Showing 264001 words to 267000 words out of 355604 words
wani lecture ma ya wuci tunanin ta, Akila bata ji kunyar idanunsu ba take rikita masu ɗan uwa, A'afia kuwa ji take yi daga yau ta daina ganin yaya Irfan da wani girma, saboda yadda ya zage yake zuba kamalan love tamkar ba shi ba, ga shi kuma wayar Akila a volume take, suna iya jiyo duk abin da yake faɗe, ita kam Rimsha ta ma rabu da su yanzu, tana can duniyar tunanin mafita akan yadda zata yi da case ɗin Ayla, abin ya shigeta sosai.
A ɓangaren su Abba kuwa, sai hira suke zubawa a palo suna tattaunawa akan waye zai ɗauki Rimsha, Abbi dai ya ce shi zai riƙeta, Aunty kam ko ajikinta, koma ƴaƴa dubu Abbi zai kawo tsab zata ruƙe su da amana tamkar kanneta, bata da wata matsala a rayuwa.
Cikin dabara Akil ya zame ya fice daga palon ya nufi waje.
Yana fita ya kira Umaishansa a waya akan ta zo cikin mota ta same shi, baafi minti 5 ba sai gata ta fito, cike da jin kunya ta wuce su Abbi zuwa waje, duk abin da suke yi a gidan Aunty na ganinsu tana jiran zuwa dare ne duk ta yi masu tsiya idan sun haɗu a dining table, da yake a nan za su kwana kamar yadda daddy'n jelly ya faɗa.
Tana shiga cikin motar ya jawota jikinsa tare da sauƙe ajiyar zuciya, ita ma rungume shi ta yi sosai tare da zura hannunta ɗaya cikin rigarsa ta kasa tana mashi wasa da cibiyarsa.
"Wife na sha kewa sosai fa yau, mun kai minti 30 fa yau ba tare da juna ba" ya yi maganar yana shafa kanta zuwa wuyarta da yake ba ta sanya hijabiba ta fito.
Murya kasa kasa ta ce "Yaya Akil Allah ina yawan tunanin idan muka koma Madina ka koma school ya ya zanyi da rayuwata, kaga a nan Naija baka da aikin komai sai dai mu wuni manne da juna, amma a Madina kuma zaka je school ina...." Bai bari ta kai karshen maganar ba ya ɗaura yatsansa a saman lips nata yana girgiza mata kai alamar baya ma son jin maganar.
Shiru ta yi tana sauƙe numfashin a hankali, cikin salo da dabara ya cusa hannunsa cikin rigarta ta fara wasa da abubuwan da ya fi so a jikinta wato breast, ga shi kuma ya yi babbar sa'a tana da halittarsu sosai, daidai da jikinta, dan gaskiya Umaisha dirarriya mace ce ajin farko, kamar ita ta yi wa kanta surar jikin nata, hakan yasa take kiɗima shi sosai, kuma idan ya damketa baya yi mata ta daɗi, kullun sai ta yi mashi kuka, har yanzu ta kasa sabawa, sai iya yi mashi wasa, nan kam ita ce akan gaba, amma da anzo asalin zance sai kuka.
A ɓangaren Lion kuwa, bayan ya gama abin da yake yi fita ya yi tare da sojan dake yi mashi girki, bai dawo ba sai bayan sallar la'asar.
Da ya dawo ɗakin James ya fara shiga ya miƙa mashi wata sabuwar waya kyakkyawar gaske mai tsada, akwai sim card na Nigeria da komai a cikin wayar, Michael na yawan damun shi akan ya haɗa shi da Areef ɗin ne yasa ya sai mashi waya dan ya huta.
Yana bashi wayar ya wuce bedroom nasa. Wanka ya fara yi ya shirya cikin pajama white color, ya yi kyau sosai sai dai kamar kullum fusataccen fuskar nan tasa a ɗaure sosai kamar hadari, ya saki wannan dark black curly hair nasa bai ɗaure ba, idanuwansa duk sun yi jawur da alama akwai wani abin a kasa.
Saman bed nasa ya haye, ya gaji sosai yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
Minti biyar da fara yin barcinsa ya fara mafarkin da ya saba na mum ɗin su, sai dai a wannan karon bata zo mashi da wayan na yi fararen kayan nata ba, ta zo mashi ne da jajayen kaya kalar jini, yau tana ruƙe da wata katuwar wuƙa mai kaifin gaske, haka zalika yau ba faɗa suke yi da ɗayar matar da suke zuwa mashi a tare ba, yau ita kaɗai ta zo mashi fuskar nan tata a ɗaure, idanunta sun yi jawur kamar jini.
Akan shi ta tsaya cikin tsawa ta fara tambayar shi akan menene yasa yake bincike akan G.M.A ya gaya mata ko ta kashe shi, kamar dai kullun yau ma dai kallon sama da kasa ya yi mata sau ɗaya tare da kawar da kansa gefe tamkar bai ganta ba, a fusace ta ɗaga wuƙar zata burma mashi a ciki, da hannu ɗaya ya ruƙe wukar tare da zaro mata idanunsa, ba ƙaramin tsorata da ganin idanunsa ta yi ba, hakan yasa da sauri ta janye wuƙar daga hannunsa, janye wukar da ta yi kuma yasa wukar ta yanke shi a hannu, nan take jikinsa ta fara zuba, ɗan ciza laɓɓansa na kasa ya yi, idanun nan nasa sun yi jawur da su, rai ka matuƙar ɓace ya nufeta gadan gadan, a zafafe ta juya zata gudu, yana ƙoƙarin damkar wuyarta kirar wayarsa take saman bedside drawer ta farkar da shi daga barcin da yake yi.
A hankali ya waro idanunsa masu ɗauke da barci, ji ya yi gaba ɗaya jikinsa na yi mashi ciwo, tunani ya fara yi akan tabbas zargin da yake yi akan Mummynsu ya fara tabbata, tabbas tana da alaƙa da G.M.A domin dama yana yawan mafarkinta akan abubuwan tsafi, hakan yasa ya fara zarginta, to yanzu kuma daya bincika ya gano cewa James na ɗaya daga cikin members na ƙungiyar wannan dalili yasa kara faɗaɗa zarginsa akan ta, domin James bai san taya ya akayi ya shiga wannan kungiya ba, dole dai da wani makusancinsa aka haɗa baki aka shigar da shi ta hanyar bashi wani abin ya ci, tabbas james ya je wajen Josephine sosai abaya, har cikin gidan ta ya sha zuwa sau ba adadi, hakan yasa Lion ya fi zargin ita ce ta ba shi abin sha wadda ta sanya wa wannan kambun na tsafinsu.
Masu son sanin menene G.M.A wata kungiya ce ta shan jini ta matsafa dake a cikin New York City wato dai can kasarsu, Areef ya tsinci kansa a cikin wannan ƙungiya ba tare da ya san ta ya ya akayi ya faɗa ba, tun bai musulunta ba yake a cikin kungiyar, bayan ya musulunta ya yi ƙoƙarin fita amma ba hali domin akwai abin da suka sanya mashi a jikinsa, babbar matsalar kungiyar duk yadda kuka kai ga sabo da mutun kana iya shanye mashi jini, Areef yana jin kwaɗayi tare da sha'awar jini aduk lokacin da dodan tsafin nasu ya juyo ta kansa, da yake dai Allah yana son shi da rahma duk lokacin da hakan ta fara faruwa mashi yana iya ka bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ya karanta duk adduar da ta zo bakinsa, idan ya sami dama ya yi hakan kuma to fa yana iya kaucewa wannan kuduri na dodan tsafin nasu na son ganin lallai sai sun sanya shi shan jini, babbar abin burgewa da kuma jin daɗi shine, duk wani ɗan ƙungiyar dolene ya rinƙa kasancewa kusa da ƙungiyar amma banda Areef, shi bai taɓa zuwa ba, hasalima bai san a ina ƙungiyar take ba, kuma babu abin da suke iya yi mashi, saboda karfin musulunci, kawai dai sometimes suna samun dama su ɗan yi control nasa, amma bayan haka ba wani abin da suka isa su yi mashi, sun yi sun yi sun kasa saka shi shan jini, haka zalika da suka yi ƙoƙarin shan jininsa su kashe shi ma sun kasa, ya zama tamkar kaddararsu, yanzu so suke yi ma su cire shi daga cikin kungiyar, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, sai suka kasa cire shi daga ƙungiyar har Lion ya farga ya fara bincike akan su, yanzu babban abin dake a gaban Lion shine ya gano abin da suka sanyawa Areef ɗin suke sanya shi ya rinƙa jin sha'awar shan jini time to time, yanzu kwata-kwata Lion ya ajiye zancen CIA a gefe ya gano babban case da ya kamata ya fara dakatarwa tukunnan, idan ya gano in da suka sanya wa Areef sha'awar shan jini ya lalata wajen sai ya binci a ina ma kungiyar take gaba ɗaya ya sanya sojojin su yi masu diran mikiya su tarwatsa shegu, abin da yake ta fama kenan yanzu, bawan Allah idan ka ganshi ba zaka taɓa cewa yana cikin damuwa ba, dan kullun a haka yake, fuska a ɗaure, amma Allah ne kaɗai yasan raɗaɗin dake acikin zuciyarsa, dan ma dai daɗin abin ɗaya shine Areef bai taɓa shan jini ba, Allah na tsare shi, a takaice dai G.M.A sun ɗauko kaddararsu kuma sanadiyar tarwatsewansu baki ɗaya a doron duniya wato Areef kenan, dan idan Lion ya gano su ba zai yi masu ta daɗi ba!.
STORY
Ya ɗan jima kwance idanunsa biyu yana haɗa maganganun mummyn nasu dana daddynsu, zancen daddy ya tabbata gaskiya, kenan mummy matsafiya ce, tana ƙungiyar matsafa, sannan kuma da gaske ne kenan ta ba da su ayi mata kuɗi da su da suna yara? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, har ga Allah har cikin zuciyarsa baya jin zai iya kashe Mahaifiyarsu da hannunsa, duk da baya son ta saboda abin da ta yi masu, amma tabbas ba zai iya kasheta da hannunsa ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kuma irinsu kamata ya yi a kashe su domin basu da wata amfani a duniya, idan ban da kashe rayuka da lalata al'umma ba wani abin da suke aikatawa.
Da kyar ya miƙe zaune a tsakiyar gadon, wannan wace iriyar bala'i ce, wace iriyar jarabawa ce, uwar da ta haifesu, gaskiya abin akwai ciwo sosai, sai mutun ya kai zuciya nesa idan ba haka ba zai iya mutuwa da bakin ciki, zuciyarsa zata iya bugawa.
A ɓangaren shi kuma Areef yana karɓar wayan bawan Allah Michael ya fara kira dan yana da numbersa akan sa, bawan Allah mai zuciyar zinari, an cutar da rayuwarsa sosai ba tare da ya sani ba, kawai dai yana ji wata sain kamar ana control na jikinsa ne, yana jin kamar ana amfani da shi, haka zai daure ya yi ta addu'a har sai abin ya sake shi.
Bugu ɗaya ya yi wa Aseef, Aseef ɗin ya yanke kiran ya kirashi domin ya ga number bata kasar su bace so ya yi tunanin dama Lion ne ko kuma dai shi Areef ɗin, shiyasa ya katse kiran shi ya kira, dan idan ya yi picking call ɗin Areef ɗin ba za su samu jituwa ba ta hanyar network, network zata rinƙa yi masu gargada tana yanke masu magana, shiyasa mafi yawancin lokaci shine mai kiran Lion ba Lion ke kiransa ba, dan su sami network mai kyau su yi magana yadda ya kamata.
Yana ɗauka ya ce "Assalamu alaikum My Tiger" daga can ɓangaren yana kwance daga saman bed nasa wani cool murmushi ya saki tare da gyara kwanciyarsa yana faɗin "Blood ka sayi waya kenan?" E Areef ya amsa mashi da shi.
"Wow dama na yi tunanin kai ne that is why na yanke kiran" shima Areef ɗin fuska ɗauke da murmushi ya ce "Where is dad? I want to talk with him".
Miƙewa daga kwanciyar da yake ya yi ya diro kasa daga saman katafaren bed ɗin nasa, daga shi sai shot da singlet, yanzu ya kara natsuwa sosai, ainahin haiba da kalama ga kwarjini da farinjini na jininsu na kara bayyana a tattare da shi, ya dawo sak Triplets nasa, jini ba bawa ba sai rikiɗewa yake yi yana komawa kamannin Lion, dama sun fi kusa, duk da yanzu yake gym sosai, amma yanayin kirar jikinsa dukka iri ɗaya ne, duk suna da kirar jarumai, sai dai jikin Lion da Areef ya fi nasa murɗewa, saboda sun jima suna gym, shi kuma sai yanzu ya mai da hankali yana yi, shima abaya yana yi amma sai randa ya ga dama yake shiga ya ɗaga karfe ɗaya biyu ya ajiye ya fita, amma yanzu kamar yadda kowa yake dagewa ya yi haka shima yake yi, kuma mafi yawancin lokuta a tare da Musharraf suke yi, domin shima Musharraf yanzu ya saba da ukubar da Tga yake bashi.
Yana fita kai tsaye ɗakin daddy ya nufa, kwance ya isko shi yana kallon news a makeken Tv dake manne a jikin bangon ɗakin, miƙa mashi wayar ya yi tare da nufar waje yana faɗin "Daddy it's James" tsabar farinciki daddy jikinsa har kerma take yi wajen sanya wayar a kunnensa, suka fara magana.
Shi kuma Aseef yana fita Palon kasa ya nufa, can ya hango Musharraf a cikin kitchen, da fara'a ɗauke akan face nasa ya karisa cikin Kitchen ɗin yana faɗin "Uncle what are you cooking for us?" Shima Musharraf murmushi ne ta bayyana akan face nasa kafin ya ce "Am cooking Nigeria food, rice and beans with steew, ba shine abin da na saya jiya a kasuwa da muka je ba" jawo kujera Aseef ya yi ya zauna yana faɗin "Okey yau zan ci African food kenan" yana magana ya murmushi.
"Ai da wuya ka iya cin irin abincin mu, kai da damu ka je kasuwar ma ko fita a mota ka kasa yi saboda karnin nama da su ganyen miya da sauransu, ina ga kuma na dafa, na san ba zaka iya ci ba".
Miƙewa ya yi ya karisa wajen Musharraf ɗin tare da sanya hannu ya fara taya shi wanke Tomatoes da yake yi.
Abin da bai taɓa kwatanta makamancin shi ba a rayuwarsa, ko Kitchen ɗin gidan baya shiga, bai iya komai ba sai dai jibga-jibgan sojojin nan su dafa su kai palo su jere a saman table, bodyguard kuma su yi serving nasu suci, amma yau saboda Musharraf shine a cikin kitchen har da sanya hannu yana wanke Tomatoes, sojojin dake a cikin Kitchen ɗin ba ƙaramin mamaki suka sha ba, abin ya girgiza su, har sanya hannu suka yi a idanunsu suna murjesu dan su tabbatar da gaske ne abin da suke gani, ko sau ɗaya ba su taɓa ganin ɗaya daga cikin ɗan gidan a kitchen ba bayan Areef, Areef shi kaɗai ya taɓa shiga kitchen, a takaice ma ko serving abinci da kansu ba su iya shi ba, sai dai ci kawai.
Ganin sojijin sun saki baki suna kallon shi ne yasa ya ɗan watsa masu ragowar ruwan wanke Tomatoes ɗin dake a hannunsa yana faɗin "Me kuke yi mani irin wannan kallo haka?" Cikin sauri suka yi kasa da kansu suna faɗin Sorry sir.
Kayatatcen murmushi ya saki tare da matsowa kusa da su yana faɗin "Ku kalle ni iya son ranku ni ba Lion bane bare ku ce bana son kallo, kuma ku yi mamakin ku a bayyane ba a cikin zuciya ba, Allah kenan mai yin yadda ya so da bawansa, ni yanzu ma kunga African food zan koma ci, amma kada ku gayama daddy!". Kallon juna suka fara yi suna masu maimaita kalmar sunan Allah da ya kira, abin ya ɗaure masu kai to wani Allah kenan Michael yake nufi? Nasu na church ko wanne, ma'ana Jesus kenan.
Kyasta masu yatsunsa ya yi a saman face nasu yana faɗin "Daga yau mun zama friends ku ɗauka a haka kuma, da mai kuɗi da talaka dukka Allah ne ya yi su, kuma babu wanda ya fi wani agaban Allah sai wanda ya fi ka jin tsoron sa ya kuma fika yin bautarsa, dan haka kuma ya kamata ku san da hakan, kuma duk yadda kuka ga na zama yanzu ku sani Allah ne ya hukunta hakan, na gane cewa da talaka da mai kuɗi duk ɗaya ne ta sanadiyar addin musulci addini mai niima kuma ina maku fatan shigarta dan ku samu rahmar Ubangiji" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya koma gaban manya-manyan gases dake a cikin kitchen ɗin.
Jugum jugum suka tsaya, sun rasa me za su yi, biyu daga cikinsu tabbas sun gamsu da zancen Aseef domin sun san abin da zai canza familyn William jacop daga izza da isa da taka mutane su koma sauƙin kai har su iya shiga kitchen gaskiya ba karamin abu bane, kuma lallai yana da kyau aduba wannan abin saboda ba abin wasa bane, hakan yasa biyu daga cikin huɗun masu nazari da tunani suka fahimci e tabbas wannan Addinin Musulunci koma ya yake akwai matukar gaskiya da kuma tausayi a cikin sa, ga shi dai yadda yau Aseef ya shigo Kitchen har da yi masu dariya, abin da ko hakwaransa ba su taɓa gani ba, abaya kullun face nasa a ɗaure kamar hadari, kwata-kwata basu ishe shi kallo ba, biyu daga cikin su kuma shiru suka yi suna nazari akan kalaman da ya yi masu.
"Sir please zan iya magana?" Ɗaya daga cikin su ne ya yi magana, har wani zaro idanu waje sauran suka yi, domin sun san a baya basu isa su yi wa ɗaya daga cikin TRIPLETS magana ba.
Yana neman ta ina ake kunna gas ɗin dan ya kunnawa Musharraf ya amsa da "Yes kana da damar yin maganar ka, ai yanzu na gama gaya maku dani da ku duk ɗaya ne a wajen Allah, so kawai yi maganar ka kai tsaye".
Dukkansu sun sha jinin jikinsu yayin da shi kuma ya rasa ma ta ina zai kunna gas ɗin dan bai iya ba, sai faman dube dube yake yi.
"Sir gaskiya na ji ina son wannan addinin musuluncin da ka faɗa, dan naga yana da kyau" a tare suka juya shida Musharraf.
Musharraf na ƙoƙarin nufar sojan Aseef ya dakatar da yana faɗin "Wait uncle, bari na tambaye shi, kana son addinin musulunci ne saboda ina cikinsa ko kuma dai har ga Allah ya shiga ranka?".
Kasa ya ɗan yi da kansa kafin ya ce cikin girmamawa "Sir saboda kana cikine yasa nima naji ina son addinin sosai". Juyawa ya yi ya cigaba da abin da yake yi yana girgiza kai ya ce "No Robertson bamason musulci ka har sai idan saboda Allah zaka yi shi, kada ka ji sha'awar addinin musulunci saboda wani, kada ka shigeta saboda wani, komai zaka yi a rayuwa ka yi shine dan Allah, domin saboda idan ka shiga wata matsalar Allah ya fitar da kai, kaga duk abin da muke da shi aduniyar nan,