Showing 291001 words to 294000 words out of 355604 words
hoton irin face nata kawai zai bincika, idan ya bincika sai mu san a ina take".
Tsabar daɗi Imran bai san time da ya sake rungume shi ba, yau zuciyarsa fes, dama yasan idan Lion ya san da haka a cikin 24 hours zai nemo mashi Jellyn sa, suna da kayan aiki sosai, akwai wata shegiyar computer dake a gidansu a ɗakin bincikensa, idan ka sanyawa wannan computer sunan kasa da kuma abin da kake buƙa ta, kamar yanzu idan suka sanya hoton jelly da sunan kasarta suka ce suma buƙatar masu irin wannan face ɗin, searching system ɗin zai fara yi sosai akan fuskokin dake a Nigeria, da gudu gudu zai rinƙa searching ɗin, ba kamar kwakwalwar ɗan adam yake ba, akwai saurin yin aiki, abin da yasa basu gane ina James yake da wuri ba lokacin da ya ɓata saboda basu san a wani kasa ta ka maimai yake ba, wannan dalili kuma yasa Aseef ya ce duk ma in da Tga yake Lion ya sani.
Number Tyrone Lion ya tura wa Imran ɗin akan ya tura mashi hoton Jelly shi zai yi mashi bincike akan ina take. Daga haka suka yi sallama kowa ya wuce, Lion ya haye saman bed, shi kuma Imran ya wuce ɗakinsa ya je ya kwanta.
Washegari sai mi salin karfe 8 Rimsha ta farka daga barcin da ya ɗauketa tun bayan sallar asuba, da yake bata sami damar yin barcin dare sosai ba shine sai ta biya da barcin safe.
A hankali ta waro idanunta, ta ɗan jima kwance tana kallon sama, yau barcin ya yi mata mugun daɗi sakamakon Kamshin perfume ɗin Lion dake a jikin jacket ɗin jikinta da ta sanya, ji ta yi tamkar tare da shi ta kwana, yau mafarkinsa ma na musamman ta yi. Shiru ta kwanta tana tunanin mafarkin nata, abin ya kayatar da ita sosai, domin yau har taɓa kyawawan lallausan laɓɓan bakinsa ta yi a mafarkin, abin ba ƙaramin burgeta ya yi ba, bugu da kari na sharri irin na mafarki har da ce mata ya yi tana buƙatar lips ɗin ne, (oho Rimsha duniya.🤣)
Tuna hakan yasa ta sanya hannu ta rufe fuskarta dan rashin kunya wai kunya ta ji, hannu ɗaya ta kai saman tula tulanta tana shafawa tana tunanin sahibin nata.
Wani irin ƙugin yunwa cikinta ya fara yi, dama tun daren jiya tana jin yunwar bata wani ci abincin kirki a gidan Abbi ba sakamakon kewar ganin Lion da ke damunta, dannewa ta yi ta kwanta barci da yunwan dan ta ji kiwuyar shiga kitchen ɗin, kuma bata son ta bawa Imran wahala, ta san idan ta ce mashi tana jin yunwa a daren zai sake fita ya nemo mata abinci, dan haka sai hakura ta kwanta.
A hankali ta miƙe zaune tare da zuro kafafunta kasa sannan ta miƙe tsaye gaba ɗaya, hanyar fita daga cikin ɗakin ta nufa kai tsaye.
Har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo ta shiga dressing room dake a cikin ɗakin.
Jim kaɗan ta fito ba tare da jacket ɗin ba, da alama cire shi ta yi ta ajiye, kai tsaye waje ta nufa tana faman gyara hular barci dake a kanta.
A hankali take tafiya har ta sauƙo palon kasa, wani irin bakin yunwar safe ne ke nukurkusan cikinta, kai tsaye kitchen da Imran ya nuna mata ta nufa dan ta dafa abin da zata ci.
Tana saƙo kafarta a cikin kitchen ɗin da wannan sojan dake yi masu girki ta fara cin karo, yana tsaye a gaban gas daga shi sai Army three quarter trouser, daga ta sama kuma Army t-shirt ne a jikinsa, sai faman aikinsa yake yi, sai faman zuwa kwai a cikin ɗanyen namar da ya markaɗa yake yi yana kwaɓawa.
Wani irin warine ya daka mata kofofin hancinta, kamshin abin cin nasu ji tayi yana mata wani irin wati kamar zuciyar zai fito waje da ta shaƙa, su suna jin warin nata abin ita ma warin nasu take ji.
Daurewa ta yi ta gwada shiga cikin kitchen ɗin, sojan yana tsaye kamar gunki, tamkar bai san da shigowar mutun ba, dama kuma haka suke aikin gabansu kawai suke yi a gidan, basa shiga wani aikin da bai shafesu ba.
A guje ta sa kai ta fita kitchen ɗin sakamakon wani amai daya yunkuro mata, still har lokacin sojan nan bai ɗago kai ba, kamar ba shi a wajen.
Kai tsaye sama ta nufa tana toshe da baki dan kada ta yi masu amai a cikin palo.
Sosai take gudu domin amai ya ci karfinta bata ganin gabanta, bata ankaraba tana isa tsakiyar palon sama ta yi karo da mutun, wani irin baya baya ta yi ta faɗi kasa.
Kamshin perfume nasa ya isar mata da sakon koma wanene dan haka sai ta kasa ɗago kai ta kalleshi, tsabar tsorata kuma tasa gaba ɗaya ta nemi amai ɗin da take jin ta rasa, amai ya tafi kwata kwata bata jinshi.
Shi kuma yana tsaye bai motsa daga in da yake ba sakamakon wayarsa da ta buge mashi ya faɗi a saman cinyarta bayan ta faɗi ita ma kenan.
Jin yana tsaye shiru ne yasa tayi ƙoƙarin ɗago kanta ta kalli ko me ya tsayar da shi, dama kuma jira yake yi ta ɗago kai ya bata lafiyayyen mari wadda zai saka ta jin kamshin mutuwa, da yake Allah ba azzalumin bawan sa bane sai ya aiko masu Imran a daidai lokacin kafin ta ɗago kan nata.
Ganin abin da yake faruwa ya sanya Imran karisowa wajen da sauri yana faɗin "Rimsha lafiya me ya kawo ki nan..." Bai kai karshen maganar ba idanunsa suka sauƙa a kan wayar Lion dake a saman cinyarta ga shi kuma Lion ɗin yana tsaye yana fuskartar hanyar fita daga palon, so yake ta yi gigin miƙo mashi wayar nan na lahira ya fita jin daɗi, idan kuma bata miƙo mashi wayar ba nan ma ball da ita zai yi domin ya fi karfin ya duƙa ya ɗauki wayar sannan kuma baya son dukanta tana zube a kasa haka, idan ya ce zai daketa a haka to zai iya kasheta ba tare da ya sani ba shiyasa yake son sai ta ɗago tukun nan ta sha mahaukacin mari.
Imran ne ya ɗauki wayar tare da ce mata ta wuce ɗaki, cikin sauri ta miƙe zata gudu, "Come here!" ya daka mata ƴar tsawa.
Tsorata da razana da jin voice nasa ya sa ta yanke jiki ta faɗin ƙasa sumammiya a wajen.
Kallonta Imran ya yi kafin ya maido da kallonsa a kan Lion ɗin, ganin ta suma ya sa Lion ya wuce ya nufi waje dan ya lura wannan yarinya idan ya ce zai taɓa ta ma mutuwar tsaye zata yi mashi a wajen, yanzu daga magana ma ta sume masu a waje, ina ga kuma tasha marinsa ai shikenan kuma sai mutuwa.
Zura wayar a aljihu Imran ya yi kafin ya nufi wajen da take sume, hannu yasa ya ɗauketa cak, duk jikinta ya saki ta yi wani irin da ita, da kyar Imran ya iya kai ta bedroom nata domin yanzu ya tashi barci jikinsa babu kwari.
Saman bed nata ya kwantar da ita yana faɗin "Ko wani tsautsayi ya saki haɗuwa da Saif da sassafen nan, shin me ma ya fito dake oho?".
Sai surutu yake yi kasa kasa da haka ya fita daga cikin ɗakin ya bi bayan Lion domin ya kai mashi wayarsa.
A palon kasa ya iskoshi saman table yana cin abinci, ba ƙaramin mamaki Imran ya sha ba ganin yau yana cin abinci da safe haka.
Gefensa ya zo ya zauna tare da ajiye mashi wayarsa a gefen nasa, shiru Lion bai kula shi ba har ya kammala cin abin da yake yi sannan ya miƙe tare da ɗaukar wayar tasa ya nufi kofar fita, sojan da yake yi masu girki wadda kuma shine yake serving nasa abin ce, shine ya bi bayansa dan bayan girki da serving ma shi ne driversa, ɗayan sojan kuma yana bakin gate ne kawai, baya motsawa ko nan da can.
Har ya kai bakin kofa ba tare da ya jiyo ba ya ce da Imran "I don't want to see this girl again, idan ta bari muka sake haɗuwa...." Bai karisa magana ba sai ya ce "Ka tashi mu tafi yau da kai zamu yi tafiyar, kai zaka ja motar".
Godiya ga Allah Imran ya yi domin yasan cewa saboda shine ma yasa yau Lion bai take Rimsha ba, ba dan haka ba da wani zancen ake yi yanzu, duk da basu wani hira sosai amma Lion yana dannewa yana yi mashi kara sosai, saboda har ga Allah yana kaunar Imran fiye da tunanin mai tunani, yau ba da ban Imran ba da tabbas ko Rimsha bata mutu ba kaɗan ne zai rage mata na rai a jikinta, ko Areef ne ya yi mashi irin bugewar da Rimsha ta yi mashi har wayarsa ta faɗi sai ya wanke mashi fuska da mari bare kuma wata bare, kuma badan sumar da ta yi ba da sai ya doɗe mata kunne da mari koda guda ɗaya ne dan gobe ta kula amma Allah ya taimaketa ta suma.
Har bakin mota sojan dake yi masu girki nan ya rakasu, Imran ne ya ja motar shi kuma Lion kamar kullun wanan izza tana nan gidan baya ya shiga.
Da gudu Imran ya figi motar suka bar gidan, dan Lion baya son tuƙin mota a hankali, hakan ba karamin ɓata mashi rai yake yi ba ya fi son yaga ana sharara uban gudu da mota.
"Saif ina muka nufa ne?" Imran ya tambaya yana kallonsa ta cikin mirror motar.
Ya jima kafin ya fara magana a nutse "For now dai ka fara zuwa gidan cin abinci ka sayi breakfast daga nan mu wuce babbar masallacinku ina son nayi magana da malamanku".
Sosai Imran ya ji daɗi ko ba komai Lion a duk in da yake yana daraja malamai na ko wace kasa, yana mutuntasu, kafin musulunci ta zauna a zuciyarsa sosai aikawa yake yi a ɗauko mashi malaman a kawo mashi har wani gidan hutawarsa dake a cikin daji ta bakin ruwa, wajen babu mutane haka kawai ya zaɓi da ya je ya yi gini a can, amma yanzu da musulunci ya ratsa shi yana iya tashi da kansa ya je ga malamai, yana kuma girmamasu.
Babban abin farinciki wadda ya sanya Lion zai je wajen malamai shine dan su yi wa Areef addu'a tare da sauƙar Al Qur'ani mai girma, duk da ya sanya a kasarsu ana yi masu amma bai ishe shi ba, yana so a nan ma ayi masu.
A ɓangaren Rimsha kuwa, good 3 hours ta ɗauka a sume kafin Allah ya sa ta farfaɗo, baiwar Allah har wani wiki wiki ta yi kamar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi, ta tsorata ainun ba kaɗan ba.
Da kyar ta iya sauƙowa daga saman bed nata ta nifi toilet, wani irin wahalallen jirine yake ɗebanta saboda yunwa da take ji, sai faman dafa bango take yi domin ta isa toilet lafiya ba tare da ta taɗi ba.
Allah ya taimaketa ta shiga toilet lafiya ta yi wanka ba tare da ta faɗi ba, tana fitowa ta nufi wajen trolley ta dake a cikin dressing room na ɗakin, sauri sauri ta shirya cikin wata daguwar riga abaya black color, ta yi kyau sosai sai dai har lokacin jiri sosai take ji.
Bayan ta gama shiri fes sai tashin kamshi take yi, da kyar ta lallaɓa ta nufi waje. Kitchen ɗin ta sake komawa dan har ga Allah yunwa take ji, sai dai a wannan karon tana tafiya ne tana sanɗa kamar wata ɓarauniya, sai lallaɓawa take yi dan kada su sake haɗu, yau gaba ɗaya yasa ta ji bata son sake yin ido huɗu da shi, tsoronsa ya sa zuciyarta ta sake yin nesa da shi sosai, gaba ɗaya ta ji jikijta ya mutu, bata fatar rana irin ta yau ta sake zuwa a cikin rayuwarta, sai dai kuma fa son shi da kauna shi kara ninkuwa ya yi a cikin zuciyarta, wani irin azababben son take yi mashi wadda baki bai isa ya iya furtawa ba.
Har ta fito palon kasa babu kowa, Kitchen ta sake wucewa nan ma babu kowa, duba kayan abinci ta yi da wasu abubuwa da zata buƙata, kwata kwata babu indomie bare su supaght amma dai akwai dankalin turawa dan suna cinsa suma, sannan akwai nama da kuma kwai sosai da sosai, nama da kwan (eggs) sun fi komai ma yawa a cikin kitchen ɗin, sai wasu kalolin cimar da bata taɓa ganin irinsu ba, tunawa ta yi da yadda ta ga sojan nan yake haɗa ɗanyen kwai da ɗanyen nama waje guda yana kwaɓawa, wani iri ta ji ajikinta, abicinsu sai su, bai dafa namanba ya zuba ɗanyen kwai ya kwaɓa kafin ya yi shi kamar yam balls ya soya bayan ya zuba kayan haɗi kenan.
Guntun tsaki ta ja a fili ta ce "Allah ya kiyaye, ba a dafa nama ba ake soyawa, shima soyawar sai a rasa dame za'ayi sai da kwai, bayan nan a zuba wasu shegun kayan haɗi marasa kan gado, Allah ya sawwaka ya kiyaye na ci irin wannan abincin, anyama waƴan nan suna da maggi kuwa? Naga ranarma kamar kazarsu ba maggi, ko dai wani abin suke sakawa a matsayin maggi ne? Oho dai matsalarsu ce, amma anya abincin nan zai yi karni kuwa? Na san dai GAR ba zai taɓa cin abu mai karni ko wari ba, dole dai akwai yadda suke yi wa wannan irin abincin nasu dan kada ya yi wani abin da ba shi ba".
Ta ɗan jima tsaye tana surutanta kafin ta wuce ta ɗaura ruwa a saman gas da wani ɗan ƙaramin kyakkyawan pot mai shegen kyau da tsada, sai kyalli jikin pot ɗin yake yi tamkar yanzu aka fitar da shi daga kwalinsa.
Bayan ta ɗaura sai ta ɗauko dankalin turawa ta ɗebo daidai yadda take buɗakata tare da ɗebo kwai guda uku sai nama kuma ta ɗauki na kaza, bata ɗauki kazar gaba ɗaya ba sai ta yanki rabi ta mayar da rabi cikin freezer, sannan ta buɗe drawers dake a cikin kitchen ɗin dan neman irin su Maggi da su mai (oil) ta sami mai amma bata sami maggi ba sai dai wasu kayan haɗin wadda bata ma san tayaya ake amfani da su ba, ajiye wa ta yi ta koma wajen ɗayar freezer a nan ta sami fresh kayan miya masu kyan gaske, tattasan manya manya Tomatoes ɗin kam zaka ce mutun ya tsara shi, dan ko ance ka yi halittar Tomatoes da kanka ba zaka wuce yin manya manya masu kyau fresh kamar su ba, ga attarugu manya da su chilling pepper, albasar su ma wani irin smoot jikinsa yake gasu manya farare tas.
Ɗebar abin da take buƙata ta yi ta koma gaban gas ta fara aikinta.
Bayan ta haɗa abubuwan da zata buƙata dan yin jalof ɗin dankalin, ta gyara komai ne ta wuce ta fita a kitchen ɗin, ɗaki ta koma ta duba jakar school nata ta ɗauko 1k da Imran ya bata tare da ɗaukar hijabi har kasa ta sanya a jikinta ta nufo waje dan ta je ta sayi maggi.
Tana fitowa ta isko sojoji guda biyun nan, da mai yi masu girki sai kuma mai gadin gate ɗin suna zaune saman wasu lafiyayyun luntsuwa luntsumar kujeru masu kyau da tsada a bakin gate ɗin.
Sannu ta yi masu zata wuce ta fita sojan dake yi masu girki ya daka mata wani mahaukacin tsawa wadda ya sanyata yin baya a sukwane.
"Where are you going?!!" Ya faɗa fuskarnan babu annuri ko kaɗan, ita bata san cewa gidan Lion sai da izininsa ake shi kuma sai da izinin sa ake fita ba, shiyasa ranar da Akil ya kawo mata kayanta sai da ya kira Imran akan ya zo ya karɓi kayan sun hana shi shiga.
Cikin rawar murya ta gaya mashi maggi zata sawo a waje, tsawa ya kuma daka mata akan ta wuce ta bashi waje ta koma cikin gida ko kuma ya yi kwallo da ita, sojan dake tsaron gate ɗin ne ya dakatar da su da cewa ta koma bari ya saya mata maggin, shi har ga Allah Rimsha ta yi mashi, tun ranar da ya fara ganinta, shiyasa ya yi mata sauƙin kai har da cewa zai je ya sawo mata maggin.
Da mamakin sojan dake yi masu girki yake kallonshi, miƙewa ya yi ya nufi waje, tana tsaye tana kallonsa jikinta sai kerma yake yi, har ga Allah tana tsoron sojoji sosai amma a haka zuciyarta tayi mata rashin adalci ta kamu da son GAR.
Har ya kai bakin kofa zai fita sai kuma ya juyo cikin harshen turanci ya ce ta bashi kuɗin Nigeria dan shi dollars ne ke gare shi, kuɗin kasar su gaba ɗaƴansu suke da shi, tun da suka zo basu fita waje ba bare kuma su ce zasu je canjin kuɗi.
Cikin sauri ta miƙa mashi 1k dake a hannunta, jujjuya kuɗin ya yi yana karewa kuɗin mu kallo kafin ya ɗago ya tambayeta me sunan abin da zai saya mata sannan kuma a ina zai saya mata ɗin.
Cike da tsoro ta ce mashi ko ta zo su tafi tare ne? Girgiza mata kai ya yi ya ce ta zauna a gida domin fitarta sai ya fi zama masu haɗari akan nasu fitar, duk wanda ya shigo gidan idan suka bari ya fita ba da sanin Lion ba sai ya hukuntasu, sannan kuma su har ga Allah suna yi mata kallon tana da matukar muhimmanci tun da har Lion ya iya bari ta zauna agidansa abin da a baya ko da gigin wasa basu taɓa ganin makamancin hakan ba, basu san cewa darajar Imran ta ci ba, Imran ya yi wa su Lion abin da ba zasu iya mashi wani wulakanci ba shiyasa kawai take gidan.
Wucewa sojan ya yi ya fita shi kuma ɗayan yana zaune kamar wani gunki yana latsa waya, fara zagaye gidan ta yi tana ƴan dube dube, ba karya gidan ya haɗu iya haɗuwa.
Can ta hango kamar mutane ne a ta bayan wajen garden ɗin gidan, da sauri ta karisa wajen, waƴan nan masu kwacen waya da Lion ya kama ne, suna zaune sun gama cin abincin da