Showing 168001 words to 171000 words out of 355604 words
Afnan, sanin haka yasa ya samu waje saman chair ɗin tabla ɗin ya zauna yana faɗin shima a zuba mashi abincin kawai ya ci.
Cikin sauri Ummi ta ce "Fitar fa ya zaku yi?" Rai a ɗan ɓace ya ce "Haba Ummi kinsan dai idan Baby ta samu kaza ba'a magana, bata kula kowa, bata kasancewa a duniyar mutane, dan haka a barshi kawai sai wata saan".
Cikin mayen kaza da kuma santi ba tare da ta kalli in da yake ba ta ce "Yaya Nawid ka faɗi gaskiya, aradu kaza tafi duniya daɗi, wai yaya Nawid ka cire wannan abin da aka rufe maka a kasar gadonka kuwa? Sannan na gaya maka wannan Abbon kwarto ne amma kaki yarda, to yanzu kuma ya zama ɗan iska domin yana kallona sosai". Girgiza kai kawai Ummi ta yi babu wanda ya ɗauki zancenta da gaskiya domin suna yi mata kallon mahaukaciya, bare kuma idan ta samu kaza ai shikenan kuma, sai ta kara haukacewa da gasken-gaske.
Ba wanda ya kulata suka zauna suka gama cikin abincinsu, ita kuma har lokacin tana fama da kaza, kamar wata mai aljanun kaza a kai.
A ɓangaren su Rimsha kuwa, kamar yadda Akil ya basu umarnin kawo hadda da karfe 5 haka suka shirya suka yi wanka, suka yi sallah tare da cin abincin rana da suka girka suka shiryawa kansu, a palon Imran suka zauna suna jiransa. Sai 5:10 ya shigo shi da Umaisha, sai murmushi suke yi wa juna, da alama dunuyar tana yi masu daɗi, daga gani kasan sun mace akan juna.
Saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna su kuma suka yi maza suka sauƙa kasa, Akila tana ruƙe da Alkur'ani mai girma, ita kuma Rimsha ta ce zata kawo da kai ba tare da Alkur'ani ba, sai dariya Umaisha take yi wa Akila da alama wani munafurcin suka haɗa, kasa ya ce ita ma Umaisha ta sauƙa, ba musu ta sauƙo kasa, kafin ya fara karɓar haddan nasu ne ya tambayi Akila ina A'afia bata dawo bane, E ta bashi amsa, shiru ya ɗan yi kafin ya ce to su kawo haddansu zai je gida ya same ta.
Da haka suka rufe babyn Aafia suka fara bada haddansu, dukkansu sun kawo daidai, kuma ya jinjina masu, kyautar maki mai girma ya basu, sai ya ce su kara tusawa domin ya zauna a ƙwaƙwalwarsu da kyau, sai zuwa gobe da safe zai kara masu wani shafin. Sai murna suke yi suna zuba mashi godiya, a tare suka miƙe za su tafi.
"Karatun boko da luttatafai fa?" Ya jefo masu tambaya, cikin sauri suka dawo suka zauna, Akila ce ta ɗauko takardunta suka fara koyan karatu, ita kuma Umaisha ta ɗauko masu littafai irin su Nahhu, muɗalaa, malumat, da dai sauran littatafan musulunci, zama suka yi suna ɗaukan karatu da kyau, har da ƙawa'idi, ahlari a ciki, sai karfe 6 kamar yadda ya faɗa suka tashi, cikin hanzari suka faɗa kitchen dan su shiryawa bakon yaya Imran girki kamar yadda ya faɗa.
A tare suka fara aikin, wannan ta kama wannan, wannan ta kama wancan, sai hira suke yi Akila tana bawa Umaisha labarin saurayin Rimsha, wato yaya Ahmad, ɗan anachen Rimsha in ji ita Akilar, shine sunan da ta bashi, sai dariya suke yi, ita kuwa Rimsha ta tsare gida kam, babu alamar dariya ko wasa a tattare da ita, ta yi shiru sai ki rantse da Allah bata a wajen.
Fried rice suka yi ya ji kayan kamshi, su green beans da sauransu, Rimsha ce mai basu command, ita ma wani abin sai ta buɗe takardun girkin sannan take dubawa.
(Manya suna aiki fa.)
"Aunty Akila ke ki haɗa mana ganye, ke kuma Aunty Umaisha ki zuba abincin a kuloli ni kuma bari na haɗa pepper chicken" to suka amsa da shi sannan suka fara aikin da ta basu, abin duk wanda ya gansu sai sun ba shi sha'awa, sosai sun haɗa kansu kaman yan uwan juna, da yake Akila da Umaisha duk basu da matsala sai suka ja Rimsha sosai ajikinsu.
Bayan sun gama tsab, suka fito palo ana kiraye-Kirayen sallar mangariba, bedroom na Rimsha suka wuce, Akila ta ce a nan za ta yi wanka, ita kuma Umaisha ba dan ta so ba ta wuce Part nasu, Akil da Imran kuma sun tafi masallaci.
Rimsha ce ta fara yin wanka tare da ɗauro alwala, bayan ta fito Akila ta shiga.
Zama Rimsha ta yi a gaban mirror ta shafe jikinta da mayukanta masu daɗin kamshi tsab, sannan ta feshe perfume nata masu daɗin kamshi, kafin Akila ta fito har ta gama shafa mayukan da duk wani abin da zata yi a gaban mirror, saura saka kaya, lokacin ita kuma Akila ta fito ɗaure da towel a kirjinta, itakuwa Rimsha lokacin da ta fito, bayan towel da ta ɗaura sai da ta sanya ɗan karamin mayafinta da ta shiga da shi, wato gyalen abayar ta, dan bata son Akila ta ga zanen dake a kan kirjinta, shiyasa ta sanya mayafin a kanta ta rufe har kirjinta.
Riga da wandon da Akila ta ce su yi anko shi, shi ta ɗauko ta sanya, kayan sun karɓeta sosai da sosai, da rigar da wandon dukka masu kama jikine, sannan rigar zuwa gwiwarta ya tsaya mata, an zuba mashi kwalliya a gaba sosai, kai da gani kasan yana da tsada sosai dan ya haɗu over, launin pink color ne da milk, haka ta sanya su, amma kafin ta saka sai da ta sanya vest a ciki, domin wuyar rigar tana da ɗan girma, idan har bata sanya vest ba wannan zane na sunan Lion zai iya bayyana kowa ya gani, dama kuma saboda zanen yasa da suka je shopping ta ɗauki dozen na irin vest ɗin nan masu kama jiki sosai kamar roba, dan bata son kowa ya gani ma bare kuma ya tambayeta me yasa zata rubuta sunansa.
Bayan ta gama shiri sai da ta sake fesa turare sannan ta zura hijabi har kasa ta zauna a bakin gado tana jiran Akila, domin ta tafi sanya nata kayan ita ma.
Jiran minti goma ta yi sai ga Akilar ta dawo shirye cikin nata kayar irin ɗaya suka yi anko, akalla Akila zata bawa Rimsha good 4 years da yan ɗori, amma da yake Rimsha tana da tsawo sai kansu ya yi kusan ɗaya, da kaɗan Akila ta ɗara ta, dan suma ƴaƴan Abba ba baya ba wajen tsawo. Yanzu Rimsha an fara zama ƴan mata tula-tula sun fara girma.
A tare suka yi Sallah, bayan sun idar suka wuce palo dan su ɗan yi kallo. Suna zama saman sofa Rimsha ta ɗauki remote ta shiga News, Rimsha yarinya mai Sa'a duk time da ta shiga News zancen mutumin nata ake yi, yau ma ta yi Sa'a maganarsa ake yi, ga kuma hotonsa nan an kafe kamar kullum yana sanye da face mask.
Kamar ance ta kalli fuskarsa, ai kuwa idanunta suka sauƙa akan nasa, ba abin da ya faɗo mata a ƙwaƙwalwarta irin yadda taga idanuwansa a zahiri cikin mafarkinta, yadda ta gansu muraran, tuna hakan yasa ta runtse idanuwanta, tana tunanin yadda yake a zahiri, wannan idan ka ganshi zaka iya mutuwa.
Ji tayi ba zata iya ganin fuskarsa ba, koda kuwa a hoton ne, mugun razana ta yake yi, hakan yasa ta yi maza ta canja tasha. "A'a Rimsha me yasa zaki kashe mani jarumina ina tsaka da kallo?". Cewar Akila.
Ba tare da tayi magana ba ta miƙe da sauri ta koma cikin ɗaki, daidai lokacin aka kira sallar isha. Saman dadduma ta hau tana hawaye tana Sallah, ta rasa meke damunta, tana bala'in son wannan mutumi, amma kuma duk lokacin da ta kalli even pic nasa da glass ba iya face mask ba, sai ta yi mugun razana, sai ta fi awa uku tana takure waje guda tana razana, kamar wadda taga wani dodon ko wani abin, idan kuwa tana kwayar idonsa a hoton, ma'ana babu glass wunin ranar zata yi shine ba cikin walwala ba, ta rasa menene dalili, tana sallah tana kuka, ko da ta kai sujjada, ya jima sosai tana kuka tana rokan Allah da ya rabata da son wannan mutumi a zuciyarta, ta kuma yi danasanin rubuta sunansa a kirjinta.
A wannan hali Akila ta iskota, bata kawo komai a ranta ba, ganin tana sallama yasa ta yi tunanin kenan dama ƙiran Sallah da akayi ne yasa ta baro palo da gudu ta dawo ɗaki, da farko ta zaci ko wata matsalace, amma ganin tana sallah yasa ita ta tsaya kusa da ita tare da tada kabbara ta fara Sallah.
Rimsha bata bari Akila taga hawayen fuskanta ba, tana idar da sallah ta miƙe ta shiga toilet, lokacin kuma ita Akila tana raka'a na uku ne, tana shiga toilet ta wanke fuskarta sosai, sannan ta fito ta zauna gaban mirror ta ɗan gyara fuskar tata, ta miƙe ta nufi palo.
Bayan Akila ta idar da sallah ta yi addu'a sannan ta bi bayanta, daidai lokacin su Imran suka dawo masallaci, shi da Akil.
A palon suka baje suna hira da dariya, fito da wayarsa Akil ya yi ya kira Umaisha dan ta zo su yi hira a tare, aikuwa ba ɓata lokaci sai ga ta nan ta shigo, haka suka cigaba da hira cikin annashuwa, shi kuma Ahmad sai kiran layin Rimsha yake yi amma wayar na ɗaki ta sanya ta a silent. Sai wuraren karfe 9 da Imran ya samu sakon Nawid akan ba zai samu damar zuwa ba, saboda Jelly ta samu kaza, dariya Imran ya yi sosai ya ce "Ashe kuna da maganinta a gida ma ka tsaya kana wahalar da kanka, ai nan gaba idan ta dameka da ku fita yawo kaza kawai zaka saka Ummi ta soya mata sai ka haɗa ta da shi ka huta". Shima Nawid ɗin dariya ya yi, Imran duk ɗaukansa kanwar Nawid ɗin da ya ce an kawo ta da ga family Abbo ya zaci yarinya ce da bata wuci 8 to 10 years haka ba, shiyasa ma yake yiwa Nawid tsiya irin haka.
Haka suka yi ta hiransu na abokai daga bisani suka yi sallama da juna, Imran ya cewa su Rimsha su kawo masu abinci su ci, saboda Nawid ya ce ba zai samu zuwa ba, cike da murna suka kawo abincin Akil sai mamaki yake yi, yar yarinya kamar Rimshan nan ne ta iya girki, da farko ya ce ba zai ci ba, domin yana ganin kamar jagwalgwalo kawai suka yi, amma daga baya da Imran ya matsa mashi, sai ya ce a sanya mashi kaɗan, ai kuwa yana fara ci ya ce a kara mashi, sai dariya Akila ta ke yi mashi, ta ce "Wai yaya Akil ka manta ka ce duk mace da bata haura shekara talatin ba, ba zaka ci girkinta ba, domin ko masu shekara ashirin da biyar yara ne kamar mu, ba'a gama ya ye mu ba?". Harara ya wurga mata ita kuma Umaisha cewa ta yi "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dama yaya Akil abin da ka faɗa kenan? Lallai ma, to wlh yanzu zan ko yi girki idan ba zaka ci nawa ba, ni ma ba zan ci na restaurant ba".
A kule ya ce "Idan kuma na bada umarnin ki ci dole fa?" Still dai fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "E sai na ci mana tun da kai kace, to bama dole na ba" Wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, Akil akwai bala'in son girma, wato tun da idan ya bada umarni zata ci shikenan ai ya huce, shi dai Imran, shi da Rimsha ban da murmushi ba wani abin da suke bin su da shi.
Bayan sun gama cin abincin sun yi komai, sun tattare wajen ne, suka yi wa yaya Imran sallama, Rimsha ta wuce ɗakin ta, Akila da Akil da Umaisha suka wuce cikin gida, shi kuma Imran ya ɗan jima a palon kafin nan ya tashi ya shiga bedroom nasa, ya yi wanka ya shirya cikin kayan barci, sannan ya kwanta.
Itama Rimsha wanka ta yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kaya barcinta masu kyau launin pink color riga da wando, dan tana son pink color, sky blue, da kuma fari, sune best color ɗin ta.
Bayan ta gama ne ta sake feshe ɗakinta sa air freshener sannan ta haye gado ta ja bargo tare da jawo wayarta ta fara kiran layin Ayla, amma a kashe sosai ta fara shiga damuwa akan me ya samu Ayla. Haka tana ganin kiran Ahmad amma bata ɗauka ba, saboda bata cikin yanayi mai daɗi, tana tunanin Ayla sosai. A wannan daren dai da kyar barci ya yi awon gaba da ita. Asuba ta gari.
Idan muka koma Washington DC kuma.
Kamar dai yadda suka tsara haka suka yi, sai da suka yi sallah la'asar sannan suka dawo gida, haka da mangariba tun karfe 6 suka fita gida, sai karfe 8 bayan sun yi sallar isha suka dawo gida, a palon Part ɗin Michael suka zauna dan yanzu dama ba su wani cika zuwa palon kasa ba, waya Michael ya yi akan bodyguard su kawo mashi kayan tea part nasa, haka kuwa a kayi ba tare da ɓata lokacin ba, sai ga bodyguard guda biyu, kamar kullun suna cikin dressing nasu na bakaken suit tare da bakaken glasa a kan face nasu, wato no respect.
Saman dining table dake a cikin palon suka ɗaura kayan tea ɗin tare da wani kyakkyawar flaks mai kyan gaske, kayatatcen tea ne wadda aka haɗa shi da ganyayyaki masu kara lafiya a jiki, shine a jikin flaks ɗin, haka suka ajiye suka juya suka bar palon.
Kallon Musharraf Michael ya yi yana faɗin "Uncle ɗin James ka je ka haɗa tea ɗin ni bari na je na yi wanka na duba Lion yau tun safe da muka rabu a gym ba mu sake haɗuwa ba" To Musharraf ya bishi da shi, sannan suka miƙe a tare, Michael ya wuce toilet shi kuma Musharraf ya wuce saman table ɗin dan ya haɗa tea ɗin sa.
A ɓangaren Lion kuwa, lokacin da ya gama zaman shi a lambun sai ya miƙe ba tare da ya sha fruits ɗin ba, maltina kawai ya ɗauka kwara ɗaya da glass cup ɗaya ya fito daga wajen.
Ji kake dip-dip-dip wani jibgegen Bature soja fari tas ya nufishi a guje, yana zuwa ya karɓi maltinan da glass cup dake a hannunsa, cikin girmamawa ya ɗaga hannu ya sara mashi tare da buga kafa, ba musu Lion ya miƙa mashi maltina dan dama dan dole ya ɗauko su, yana jin yunwa amma kuma suna da zama a white house karfe 10 yanzu kuma har 11 ta kai bai je ba, hakan yasa ya fasa shan fruits ɗin dama kuma ba wani niyar sha yake da shi ba, kawai dai bai son cin abincin safe ne yasa ya ce zai sha fruits ɗin.
Kasa kasa ya yi magana kamar mai raɗa "Ku tashi motoci za mu wuce white house" da sauri sojan ya sanarwa da sauran sojojin dake a kusa, kan kace me sun haye saman bayan motoncin, wannan sojan da ya riƙe mashi maltinan shi ya buɗe mashi motarsa ya shiga cikinta, bayan ya shiga ne sojan ya zuba mashi maltina cup, cikin girmamawa ya miƙa mashi, girgiza kai ya yi alamar baya buƙata, sojan bai ji komai ba, domin idan da sabo sun saba ba zaka taɓa gane me yake so ba.
Da gudun gaske suka tashi motoncin suka fice daga gidan, kai tsaye white house suka wuce, kamar dai ko yaushe duk wata abin hawa dake a kan hanyar sauka take ta basu hanya su wuce.
Lokacin da suka isa white house, gidan a cike yake tab da jami'an doka sojoji manya-manyan yan siyasa da duk wasu masu faɗa a ji a kasar, gaba ɗaya ko ina ka waiga sojoji da yan sanda ne cike makil a gidan, tun da jerin gwanon motocinsa suka shigo gidan, gaba ɗaya sojojin dake a cikin gidan suka fara kamewa suna sara mashi, wani sojan kam ma, saboda kamewa sai ka rantse da Allah baya numfashin. Lion duniya
Kamar dai kullum kun san mai hali baya fasa halinsa, to haka ne, Lion dai bai kula kowa ba, ko kallon in da suke ma bai yi ba, ya sanya face mask a fuskarsa ya fito, kai tsaye fadar shigaban kasa ya wuce, sojojin sa kuma suka dakata daga bakin kofa.
Yana shiga cikin fadar ya wuce Roosevelt Room, nan ya isko kowa ya haɗu ana jiransa, da gani ran kowa dake cikin wajen a ɓace yake, domin Lion ya ajiye su suna ta jira, ga Tga nan tun ɗazun ya iso wajen, amma shi sai yanzu, kuma haka za su hakura ba yadda suka iya da ahi.
Daga gefe kuma ga yan jaridun white house, wato yan jaridu masu fitar da abin da ke faruwa daga fadar shugaban kasar, manya-manyan mutane suna zazzaune saman tsadaddun kujerun dake a cikin ɗakin, wayan nan kujeru sun haɗu matika gaya, kuɗin wayan nan kujeru ba zai faɗu ba saboda tsadarsu, ta ko'ina Kamshi ke tashi a cikin fadar, amma Lion na shigowa kamshin perfume na jikinsa ya rinjayi gaba ɗaya kamshin da yake a wajen, sai room ɗin ya gauraye da irin kamshin perfume nasa, wani daddaɗar sanyin Ac ne ke a cikin ɗakin, wadda sanyin yana gudu daidai misali ba na wuce ka ida ba, ko wannan su akwai kayan sha masu bala'in sanyi a gabansu ga kuma kyawawan glasses cups a gabansu kusa da abin shan.
Shigowar Lion yasa gaba ɗayan su suka ɗago suka kalle shi, dayawa daga cikinsu kallo ɗaya suka yi mashi suka kawar da kansu suna ɗan satar kallonsa. Bai bi ta kan kowa ba, saman kyakkyawar kuma tsadaden kujerar kusa da His Excellency ya je ya zauna, shiru suka ɗan yi kafin His Excellency ya buɗe masu taro da fara magana.
Kasa Lion ya yi da kansa dan bai ma san akan me zasu yi maganar ba, lokacin da aka kawo mashi takardan bai duba ba, yana wani aikin, sai dai Tga ya sanar mashi cewa karfe 10 za'a yi zaman, iya abin da ya sani kenan, kuma dama bai nemi sanin akan me za su yi taron ba, domin ba ɗaukar maganar su yake yi ba, abin da ya