Showing 174001 words to 177000 words out of 355604 words
ɗauke da kayatatcen murmushi ta juyar da kallonta izuwa kan baƙon. Yana zaune saman dadduma yana Fuskantar kofar shigowa, sai dai kansa a kasa yake, jikinsa na sanye da jallabiya fara tas mai bala'in kyau.
Sakin plate ɗin hannun nata ta yi ya faɗi kasa, da karfi-karfi kirjinta ya fara dukan uku uku, numfashinta ya fara fita da sauri-sauri, laɓɓanta sai kerma yake yi, jikinta na ɓari, hakwaranta har wani haɗuwa suke da juna, da kyar ta iya motsa lips ɗin nata ta murya na rawa ta furta "G..A..R..." Bata iya karisa fitar da R ɗin ba ta yanke jiki ta faɗi kasa sumammiya.
A zafafe Imran ya miƙe ya yi kanta yana kiran sunan ta. Shi kuwa Saif tamkar bai san da mutane a ɗakin ba, bai yi wani motsi da zai nuna cewa ya san ma da mutane a ɗakin ba, amma fa har cikin zuciyarsa ya ji sunansa da ta kira, kuma idanuwansa suna son gane mashi wace ce wannan da har zata iya gane fuskarsa, bayan kuma shi ba wanda ya san ainahin face nasa a Media, sai dai a gidansu, amma ba zai iya ɗaga ido ya kalli koma waye bane, domin bai kai matsayin GAR ya ganshi ba.
Tofa ya kuke ganin wannan lamari, me ya kawo GAR Nigeria? Dama shi musulmi ne? Me ya haɗa shi da Imran? Me yazo yi? Anya shine kuwa? Ko dai mafarki Rimsha take yi? Ni dai na yi na sai mun haɗe idan mai dukka ya kai mu
💖TRIPLET'S💖💖
49-50
A zafafe Imran ya miƙe ya yi kanta yana kiran sunan ta. Shi kuwa Saif tamkar bai san da mutane a ɗakin ba, bai yi wani motsi da zai nuna cewa ya san ma da mutane a ɗakin ba, amma fa har cikin zuciyarsa ya ji sunansa da ta kira, kuma idanuwansa suna son gane mashi wace ce wannan da har zata iya gane fuskarsa, bayan kuma shi ba wanda ya san ainahin face nasa a Media, sai dai a gidansu, amma izza ba zai bari ya iya ɗaga ido ya kalli koma waye bane, domin bai kai matsayin GAR ya kalle shi ba.
Da karfin Imran yake kiran sunanta amma ina ko motsawa ba ta yi ba, hankalinsa ba karamin tashin ya yi ba, gaba ɗaya ya birkice, kamar wata baby haka ya ɗauke ta fice da ita zuwa nata ɗakin, saman bed nata ya kwantar da ita, cikin sauri ya dawo bedroom ɗin nasa, yadda ya bar Lion haka ya dawo ya same shi, ko ɗago kai sa bai yi ba, tattare ruwan da drinks da Rimsha ta kawo ya yi, sannan ya mai da saman plate ɗin, shi kuma glass cup ɗin already ya fashe, Imran bai lura da ya fashe ba sai dai kawai ya ga jini na zuba daga ƙafarsa, bawan Allah tsabar kiɗima bai san lokacin da ya taka glass ɗin ba. Guntun tsaki ya ja tare da ɗaukar plate ɗin ya fice waje, bai damu da jinin dake zuba mashi a kafarsa ba, ya koma Kitchen.
Sauri-sauri ya sake shiryawa Lion wani ruwan faro mai sanyi da wasu drinks ɗin, abin da ya sanya ya ɗauko mashi wasu kuma ya san halinsa sarai tsab zai iya cewa ba zai sha wayan nan ba, domin yana da tabbacin ya san da faɗuwar su kasa, hakan yasa ya canzo mashi wasu.
A gaban shi ya zo ya ajiye mashi sannan ya wuce toilet dan ya wanke jinin dake zuba mashi a kafarsa ya yi dressing na wajen. Bayan ya wanke ya yi komai ya fitone sai ya ga Lion bai ko kalli ruwan da ya kawo mashi ba, bare kuma yasa ran zai sha.
Cike da kulawa ya ce "Saif ga ruwan ka yi buɗa bakin mana?" Kamar dai ko yaushe shiru ya yi bai ɗago kai ba bare kuma Imran ya sa ran zai amsa mashi magana, kasancewar Imran ya saba da halin nasa sai bai wani damu ba, domin ba yau suka saba ba. Goge wajen da jininsa ya zuba kawai ya je ya yi tare da kwashe glass da ya fashe ya gyare wajen, sannan ya dawo saman gefen bed nasa ya zauna.
*Nasan kowa daga cikin ku bashi da wata burin da ta wuce sanin ya akayi Imran ya san Lion? Ya akayi Lion ya kasan ce Musulmi? Ya akanyi ya zo Nigeria? Ya akayi yana musulmi kuma bai musuluntar da yan uwan sa ba? Ya akayi ya ɓoye cewa shi musulmi ne? Ta ya ma ya musulunta? Wannan tambayoyin na san sune cike a ranku, to a yanzu dai za ku samu amsoshin guda biyu, saura kuma sai gaba.*
Lion dai a tare suka yi makaranta da Imran da kuma James, a lokacin ma har da Michael, idan ba ku mance ba, James ya gayawa Musharraf yana da aboki musulmi, haka zalika shima Michael ya sanar da Musharraf Lion yana da aboki musulmi, to amsar ku ta farko dai shine, Lion tun bai zama babban soja ba suke tare da Imran, tare suka yi makaranta, duk duniya Lion bashi da wani aboki biyun Imran, shi kaɗai ne friend nasa sosai, kuma shine mutun na farko da Lion ya fara yarda da shi a duniya, kuma har gobe bayan Imran ɗin bai sake yarda da wani ba, ko su Tga ba komai na sa yake gaya masu ba, amma Imran yana gaya mashi halin da yake a ciki. wannan shine amsarku ta farko.
Tambaya ta biyu, me ya kawo Lion Nigeria?. Amsa ba Nigeria ya zo ba African ya zo ma'ana. A.E.I.D.S.A
(1).A. America. (2) E. England. (3) I. India (4)D. Dubai (5) S. Spain. (6) A. African. Wayan nan sune kasashen da yake nema, so James yana African, sai dai bai san a takamaiman wata kasa yake ba a African, abin da kuma yasa ya zo Nigeria shi ne, ba wanda ya sani gaba ɗaya faɗin African sai Imran da yake Nigeria, wannan dalilin yasa ya zo Nigeria, kuma yana zargin James yana tsakanin Niger da Nigeria hakan nema ya bashi kwarin gwiwar nufar Nigeria kai tsaye. Wannan shine amsa guda biyu da za ku samu sauran kuma sai dai gaba, mu koma cikin story kai tsaye.
Ya jima kansa a duƙe yana kallon kasa, daga bisani ya miƙe tsaye, wani tsawo ya kara sosai cikin jallabiyar nan, bakin gado ya koma ya zauna yana jawo wayarsa dake a saman bedside drawer Imran.
"Saif dan Allah ka yi buɗa bakin mana?" Nan ma shiru ya sake yi wa Imran, zuba mashi ido Imran ya yi yana karantarsa na ɗan lokaci sai daga baya ya fahimci cewa ruwan Faron ne bai yi mashi ba, ba zai iya sha ba. To fah tashin hankali, babbar magana yau ake yinta, ruwan faro mai gaba ɗaya bata yi mashi ba, to ina za'a samo mashi wani ruwa yau ya yi buɗa baki? Sosai tausayinsa ya kama Imran, dan yasan dama da wuya ya iya zama a Nigeria, dan rayuwar ba ɗaya ba.
Miƙewa ya yi ya nufi waje, yana faɗawa Lion yana zuwa, yana fita kai tsaye cikin gida ya nufa, bedroom ɗin Abba ya shiga, dan yasan Abba yana da dabino masu kyau tsabtatatu wadda ake kawo mashi daga Madina, da kuma ruwan zamzam. Kwali biyu na dabinon ya ɗauko tare da zamzam gora biyu masu ɗan girma, sannan ya dawo part nasa, ya wuce ya san zamzam ɗin a cikin fridge, dabinon kuma ya wuce da su ɗakinsa.
Lion na zaune a in da ya barshi yana riƙe da wayarsa, kusa da shi Imran ya zo ya zauna tare da buɗe mashi kwali ɗaya na dabinon yana faɗin "Please Saif ka yi buɗa baki da wannan sai ka sha maltinan, shi kuma ruwan sai ka gaya mani irin wanda kake so, sai mu nemo maka, amma na sa maka zamzam a fridge idan zaka iya sha".
Sai da ya ɗauki good 10mins sannan ya karɓi dabinon, kwara ɗaya ya ɗauka ya kai ɗan bakinsa, tare da yin Bismillah, bayan ya ci ne sai ya ajiye wayarsa a saman gadon, ya sauƙa kasa ya fuskanci gabas ya yi addu'a na masu buɗa baki, da ya gama sai ya koma bakin gadon ya zauna.
Lokacin da ya ajiye wayarsa ya sauƙa dan yin addu'a shi kuma Imran ya ɗauki wayar yana kallon abin mamakin dake acikin wayar.
Video Michael ne lokacin da yake zaune saman bed nasa yana ta karatan suratul Fatima da Musharraf ya koya mashi, sai kokarin haddarta ya ke yi, ga kyakkyawar fuskar nan tasa ɗauke da kayatatcen murmushi, wani mugun farincikin Imran ya ji ta kulluɓe shi, sannan kuma abin ba karamin mamaki da kuma burgewa ya yi mashi ba
Na san kuma kuna son sanin ta ya akayi ya samu wannan video, kuma ya akayi ya ajiye a wayarsa yake gani, to dai ku cigaba da bibiyar TRIPLETS a hankali za ku sami amsoshin ku gaba ɗaya, amma dai Lion mutun ne mai abin ban mamaki, baka taɓa gane ina ya dosa, sai dai ka bishi a yadda ya zo maka.
Abin da ya sanya kwana biyu yake matukar shiga yana mai daɗi kenan, saboda Michael ya musulunta kuma ƙwaƙwalwarsa ta samu lafiya, sannan yana ɗaukar karatun yadda ya kamata, ko da yaushe Lion yana bibiyarsu sosai, domin ya ga a ina karatun Michael ya tsaya, ranar da suka je Masallaci ma duk yana kallonsu, duk wani motsi da za su yi a gidan har ma da wajen gidan, to fa akan idanunsa suke yin shi, yana sane da komai, kawai dai shi baya shiga harkar kowa ne, a da baya kafin ya musulunta ko mai zaluncin da ake yi wa mutane baya shiga harkarsu, amma daga baya da Musulmici ta ratsa shi ne yake iya saka baki idan ana zalunci a gidan, bacin haka shi ba zaka taɓa ganin shi yana shiga har kar kowa ba, abin dake a gabansa kawai yake yi, lokacin da ya kasance musulmi alokacin ne ya kafa masu dokar hana su zina, ya ce duk mai son mata ya yi aure, domin alokacin ya san hukuncin mazinaci, a baya ba ruwansa da irin wannan baya shiga wannan harkar, koda kuwa akan titi za'ayi zinar ba ruwan shi, kunsan dai yadda turawa suke, yin zina ba wani abin azo a gani bane a wajen su, basu ɗaukar shi kamar laifi ba ne, sanna kuma lokacin da musulci ta ratsa shine ya san darajar iyaye shiyasa har yake kokarin kula da daddy, idan na ku mance ba akwai lokacin da daddy ya ce yana mamakin Lion a yanzu ya sauya yana bashi kulawa, to hasken musulunci da kuma imani tasa, kun san dai da abaya ne lokacin da zuciyar kafuran farko take a kirjinsa da Rimsha bata isa ta shiga wannan ɗakin ba, amma yanzu abin da ɗan sauki musulci ba wasa ba, amma dai still har gobe yana da bala'in zuciya wadda kuma kun san wannan halittace, haka zalika har gobe mace bata a gabansa, shi yanzu ma da za ki tambaye shi ya mace take a suffa, wlh ba zai taɓa iya gaya maki daidai ba, domin bai sani ba, kai ko halittar namiji ba dan ya kasance irin sane a jikinsa ba, da shi ma mawuyacin abune ya san shi, domin idan baku mance ba, shi baya kallon mutane kuma baya son a kalleshi, haka yake, dan haka baya ce maki ga yanayin yadda mata suke dressing da sauransu ba, a karatu dai ya karanci iya abin da ya karanta, shima dai ba wani bada himma akai ya yi ba, saboda da ya zo wajen yake karawa gaba ya ce shirmen banza, bugu da kari Musulci tasa ya kafawa su John doka masu kyau a gidan, ya kuma hana ɗaya ya zalunci ɗaya, sannan kuma ya bawa kowa yanci a cikin gidan, kuna tunanin ba dan musulci ba dan John ya kalli Blue film a gidan zai damu da shi ne? Kada ku mance yin hakan ba wani abin tsiya bane a wajen su.
Mu koma cikin story mu
Bayan ya zauna saman bed ɗin ne cike da murna Imran ya ce "Saif Michael ya musulunta ne?". A maimakon ya bawa Imran Amsa sai ya ce "Prof Ina buƙatar gida yanzu zan saya na koma can". Zaro ido Imran ya yi duk da cewa ya san dama Lion ba zai zauna a gidan su ba, amma bai yi tsammanin barin shi gidan da wuri haka ba, ya yi tunanin sai gobe, dama kuma dole ce ta sanya shi sauƙa a gidan su Imran ɗin, idan ba ku mance ba family William jacop basa zama a hotel sai in ya zamar masu dole, sannan kuma shi Lion tafiyar sirri ya yi baya son asan yana African ko His Excellency bai gayawa ga kasar da zai je ba, wannan dalilin yasa gwamnatin Nigeria bata yo mashi tarba ta musamman ba, da ba tafiyar siririn bace da tuni His Excellency wato kakan sa ya kira President na Nigeria ya sanya a tanada wa jikansa wajen sauƙa mai rai da lafiya, na musamman, amma tafiyar sirri ce dole ya yi komai nasa a sirrance, abubuwa biyu ne kuma yasa shi ya yi tafiyar sirri, na farko wayan da suka kama James a yanzu sun gano cewa ɗan uwansa ne, so idan suka san ya shigo neman James za'a iya samun matsala, abu na biyu kuma daddy, idan daddy yasan ga abin da yake faruwa na ya tafi neman James ne to zuciyarsa zata iya bugawa ya mutu, shiyasa ya ki gayawa su Tga ma ga in da zai je, Michael kawai ya gayawa, shima Michael ɗin massage ya yi mashi lokacin yana cikin jirgi.
"Saif please ka yi hakuri sai zuwa gobe sai mu samu gida mai kyau". Shiru ya yi bai sake magana ba, a hankali ya ɗago idanuwansa yana bin ɗakin Imran ɗin da kallo, duk daular dukiya da aka narka wa wannan ɗaki, amma Lion ji yake yi tamkar yana keji, ko gidan yari, gaba ɗaya a takure yake jinsa, Nigeria ga zafin bala'i, shi kuma baya shiri da zafi ko kaɗan, kusan gaba ɗaya Imran ya kure gudun Ac ɗakin, amma Lion ya ce za fi yake ji, tun karfe uku Imran ya je Airport ya ɗauko shi, daga karfe uku zuwa yanzu karfe 7:30 ya yi wanka ya kai sau 7 saboda zafi, su Imran suna saka kayan sanyi shi kuma yana kara yin wanka domin ya sami iska, sosai Imran yake tausaya mashi domin bai saba ba.
Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, cikin sauri Imran ya miƙe ya bi bayan sa, har sun kai bakin kofar fita, sai kuma ya juyo ya dawo ya ɗauki wayarsa tare da ɗaukar face mask nasa suka nufi waje.
A palo suka wuce Akila da Umaisha, ita kuwa Rimsha tana can kwance baiwar Allah,. Sai kallon shi Akila da Umaisha suke yi, sun saki baki, Akila sai kokarin son ganin fuskarsa take yi domin ta tantance wanene amma bata samu dama ba, dan kafin ta ɗago ta kalle shi ma ya wuce abinsa, dan ba tafiyar yara yake yi ba.
Imran ya zo fita palon ne ba tare da ya juyo ba ya ce da Akila ta yayyafawa Rimsha ruwa, to Akila ta ce mashi tare da miƙe wa suka nufi bedroom ɗin Rimshan da sauri, dan ita a tunaninta barci Rimsha take yi.
Su kuwa Lion kai tsaye waje ya nufa, dan har ga Allah ba zai iya zaman gidan su Imran ba, dole komai dare a sama mashi gida.
Jerawa suka yi da Imran suna fita wajen gate ɗin, suna fita wayarsa ta fara kara, dubawar da zai yi Michael ne yake kiran shi, bai ɗauka ba har kiran ta katse wata ta sake shigowa, ita ma sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka, har lokacin tafiya suke yi, shi Lion bai san ko'ina ba tafiya kawai yake yin, shi kuma Imran yana biye mashi suna ta tafiya saman titi abinsu har sun yi nisa da gida.
"My Lion fatan dai ka isa African lafiya?" Michael ne ya tambaya, shiru ya yi har na tsawon minti ɗaya kafin gently ya ce "Lafiya lou Alhadulillah fatan kana karatu sosai?" Michael zai yi magana kenan Lion ya ji an fusge wayar daga hannunsa, a tunaninsa ma Imran ne, sai da ya juyo sai ya ga ba Imran bane, yan kwancen waya ne, abin ma, mamaki ya ba shi, zubawa matashin da ya kwance wayar nasan idanu ya yi, yana kallonsa yadda yake ta tikar gudu, shima Imran bai wani damu ba, domin tun da ya ga Lion bai damu ba sai shima bai wani damu ba.
A ɓangaren Rimsha kuwa Lokacin da su Akila suka zuba mata, a firgice ta tashi, tana ƙokarin sauka daga gadon akila ta yi saurin riƙota tana faɗin "Rimsha lafiya? Me ya same ki? Ina zaki je?" Ina ai bata jin su kamar wadda ƙwaƙwalwarta ya taɓu baiwar Allah a zafafe ta diro kasa daga saman gadon da sauri ta yi waje, kai daga gani kasan bata a cikin hayyacinta, tana fitowa palo kai tsaye kofar waje ta nufa, daidai lokacin shi kumu Akil zai shigo, a kofar palon suka yi karo, bata wani damu dan ta bugeshi ba, ita dai burinta ta yi waje kawai.
Ganin su Akila sun fito da gudu suna kiran sunan tane yasa Akil ya yi damkota, dama kuma daga ganin yadda ta buge shi bai damu ba, yasan ba lafiya ba, kokarin kwace hannunta ta yi dan ta fice daga palon, ganin haka yasa ya riƙe ta da kyau yana faɗin "Rimsha kina lafiya kuwa?".
Jin abin da ya ce ne ya sa ta fashe da kuka, Allah sarki, ta razana sosai har abin ya kusa taɓa mata kwakwalwa, riƙota sosai Akil ya yi, ita ma sai ta sake mashi jikinta a jikinsa tana kuka, abin ya ɗaure masu kai sosai, bai wani damu ba, sai ya runmeta a jikinsa, dan ya lura ta birkice sosai ne, sai Allah kaɗai yasan me ye ta gani ya razana ta haka, ya faɗa a cikin zuciyarsa tare da duƙawa ya ɗauketa cak izuwa cikin palon, sosai abin ya sosawa Umaisha rai, tabbas tasan ita ma