Showing 237001 words to 240000 words out of 355604 words

Chapter 80 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2774

tafiya ita kaɗai ba, nima kai na nayi mani ciwo zan ɗan kwanta, idan ya sakeni sai mu yi magana kun ji?".

DOLE KANKI YA YI CIWO IRIN WANNAN KASADA DA RAYUWA HAKA, BAKI SAN WAYE ALHAJIN BA? BAKI SAN ME ZAI IYA YI BA? FAROOQ MA IYA VOICE NASA KIKA YI MASHI KARYAR KIN ƊAUKA YA AIKO A KASHE KI, TO INA GA WANNAN DA YA KASANCE DA GASKE KIN ƊAUKI VIDEO NASA, KUMA TSIRARA, YA KUKE GANIN WANNAN WASA?, KUNA TUNANIN ANYA ZAI BARTA KUWA? KU DAI DUBA YANAYINSA KU GANI!!!!.

Riƙo Maryam Adiva ta yi suka wuce toilet ita kuma A'isha ta miƙe zaune tana binsu da kallo tana mamakin me Jehan ta yi ta karɓo Maryam cikin ƙanƙanin lokaci haka, ko kallon in da take Jehan bata yi ba, ta haye gado abinta ta kwanta tare da ajiye wayar Adivan a gabanta tana sauke ajiyar zuciya, yau taga abin da ya fi karfin ganinta, ta ga abin da ya kwance mata lissafi kwakwalwata gaba ɗaya, har wani sarawa kanta ke yi mata idan ta tuna da wannan abin.

Adiva ma bayan ta kai Maryam toilet sai ta dawo ta haye bed ɗin kusa da Jehan ɗin ta kwanta suna fuskantar juna, ita kuma A'isha ta kasa wani kataɓus ta zuba masu ido kawai dan har ga Allah ta yi matukar mamakin Jehan, kuma ita Hajiyar daɗi ta riga da ta saye ta.

Maryam kuma bayan ta yi wanka ta ɗan samu kwari, sai ta fito ɗaure da towel da ake sanya masu a toilet ɗin, tana ƙoƙarin ɗaukar kananan kayan da aka basu Jehan ta katseta da cewa "Ki ɗauki abaya a cikin kayan Adiva". Ba musu ta ɗauki abayar ta sanya, kuma ya yi mata daidai da yake duk kusan shekarun nasu ɗaya, kawai dai ɗan tazarar watanni ne a tsakani.

Kusa da su ta zo ta kwanta, suka yi shiru kowa da abin da yake ayyana wa a ziciyarsa, bayin Allah Allah ya kuɓutar da ku.

Ni kuma na haɗa kayana sai mu haɗe da ku a gidan Abbi gobe idan mai dukka ya kai mu yau na sha typing, har zafi hannuna yake yi mani😭🥺

💖💖TRIPLETS💖💖



*Idan kun samu typing error amin afuwa 👏 keyboard ɗin tana bani matsala sosai kwana biyun nan, to na yau ma ya fi tsananta, sai na danna girki sai ya koma kirki 😭*


BY FATEEMA MUSA (PRINCESS TEEMA)


E 63


💖GIDAN ABBI💖

Ayla

Bayan ta fito daga wanka, doguwar riga ta zura tare da hijabi, ta shinfiɗa dadduma ta tayar da Sallah.

Bayan ta idar ta shafa mayukanta tare da perfume nata, ta ɗauko wasu riga da wando ta sanya, wandon jeans ne blue color, akwai stones a jikinsa sosai daga ta kasa zuwa sama wurin gwiwa amma, shi kuma rigar irin wayan nan t-shirt ɗin ne masu ɗan tsawo wadda ya tsaya mata iya cinyoyinta, kayan sun fito mata da shape nata sosai.

Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta, ta yi kyau sosai, ga shi dama Aunty ta gyara mata gashin kanta jiya, ta wanke mata shi kafin suje asibiti wajen Aafia, sai sheki gashin nata yake yi.

Hijabi ta ɗauka ta zura a jikinta har kasa, sannan ta nufi Palo.

A wannan karon Hanan kawai ta samu a palon, "Aunty Hanan ina Abbi da Aunty ɗin kuma?" Ta tambaya tana nufar dining table ɗin dan ta ɗaukawa mijinta abinci.

"Wata mata ta zo ta kira Abbi, wannan mata da a asibiti ta ce ni da yaran Abbi daban daban, to ita, ta zo ta kira shi, ita kuma Aunty ta haura sama tana kuka".

Shiru Ayla ta ɗan tsaya a gaban table ɗin tana tunanin wannan bala'i na cikin gidan nan, haka jiya kafin su tafi asibiti sai da suka yi dirama, Aunty ta ce lallai Abbi a ɗakin ta yake dan haka a ɗakinta zai je ya shirya, ita kuma Hajiya Hadiza ta ce bata san da wannan zance ba, da kirsa da makirci ta ja Abbi zuwa ɗakin ta, a can ya yi wanka ya shirya, sosai Aunty ta sha kuka, a haka dai suka lallaɓa suka ta fi hospital ɗin.

Ta ɗan jima a tsaye kafin ta shiryawa daddynta kuma mijinta abinci ta ɗauka a ƙaton tray ta nufi waje tana faɗin "Idan Aunty ta fito ki ce mata na kai wa daddy abinci" to kawai Hanan ta amsa mata da shi, da sauri ta wuce dan ta ɓata lokaci.

Da sallama ta shigo cikin palon, kamar dai ɗazun baya nan, yana cikin ɗakin. Saman carpet ta ajiye abincin sannan ta nufi ɗakin nasa.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin ɗakin, yana tsaye a gaban mirror yana gyara hular kansa, yau ba wankar kananan kaya ya yi ba, dakakkiyar shadda fara tas ya sanya tare da kyakkyawar hula baka, ya yi kyau sosai, sai kamshi yake zubawa.

Ta cikin mirror ya hangota, zuba mata wayan nan idanun nasa ya yi yana kare mata kallo.

Kusa da shi ta zo tana ƙoƙarin tsugunnawa ya yi saurin juyowa ya rungumeta yana faɗin "Wannan shine irin Welcome ɗin da zaki rinƙa yi wa mijinki, daga yau na soke tsugunnawa, idan ina zaune ne, kai tsaye ki haye saman cinyata ki zauna tare da yi mani kiss, idan ina tsaye kuma rungumeni zaki ki, idan ina kwance kuma a saman kirjina zaki zo ki kwanta, kina ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e.

"Good amma kin san cewa gobe zaki tafi school ko? Tun tanar Monday ya kamata ki fara zuwa, amma saboda matsalolin da muka tsinci kan mu a ciki yasa ba mu sami damar zuwanki school ba, amma yanzu gobe dole na kai ki, dan lokaci na kara tafiya ne kin ji ko?"

"E daddy na ji, kuma ina godiya" juyo da ita ya yi suna fuskantar mirror, wani irin faɗuwar gaba ya ji lokacin da ya ga fuskarta a cikin mirror, sai ya ga wani irin muguwar kamannin tsakanin ta da maman Jelly, sake waro ido ya yi yana kallonta da kyau, ya jima yana yi mata kallon fuskar kamar wadda ya sani, amma ya kasa tantance fuskar waye ne sai yau, tabbas mugun kama ta yi mashi da mummyn Jelly, ga shi har kamannin Jellyn ma ya bayyana a face nata.

Wa kuke tunanin Ayla zata kasance? Shin kenan maman Jelly ita ce mamanta? Ko kuma dai yaya? Domin dai maman jelly bata da kanwa, kuma bata yaya, ita kaɗai ce wajen iyayenta? Wannan shine cakwakiya!.

Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna, tsab ya kare mata kallo, tabbas ba karya idanunsa ke yi mashi ba, kamannin maman Jelly ce a face nata, abin ya ɗan ɗaure mashi kai.

"Baby asalin da waye kike kama mama ko baba? Sannan kuma asalin ku yan wace jaha ce?". Ya yi maganar a ɗan ruɗe.

"Daddy ni ban san daddy na ba, amma dai bana kama da mamana sosai, kuma ni dai bayan nan Kaduna, ban san wani gari kuma ba, sai da muka je Daular Mutuwa daga nan muka je Ilorin".


Wayarsa ya ciro ya fara fito da hutunan daya ajiye a Email nasa, yan uwan maman Jelly ne da dama, sai kuma maman Jelly ɗin da kuma na jelly, duk hoton yan uwan maman Jelly da zai ga ni sai ya ga suna kama da Ayla, abin ya ɗaure mashi kai sosai, yau dai ga kamannin sun bayyana ƙarara, tunani ya fara yi to ko dai Umaima tana yare ne? Babbar magana.

Nuna mata hotunan ya fara yi yana tambayarta ko ta taɓa ganin mutun ɗaya daga cikinsu, ita ma tasha mamakin ganin duk suna kama da ita, musamman ma mummyn Jelly, kamanninsu ya yi yawa, sai ma taga kamar mamanta lokacin da take budurwa.

Duk ta ce mashi bata sansu ba, bata taɓa ganin ƙo ɗaya daga cikinsu ba, jiki ba kwari ya karɓi wayar tasa ya maida aljihunsa tare da riƙo hannunta ya ce "Muje ki bawa mijinki abinci a baki ko? Yau amarya ta ce zata bani abinci a baki, su Imran ma sun ce za su zo suyi mani murna dan Abbi ya gaya masu, sun ce za su zo, amma nace su bari sai gobe domin yau ranar ki ce, shiyasa na yi maki shigar manyar kaya, na fito a angona, kuma daga nan har dare muna tare".

Ya kai karshen maganar daidai lokacin da yake ƙoƙarin zama a saman lallausan carpet ɗin.

Gefensa ta zauna tare da zuba mashi abin cin, jikinsa duk a mace saboda tabbas Ayla tana kama da mummyn Jelly har ma da Jelly sosai, kada ya zo ya yi abin da ba shi ba, dan tunanin da ya fi yawa acikin kwakwalwarsa shine ko dai mummy'n Jelly na raye yarta ce Ayla, ko dai da cikinsa ta tafi ne, daga baya ta haifi Ayla, dan ya san mummyn Jelly bata da kanwa ko yaya, abin ya bashi mamaki sosai, kuma ya kashe mashi jiki, ya kuma kudiri niyar fara neman mahaifiyarta tun da shi baban nata bata san shi ba.

A baki ya rinƙa bata abinci tana ci har sai da ta ƙoshi, sannan shima ya ci nasa, bayan sun kammala sun tattare komai ne ya kama tannunta suka wuce cikin bedroom nasa, domin kada Irfan ya dawo da abokansa ya same su.

Soyayya mai tsabta suka shigayi babu kama hannun yaro, sai dai bai wuce gona da iri ba, ko breast nata bai yarda ya taɓa ba, dan jikinsa amace yake da ita, yana tsoron ya kasance wadda ta zama mashi haramun ya aure ne ya aure, domin wannan kamanni dake akan face nasu ba'a banza ba, dole akwai wata alaka mai karfi, kamar ta yi yawa, wannan dalili yasa ya ce dole ya nemo mamanta dan su ji waye babanta shin shine ko kuma waye? Dama yana mamakin irin bala'in kaunar ta da yake yi, abin yana ɗaure mashi kai.

A ɓangaren Irfan kuwa lokacin da ya sami saƙon cewa daddyn Jelly ya auri Ayla, har kwallah sai da ya yi, domin yana bala'in sonta fiye da tunanin mai tunani, kullun da sonta yake kwana yake tashi, bai gaya mata bane saboda yana yi mata kallon yarinya, ya hakura sai ta kara girma ne, wunin ranar dai kaf bai fita waje ba, yana ɗaki yana kwance kamar mara lafiya.

Su Akil kuwa murna awajensu ba'a magana, Imran ya ce ya ɗauki nauyin kayan lefe, amma ina daddyn Jelly ya ce wannan huruminsa ne, Akil ya ce to shi zai sayawa amarya komai da komai na kayan ɗaki da Kitchen, nan ma daddyn Jelly yaki yarda, ya ce zai yi wa matarsa komai da komai, haka suka hakura ba dan sun so ba suka kyalesa, amma kowannensu ya dunkule kuɗi makudai ya zuba mashi a account nasa, sosai ya yi masu godiya, tare da fatan alkhari.

A ɓangaren Rimsha kuwa After one day.

Misalin karfe 8 na dare, tana zaune a palon Imran tana dube dube a takardunta kamar dai kullum, ita kuma Akila tana ta faman latsa waya tana daga kwance sama sofa, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya.

Suna hira jefi jefi, da yake kowa da akwai abin da yake yi.

"Rimsha menene mafarkin ki? Me kike son ki gani an miki yanzu a rayuwar ki na jin daɗi da morewa?" Cewar Akila, ta yi maganar tana dawo da kallonta izuwa kan Rimshan.

Yar murmushi ta yi har sai da dimple nata suka lotsa sosai kafin ta fara magana. "Aunty Akila ina son in ganni a cikin daji daji haka, a irin wannan bakin teku na turawa, ina zaune ina kallon ruwa da tsuntsaye, sannan ina shakar iska mai daɗi, daga jefe kuma ga irin wannan bukka da turawa da suke yi a bakin ruwan nan, wanda zaki ganshi kamar da tampol ne ko me suka yi shi, to shi dai, haka nake...." .

Bata kai karshen ba Akila ta katse ta da cewa "Eyeee ah..ah..ah ga yar soyayya mai lasisi, wato dai haka ki ke so ko?, to daga nan kuma sai ga GAR da gajeren wando ko?, ke kuma da singlet nasa, rabin Tula-tulan dukka a waje, dan abin ya fi bata armashi, to daga nan sai ya zo ya yi sama dake zuwa cikin wannan ɗakin bukkar, ya baki jikin ki sai kin ce kin tsanesa kin tsani soyayya, ke Rimsha ina rabaki da zancen soyayyar nan kwata-kwata ke bakya ji ko? Wato har da kina shakar iskan wajen ko? To ki jira zaki shaka da tushe, wlh ina ga in wannan GAR ɗin ya rike ki, sai kin gane annabi ya faku, kinga wannan ɗan bakin naki, wlh ba zai iya fitar maki da ihu ba ranar, kina ganinsa namijin duniya, wlh ki fita sabgar irin mazan nan, dan hannu ɗaya zai sa ya ɗaga gi sama ya jefa saman gado kamar kayan wanki, ga ki yar firitu dake sai shegen son shaukin soyayya, to wlh zaki ga shauki ganin idon ki, wato ma ke har da ganin tsuntsaye ko? To wlh na gaya maki zaki yi bayani, ke nifa tun da na kalli yadda Bgs ya kare da Hiyana a Duk Karfin Izzata na fita sabgar maza masu training ɗin nan, haka zalika ba cire sojoji a lamurana, barni na sami ɗan baby wanda ya iya zuba Love ya iya rarrashi wadda ina kuka shima yana yi, mu rarrashi juna, ni yar Abba da Ammie rabani da irin TRIPLETS dukkansu babu na wasa a cikinsu, wlh kina ganin kirar jikinsu baki ga alamar wasa ba, ke yo......"

Bata kai karshen maganar ba Ammie ta shigo palon ba ko sallama, ta shigo duba Akila ɗin, domin ta je ɗakinta bata nan, kuma ta san cewa Imran baya nan Akil baya nan, ina Akila zata je da daddaren nan, ita da ko da rana ma bata fita, bare kuma yanzu dare, shine da bata ganta ba, ta duba Part ɗin Akil bata a ciki, shine ta zo nan.

Jin shigowar mutun yasa gaba ɗayarsu suka ɗago kai, a razane Ammie ta dakawa Rimsha wani irin mahaukacin tsawa "Me ya zaunar dake a cikin gidan nan? Ba nace ki fita ba?!!."

Akila jiki na kirma ta miƙe daga kishingiɗar da ta yi, ita ma Rimsha miƙewa tayi daga zaman da take, dukkansu sun tsorata, sai kerma jininsu ke yi.

"Ke zoki fita a cikin gidan nan ko kuma yanzun nan na kashe ki!!!".

A razane Akila ta ɗaura hannu a saman bakinta tana hawaye, tsawa ita ma Ammie ta daka mata akan ta rufe mata baki.

Zube gwiwowinta kasa ta yi tana kuka ta fara magana "Ammie ki yi hakuri, wlh Rimsha bata da kowa, idan ta fita gidan nan cikin daren nan ina zata je? Dan girman Allah Ammie ki yi hakuri kin ji?.

A zafafe Ammie ta karaso cikin ɗaki sai huci take yi, hankalin ta ya yi matukar tashi, karo na farko da ta fara wanke wa Akila fuskarta da mari tare da daka mata wani mahaukacin tsawa wadda ya sanyata miƙewa a guje ta nufi waje.

Ita ma Rimsha tana hawaye ta ɗauki wayarta ta nufi waje da gudu.

Akila ta nufi chikin gida while ita kuma Rimsha ta nufi waje, ga shi bata ɗauki ko hijabi ba haka ta fita da gudu tana yi tana kuka hawaye bibbiyu.

A ɓangaren Jelly kuwa, yau saura kwana shidda biki, abubuwa duk sun kankama, kuma yau Hajiya batula ta zo, ta rage kwana ɗaya a cikin wayan da ta ɗiba.

Sosai ta fara gyaran Amarya, amma ta yi mamakin ganin Jelly sosai, ta ce tana mata kama da Hassan da Hossain, wato yayyunta, sai kallonta take yi, tana ji tamkar jininta ne, dan kamannin ya yi yawa, ba iya su kaɗai take kama da su ba, har da Abla yar Hajiya Batula ɗin, sun yi kama sosai, jini ba wasa ba, ga idonta irin na daddynta sak.

Har hotonta Hajiya Batula ta ɗauka akan idan aka gama biki ta koma zata nunawa Abla da kuma Akila da Imran, dan Akila da Imran sune kaɗai masu zuwa wajen ta, ko Akil baya zuwa, sai ma da ta yi tunanin Imran sai ta kara ganin kamannin fuskarsa akan fuskar jelly ɗin, da yake jini ba wasa ba, kunsan ko wani lokaci da irin siffar da ɗan adam ke kallon ɗan uwansa ɗan adam, kowa da irin kallon da yake mata, wani anasa ganin ka yi mashi kama da wani, wani kuma sai kaga bai ga wannan kamanni ba wani yake gani a tattare da kai, to ita dai Hajiya Batula ganin jininsu kawai take yi wa Jelly, da yake bata san da ɓatar Jellyn ba, hasalima bata san Jelly ɗin ba, ta dai san Maik ya yi aure, amma bata san ya mace ya samu ko namiji ba, tun da Imran ya ke zuwa wajen ta, bai taɓa gaya mata ga irin abin da daddy'n jelly ya haifa ba, bai taɓa bata labarin ahli ba, sai dai hirar yaushe rabo, shiyasa bata san da labarin Jelly, Aafia, Umaisha, har Akil, duk bata san mata suke ko maza ba.

Sai gyaran Amarya ake yi babu kama hannun yaro, ita kuwa jelly ko a jikin ta, bama su isheta kallo ba, wata shain ma, ana mata gyaran tana cin wani abin, ko kaza ko wani abin.

Shi kuma ango Nawid yau yake son zuwa wajen Rimsha, sai zumuɗi yake yi, ya ji daɗi rana ta farko ta kula shi har ta zauna suka yi hira sama sama, hakan yasa ya ce yau zai koma su sake zantawa ko Allah zai sa ya yi nasara.

A ɓangaren shima A'A SALAHUDDEEN yana can yana shirye shiryen sa, gobe Jumma'a zai diro cikin Kaduna dan ya ga Rimshan sa

Yayin da ita kuma Rimshan tana fita ta kama hanyar titi, tana tafiya tana kuka, bata san ina ta nufa ba, kawai tafiya take yi har ta yi ɗan nisa, Horn ɗin motar da ta ji abayanta ne yasa ta juya da sauri, bata iya ganin su waye ne dan sun haske mata wutar motar.

Cigaba da tafiya kawai ta yi tunda bata gane su waye bane, da sauri Imran ya buɗe kofar motar ya fito yana faɗin "Thank you Saif". Gabanta ya sha da sauri yana faɗin "Sorry our First Lady" kuka mai sauti ta kara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login