Showing 159001 words to 162000 words out of 355604 words
jacop ba dai kyautaba, gaba ɗaya Triplets suna da kyau da akwairi sosai, ba su jin kyashi wajen bayarwa, haka zalika idan za su bada basu duba cewa wanna ba addininsu ɗaya ba ba zasu ba shi ba, a'a duk da cewa basu son wata addini sai nasu hakan baya hana su bawa kowa kyauta idan suka ta shi. Ikon Allah kenan
Wani bawan Allah da Michael ya bashi kuɗin, duƙawa kasa ya yi ya fuskanci gabas ya yi sujudur shukur yana hawaye, taɓa Musharraf Michael ɗin ya yi yana tambayar sa me yasa wannan mutumin kuma ya yi sujjada ba lokacin sallah ba, a takaice Musharraf ya warware mashi me sujudur shukur yake nufi.
Jin haka yasa Michael ya duƙa suna fuskantar juna da mutumin, cikin mutuntawa ya ce da mutumin "Me yasa yake jin matukar daɗin dan ya ba shi wannan ɗan kuɗin?".
Mutumin yana hawaye ya fara magana "Yau tun da na shigo masallaci nake ta rokan Allah da ya bani abin da za mu ci ni da family na, lokacin da na yi sujjadar karshe a sallah har hawaye sai da na yi dan yau kwana biyu ba'a yi girki a gida ba, Alhadulillah, Allah shine arrahman mai rahama akan bayinsa, shine wadda idan ka roƙe shi da kyakkyawar niya da kuma yakinin bayan shi ba mai iya baka, to zai cika maka burinƙa cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga shi ban bar masallacin ba Allah ya biya mani bukata ta da na roƙe shi, Alhadulillah Alhadulillah, Allah ne ya bani ta sanadiyar ka, ina godiya ɗan uwana" ya kai karshen maganar tare da miƙe wa ya nufi hanyar fita daga masallaci.
Dawo da kallonsa kan Musharraf ya yi domin ya yi mashi karin bayani dan gane da mutumin nan, ai kuwa tun bai tambaya ba Musharraf ya fara yi mashi karin baya ni, daga karshe ya rufe da cewa "Mutumin yana da karfin imani, idan da wani ne, kai zai ta zubawa godiya yana faɗin ka taimake shi ka bashi kuɗin sayen abinci, amma da yake wannan yana da imani ya san ya kamata, sai ya fara godewa Allah sannan ya gaya maka da bakinsa cewa Allah ne ya bashi ta sanadiyar ka, wannan shine gaskiya, idan da wasu ne cewa za su yi kai ka basu, irin mutanen nan basu da yawa sosai a duniyar yanzu".
Yana kai aya a maganarsa Michael ya jawo hannunsa suka nufi mota, bai yi magana ba dan yasan dole akwai dalilin da ya sanya Michael ya yi hakan.
Bayan sun shiga mota sai ya kunnata suka bar masallacin.
"Michael ina kuma za mu je? Ka mance cewa za mu jira sai anyi sallar la'asar ne kafin mu koma gida?" "Uncle ban mance ba, ai ba gida za mu koma ba, kai dai ka jira ka gani" to kawai Musharraf ya amsa da shi, sai gudu yake shararawa da motar har suka fita daga kan titi suka tsallaka cikin wata unguwa, wadda da ka ganta ka san yan unguwar nan takaici ya yi masu katutu.
Haka ya ci-gaba da kutsawa motarsa cikin wannan anguwar. Bakin wani gida wadda da ka ganshi kasan talauci ya yi masu katutu over, a nan ya juya kam motarsa suka sake fitowa daga unguwar suka nufi wata tampatsetsen Super market, wadda ya amsa sunan sa super market.
A bakin gate ɗin shiga Super market ɗin tambarin sunan James ne a wajen, hakan na nufin Super market ɗin mallakin james ne.
Ciki ya kutsa motarsa, bayan ya yi barkin ya fito, suka shige cikin shopping ɗin, kai da ga ganin wannan wajen kasan babu abin sa zaka nema ka rasa, mutun ne kawai basu saidawa.
Kayan abinci Michael ya fata loda da abubuwan amfani na gida, ciki har da fridge mai ɗan girma, sai binshi da ido kawai Musharraf yake yi, duk wani abin da yasan ɗan adam zai buƙace shi a gida sai ya nunawa ma'aikatan dake binsa a baya, masu kula da masu sayan kaya dan su taimaka masu ta in da suka gaza, idan ya nuna masu sai su fitar mashi.
Sai da ya lodi kaya har sai da Musharraf ya ce mashi ya isa haka nan, ina zai kai uban kayan nan haka? Bawan Allah tausayi ya rufe mashi ido, anguwar talakawan nan ya tayar mashi da hankali, mutumin da ya bawa kuɗi a masallaci nan ya tsaya mashi a ransa, kuma hakan yasa ya bi bayan mutumin har zuwa anguwar su, a nan ya ga tashin hankali, domin sosai ya rinƙa karo da yara ba takalmi a kafarsu, suna kuka riƙe da kwano a hannunsu alamar suna jin yunwa, kawai hakuri ya yi ya daure ya kawarda kansa domin ya bi bayan mutumin kada ya ɓace mashi, da suka je ya ga gidan ne sai ya juyo suka zo wannan shopping ɗin.
Ɗaya daga cikin motoncin super market ɗin ne ta kwashi duk kayan da ya saya, dama suna da manyan motonci masu baya wadda idan ka yi shopping ɗin da motarka ba zata iya kwashe su ba, sai su ɗaukar maka da motorsu su kai maka har in da zaka je, kuma kyauta ne shi wannan kai kayar.
ATM nasa ya bada suka ciri kuɗin kayan, sannan aka loda su a bayan motar, shi kuma shi da Musharraf suka shiga nasu motar suka yi gaba motar super market ɗin ta rufa masu baya.
Kai tsaye kofar gidan wannan mutumin da ya bawa sadaka a masallaci suka nufa, a wannan karon daga ɗan wajen anguwar ya yi parking na motarsa ya fito suka kariso da kafarsa da Musharraf, wancan karon da kyar ya iya fitar da motar tasa daga unguwar ne, shiyasa yanzu ya barta a waje.
Knocking na kofar gidan mutumin ya yi, kofar katako ce taci wuya sosai, wannan karamin yaro ma idan ya bugata da karfi zata ɓalle, ta sha ruwa sosai ga rana, duk ta zazzage.
Daga cikin gidan wata mata ta amsa da ana zuwa, komawa gefe ya yi ya tsaya yana jiran fitowar su, yan unguwa kuma sai kallonsa suke yi.
Mutumin da ya bawa kuɗin a masallaci ne ya fito, ganin su yasa ya fara ba su hakuri ya ɗauko kuɗin da Michael ɗin ya ba shi daga aljihunsa da nufi ya mai do musu da shi, dan a tunaninsa kuɗin su suka zo karɓa, Michael ya sanya face mask ga glass ba wanda ya gane wanene, nan take yan unguwa suka fara fitowa suna karisowa wajen dan su ji menene.
Mutumin nan kuka yake sosai yana gaya musu idan ma wani laifi ya yi mu su to dan Allah kada su taɓa mashi familynsa shi su hukunta shi, idan kuma kuɗin su suka biyo to ga kuɗin nan dama yanzu zai je ya sawo masu abinci, yana magana yana hawaye gwanin ban tausayi, dan a irin kallon da ya yi wa dressing ɗin jikin Michael yasan ko a ƴaƴan manyan kasar ma sai wane da wane za su saka irin kayan, hakan ne ma yasa ya kara tsorita sosai da sosai.
Matsowa kusa da shi Micheal ya yi ya rungume shi, dama shi ma ba baya ba wajen ruwan hawaye, nan take ya fara nasa hawaye, dan har ga Allah zuciyarsa ta yi mugun taɓuwa ganin mutanen nan cikin wannan hali, Allah sarki tun bai san menene falalar sadaka ba ma tukun nan, domin karatunsa bai kai nan ba, yana da tausayi sosai, dama ciwonsa ta mai da shi mara tausayi mara imani, ina da yakinin yawan sadaka da kyauta da yake yi ne ya sanya Allah ya cito shi daga duhun kafurci izuwa hasken musulunci.
Wayan su yaran mata kanana guda biyu ne suka fito daga cikin gidan, dukkansu mata ne ba za su wuci yan shararu 6 zuwa 8 ba, sakin mutun Michael ya yi ya riƙo hannun yaran yana tumbayarsu menene sunan su, tsoro ya hana su gaya mashi sunan su, sai kallon babansu suke yi, ciro handkerchief daga aljihunsa ya yi, ya gogewa mutumin hawayen da ke a kan fuskarsa, shi ya sanya face mask a fuskarsa nasa hawayen bai bayyana ba, sannan ko kaɗan bai ji kyamar mutumin ba, duk da yake talaka yana da tsabta sosai, jikinsa tsab, shiyasa ma ya rungume shi ba tare da ya ji kyama ba, haka kuma yasa ya goge mashi hawaye da handkerchief nasa ba tare da ya ji wani abu ba.
"Baba kana da yaro namiji". Michael ɗin ne ya tambaya, sai kallon shi mutumin yake yi da ya yi magana, domin yana son gane wanene, amma Michael bai bari hakan ta faru ba, saboda bai son asan ya je masallaci, idan aka sani a gida, yana da tabbacin wlh kashe shi za su yi, sai dai su kashe shi suna kuka, amma sai sun harbe shi.
"E ina da yaro amma karamine 15 years yake da shi" to Michael amsa da shi sannan ya ce ya kira mashi yaron, wayan nan yara biyun da suka fitone, ɗaya daga cikin su baban ya aika ta kira mashi yaron, shi kuma Michael ya sanya wayan nan ma'aikata super market kwara biyu da suka biyo su akan su sauƙe masu kayan abincin.
Ba ɓata lokaci suka fara sauƙe abin cin, da kansa ya raba abincin ya nuna masu wadda za su shigar wa da baba cikin gidansa, saura kuma su rabawa mutanen unguwa, har kasa baba ya duƙa yana hawaye, ganin farincikin da yake a kan fuskar bawan Allah nan sai da ya sanya Michael zubar da wani hawaye, ba zai iya jure ganin yadda jama'a ke ta yi mashi ruwan hawaye suna duƙawa suna zuba mashi godiya ba, dan haka sai ya kama hannun yaron baba da ya fito yanzu suka ɗan koma gefe suka bar wajen.
"What is your name?" Ya tambaya yana shafa kan yaron, yaron ga shi kyakkyawa, ga innocent face irin na babansa, da gani ya samu tarbiya irin ta addinin Musulunci, ya samu ilimin addini sosai, a nutse sosai yake.
"My name is Aryan" yaron ya bashi amsa, maimai ta sunan Micheal ya yi yana kokarin tunano a ina ya taɓa jin wannan suna, sai bayan wasu yan sakannin sai ya tuna ashe sunan da Musharraf ya ba shi ne farkon musuluntar shi, yar murmushin ya yi, Micheal kenan duk gidan William jacop shi kaɗan ke murmushin, ko su John basu murmushin, shima ɗin da addinin musulunci ta ratsa shi ne ya san e murmushi Sunnah ce da fiyayyayyen halitta manzon tsira manzon Rahma Annabi Muhammad (SAW) hakan yasa yake yin murmushin sosai a yanzu, bayan shi ba wani mai murmushi a cikin su, Lion da Tga kam ai dama su sai dai ma ace zuciyar kafuran farko ce ko kuma dutse ne a kirjinsu saboda kwarewar su a zafin kai, zafin zuciya, da mugunta.
"Matakin karatun ka fa a ina ka tsaya?" Nan Aryan ya gaya mashi yana Jss 2 kuɗin makaranta ya kare ya dakata da karatu bai cigaba ba, shiru ya ɗan yi kafin ya sake cewa "Idan na buɗe maka business zaka iya zama har ka kula da shi ka taimaki iyayen ka da yan uwanka?". Michael kenan akwai kaifin basira, ya san cewa ka bawa mutun kuɗi ko abinci idan ya zo neman taimakon abin da zai ci ba shi ne ba, idan ka ba shi kuɗi ko abinci cikin ƙanƙanin lokaci zai cinye su, amma idan kana da hali ka taimaka mashi ka gina shi akan sana'a to nan ne ka yi mashi babbar taimako wadda koda million nawa ya samu agaba duk lokacin da ya taimaki wani ɗan adam da wannan kuɗi kai ma kana da lada sosai, kuma bashi sana'a da zaka yi hakan zai sanya zuciyarsa ta yi kwari ta ki mutuwa, zaka karfafa shi ya miƙe da kafafunsa, Michael akwai kwakwalwa wajen tunanin tun da Allah ya buɗe mashi ƙwaƙwalwarsa sanadiyar addua'o'i da Musharraf ke yi mashi, wa su addua'o'i ya tofa mashi a ruwan sha, wa su kuma a kan nasa yake tofa kashi, hakan yasa ƙwaƙwalwarsa ta fito da asalin kaifinta, gaba ɗaya yaran William jacop akwai su da kaifin kwakwalwar balai, har shi kan shi daddy yana da ƙwaƙwalwar domin lokacin da yake school kullun shine first class, mara kwakwalwa ba zai iya zama babban likita kamar shi ba, sai dai shaye-shaye da ya rinƙa yi bayan ya fara tsufa ce ta taɓa mashi lafiya, amma shima ba baya ba wajen kaifin basira.
Cikin sauri Aryan ya ce "E zan yi sana'a koma wace iriya ce" "To gaya mani idan ka samu kuɗi sosai a wajen business ɗin me zaka fara yi da su?" Ba tunani ba komai kai tsaye Aryan ya fito da amsoshinsa, ta yadda zaka san abin yana ransa sosai.
"Zan mai da su Suhana school, zan je in biya masu school fees, daga nan in sawo abinci sosai in kawo gida, dan baba ya daina shan wahalar neman, kullun idan ya fita sai kaga ya dawo a gajiye, wata sa'an ma sai ya dawo ya shiga ɗaki ya yi ta kuka, kuma duk saboda abinci, saboda bai kawo abinci ba, su Suhana suna kukan yunwa, ina jin zafin hakan, tom abinci shine abu na biyu da zan kawo gida, na uku kuma kullun ranar Jumma'a zan rinƙa sawa ana girka abinci sosai ana kaiwa masallaci domin wayan da basu da shi su rinƙa samu suna ci a can, na huɗu kuma zan rinƙa koyawa kannena sana'a, ma'ana idan sun sami hutun makaranta akwai in da ake koyar da sana'o'in sosai, can zan je na biya kuɗi su rinƙa koya, dan karda su taso ba su iya wata sana'a ba, suce sun dogara da baba, bayan kuma shima fama da kansa yake yi, na biyar kuma...." Michael bai bari ya karisa ba ya rufe mashi baki yana faɗin "Irin ku ake bawa jari wayan da suka san abin da suke yi, ga shi yanzu a maganar nan taka kasa na samu karin wata haske, dole nima zan nemo kwararru wajen iya girki, arinƙa dafa abinci ana kaiwa masallatai dan marasa karfi su ci".
Sosai Aryan ya ji daɗin yadda Michael ya karɓe shi hannun bibbiyu, a wannan hali Musharraf ya isko su, nan ya tambayi meke faruwa, Michael ne ya labarta mashi yadda suka yi da Aryan, ba ƙaramin daɗi Musharraf ya ji ba, ya yi murna sosai hakan yasa ya kara karfafa masu gwiwa ta hanyar gaya masu falallar sadaka, duk masifar da musulmi yake ciki, matikar zai juri yin sadaka, tofa Allah subhanahu wata'ala shi ka kansa ya yi alkawarin ya ye mashi wannan damuwa, sannan aduk sadaka da mutun zai yi babu sadakar da ta fi falala irin sadakar abinci, tana da falala fiye da tunanin mai tunani, cikin kankanin lokaci Allah zai warware maka damuwar ka, matukar zaka juri yin sadakar abinci koma ya ya take.
Wani karin karfin gwiwa na musamman Michael ya ji a tattare da shi, lokacin guda ya ji zai iya karar da duk wani abin da ya mallaka akan sadaka da taimakawa bayin Allah.
Da wannan shawara Michael ya ce da Aryan gobe zai dawo su je ya duba irin sana'ar da zai iya sai ya buɗe mashi shago a kasuwa, sannan batun makaranta zai je har school ɗin ya biya masu kuɗin makaranta, daga haka suka koma wajen baba, already ma'aikatan Super market ɗin James sun gama rabon kaya sun shigarwa da baba nasa cikin gida, sun koma wajen aikin su, wato sun koma super market ɗin, jama'a sun watse.
A kofar gidan Michael ya tsaya ya ce da Aryan ya kira mashi babansa suyi sallama, da sauri Aryan ya shiga cikin gida, shi kuma Michael ɗin suka cigaba da hira da Musharraf, yana kara gaya mashi falalar taimako da sadaka.
A haka baba ya zo ya isko su, ya ce su zo su shiga cikin gida, fuska ɗauke da murmushi Michael ya ce a'a nan ma ya isa tafiya za su yi yana son sanin ko akwai wani abin da yake buƙata ne, cikin sauri baba ya ce a'a baya bukatar komai ya kara da zuba masu ruwan albarka da godiya sau ba adadi.
Ganin godiyar baba ba zai kare ba ya sa Michael ya yi musu sallama, Aryan ya raka su har wajen mota, Michael yana jin kaunar Aryan a ranshi tamkar ɗan uwansa na jini, tsabar farinciki har ya rasa me zai bawa Aryan, sai ya ɗauko ruwa daga cikin motar tasa roba ɗaya ya miƙa mashi, sai murmushi Musharraf ya ke yi, haka suka ja motarsu suka koma masallaci.
A ɓangaren Lion kuwa.
Sai karfe 8 na safe ya farka daga barci, a hankali ya waro dara-daran blue eyes nasa, sai wani kyalli fuskarsa take yi, wow yau ya sami barci mai daɗi, ga yanayin gari ga shi kuma yana wani irin yanayi mai daɗi wadda shi kaɗai ya san menene silar shigarsa wannan yana yi, a hankali ya janye lallausan bargon dake jikinsa, shiru ya ɗan yi na mintoci yana tunanin akan mafarkin mum ɗin su da ya yi daren ji, me yasa take yawan zuwa mashi a mafarki a cikin wata iriyar suffa mai wuyar gane wa, yana buƙatar amsa akan hakan.
Ya jima kwance yana ta zarin abubuwa guda biyu, na farko mum ɗinsa, na biyu kuma tafiyar da zai yi gobe. Bayan wani lokaci a hankali ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasa kafin ya miƙe gaba ɗaya, ya zauna a bakin gadon, bin ɗakin nasa da kallo ya fara yi, tun karfe shida na safe Tga ya gyara mashi ko ina ya feshe ko ina da daddaɗar air freshener sa mai bala'in kamshi da kyau da tsada, kasa tiles ɗin ɗakin tsabar haske kamar madubi, da yake tiles ɗin fari ne kana iya ganin kanka a ciki, ga shi yana samun gyara, sai ka rantse da Allah kafa bai taɓa taka shi ba saboda haske.
Jawo laptop nasa ya yi domin ya yi bincike a cikin camerar da ya sanyawa mum ɗin sa a kofar gate ɗin shiga gidan ta, saboda yana son gane gaskiya tsakanin ita da daddy, waye ya cuci wani, sannan kuma yana zarginta da shiga irin kungiyar su James, domin wayan can mutane guda biyu da ya taɓa kamawa, ya kama sune da manyan kwayoyin maye da kuma sun yi wa wata yarinya