Showing 195001 words to 198000 words out of 355604 words
shi tare da komawa ta kwantar da kanta a saman kirjinsa. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da jan motar suka bar wajen.
Tafiya kaɗan suka yi, suka isa *ABC SUPERMARKET* da ya yi parking a parking space nasu sai ta ɗago kai tana faɗin "Daddy in fita ne?" Tsareta da ido ya yi haka kawai baya gajiya da kallonta, wata sain har mamaki yake yi na rashin son daina kallonta da yake yi.
"Babayn daddy kin ga ji ne da daddyn naki da har kike saurin fita?" Murmushi ta yi tana faɗin "Daddy ban ga ji da kai ba, ai naga mun iso ne kawai shiyasa na ce in fita ne". Shafa kumatunta ya yi kafin ya ce "Duk yadda aka yi mama ko baba ɗaya yaren mu ne, dan ba'a banza zaki yi wannan kyau ɗin haka ba". Yar dariya ta yi har sai da fararen hakwaranta suka bayyana, ta cusa kanta a cikin kirjinsa tana ɓoye fuska.
Rungumeta ya yi yana faɗin "Ai gaskiya na faɗa ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alama e. "To waye daga cikin su ne Yaren namu?" Kasa kasa Muryar ta ke fita saboda ta cusa kanta cikin kirjinsa, tana ta jefa bawan Allah cikin yanayi.
"Mama ta ce" kara ruƙeta da kyau ya yi yana ɗago haɓarta da hannunsa ɗaya, zuba mata ido kawai ya yi yana kallonta, ita kuma ta rufe ido tana murmushi.
A haka kawai ya tsinci kansa da matso da fuskarsa daf da tata, daga karshe ya haɗe fuskokin nasu yana jan dogon numfashi.
Jin fuskarsa a saman tate ne yasa ta buɗe idanuwanta, ai kuwa tana buɗewa sai cikin tasa idanun, da sauri ta mai da nata ta runtse su.
"Babyn daddy kina kunyar daddyn ki ne?" Ya yi magana yana kara riƙota a jikinsa sosai, zuciyarsa na ingiza shi akan ya yi kissing lips nata, idanuwansa na akan lips ɗin tata, ya yin da ita kuma sai murmushi take yi tana faɗin "A'a daddy bana ji" yadda ta motsa lips ɗin nata ta yi magana kusa da shi bakaramar fusgar shi ta yi ba, gaba ɗaya ta sanya ya mance shin wai a ina ma yake? Da waye yake tare? Duk ya mance.
(Sheɗan na daga gefe yana kallonsu😭)
Kara matso da bakinsa ya yi kusa da tata yana ɗan goga lallausar lips ɗin nasa a saman tata, Allah ne kaɗai yasan irin abin da yake ji a cikin zuciyarsa, yau shekararsa 16 ba mace, shakara 16 kenan da rasuwar mummy jelly, lokaci guda ya canza, ya shiga wani irin yanayi mai wuyar misiltawa, riƙota sosai ya yi a jikinsa tare da ɗaura lips nasa saman tata, ya kasa janye wa kuma ya kasa aiwatar da abin da zuciyarsa ke ingiza shi da ya aikata, ita kuma jin ya ɗaura lips nasa a saman tata yasa ta waro idanuwanta, kai tsaye sai cikin nasa da suka yi jawur kamar wuta.
Ba ƙaramin tsorata ta yi ba, nan take jikinta ya fara kerma ta fara ƙoƙarin kwacewa daga jikinsa, duk da cewa ba wani ilimi take da shi ba, ɗan zamanta da Rimsha ta fahimci abubuwa da dama, wadda a ciki kuma harda gudun wani namiji ya taɓa ki, sai kuma ta tuna in da Rimsha ke ce mata mum tasu ta ce mata idan mutun ya fara period namiji ya taɓa shi to zai samu ciki, tuna hakan yasa ta kara tsorata, ta fara yunkurin barin jikinsa.
Riƙeta sosai ya yi, yana jin tamkar ya yi kissing nata, amma ya kasa, saboda ba halinsa bane, ba zai iya yin haka ba, idan ya tuna cewa duk abin da ya yi mata to yana nan a rubuce za'a yi wa Jellynsa hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa ya daure ya jure ya kame kansa bai kai ga yin kissing ɗin nata ba, jin zuciyarsa yake yi tamkar ana hura mashi wuta a cikinta, har wani sara mashi kansa yake yi, da kyar ya iya furta "Babyn daddy please ki zauna shiru kin ji? Babu wani abin da zan yi maki" da kyar ya iya kai karshen maganar yana haɗe words.
Jin yadda ya yi magana kamar mara lafiya ne yasa ta san daddyn nata ba lafiya yake ba, kuma ta kara jin tsoron shi sosai a ranta, shiru ta yi tana tunanin me yake damunsa lokaci guda haka?. Shi kuma cigaba ya yi da goga lips nasa a saman tata, yana jan numfashi da kyar da kyar.
Sun ɗan jima a haka kafin ya manna mata sumbata a saman lips ɗin nata, sannan ya saketa tare da kawar da kallonsa daga kanta, lokaci guda wani irin kunyarta ta kama shi, kasa-kasa ya ce "Babyn daddy je ki kiyi shopping ɗin ki dawo ina nan ina jiranki" tashi daga jikinsa ta yi, ita ma gaba ɗaya ji tayi kunyarsa ta kamata, sai wani sunnar da kai kasa take yi, cikin girmamawa ta ce "To me zan sawo daddy?".
Har lokacin gefe yake kallo, ya ki kallonta ya ce "Jeki fara ɗaukar duk wani abin da ya burgeki, ciki kuma ki haɗa da jakar school irin wadda kike so, sai ki haɗa da kananan kaya zan biyo ki daga baya". To ta amsa mashi da shi, sannan ta buɗe kofar motar ta fita.
Jingina kansa da jikin kujerar motar ya yi yana sauke nauyayyar ajiyar, kasa kasa ya fara magana shikaɗai "Zancen Sadiya ya tabbata, tabbas ina kaunar Ayla, ban san da haka ba sai yanzu, why soyayya zaka yi mani haka? Why?" Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu yana shafa lips nasa, a hankali ya lumshe idanuwansa, bayan wasu yan mintoci ya sake warosu, har lokacin suna nan jawur basu koma asalin kalarsu ba.
Ya ɗan jima a haka kafin nan ya fito daga cikin motar ya nufi cikin shopping ɗin.
Can wajen mayukan shafawa ya hangota, zuba mata ido ya yi yana kare mata kallo, a shekaru ba zata wuci Jellynsa ba, amma jelly zata fita tsawo, ita kuma ta ɗan fi Jelly kiɓa, kuma da alama ma tama ji kin yin kiɓa, sai dai ba sosai ba, irin kibar nan mai kyau, idan ta samu natsuwa da hutu zata murmure sosai, wani irin yanayi mai daɗi yake shiga idan yana kallonta, babban kuskuren da ya yi wadda yasa har sonta ya shige shi cikin ƙanƙanin lokaci shine ɗaukarta da ya yi kamar Jelly, ya manta cewa jinin uba da ƴa daban-daban da yar da ba kai ka haifeta ba ka mai da ƴa, komai haɗa jiki da uba da ƴa za su yi ba za su taɓa jin sha'awar juna ba, sai dai idan son zuciya irin ta ɗaya daga cikinsu kuma sheɗan ya buga masu ganga, amma babu wannan a jinin uba da ƴa, ya mance da haka ya rinƙa jawota jikinsa, idan tana kuka haka yake rungumarta yana rarrashinta kamar yadda yake yi wa Jelly, da farko kin yarda take yi, daga baya ta saki jiki da shi, hakan yasa suka yi irin wannan irin sabo, ita ma a daddy take ɗaukarsa kamar yadda yake gaya mata, wannan kuskuren tasa soyayyarta ta yi mashi shigar faraɗ ɗaya.
Ganin ta kasa zaɓar mai ɗin sai rawan ido take yi dan bata saba ba, a gidansu ma bata da mai ɗin bata taɓa shafawa ba. Hakan yasa ya karisa wajen yana faɗin "Babyna baki sami irin wanda kike so bane?"
(Waye ya lura da canjin sunan da aka samu lokaci guda?🤣 Daga babyn daddy zuwa...🤐🤣)
Shiru ta ɗan sunkuyar da kanta kasa, dan yanzu haka kawai take jin kunyarsa.
Hannu ya kai yana duba wadda zai dace da kalar fatar ta, yana yi yana kallonta, sai wani yan kame-kame take yi mashi, shima dai bala'in kunyarta yake ji a yanzu.
Haka ya zaɓa mata mai wadda yake ganin zai dace da skin nata, daga nan ya riƙo hannunta suka wuce wajen kaya da sauran abubuwa, komai shi ya zaɓa mata da kansa, dan tun da ya shigo ta kasa sukuni, taki sakin jiki, shima kuma bai damu da ya sata ta saki jikin nata ba, hakan da tayi ma yafi mashi, dan ya ɗan samu sassaucin abin da yake ji idan tana magana a kusa da shi.
Sosai suka lodi kaya sannan suka wuce wajen biya, katinsa ya bada suka ciri kuɗin, ma'aikatan wajen suka kwasa mashi kayan zuwa cikin motarsa.
Bayan sun shiga cikin motar ne ya kalleta ya ce "Sorry babyna" sai lokacin ta ɗago ta kalleshi, ganin ita yake kallo ne yasa ta mai da lallonta kasa tana wasa da yatsun hannunta, bin hannun nata da kallo ya yi, yatsun nata yan gajeru da su gwanin birgewa. Yar murmushi ya saki tare da kunna motar suka nufi gida.
Suna isa ya fice zuwa part nasu, ya ki tayata kwasan kayan zuwa cikin gida, dan baya son haɗa ido da Aunty, saboda yasan halinta sarai yanzu zata sako shi a gaba da tambayar ya akayi, shiyasa ya gudu abinsa.
Ita kuma haka ta kwashi kaya niki-niki zuwa cikin gida, Aunty bata a Palo, zube kayan ta yi a palon ta zauna saman sofa tana mai da numfashi, a hankali abubuwan da suka faru a mota ya fara dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, haka kawai take jin matuƙar kaunar daddyn nata, shiru ta yi idanuwanta suna gane mata lokacin da suka haɗa ido idanuwansa sun yi ja sosai. Yar firgita ta yi sakamakon taɓa ta da Aunty ta yi tana faɗin "Babyn daddy yaushe kuka dawo?".
Fuska ɗauke da kayatatcen murmushi ta ce "Yanzu muka dawo" zama Aunty ta je ta yi a saman sofa mai zaman mutun 3 tana ɗan kishingiɗa tare da tambayar Ayla ɗin ya tafiyar tasu ta kasance.
Da yake Ayla ba karatun sosai ta yi ba, kuma ba ta da wani sani akan hakan, ba waye wa, dan dai kunga yadda rayuwarya yake, ba da ban Rimsha bama da abin sai ya fi haka taɓarɓare wa, hakan yasa ta gayawa Aunty duk abin da ya faru a tsakaninta da daddy'n Jelly a tafiyarsu har suka dawo.
Sosai Aunty ta ji daɗi tare da ja mata kunne akan kada ta kuskura ta sake gayawa kowa sirrin ta ne, ko ita bata ce ya gaya mata ba, amma dai ta yi mamakin jin cewa daddyn Jelly ne ya aikata hakan, ta wani ɓangaren kuma tausaya mashi take yi matuƙa, ta kuma jinjina mashi sosai, dan ya ma yi namijin ƙoƙari da ya iya tsayawa a iya haka, shekara 16 ba wasa ba, nan fa Aunty ta shiga bata shawari da kuma karin bayani akan abin da daddyn Jelly ke nufi da ita, wato yana son ta ne.
(Kuji Aunty da ƙokari sai kace ya ce mata yana son ta🤔)
Tun da Ayla ta ji haka sai ta ji wani irin kunyarsa ta karu mata, amma kuma ta tsinci kanta cikin matsananciyar farinciki wadda ita kanta bata san daga ina farinciki yake ba.
"To tashi ki ɗauki abincinsa ki kai mashi kin ji? Dan nasan yana jin yunwa" To Ayla ta amsa da shi sannan ta miƙe ta bar niki nikin kayan nata a wajen, ta nufi Kitchen, sai murna Aunty take yi, dan daddyn Jelly yana da kirki sosai yana son ta, tana masa fatan ya yi aure ko zai rage mashi damuwa. Mai aikin su ne ta zo ta kwashe shopping ɗin na Ayla izuwa cikin ɗakinta.
Ita kuma Ayla kamar yadda ta saba haka ta fito da tray mai shake da kayan abincin nasu shi da Irfan, ta ɗaura saman dining table tana kokarin tattare hijabinta ta gyara dan kada ya kayar da ita.
"Ayla ki je ki yi wanka ki cire kayan nan tukunnan sai ki zo ki kai mashi abincin" Cewar Aunty, to ta amsa nata sannan ta bar abincin sama table ɗin ta haura sama
(Aunty!! Aunty!! Akwai iya karawa abu gishiri da sugar 🤣)
A gurguje Ayla ta yi wanka ta shirya cikin doguwar riga mai bala'in kyau launin pink da baki, ta yafa mayafin rigar a kanta, Rimsha ta koya mata sanya turare, hakan yasa take yawan sawa, kuma kullun saboda Rimshan take sakawa, idan ta sanya tana yawan tunata sosai, haka ta fito ta yi kyau sosai. Kai tsaye wajen abincin ta nufa, zata ɗauki abincin Aunty ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ke haka ake zuwa kai wa miji abinci (miji kuma?🤔) Babu kwalliya ba komai, wuce muje na maki kwalliya" to Ayla ta ce tana sunkuyar da kanta kasa, tana jin wani irin yanayi daddynta ya zama miji kuma?.
Haurawa sama suka yi, ɗakin Aunty suka wuce ta fito da kayan make up nata ta fara tsantsara mata simple make up. "Aunty ina Inna ne?" Cewar Ayla.
"Inna ai ta koma, ɗazun bayan tafiyarku yaya Irfan ya mai da ita gida, ta ce na samu lafiya zata koma" "Allah sarki har na fara kewarta" ɗauko lips balm aunty ta yi tana sanya mata a baki tana faɗin "Ke dai bari Ayla kamar zan yi kuka da zata tafi" "Ai dole ne mama fa hmmm" kallonta sosai Aunty ta yi kafin ta ce
"To tashi ki tafi, ni ban ce ki tuno da zancen mama ki mani kuka ba, kada ki sa yaya maik ya zo ya mani duka, nasa mashi babynsa kuka, tashi ki je mijin ki na jin yunwa, saura idan kin je ki yi mashi shirme, ki natsu ki bi komai a nutse, kowani namiji yana son mace mai natsuwa da kamun kai, dan haka ki natsu, kuma kamar yadda kika saba wasa da dariya da shi haka za ki yi, ki zuba mashi abincin, idan ya ce ki zauna kuci kamar shekaran jiya, to ki zauna kuci tare, ina da tabbacin yaya Maik ba zai taɓa yi maki wani abin da ba daidai ba, ki kula da shi sosai, dan yanzu yana son kulawa sosai".
Ita dai Ayla ba abin da take yi sai binta da to kawai. A tare duka jero zuwa palon, ita Aunty ta zauna saman sofa, ita kuma Ayla ta ɗauki abincin ta fice, sai tashin kamshi take yi abinta, ga shi make up ɗin nata ba karamin kyau ya yi mata ba.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo cikin palon, babu kowa shiru palon, saman lallausan Chinese carpet dake a tsakiyar palon ta ajiye abincin dan tasan ko ta kai saman table ma zai ce ta dawo da shi kasa ne, ya fi jin daɗin ci a kasa.
Zama ta yi ta tankwace kafafunta tana jiran fitowarsa. Zaman minti 30 tayi sai ga shi ya fito jikinsa sanye da ƙananan kaya, wandon jeans baki da t-shirt fara, bai san da mutun a palon ba, saboda bai ji shigowarta ba, lokacin yana wanka, daya fito kuma ya shirya zai fita ne ma gaba ɗaya. Ganin ta yasa ya ɗan zuba mata ido yana faɗin "Baby yaushe kika shigo?" kasa ta yi da kanta cike da kunyarsa ta ce "Tum ɗazun" "Oky tom kin ci abincin ne?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.
Ɗan gefenta ya zauna yana faɗin "To zuba mana mu ci tare" to ta amsa mashi da shi tare da ɗaukar plate ɗaya ta fara zuba mashi abincin, white rice ce da steew, ha ji kayan haɗi ga nama zuƙu-zuƙu a cikinta. Bayan ta gama zuba komai ne ta turo mashi gabansa tana sanya mashi spoon a gefensa.
Ɗaukar spoon ɗin ya yi ya fara ɗibar abincin, a maimakon ya kai bakinsa, sai ya kai mata saitin ɗan bakinta yana faɗin "Bari na fara baki ki ci tukun nan, idan kin ƙoshi sai ni ma na ci" kanta a kasa taki ɗagowa ta kalle shi, kuma taki buɗe bakin nata. "Baby wai me ya faru ne yau kuma? Gaba ɗaya kin canza, sai wani ɓoye mani face naki kike yi, ko dai akwai wani abin ne?".
Kasa kasa ta fara magana "Babu komai daddy" "A'a ban yarda ba, me Sadiya ta gaya maki da kika shiga cikin gida? Dan nasan ba haka muka rabu da ke ba".
Kara sunnar da kanta kasa ta yi, a nutse ta fara bashi labari "Aunty ta ce wai kana so na ne, kuma daga yau na daina ce maka daddy sai dai miji, kuma ta ce na rinƙa baka kulawa dan kana son kulawa".
(Innalillahi Ayla ta gama tuna asiri,🤣 kai gaskiya rashin ilimi babbar ciwo ne😭)
Tsareta da ido kawai ya yi yana kallon yadda take magana har ta kai karshen, ya ɗan jima yana kallonta kafin ya fara magana "To baki son daddyn naki ne?" Sai lokacin ta ɗago da kallonta a kan fuskarsa, cikin sauri kuma ta kawar da kallon nata tana faɗin "Ina son ka mana daddy".
Ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi tare da ɗan matsowa kusa da ita, ya sanya hannayensa ya riƙo nata hannayen dukka biyu kasa-kasa a nutse ya fara magana "Faɗa mani gaskiya kina son daddy ko baki son shi? Domin abin da Sadiya ta gaya maki gaskiya ce, babu karya a ciki, ina son ki, kuma auren ki zan yi ba da jimawa ba, ina son ki gaya mani gaskiya kina so na ko kuma kina da wanda kike so?" "Ina son ka daddy" "To in dai kina so na ɗago ido ki kalle Ni".
A hankali ta ɗago da kallonta zuwa kan fuskarsa, wani irin cool murmushi ya sakar mata kafin ya saki hannayen nata, ya ɗauki spoon nasa yana faɗin "Za ki yi kyau da kayan amarci" Duk da bata san me ya ce ba ta ji daɗi kuma ta saki mashi cool murmushi.
Ɗeban abin ya yi ya kawo mata sai tin bakinta yana kallonta, a hankali ta buɗe baki ta karɓa, wani irin daɗi suka ji dukkansu biyu, haka ya rinƙa ciyar da ita har sai da ta ƙoshi, sannan shima ya ci kaɗan ya ajiye spoon ɗin.
"Daddy ya naga ka ci kaɗan?" Jan hancinta ya yi yana faɗin "Naƙo shi ne babyna, kuma daga yau ki daina ce mani daddy, ki kirani da Maik ko kuma Abdul Malik" toshe baki ta yi tana zaro ido "Daddy ni fa ba zan iya kiran sunan ka ba" "To ki kirani da baby ko mijinki duk wadda ya yi maki" da gudu ta miƙe zata bar wajen, cikin sauri ya riƙota ta faɗa jikinsa yana faɗin "Ina zaki je? Na sallame ki ne?"