Showing 21001 words to 24000 words out of 355604 words

Chapter 8 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2738

ɗakin yar aikin da Abbi ya kawo, ta kirata akan tazo ta taimaka mata susa Aunty a mota su wuce asibiti kafin Abbi ya fito.

Yar aikin yarinyar kirki ce, haka tazo tasa iya karfin ta, Aafia ta dage, da kyar suka ɗaga Aunty zaune, kun san dai idan mutun ya suma, ba karamin nauyi yake karawa ba, saboda jikin sa duk ya saki,

Sun yi nasarar miƙar da Aunty zaune, amma ba su iya ɗaga ta sama ba, wannan miƙar da ita zaunen ma da sukayi, sai haki suke kamar wayan da suka tiki uban gudu suka koshi.

Sun kasa miƙar da Aunty tsaye, kuka Aafia tasa mai sauti tana faɗin "Mun shiga uku!" Itama yarinyar ta tsorata sosai da sosai, dan koda Aunty ta suma, jinin jikin ta bai dai na zuba ba, tana bleeding sosai.

Tsabar ruɗu da shiga tashin hankali yasa Aafia ta fara jan Aunty a kasa, suka nufi wajen, yar aikin ma ta bi bayan su.

Bayan sun fito wajen palon ne, ta bar Aunty kwance a kasa ta koma cikin ɗaki, ta ɗauko wayar ta, sannan ta wuce ɗakin Abbi ta ɗauki key ɗin motar sa, dan nata motar yana gidan su Akil, duk wannan abun dake faruwa, Abbi da daddyn Jelly suna toilet suna faman cetan kan su suma, dan sun kasa ko fita waje, da sun miƙe zasu kuma komawa, Aafia ta musu tsiya ba kaɗan ba.

A ɓangaren Aafia kuwa, tana fitowa, ta wuce wajen motar Abbi, ta shiga ta kunna motar, ta jawo shi zuwa wajen da Aunty ke kwance, sannan ta fito ba tare da ta kashe motar ba, ta buɗe gidan baya, suka haɗu tare da yar aikin, da kyar suka tura Aunty cikin motar, sai wani uban nishi suke kamar wayan da suka ɗaga tayar trailer.

Suna shigar da ita Aafia ta rufe motar ta shige gidan gaba, da gudun gaske taja motar, mai gadi dake tsaye tun ɗazun yana kallon su ba halin yazo ya taimaka musu, dan bai shafi aikin saba, tun Aafia bata kariso wajen ba, ya wangale mata gate ɗin gidan, da gudu ta fice, ta nufi asibiti.

Abbi da daddy suna can, suna ta kan su, bayin Allah, Aafia tajaza musu wahala.

A ɓangaren Umaisha kuma, bata farka daga nauyayyar barcin daya ɗauke ta tun bayan sallar asuba ba, sai karfe 9 na safe, shima ba ita ta farka dan kan ta ba, Ammie tazo ta tashe ta, lokacin Akil baya nan ya fita, Akila kuma ta tafi school.

Wani gigitacen tsawa Ammie ta daka mata wadda ya sanya ta jin duk wani barci da take ji ya gudu "Ke zaki tashi ne ko sai na sa kafa na hanɓare ki sai kin faɗi kasa!!" Da kyar Umaisha ta iya miƙewa zaune, dan har yanzu jikin ta ba wani kwarin kirki

Zubawa Ammie dake tsaye a kan ta ido tayi, sai wani turɓune fuska Ammie take, tana mata kallon kankanci

Cikin tsawa Ammie ta fara magana cike da bada umarni, da nuna izza da kuɗi "Ina son ki buɗe kunnan ki da kyau ki saurare ni, daga yau tun karfe 6 zaki rinƙa tashi ki mana shara da wanke-wanke, sai gyaran ɗaki, shima ki mana shi tsab, da ɗaki na dana, Abban Akil, har dana su Akila, idan kin gama ki wanke toilets duka, sannan kiyi mopping na ko'ina, shi dai girki, Allah ya taimake ki bama son naki kina jina?!!" Gyaɗa mata kai Umaisha tayi alamar eh, kun dai san yadda gidan Hajiya Umaiya yake basai na sake faɗa muku ba, kuma kun san dai yadda ita kan ta Hajiya Umaiyar take, da kazan ta, datti ta ko'ina, babu gyaran gida babu na jiki, duk wasu yan aiki idan aka kawo mata, sai sun gudu saboda masifar ta, ga saurin hannun dukan ƴaƴan mutane, ga bakar zuciya kamar kafuran farko, bata da mutunci ko kaɗan, ga yiwa talaka kallon kaskanci, bugu da kari ga makirci, makirace ajin farko.

Tsawa ta kuma dakawa Umaisha "zaki tashi ne ko dai sai na kwasheki da wawan mari?!" A hankali Umaisha ta zuro kafafun ta kasa, ta miƙe a nitse, da kyar da kyar take ɗaga kafar nata, saboda har ga Allah zafi wajen yake mata, haka ta nufi hanyar fita daga ɗakin, tana jiyo Ammie tana ta ruwan bala'i, wai Akil ba zai zauna da yar talakawa ba.

Tofa wannan shine gaba da gaban ta, muje zuwa

Shi kuma Akil bawan Allah yana can super market yana mata sayyan kaya, shi saboda tsabar kishin sama, bai yarda suje super market da ita ba, gara ya tafi shi kaɗai yaje ya sayo mata kayan ya kawo mata, idan ma colors ɗin da ya sayo mata ya mata fine, idan kuma bai mata ba, nan ma ita ta jiyo, shi dai ya sayo kuma dole tasa masa ya gani, duk abun da ya masa kyau kawai yake ɗauka, ba ruwan shi da zai burgeta ko ba zai burgeta ba, in dai shi zai burge shi.

Yau Umaisha taga ta kan ta, dan ko bata iya aikin komai ba, wannan dalilin yasa ake cewa, duk abun da kayiwa wani sai an maka, lokacin da suka sako Aunty a gaba, suka rinƙa takurawa matar nan baji ba gani, bata isa tayi wani motsin kirki ba ita da gidan mijin ta, Allah sarki ita kuma kullun nasihar da take musu, ku mata ne baku san in da aure zai kai ku ba, ku bi a hankali, amma duk basu ji suka sa kafa sukayi fatali da duk wani shawara da nasiha da take musu, sukayi kunnan uwar shegu, to yau dai ga gari ya wayan wa Umaisha, kuma da garin ya tashi wayan mata, sai ya wayan mata a gidan Hajiya Umaiya, wadda bakin ta kaɗai idan aka bar mutun da shi, ya isa ya sashi yayi ta rama har ya mutu, ina ga ankai kan sauran aikin kuma, ai sai dai muce Allah ya kyauta.

Palo Umaisha ta fara gyarawa tana yi tana tuna yadda taga Aunty na aiki a gida, gashi gaban ta na mata zafi sosai, da kyar take iya ɗaga kafar ta, har wani zufan wahala take haɗawa.

Da kyar ta iya gyara palon, amma ta ɗauki wajen 1 your a palo kawai, kuma iya shara da shirya pillows na kishin kawai, ba'a kai ga mopping ba, sannan ta wuce cikin kitchen, gaba ɗaya kitchen ɗin sai warin rubaɓen abinci da su fruits da sauran abubuwa yake, haka ta daure, ta zage ta fara aiki babu kama hannun yaro, tanayi tana kuka, ita kuma Ammie ta wuce sama abun ta, ta samu sabuwar yar aiki, sai kuma abun da hali yayi.

Tana kitchen Akil ya dawo bata sani ba, bedroom na su ya wuce hannun sa riƙe da wani katon trolley yana ja, dan shi saboda kishin sa bai yarda mai gadi ko mai bawa flowers ruwa ko driver su taya shi ɗaukan kayan matar sa zuwa cikin gida ba, a'a da kan sa ya jido komai zuwa cikin bedroom na su.

Yasha mamakin ganin Umaisha bata ɗakin, shi da yayi tsammanin zaizo ya same ta kwance, dan bata jin daɗi, sai kuma yazo yaga bata nan.

Bayan ya gama shigo da kayan, toilet ya fara leƙawa, wayam ba ta ciki, hakan yasa ya fito waje dan ya duba ta.

Lokacin da ya fito palo, lokacin ita ma Ammie ta fito daga bedroom nata, ta sauƙo ƙasa

"Ammie where is my wife" ya faɗa yana ɗan waige waige kamar mai neman wani abu, Murmushi makirci Ammie tayi kafin tace "Ashe yarinyar nan yar albarka ce Akil am, ni ban sani ba, na dage ka rabu da ita, ashe yar halak ce, tun ɗazun ta fito ta fara shara da mopping, nayi nayi ta bari amma taki, tace ita kam tana son taga tana yimin aiki, dan a matsayin uwa ta ɗauke ni, tana cikin Kitchen tana faman gyarawa", murmushi shima yayi kafin yace "Ai daman Ammie na faɗa miki, zaki so ta In Sha Allah dan tana da hankali" kara faɗaɗa murmushi ta Ammie tayi tanan faɗin "Ai tunima na kamu da son ta, yarinya yar albarka haka, ina hana ta aikin nan, yarinyar nan tace sai dai na kyale ta tamin, nace ta bari bata da lafiya, amma taki tace zatayi, har da kuka ta samin, kamar yadda kaga Akila ke yimin ita ma haka ta min, baiwar Allah a uwa ta ɗauke ni" shima kara faɗaɗa murmushin sa yayi yace "To yanzu dai ta bari tazo taci abinci tasha magana, sannan tazo ta ci-gaba" shiru Ammie ta ɗan yi kafin tace "Eh hakan ya kamata" wucewa yayi ya nufi kitchen ɗin ba tare da ya sake magana ba, harara Ammie ta bishi da shi, a zuciyar ta tana faɗin "Sai ka koreta da kan ka, In Sha Allah, ko kuma ita da kan ta, ta gudu"

Umaisha na aikin wanke-wanke tana kuka, kusa da ita yazo ya tsaya, tare da rungumota ta baya yana faɗin "Ke kika jawa kan ki, kin san baki da lafiya me na cewa lallai sai kin yi aiki? To gashi yanzu kina yi kina kuka, nasan kuma dole daman kiyi Kuka, saboda ba koshin lafiya gare ki ba, yanzu dai ajiye aikin muje na baki abinci, kici ki sha magani ki ɗan huta, sai ki dawo ki ci-gaba da aikin" ajiye soson wanke-wanken dake hannun ta tayi, tare da kunna pampo ta wanke hannun ta, sannan ta juyo ta rungume sa da kyau tana kara faɗaɗa kukan da take

A ɗan ruɗe yace "Lafiya? Me kuma ya saki kuka?" Yayi maganar yana ɗago haɓar ta, cikin kuka tace "Yaya Akil dan Allah ka mai dani gida kaji?" Hannu yasa yana goge mata hawayen dake zubowa yana faɗin "Ya isa haka, kiyi shiru, zan kai ki gida amma ba yanzu ba, kiyi hakuri sai bayan sati biyu kinji ko?" Gyaɗa masa kai kawai tayi bawan dan ta gaji da rokan sa ba, a'a sai dan bakin ta ya mata nauyi, ta sha wahala, tun da Akil yayi dis virgin ɗin ta take cikin wahala da azaba, ta gala bai ta sosai, tasha wahala.

Hannun ta ya riƙo yana faɗin "Muje ko?" Da kyar ta iya ɗaga kafa ɗaya, tana kara sautin kukan nata, ganin haka yasa ya ɗauke ta cak ya fice daga kitchen ɗin.

"Akil me ya faru? Lafiya ka ɗauko ta haka?" Cewar Ammie tayi maganar cike da nuna damuwa na makirci, "Ammie kafar ta ke yi mata ciwo" ya faɗa yana haurawa sama, bin sa da kallo takaicin Ammie tayi har ya shige part ɗin sa.

Saman sofa ya zaunar da Umaisha yana faɗin "Sorry my wife" sai jan hanci take, alamar tasha kuka har ta koshi.

Abinci ya ɗauko mata, da kan shi ya zauna kusa da ita, ya fara bata a baki, tana ci tana kallon cikin idon sa, lokaci guda taji mugun son shi na shigar ta, "Ke wai me yasa kike yawan kallon fuska nane?" Ya tambaya yana kallon ta shima, shiru tayi ba tayi magana ba, dan bata da amsar da zata bashi "Ba za kiyi magana ba?" Nan ma shiru tayi, kuma ba ta daina kallon nashi ba, "Ki dai na kallo na, kada ki haifa min baby mai kama dani, dan ni mai kama dake nake so" nan ma shiru ta masa, still har lokacin ko kyafta idon ta ba tayi ba, ta tsare sa kawai tana kallon sa, duk abubuwan da yake faɗa ma, basa shiga kunnan ta, tana can duniyar tunanin son da take masa, da kuma yadda za tayi ta bar wannan gida, dan zaman ta da Ammie ba zai yiwu ba.

Hannu yasa ya rufe mata ido yana faɗin "Zan rinƙa saka nikaf kada ki kwashe min kyau na, da wanan irin kallon naki" murmushin cikin kuka tayi har sai da ta sanya shi sauke nauyayyar ajiyar zuciya, uhm soyayya daɗi.

Sosai ya ɗura mata abincin nan, sai da ya tabbatar ta koshi, sanann ya ɗauko maganin ta ya bata, bayan ta sha, ya ɗauke ta zuwa toilet, da kan sa ya mata wanka, yana yi yana tsokanar ta, har suka gama suka fito, ya buɗe trolley da ya sayo mata kaya, ya ciro mata wani dogon riga mara nauyi, ya bata ta karɓa ta sanya.

Bayan ta gama shiri, yace ta hau gado ta kwanta, ba musu ta haye gado ta kwanta tana jin matikar kaunar mijin nata har cikin ranta, shi ba mugu bane kamar yadda take tunani, idan ka fahimce shi zaka ji daɗin zama da shi, shi raini ne baya so, kuma yana son a nuna masa shine a sama da mutun, yana son abashi kulawa, kuma a nuna masa ya isa da mutun, baya son a masa jayayya da maganar sa idan yayi, ya fison da yace abu ace masa to, kuma baya son ya kawo abu ya baka kace masa color ko wani abu bai yi maka ba, a takaice dai shi ka nuna masa shine boss, idan kayi haka zaku zauna lafiya, zai maka abun da ma baka taɓa tunani ba na alkhari da kyautatawa.

Har ta fara barci sai taga yana kokarin fita, zubur ta miƙe zaune tare da saka masa kuka tana faɗin "Yaya Akil dan Allah karka fita" juyowa yayi yana kallon ta da mamaki, ganin da gaske take masa kuka har da hawaye yasa ya dawo kusa da ita ya zauna tare da ɗan rungumota kaɗan yana faɗin "My wife me yasa kike kuka?" Kankame shi tayi tare da kara faɗaɗa kukan nata, dan tasan yana fita Ammie zata zo ta saka ta aiki, kuma jikin ta na mata ciwo
"My wife kiyi magana mana, me yasa kike kuka?" Cikin kuka tace "Yaya Akil dan Allah kada ka fita, ka zauna kaji?" Mamaki ne ya kara kama shi, hannu yasa ya ɗago haɓarta yace "Wajen bappa zanje fa, yaya Imran ya aike ni, yace lallai naje gidan ku na duba masa ina bappa Maik ya kai Jelly, dan kullun idan suka kira shi, sai yace musu ko tana barci ko ta tafi shopping da Aafia, shine yaya Imran yace naje na duba masa, dan ya shiga damuwa sosai yana ji a jikin sa kamar ba lafiya ba, akoi abun da bappa Maik da kuma Abbin ku suke ɓoye masa, ki bari naje na dawo, ba zan jima ba kinji?" kara kankame shi da kyau tayi tana cusa kan ta a kirjin sa, cikin kuka tace "Ni dai a'a wlh ban yarda ba, sai dai mu tafi tare, ko kuma ka zauna babu in da zaka je" lokacin guda yaji wani bakin ciki ya ziyarci zuciyar sa, ba komai ne ya hassasa hakan ba, face cewa da tayi ya zauna babu in da zashi, a nashi ganin ta raina shi umarnin ma take bashi, dan haka sai ya daka mata tsawa "Ni zaki gayawa abun da zan yi? Wato umarni ma kike bani, na zauna babu in da zanje, to baki isa ba, ke mata tace a karkashi na kike nine zan baki umarnin ba kece zaki bani ba, I am the boss here" ya kai karshen maganar tare da kwace jikin sa daga riƙon da ta masa, ya miƙe ya fice daga bedroom ɗin yana wani hucin ɓacin rai, yau Umaisha ta raina shi.

Oh Akil manya, wannan ma bashi ne babba a gidan ba, idan da shine Imran kam, ai da shikenan an shigesu, mutun sai bala'i son girma, Umaisha aiki na gaban ki, babba kuwa. Masu karatu mukoma wajen First lady wato Rimsha, Meesha, Siha, first lady, duka sunan tane, ɗaya tamkar da dubu in ji daddy ta, bari mu leƙo ta mu dawo.

Ayla da Kausar tas suka take abincin nan, Kausar kam har da lashe kwano da harshen ta, tas tayi wa kwanon kamar an sanya ruwa an wanke kwanon
miƙewa tayi hannun ta riƙe da kwanon tuwo dana miyar duka bayan ta gama lashewa "Ina zaki je Kausar?" Cewar Rimsha, kumbura kumatu tayi tana ɗan jujjuya ido tace "Zanje in ce su kara min abincin mana" salati Ayla tasa tana tafa hannu, Rimsha kam ta rasa bakin magana dan Kausar tafi karfin ta, daman haka Kausar take, a daular mutuwa ne take kamar malama, tab lallai daman idan kuna cikin wahala da kunci baka taɓa gane halin mutun, sai kun samu freedom ko yaya ne.

Suna tsaka da tunani, basu san lokacin da Kausar tayi wuce wan taba, basu fargaba sai ganin Kausar sukayi da wani kula a hannun ta, zama tayi a in da ta tashi, ta bude kulan abun ta ta fara cin abincin "Ke Kausar waya baki wannan abincin?" Cewar Rimsha, turo baki tayi tace "Gani mana nayi na ɗauka" salati Ayla tasa tana faɗin "Wlh abincin yaron sarki ne, kuma bashi da mutunci mashayin giya ne lamba ɗaya, shekaran jiya dana zo gidan nan, wlh ya kusa yimin fyaɗe dan yasha ya bugu, da kyar maman sa ta kwace ni a hannun sa"

ina ai su Ayla zancen su kawai suke ita kausar bata tare da su, loma kawai take kaiwa baki abun ta, hannu baka hannu kwarya, har wani lumshe ido take, saboda daɗin miyar matar sarki, hannu Ayla tasa ta janye kulan abincin daga gabar Kausar, ta rufe tana faɗin "Ke so kike a koremu daga gidan nan ko? To wlh ki dawo cikin hankalin ki, kin samu sun bamu abincin da masauki ba zamuyi taka tsantsan dan mu samu mu rabu da su lafiya ba" turo baki Kausar tayi kafin tace "Ori dafun" kallon Rimsha Ayla tayi, sannan ta dawo da kallon ta kan Kausar tace "Ke kika san shi" murmushi Rimsha tayi kafin tace "Ita ta san me kuma Ayla" "Ita ta san shi Ori dafun ɗin mana" dariya Rimsha tayi kafin tace "Kai amma fa idan baka jin yare akoi abu, dan a mahaukaci kake ɗaukan mai yin wannan yaren" miƙewa Ayla tayi, ta wuce kitchen na matar sarki taje ta mai da kulan abincin ta dawo ta zauna.

"Ayla dan Allah kiji mana ba gaskiya na faɗa ba, nace mu tara kuɗi mu tafi wajen GAR ɗin Meesha, dan yadda take bamu labari kinga ai mai kuɗi ne, idan mukaje zamu samu kuɗi, amma meesha tana min dariya" ita ma Ayla dariya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login