Showing 294001 words to 297000 words out of 355604 words
sojan ya basu.
Ganita yasa suka fara kallonta daga sama har kasa, cikin rawar murya suka gaisheta dan a tunaninsu matar gidan ce da yake ta zumbula hujabi har kasa kamar wata matar liman.
Mamaki ne ya kamata akan me ya kawo su gidan nan kuma, sun ci bakar wahala kamar ba gobe sun koɗe sosai, bayan abinci da ake basu ba wani abu kuma da ake basu sai horar wa, yanzu ma an barsu ne su gama cin abinci, da zarar sun gama sojan nan zai zo ya dasa daga basu wahala da yake yi, bayin Allan har sun gwammaci da basu zo duniya ba saboda bakar wahala da suka sha a gidan THE GENERAL OF THE ARMY'S duk sun rame sun zama kamar kashi da rai.
Da sauri ta juya ta bar wajen ta koma bakin gate ta tsaya, bayin Allah nan sun bata tausayi sosai da sosai.
Ta jima tuna tsaye a wajen kafin nan sojan ya dawo, shi kuma ɗayan ko ɗaga ido bai yi ya kalleta ba, kuma dama shi ba ya ganin abin da ba'a gabansa take ba, ma'ana abin da bai shafeshi ba, horon Lion ne shi, sun fi kusa da Lion shiyasa ya ke yin ɗabiu irin na Lion ɗin, yake kwaikwayon ogan nasa.
Miƙa mata pack na maggin ya yi tare da canjin 200 pack ya saya mata, karɓa ta yi tana mashi godiya, ya sha tafiya kafin ya cinma shago, danma dai ba tafiyar yara yake yi ba, dakunsa ɗaya daidai yake da koma na ƴara.
Wucewa ta yi ta koma cikin gida, da ido ya bita har ta kurewa ganinsa sannan ya koma saman kujerar da yake zaune ɗazun ya zauna yana faɗin "Mark i really like this girl, the way she is talking the way she is walking hey i like everything about her".
Ba tare da mark ya ɗago ya kalle shi ba ya ce "Are you fall in love?" Cikin sauri ya girgiza kai alamar a'a shi ba son ta yake yi ba domin suma da alama babu aure ko soyayya a tsarinsu, bai ji kunya ba ya gayawa mark shi dai kawai sha'awar ta yake yi ba soyayya ba.
Jinjina mashi kai Mark ya yi tare da miƙewa ya koma cikin gida.
RIMSHA
Tana tsaye a gaban gas tana faman juya jolof ɗin dankalinta da bai ji wani kayan haɗi sosai ba sai gayyar tattasai da nama da kwai, ba su curry da sauransu wayan da ta saba, sai dai nasu wadda bata san ya ma ake amfani da su ba, sai kawai ta yi girkinta a haka.
Tana tsaka da aiki kamar daga sama taga an ɗauki tukunyar dankalin nata daga kan gas ɗin sai cikin abin zuba shara aka wurga, a razane ta ɗago kanta tare da juyowa dan taga wanene, wannan Mark ɗin ne mai yi masu girki, yana tsaye fuska babu annuri ko kaɗan, da hannu ya nuna mata hanya akan ta fita masu a kitchen ɗin nan, duk ta buɗe masu ko'ina da warin abincinta shiyasa ya ɗauki tukunyar gaba ɗaya ya jefa a abun zuba shara.
Bakin cikine yasa ta rushe da kuka tare da wucewa da gudu ta haura sama, tana shiga bedroom nata ta faɗa saman bed tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, baiwar Allah tana jin yunwa sosai kukan nata ma baya fita sosai.
Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta miƙe ta ɗauki wayarta ta fara kiran layin Imran, bugu ɗaya ya ɗauka, cikin kuka ta gaya mashi yunwa take ji kuma ta yi girkinta soja ya zubar mata.
Hakuri Imran ya bata tare da ce mata yanzu Akil zai zo ya ɗauketa suje gidansa su wuni sai ya dawo zaizo ya ɗauketa, cike da murna ta amsa mashi da to sannan suka yi sallama.
Shiryawa ta yi fes ta fito waje, kai tsaye gardin na gidan ta nufa ta zauna a saman ɗaya daga cikin kyawawa kuma tsadaddun kujerun dake a wajen, tana zama ta fara kiran Akila a waya dan ta turo mata number daddyn Jelly su gaisa da Aylarta.
Sau uku tana kiran layin Akila amma Akila bata ɗaga ba har Akil ya iso, sojan nan ya hana shi shiga gidan ita kuma ya hanata fita, domin idan baku manta ba dokace ba'a shiga ko fita sai da izinin Lion.
Kuka ta fara yi tana kiran layin Imran, ta gama cin burin yau zata wuni da su Umaisha amma sojan nan yana son hana ruwa gudu.
Bugu ɗaya Imran ya ɗauka, cikin kuka ta gaya mashi wai ba zata fita ba har sai Lion ya bada izinin ta fita, hakuri ya bata tare da ce mata yanzun nan zai je ya yi magana da Lion ɗin yana cikin mota shi kuma Imran yana cikin banki zai ciro masu kuɗi, da haka suka yi sallama da ita akan ta bashi minti biyar yanzu zai fito daga cikin banki ya sami Lion a mota kada ta damu...........
Nima dai na wuce sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai , LONG PAGE HOT COMMENTS 🔥
💖💖TRIPLETS💖💖
E77-78💖
Bugu ɗaya Imran ya ɗauka, cikin kuka ta gaya mashi wai ba zata fita ba har sai Lion ya bada izinin ta fita, hakuri ya bata tare da ce mata yanzun nan zai je ya yi magana da Lion ɗin yana cikin mota shi kuma Imran yana cikin banki zai ciro masu kuɗi, da haka suka yi sallama da ita akan ta bashi minti biyar yanzu zai fito daga cikin banki ya sami Lion a mota kada ta damu.
Shiru ta zauna tana ta hawaye ga bakar yunwar da take ji, shi kuma Akil ransa ya yi mugun ɓaci dan haka sai ya wuce abinsa ya koma gida tun da abin ya zama raini wayo.
Koda Imran ya koma mota ya gayawa Lion bukatarsa, sai da Lion ya ɗauki good 20mins kafin ya ɗauki wayarsa ya yi sojan massage akan ya bar Akil ya tafi da ita.
Bayan minti ɗaya da tura saƙon sojan ya sake turo mashi saƙo akan Akil fa ya tafi, gayawa Imran ya yi Akil ya wuce, sosai Imran ya ji babu daɗi, kuma yasan halin Akil ko ya ce ya dawo ya ɗauketa wlh ba zai dawo ba, dan shi ba'a yi mashi walaƙanci a waje ya kuma koma wannan waje, babbar damuwar Imran ɗaya Rimsha tana jin yunwa, bai ɓoyewa Lion ba ya gaya mashi cewa Rismha tana jin yunwa kuma ta yi girki sojan ya zubar mata ga shi kuma su ba yanzu zasu koma gida ba kuma bata iya cin kalar abincin su ba.
"And so what?" Shine abin da Lion ya ce mashi, bai damu ba dan dama yasan za'ayi hakan, jan motar kawai ya yi yana ta tunanin Rimsha har suka bar bankin suka nufi babbar masallacin Jumma'a.
A ɓangaren gidan Abba kuwa, Akila na tsaka da barcinta misalin karfe 8 na safe wayarta ta fara kara, hakan ya yi sanadiyar farkawarta daga barcin ta mai shegen daɗi da take yi.
Daga ta cikin bargo ta sako hannunta ta ɗauki wayar tata a saman bedside drawer ta mai da hannun nata cikin bargon.
Idanunta duk barci ta yi picking call ɗin, murya can kasa kasa ta ce "Hllo mijin matar shi". Daga ɗayar ɓangaren Irfan ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya kafin ya ce "Matar Mijinta ba dai har yanzu barci kike yi ba?".
Turo baki ta yi kamar tana a gabansa ta ce "Yaya Irfan Allah ni sai ka biyani barcina".
"Heartbeat kin fara ko? Zaki fara rikitani ko?" Kara shagwaɓe murya ta yi cikin salon magana mai jan hankali ta ce "Allah ni da gaske nake yi yaya Irfan ka biyani barcina, haka kawai ka kama ka tasheni daga barcina mai daɗi, to ba zan yarda ba kawai ka biyani" ta kai karshen maganar tare da fashewa da kukar shagwaɓa har da wani ƴarfe hannu da kafafu kamar tana a gabansa.
Ai kuwa ba shiri ya fara rarrashinta, duk ta ruɗa bawan Allah, har wani haɗe words yake yi wajen rarrashin nata, kin yin shiru ta yi har sai da ya ce mata to ga shi nan zuwa yanzun nan sai ya goyata ta mai da barcin, sannan ne ta yi shiru tana kara turo baki kamar biro.
Sallama suka yi akan bari ya shirya yanzun nan ya zo, cike da murna ta katse kiran dan tana son ganin yayan nata kuma masoyinta, yana ranta sosai, daga daren jiya zuwa yau ta yi kewarsa sosai.
Tana katse kiran tana ƙoƙarin ajiye wayar idanunta suka sauƙa akan massages da suka shigo, ɗan taɓe baki ta yi kafin ta fara buɗe massage ɗin, wasu tun karfe biyar aka turo su, wasu kuma karfe 6 wasu 7, na farkon ta fara karantawa kamar haka.
"Amincin Allah tabbata a gareki my angel, ina fatan kin tashi lafiya, kuma ina fatan Allah yasa mafarkina aka yi jiya da daddare dan nidai nayi mafarkin ki gaskiya, na yi mafarkin ina goye da angel ɗina, so fatan kema dai kin yi nawa, na barki lafiya sai kuma anjima".
Sake buɗe sako na biyu ta yi "My angel sarkin barci kuma sarkin shagwaɓa, ina matukar kaunar wannan shagwaɓar taki, ina son jin yadda kike cewa I love you please ko zaki faɗa mani ko sau ɗaya ne?".
Daɗin massage ɗin yasa bata san time ɗin da ta furta I love you a fili ba, sai dai kawai jin word ɗin ta yi ya fito fili, ƴar murmushi ta saki kafin ta buɗe next massage "A gaskiya kin iya furta kalmar so my angel" cikin sauri ta duba time da ya aiko sakon 7:5 yanzu kuma 8:12 ne mamaki ne ya kamata yaushe ya ji ta ce i love you bayan yanzu ta yi maganar, massage ɗin kuma tun awa ɗaya baya ya turo, bata kara ruɗewa ba sai da ta ga massage na gaba in da yake cewa.
"Sarkin ruɗewa, kina mamakine dan nace kin iya cewa i love you tun baki faɗa ɗin ba? To ki daina saurin ruɗewa ki rinƙa yin tunani kafin ki ruɗe, mafiyawancin abin da nake faɗa dangane dake hasashen sa kawai nake yi, yanzu ma na yi hasashen zaki ce i love you ɗin ne yasa na yi maki wannan massage ɗin tun kafin ki faɗa, cos bana son ki rinƙa yawan ruɗewa shiyasa na gaya maki ta yadda zaki gane, idan ba haka ba muka cigaba a haka na san wata rana sai na kai yi asibitin kwakwalwa saboda ruɗewa, so kada ki rinƙa ɗaukar komai na daga magana ta kamar nasani ne na faɗa, hasashe nake yi kuma kowa zai iya yin hakan, idan hasashena gaskiya ce ki ajiye mani hot kiss zan zo na karɓa anjima da daddare, bye sako daga ɓoyayyen masoyi, Majoon ɗin Laila kuma Romeo'n Juliet".
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ajiye wayar tana faɗin "To meyasa baka bar mani hanyar da zan yi maka reply ba? Ina son ganin nima ina yi maka reply".
Ta kai karshen maganar tare da sauƙowa kasa daga saman gadon ta nufi toilet dan ta yi wanka ta shirya yaya Irfan nata yana zuwa, sai dai fa ba yaya Irfan ɗin take tunani ba ɓoyayyen masoyi take tunani, shine a cikin ƙwaƙwalwarta da zuciyata, ya iya tsara kalamai da kuma kula, daga gani yana da wasa da dariya bayan iya soyayya, daga gani gwanine wajen iya kula da mace, domin kuwa daga saƙonninsa zaka fahimci hakan.
Bayan ta yi wanka ta fito ta ɗan gyara bedroom ɗin nata sannan ta shirya cikin wata atamfa pink color da ratsin baki ɗinkin riga da sket, kayan sun zauna a jikinta sosai da sosai, takalma plat shoe baki ta ɗauko tare da mayafi shima baki sannan ta feshe jikinta da perfumes nata masu daɗi, simple make up ta yi ta yi kyau sosai ba karya.
Saman bed nata ta zauna farinciki ya sa kwata kwata bata jin yunwa a yanzu, bata da burin da ya wuce yaya Irfan ya zo ta ganshi.
Sai murmushi take yi ita kaɗai, tana zaune a wajen wayarta ta fara kara, cikin sauri ta ɗauki wayar dan a tunaninta yaya Irfan ne, tana duba mai kiran sai ta ga unknown number, cikin zunuɗi ta ɗauki kiran domin har ga Allah tana kewar jinsa.
Cikin sanyin murya ya ce "Assalamu alaiki warahmatullahi taala wa barkatuhu my angel".
Ɗan ciro wayar ta yi daga kunnenta tana duba screen ɗin dan ta ji muryar ya yi mata kama dana wani da ta sani, tabbas jiya da ta ji muryar ta ji kamar ta taɓa jin makamancin wannan zazzakar murya a rayuwarta sai dai ta rasa a ina ne, to yau ma da ta sake jin voice ɗin nasa da kyau ya sake fito mata karara kamar ta taɓa jin wannan murya, mamakine ya kamata.
Jin ta yi shiru yasa ya ce "Lafiya kuwa heartbeat me yasa kika yi shiru?".
Kakalo murmushi dole ta yi kamar yana a gabanta, cikin sanyin murya ta ce "Wlh ina tunani ne na ji muryarka ya yi mani kamar na san shi". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Mai yi wu wa amma dai da kamar wuya gaskiya, yanzu dai bama wannan ba gaya mani me zaki ci na kawo maki?".
Ƴar waigawa ta yi ko zata ga ta ina yake kallonta da har yasan bata ci komai ba. "Heartbeat na gaya maki ki daina wahalar mani da kanki, Shiyasa fa ɗazun na gaya maki mafiyawancin lokaci hasashen abu nake yi akan ki, duk da wata zubin idan bana aikin komai e tabbas ina tsayuwa in kalli duk wani abin da kike yi amma ba ko yaushe ba, wani sain canka kawai nake yi saboda na yi maki farin sani, na san abubuwan da zaki yi da wadda ba zaki yi ba, hakan yasa ma hasashen nawa yake zuwa gaskiya".
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "To dan Allah ka gaya mani sunanka ka ji abokina? Sannan ka gaya mani waye kai?". Nisawa ya yi tare da faɗin "Wow gaskiya na ji daɗi sosai da kika kirani da abokinki, daga aboki sai na zama masoyi daga nan sai miji".
Ƴar murmushi ta yi yana faɗin "Uhm to ni dai yanzu ka gaya mani sunan ka". "Heartbeat sarkin rigima, ke dole sai kin ji sunana ko? To nima kawai ki kirani da Heartbeat ɗin ki".
Turo baki ta yi a shagwaɓe ta ce "Ni ban yarda ba sunanka na gaskiya zaka faɗa Mani". "Heartbeaaaaaaat.... kina rikitani da wannan shagwaɓar taki fa, nima kuma na iya idan baki kyaleni haka na samu na yi aikin dake a gabana ba tabbas sai na yi maki kuka".
Yarfe hannu ta fara yi mashi tare da fara magana kamar zata yi kuka "Allah ni ba zan yarda ba, kawai ka gaya mani sunanka idan ba haka ba tom kuka zan yi maka Nima".
"Uhm uhm heartbeaaaaaat Allah ki bari idan ba haka ba yau ba zanci abinci ba, kuma ai nace zan gaya maki sunan nawa ko? To ki kyaleni haka nan ko dai na yi maki kuka soyayyane? Kuma ko kin rarrasheni ba zan yi shiru ba".
Wow ta furta a fili, jin yadda yake zuba shagwaɓa yasa ya kara ciro wayar daga kunnenta tana bin screen ɗin da kallo, har ga Allah shagwaɓarsa ya yi mugun tafiya da imaninta, abin ya kayatar da ita.
"Heartbeaaaaat me yasa kuma kika yi shiru? Kina son na yi kuka ne? Ko dai kina son na zo na same ki ne? Ni gaskiya na kiraki ne mu yi hira na ji muryar bugun zuciyata, dan haka ki yi mani magana masu daɗi idan ba haka ba zan yi maki kuka kuma sai kin goyani". Ya kai karshen maganar a shagwaɓe kuma da alama shima ya turo baki kamar yadda take yi saboda yadda ya fitar da maganar tasa ya nuna alamar kumatunsa a kunbure ya kuma turo baki.
"Ni dai dan Allah ka gaya mani sunan ka kaji ko masoyin ɓoye?".
Ƴar dariya mai ƴar sauti ya yi wadda ya sanyata lumshe idanunta tare da sake buɗe su a hankali, wannan dariya tasa bakaramin ratsa dukkan ilahirin jikinta ya yi ba, wani irin bakon yanayi ta fara ji a jikinta dan gane da shi yana ratsata, cike da kulawa ta ce "Yanzu ba zaka gaya mani sunan naka ba?".
"Heartbeat you have to much of complain and silly questions, i told you ni ma ki kirani da Heartbeat naki kawai, sunana kuma zan gaya maki but not now, for now dai just call me your Heartbeat".
Jinjina mashi kai ta yi tana faɗin "Okey my Heartbeat i really like this name, My Heartbeat wow so lovely name".
"Wow my Heartbeat kin ji sunan da ya fito daga bakin ki kuwa? Kamar dan bakin nan naki aka yi shi". Cool murmushi ta saki tana ɓuye fuska da hannunta ɗaya.
Shima a nashi ɓangaren murmushi yake yi. "Heartbeat zan je wajen school idan na dawo before ma na dawo zaki ga massages ɗina, idan kuma na dawo zan kira ki, Kin amince na je school ɗin?".
Kai ta gyaɗa mashi tana faɗin "E ka je adawo lafiya". Shagwaɓe murya ya yi kafin ya ce "Heartbeat ki kula mani da kanki sosai, kuma ki sani ina da kishi sosai da sosai kawai dai ina dannewa ne saboda bana son takura maki a yanzu, amma nan gaba zan ɗaura heartbeat nawa akan hanya, yanzu dai wani fata zaki yi wa mijinki idan zai fita?".
Tana bala'in son shagwaɓarsa ba karamin tafiya da ita yake ba, ya kware a iya shagwaɓa sosai da sosai, haka zalika ya iya tsara kalamai kamar dan shi aka yi su, ya san duk ta yadda ake rarrashin mace, bata san lokacin da ta narke mashi suka rinƙa zubawa juna shagwaɓa tare da kalaman sosai ba, daga karshe dai ta yi mashi addua'o'i kamar haka.
"Allah ya rabaka da sharrakin duk wani abin halitta mutun or aljani komai, Allah ya haɗaka da alkhari dake tattare da duk wata abin halitta, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhari tare da cika maka burinka na alkhari, Allah ya rabaka da mama da baba tare da duniya baki ɗaya lafiya, Allah ya tsare mani kai daga faɗawa duk wani abin da Ubangijin mu ya hanemu da aikata shi ya kuma baka iko da aikata duk wani abin da ya umarce mu da mu aikata,