nata ta rungume daddyn tana kuka kamar ranta zai fita, duk yadda take son zama kusa da Lion to bai kai rabin son kasancewa da iyayenta, tana son kasancewa da daddy ta da yanzu kewarsa ya yi mata katutu.

Shi dai Areef ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login