Showing 69001 words to 72000 words out of 355604 words

Chapter 24 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2797

shigo mu su cikin gida, har sai ya samu izinin Lion.

Daga His Excellency sai daddy a palo suna hira, lion yana ɗaki, ya ji zuwan kakan nasa amma sai ya yi kamar bai ji ba, yana kwance saman lallausan bed nasa kusa da Michael, ya lulluɓe jikinsa daga kafa zawa kirjinsa da wata shegiyar duv mai bala'i laushi kamar jikin mage, ga bala'i kyau da tsada, launin fari tas kamar yanzu a ka fitar da shi daga ledansa.

Kallon daddy His Excellency ya yi kasa kasa ya ce "William ya kamata Lion ya yi aure gaskiya, akwai wata Jesy jika ce ga babban abokina kuma tana bala'i son shi, dan kowa yasan da haka a gidansu why not ba zaka masa magana a kanta ba? Yarinyar tazo ya ganta, idan ta mishi to sai mu san abin yi"

(Tofa kai Lion ita budurwar ita zata zo ka ganta ba kai zaka je ba, a lallai mulkinka ya ka, wai wannan isa haka🤔)

Dogon numfashi dad ya ja tare da sauƙewa a hankali, ya zaro ido, sannan ya yi kasa sosai da murya kafin ya ce "Uncle ai naga ka fi kusa da shi why kai ba zaka masa maganar ba? Ni ba zan iya tinkarar Lion da wannan maganar ba, ba zan iya ba, zan iya masa magana a kan abubuwa da dama, ba zai damu ba, amma magana a kan aure, kai ina bani da wannan kwarin gwiwa, amma kai ka gwada kila idan kai ka mishi ba zai ɗauki wani action mara kyau a kan hakan ba" cikin sauri His Excellency ya ce "Ni kuma William? a'a ka rufamin asiri, kai dai zaka masa magana tunda ɗanka ne, zai fi sauraren maganar ka ai" "Ɗa nane kuma mafi soyuwa a gareni uncle, amma ai ya fi kusanci da kai, ya fi sakin jiki da kai" har wani zufa His Excellency ya fara haɗawa saboda ance ya tinkari Romeo da maganar aure, muryan sa na rawa ya ce "No William i can't gaskiya, idan ba zaka iya yi masa magana ba to ina ga sai dai a bar zancen kawai" daddy zai yi magana su ka ji takun tafiya daga bayansu ta saman bene, ko ba su juya ba sun san shi kaɗai ne mai irin wannan taku a gidan, Lion namu 1 in billion.

Tsit suka yi kamar ba su suke magana yanzun nan ba, kusa da His Excellency ya zo ya zauna, daman ya fito ne zai je ya karawa Jay wani punishment ɗin,

Shiru ya yi na yan mintoci, ya yin da suma suka yi shiru, sun kasa kunne suna sauraron su ji me zai ce, sun kuma tsare shi da ido.

Ya jima a haka kafin gently da wannan sexy voice ɗin nasa, kasa kasa a nutse ya ce "uncle yaushe kazo?" Shafa kansa His Excellency ya yi yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya kamar wanda ya aikata wani abin rashin gaskiya, har sai da lion ya kalle shi.

"Yanzu ba jimawa nazo, nazo maka barka da dawowa ne, My Michael ya kirani a waya ya faɗa mini kayi dawor sirri" ɗan kwanto da kansa Lion ya yi saman kafaɗar His Excellency bai sake cewa komai ba, sai faman lumshe ido ya ke.

Ba karamin mamaki daddy ya yi ba, dama Lion har kwanciya a jikin His Excellency ya ke yi ne, amma shi ko da sunan wasa bai taɓa kwanciya a jikin sa ba, Allah sarki daddy har wasu hawaye takaici ne ke kokarin zubo masa a idon sa, cikin hanzari ya mai da hawayen nasa dan kada su gani, har ga Allah yana mutuwar kaunar Triplets nasa, kuma duniyar sa, yana bala'i son ya gansu kusa da shi, sai dai su kuma dukkansu ba wanda yake yawan manne masa, hasalima idan sun zo wajensa to wani abin suka zo yi, haka kawai basa zuwa in da yake.

"Where is my Michael?" His Excellency ya tambaya yana kara tsurawa Lion ido, shiru ya yi wa His Excellency kamar ba shi a wajen, da alama dai bai da niyar amsawa, sanin halinsa yasa basu wani da mu ba, sun ma yi mamaki da yazo ya zauna da su haka.

After some minutes ya miƙe ba tare da ya sake yi musu magana ba ya fice daga palon zuwa wajen Jay. Kallon daddy His Excellency ya yi kafin ya ce "To William ni zan tafi, idan ka samu lokaci please ka yi wa Lion maganar auren ka ji....?" Tun His Excellency bai gama rufe baki ba dad ya ce "No uncle never" shiru His Excellency ya ɗan yi yana tunanin waye ya kamata su samu wanda zai iya tinkarar Lion da maganar, zuba masa ido dad ya yi yana kallon sa.

His Excellency ya jima yana tunani amma ba wani mafita domin babu wanda zai iya tinkarar Lion da wannan magana, ba mai kwarin gwiwar yin hakan. Haka suka hakura, His Excellency ya wuce ya nufi waje, ya je ya shiga motoncinsu suka koma white house.

Shi kuma Lion lokacin da ya isa wajen horar war tasa, nan ya isko Jay yana suma sojoji na zuba masa ruwa, idan ya farfaɗo sojijin nan ba imani bare tausayi haka za su sake miƙa masa spoon ya ci gaba, idan ya ga ji sai ya sake sumewa, babu imani ko kaɗan a tattare da su, Jay ya wahala iya wahala abin ba'a magana.

Umarni Lion ya ba wa sojojin a kan su ɗauke shi zuwa wajen mai kamar katifa yana da ɗan girma launin gree color, ruwa na feshi a wajen kamar tiyo ya fashe.

Haka suka ɗauke shi suka kai shi, ruwa ya rinƙa fesuwa a jikinsa yana wanke masa jiki. Sai da ya wankesa tsab sannan Lion ya ce su kai shi wajen wani ɗaki mai ɗumin gaske, bayan sun kai shi ne suka fito suka bar shi a ciki. Massage Lion ya yi wa Tga a kan yazo idan Jay ya ɗan sha ɗumi ya ɗaukesa ya ɗauresa a tsakiyar gidan kan shi na kallon rana, zuwa rana ta karisa faɗuwa, dan lokacin bai wuci irin 4:20 nan bane, idan rana ta faɗi sai a mai da shi ɗaki zuwa gobe ya dasa.

(Tab Jay ka shiga uku, gobe kuma ka dasa, kai kam ina ga sanadiyyar ajalinka kenan🤣)

Tun Lion bai bar wajen ba Tga ya kariso wajen dan cika aikin ɗansa kuma ogansa, wucewa Lion ya yi zuwa cikin gida.

Yana shiga bedroom nasa ya tarar sarkin rigima wato Michael ya ta shi daga barci, sai faman turɓune fuska yake yi yana turo ɗan bakin nan kamar wanda yaga wani abin ƙyamar.

Kallo ɗaya Lion ya yi masa ya kawar da kallonsa gefe tare da zama gefensa yana ajiye wayarsa saman bedside drawer.

A bayan sa Micheal ya kwanto da kansa yana turo baki, shiru Lion ya masa tamkar bai san da shi ba,. "My blood please where is James?" Wani irin yanayi mara daɗi Romeo ya ji lokacin da Michael ya jefa masa wannan tambayar.

(Allah sarki Michael duk da cewa ba shi da lafiya yana kewar ɗan uwansa, jini ba wasa ba, ya damu sosai a kan rashin ganin James, da abin yake kwana yake tashi a ransa.)

Juyowa Romeo ya yi suna fuskantar juna, kallon tsab ya yi mi shi kafin ya ce "Ni ne James mana baka gane ni bane?" Zaro brown eyes nasa ya yi da kyau yana kallon cikin idon Lion, yana son tantance gaskiya, shiru ya yi yana kallon fuska biyu a fuskar Lion ɗin, kwakwalwarsa ta kasa tantance masa waye ne a gaban sa, turo baki ya yi a shagwaɓe ya ce "No Lion ba James ba ne kai ne" ɗaure fuska sosai Lion ya yi "Ni ne James mana" ya faɗa yana zarewa mishi wayan nan dara-daran idanun nasa, dama bai zaro su bama yaya, da girmansu sosai, bare kuma ya kara zarosu, ai sai su saka mutun fitsari a wando.

Dafe kai Michael ya yi yana kallon yadda idon Lion ke canza kala daga Blue eyes zuwa Ash eyes irin na James, bayan haka, idanunsa na nuna masa fuskoki biyu a fuska ɗaya, yana ganin Lion kuma yana ganin James, duk kuma a fuskar Lion, dafe kansa da karfi ya yi ya fara kuka yana sambatu yana juyi a tsakiyar gadon kamar ba lafiya ba, zuba masa ido Lion ya yi yana kallon yadda yake juyawa, abin gwanin ban tausayi, Bawan Allah Lion ya kara birkita masa kwakwalwa, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo.

Sosai yake kuka yana sambatu, kansa na bala'i sara masa kamar zai fashe, a take wani zufa ya fara karyo masa, wasu jijiyoyi ne suka bayyana masa a gaban goshin sa, da ka gansu kasan wahala ne ya bayyanar da su, gaba ɗaya tsikar jikinsa sai tashi yake, harta gashin jikinsa sai mimmiƙewa suke.

Ya jima yana juyi a wajen dafe da kai, kafin nan ya kurma ihu tare da sakin jikinsa ya zube saman gadon sumamme. Nauyayyar ajiyar zuciya Lion ya sauƙe tare da miƙewa ya ɗauko last injection da za'a masa ya dawo ya zauna tare da haɗa injection ɗin ya masa a hannunsa. Kasa kasa ya ce "Ya zama dole na ƙure kwakwalwar kan nan ko zamu samu sauƙi"

Bayan ya gama ya tattare fankon injection ɗin ya mayar in da ya dace, sannan ya dawo ya zauna ya zubawa Michael ɗin ido yana kallonsa cike da kauna da kuma tausaya masa a halin da yake ciki.

Ya jima sosai yana karewa Michael kallo kafin ya sauƙo daga bed ɗin tare da shiga dressing room nasa. Gaban wani makeken drawer kayan sa ya tsaya, a hankali ya sanya hannu kamar zai buɗe drawer, yana kai hannunsa kusa da drawer sai ta kuɗe kanta da kanta. Kayane kala-kala masu bala'i kyau da tsada shaƙe a ciki, a shirya suke set-set, kai ka ce shangon sai da kayane a wajen, daga gefe kuma ga wa su dankara-dankaran suit masu bala'i kyau, kai da ganin su kasan an zuba dollars wajen sayan su, dollars ta yi kuka a cikin dressing room nan, abin ba'a magana, suit ɗin makale suke a abin makale kaya an jera su da kyau, sai dai ga dukkan alamu ba a taɓa sanya ko guda ɗaya ba, ba a amfani da su kwata-kwata, alama ta nuna gaba ɗaya kayan cikin wannan drawer ba a taɓa amfani da su ba, kasan cewar manya-manyan drawer kaya huɗu ne a room ɗin, Lion sarkin son kwalliya ne da gayu, shiyasa yawan kayan sawansa, su agogo, takalma, da sauransu ba za su faɗu a baki ba, dan ya fi karfin tunanin mai tunani.

Wajen wayan nan suit ɗin ya kai hannun sa ya Matsar da da su gefe guda tare da danna wani ɗan madanni dake jikin bangon wajen sai ga hoton hannun mutun ya bayyana kamar computer yana magana, alamar ya sanya hannunsa, buɗe yatsun hannunsa ya yi ya ɗaura a wajen, nan take na'uran ta yi magana tare da yin yar kara, sannan wata yar karamar kofa kamar Window ta buɗe a wajen, ba zaka taɓa cewa akwai kofa ko makamancin shi a nan wajen ba. Alama ta nuna ma ajiyar sirri ce.

Abubuwa da dama ne a cikin wajen, kama daga muhimman takardu keys, da wasu yan akwatina kanana masu bala'i kyau. Wata takarda ya ɗauko tare da rufe wajen ya fito daga dressing room ɗin, gefen bed na sa ya zauna yana duba takardan.

Ya jima yana kallon takardun wanda a kayi rubutu da wani yare na daban, domin ba da English aka yi rubutun ba.

After some minutes ya buɗe bedside drawer sa ya fito da diamond watch nasu gaba ɗaya ukun.

(To fa tambayar a nan shine James bai tafi da watch na shi ba kenan? Ko dai a Spain Lion ya samo watch ɗin?)

Zubawa watch's ɗin ido ya yi yana kare musu kallo, alamar yana tunanin wani abin. A nan ma ya ɗan jima kafin nan ya mai da watch biyu cikin drawer, ya ɗaura nasa a hannunsa, ya miƙe yana kokarin karanta menene a jikin wannan takarta.

Tun Triplets ba su fi shekara biyar a duniya ba Lion yake tare da wannan takarda, lokacin yana yaro bai damu da sanin me a cikin taɓa, amma yanzu bincike ya biyo ta kanta da dole ya san menene a rubuce a jikin ta.

Asalin takardan ya sameta ne a ɗakin mummy'n su, tun kafin su koma sabon gidan su na biyu, wata rana yana wasa a cikin ɗakin ne ya tsinci wata yar akwati karama a kasan gadon mummynsu, ko da ya buɗe wannan yar akwati takarda guda biyu ya samu a ciki masu ɗauke da wani irin rubutu, sai kuma wani ɗan siririn sarka wadda yana da tabbacin na Josephine ne wato mum ɗin su, domin tana yawan saka irin sarka, duk wani hoton ta da zai gani da irin sarkan yake ganinta, sarka uku ya samu a cikin akwatin, abin da ya ba shi mamaki yadda aka yi rubutun takardan ya kasa gane wani yarene, sannan abin mamaki na biyu duk lokacin da ya yi yunkurin bincikar abin da aka rubuta sai wani abin ya gifta ya hana shi, to yanzu yana son sanin gaskiya a kan ciwon Michael ne, hakan yasa yake bincikar kayan mum da daddyn su na baya ko zai sami wani abin, domin a binciken da ya yi a kan matsalar Micheal ya gano akwai sanadin ciwon nasa, shi ba Dr ba ne amma kwakwalwarsa ta fi tasu aiki, yana taɓa aikin likita sama-sama, kasan cewar shi a nitse yake komai hakan yasa ya fi Daddy'n sa da yake babban likita ma iya binciken lafiya mutane, dan kwakwalwar ma ba ɗaya ba.

Yanzu haka abin da yasa ya firgita Michael a binciken da ya yi ya gane cewa kwakwalwar Michael tana bukatar a rinƙa kureta sosai, a rinƙa sanya masa tsoro da razana, idan abin ya yi yawa kwakwalwar tasa zata birkice sosai daga nan kuma zata ɗauki matsaya guda. To fah

Yana da yakinin cewa tabbas wannan rubutu dake jikin takardan tana da alaka da su, kuma tana da alaka da ciwon Michael, tunani ya fara yi, ko dai ya je ya sa mum dole ta karanta masa rubutunne, dan dai wannan rubutu tata ce. Ɗayan ɓangaren na zuciyarsa ce ta ce masa "Ka manta irin abin da ta muku? Idan har ka kusan ce ta hakan yana nufi ka duƙa kenan? Ka karya maganar ka? Kenan fa ka faɗi idan har ka yi hakan" karo na farko ya ja dogon tsaki, dan shi ba abin da ya tsana a rayuwarsa irin a ce yau ga shi ya nemi wani abu daga wajen wani, baya son wannan ko kaɗan, bai taɓa ba, kuma ba zai taɓa ba, duk abin da yake so, da karfin yake kwata, idan kuɗin sa bai saya masa ba tofa mukaminsa da izzar sa zai karɓa masa, ya fi karfin ya nemi alfarma ko kuma ya nemi shawara, kai shi fa ko irin tambayar mutun wani abu ko hanya ko wani waje, baya yi, a cewarsa ya fi karfin hakan.

Baya kula kowa, abubuwa uku da ya kamata ku sani a tattare da shi, shi kansa ma bai yarda wani ɗan adam ya ce masa sorry ba, ya haramta hakan, baya son kalmar a rayuwarsa kwata-kwata idan ka yi gigin gaya masa haka, to wlh zai iya hallaka ka, abu na biyu, a cewarsa babu wani ɗan adam da ya isa ya cewa sorry, ya fi karfin bada hakuri ga koma waye, idan ya maka laifi to ya zamar maka dole ka yafe masa, idan kaki kace zaka yi wata magana, ko a siyasa kake, yana iya sanyaka ka yi dana sanin zuwarka duniya, abu na uku, baya taɓa neman wani abu wajen wani, a cewar sa ya fi karfin yin hakan, komai da izza da isa yake karɓa.

Sosai ya zubawa rubutun nan wayan nan dara-daran idon nasa, yana kokarin gane menene aka rubuta a wajen, yana daf da fahimtar wani abu daga cikin rubun ne kamar a mafarki ya ji kukan baby daga palon kasa, ga shi yaron da karfin yake tsala kukan nasa.

Ɗaure fuska ya yi sosai dan shi baya son yara ko kaɗan a rayuwar sa

(Oh ni Allah shi komai baya so, baya son a masa laifi a ba shi hakuri haka zalika suma yara baya son su, lalai akwai cakwakiya)

Dogon tsaki ya ja tare da sanya takardan a drawer bedside, sannan ya fito ya sauƙa palon kasa.

Daddy na riƙe da yaron Jay sai ihu yaron yake yana jin yinwa, ya kuma ki ya sha madara. Tga da John suna zaune saman sofa suna latse-latse a wayarsu, sun sha barcin wahala sun ko shi, shi kuma daddy sai zarya yake a palon ya ɗaura yaron a kafaɗarsa yana ɗan bubbuga masa baya, alamar ya yi shiru.

Daddy Bawan Allah ya iya reno sosai, ko da yake shi ya yi renon yan ukunsa ai, ba kuma wanda ya taya shi.

"Who is this?!!!" Wata gigitatchiyar tsawa Lion ya daga musu, yana tsaye daga saman bene.

A ɗari su Tga suka ɗago kansu tare da miƙewa tsaye suna bin Lion da kallo, shiru Lion ya yi bai sake magana ba, ya zuba musu ido yana sauraron amsa kawai.

Tga ne ya yi ta maza, ya amsa masa da cewa "Yaron Jay ne, shi ne wadda Michael ya harbi mamansa da gun kace su Major su kai ta asibiti...." Tga bai karisa maganar ba Lion ya sake daka musu tsawa a karo na biyu "Ni na ce su kai ta hospital? Suna da hankali kuwa? Uncle Herry kawai na ce su kai hospital ita kuma na ce su fitar min da ita daga gidan nan" . Tashin hankali Tsuru-tsuru da ido suka yi, dama kuma Tga ya yi mamaki da ya ji cewa Romeo ne ya ce a kai Jennifer asibiti, abin ya ba su mamaki, ashema shi cewa ya yi a je a jefar masa da ita, tab lallai kuwa.

Shiru suka yi, har shi kansa daddy ya kasa magana, dan shima kai Jennifer asibiti da a kayi ya ba shi mamaki.

"General take this boy out from this house" zaro ido daddy ya yi, me Lion


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login