Showing 207001 words to 210000 words out of 355604 words
ne akan fuskokinsu.
Da gudu Ayla ta miƙe zata gudu wajen Abbi, da sauri daddyn Jelly ya riƙota yana faɗin "Au sai kika yarda da yaya Deen, za ki bar mijinki ki gudu wajen shi? Kina ji fa cewa ya yi kada na sake zuwa wajen ki, zaki yarda da hakan? Zaki yarda daddyn ki ya yi maki nisa?" Kallon Abbi ta yi sannan ta dawo da kallonta kan shi, gera ɗaya ya ɗaga mata alamar yana jiran amsa.
Kasa-kasa ta ce "A'a ka yi hakuri ni nafi son zama da kai". Tafi Aunty ta sa tana rangaɗa guɗa, shi kuma Abbi cewa ya yi "Eyeee to ba ku isa ba, dole ku zo ku shiga da ga ciki, ni za ku yi wa tsiya, Maik Aliya lallai kun riƙa, ke wato kin fi yarda ki zauna da shi, to wlh Jumma'a mai zuwa ina ɗaura maku aure sai ki bishi ku je ku zauna a part nasu, amma ni ba za ku min iya shege a nan ba".
Sai dariya suke gaba ɗayan su, ita kuma Ayla ta sunnar da kai kasa tana jin wani irin farinciki mai ratsa jiki a tattare da ita, sosai dukkansu suka ji daɗi, domin burinsu dama ta samu farinciki da natsuwa, ta rinƙa mance damuwar da take a ciki, wannan dalilin yasa ma dukkansu suke yawan wasa da ita, shima Abbi ya san tarihinta domin daddyn Jelly ya gaya mashi komai, Aunty kuma da suka shiga ɗaki yanzu ta gaya mashi cewa daddyn Jelly na son ta, ba karamin farinciki ya ji ba, domin ya san zata samu kulawa sosai wajen shi.
Kasa kasa ya ce "Babyna kunya ta kike ji ne?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e, zai sake yin magana aunty ta riga shi da cewa
"Yaya Maik yanzu dai na dawo bayan Ayla, ka sakar mana hannu atom".
"Wai ke Sadiya duk wannan hali da nake a ciki ba ke kika jefa ni ba? Ina zaman zamana kika sani yin soyayya ba shiri, to kuma yanzu sai dai ki zuba ido, wai ma hannunki na riƙe ne ko hannun matata?" Ya tambaya yana zaro mata idon nan nasa cikin wasa.
Cikin sauri Abbi ya tari numfashin su da cewa "Dakata ai hannun matata ya fi karfin ka riƙe matso nan Halima ta" dariya suka yi, ta faɗa jikinsa tana faɗin "To ni dai mijina ko ina zan bugi kirji in ce nawa ne, kai kuma taka har yanzu for sale ce" wani irin kallo ya wurgo mata da dara-daran idanun nan nasa kamar ball, yana ƙoƙarin yin magana kenan Abbi ya riga shi da cewa "Mai da wukar, Aliya taka ce kai kaɗai ba for sale ba ce, ni dai na baka ita amana, ka kula mani da ita sosai, idan kuma ka shirya ranar Friday sai a ɗaura auren a wuce wajen, idan ya so daga baya za'a yi su walima da sauransu, tun da tana son ka, ta faɗawa Auntyn ta da bakinta tana son ka ni ban ga wani abin ɓata lokaci ba".
Sakin hannayen nata ya yi yana faɗin "Ai gaskiya yaya Deen matar nan taka yar sa ido ce, ni ko na yi auren ma ba zan zauna a nan ba, zata saka mani ido sosai, kuma gaskiya ina son abar mani baby na tayi karatu" ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita daga palon.
"Kai dawo nan, yanzu Halimar kake cewa yar sa ido a gaba na? To baka isa ba, dawo maza ka kwashi albarka ko ka yi Sa'a auren naka ya yi albarka ku haifo mana wani Hosain ɗin tun da wancan ya guje mu" Jin sunan Hosain yasa ya juyo yana faɗin.
"Yaya Deen in dai albarka Sadiya mai sa ido ne bana so, kuma ta dai'na sakawa matata ido, sannan Hosain fa ya tura mani later kafin wayan nan abubuwa su faru, shine ashe ya samawa company na wannan contract ɗin a lokacin, ko yana ina bawan Allah nan oho, ni bani wayarka ma bari na kira Imam in ji ya ake ciki"
Miƙa mashi wayar Abbi ya yi yana faɗin "Ai Hosain zuciyar bala'i ke gare shi, kyale shi idan suka gama guje gujen nasu za su dawo ne ma, muna nan muna jiran su, kuma duk halin da muke ciki yana sane, abin yana bani mamaki, kaga hakan ya nuna cewa yana kusa da mu kenan"
Karɓar wayar daddyn Jelly ya yi yana faɗin "Haka ne yaya Deen, shikenan ai tun da yana cikin ƙoshin lafiya ba wata matsala, amma dai ni ɗin ne kasan ba zan iya jure rashin shi ba, domin tsakani na da shi yafi kusa akan tsakanin shi ɗaku".
"Haka ne Maik to yanzu ya batun auren dai" Jin haka yasa Ayla ta wuce sama da sauri abinta. Bin ta da kallo daddyn Jelly ya yi har sai da ta kurewa ganin sa, sannan ya ce "Yaya Deen ka kunya ta mani mata fa, ni ina son a barta ta yi karatunta, amma dai za mu yi magana idan muka haɗu a masallaci sallar mangariba" ya kai karshen maganar tare da ficewa da sauri.
"Gaskiya Halima na ji daɗi da Maik zai yi aure, koba komai zai saku natsuwa, kwata-kwata fa shakarunsa ba za su wuci 38 years ba, amma ya azabtar da kansa da zama ba mata" "38 years kuma Abbi?! Kai ya naji shekarun nasa kaɗan?" Yar dariya Abbi ya yi yana faɗin "Wlh 38 years ya ke da shi zuwa 39 haka".
"To ita kuma Jelly shekarunta nawa?" Aunty ta kara jefa mashi tambaya tana mamaki "Ina jin 16 years take da shi, kin san Maik tun yana ɗan shekara 20 ya yi aure saboda bala'in Hadiza, hakan yasa ma bayan ya yi auren ya tattara ya koma Kano da zama, dan ya ɗan hutawa fitinarta, da aurensa bai fi shekara ɗaya zuwa biyu ba suka Haifi Jalila, ranar kuma da mahaifiyarta ta haifeta a ranar Allah ya karɓi rayuwar uwar, daga lokacin Maik ya mai da hankalinsa ga kasuwancinsa, yana kula da Jalila sosai da sosai, ba yadda ba mu yi da shi ba akan ya yi aure amma ya ki, na so ɗaukar Jalila na riƙe mashi ita, nan ma yaki yarda, yan uwan mamata sun zo ɗaukarta daga Katsina suma yaki basu, akwai wasu yan uwan maman nata a Kano, suma sun jarraba ɗaukarta amma yaki yarda, haka ya shawala ya reni kayarsa, daga karshe kuma Allah ya raba su, Maik bai taɓa rabuwa da Jalila ko daidai da na rana ɗaya ba, sai wannan ɓatar da ta yi kinga kuwa dole ya shiga tashin hankali".
Sosai Aunty ta tausaya mashi ta kuma kudiri niyar sai ta sanya shi agaba har sai ya yarda anyi auren nan da wuri, zata rinƙa gyara mashi Aylarsa sosai har sai ya kasa hakura ya ce a ɗaura kawai. (Kai Aunty kema ba baya ba🤔🤣 wai sai ya kasa hakura ya hmmm 🤣)
Wucewa Abbi ya yi ya nufi kofar fita, yana yi mata sallama, cike da so da kauna, yau ansha love komai ya wuce kamar ba'ayi ba.
Yana tafiya ta zauna saman sofa tana godiya ga Allah da sauƙaƙa mata komai, abubuwa suka zo mata cikin sauƙi.
Zaman minti 10 ta yi a wajen sai ga Hajiya Hadizatu ta faɗo mata cikin palo babu ko sallama, bata bi ta kan ta ba kawai ta haye sama abinta, binta da ido kawai Aunty ta yi tana mamakin jahilci irin nata.
Ɗaki ɗaya daga cikin ɗaku nan dake a sama ta shige ta kwanta a saman bed wai ta dawo gidan mijinta. (To fah akwai rigima kenan, Hajiya Hadizatu manya, mu dai bari mu matsa gaba ato)
A ɓangaren daddyn Jelly kuwa yana fita part nasu ya wuce, a palo ya tsaya ya kira Engr Muhammad Imam da wayar Abbi, a nan ya samu sakon da ya birki ta mashi ƙwaƙwalwa, wannan sakon kuma ba wani saƙo bane fa ce baban Muneer ya tura wa Engr Muhammad Imam wannan Video na daddyn Jelly, ya kuma ce ya bawa daddyn Jelly nan da sati uku idan bai bayyana ya kawo Jelly an ɗaura masu aure da Muneer ba, to kamar yadda ya turawa Engr Muhammad Imam wannan video haka zai turawa duniya baki ɗaya. Babbar magana.
Har wani jiri daddyn Jelly ya fara gani bawan Allah, zama ya yi a saman sofar su yana hawaye, yana dana sanin wannan rayuwa tasa, sosai Engr Muhammad Imam ya rinƙa bashi hakuri tare da gaya mashi shi ya goge video ma daga wayarsa, kuma yasan shiri aka yi mashi, yasan halinsa mutumin kirki ne shi, yasan na zai iya aikata hakan ba.
Godiya ya yi wa Engr sannan suka yi sallama ya kashe wayar ya zauna yana tunanin mafita, haka kawai zuciyarsa ke gaya mashi ya gayawa yan uwansa halin da yake a ciki, ko da akwai wani abin da za su iya taimaka Mashi da shi, shiru ya yi yana tunanin waye ya kamata ya gayamawa, haka kawai ya tsinci kansa da yanke wa kansa hukuncin ya gayawa Imran, domin Imran shine yasan komai nasa, yafi yarda da shi sama da kowa, kuma yasan Imran ya san halinsa dan haka zai masa kyakkyawar fahimta.
Ba tare da dogon tunani ba ya kira layin Imran ɗin, bugu ɗaya ya ɗauka a lokacin yana tare da Lion, shi yana kwance saman gadon, shi kuma Lion yana zaune a bakin gado yana latsawa, dan aiki yake yi sosai akan case ɗin James da batun zuwan su Tga.
Ba tare da ɓata lokaci ba daddyn Jelly ya sanar da Imran duk abin da yake faruwa, tashin hankali iya tashin hankali Imran ya shiga, har wani miƙewa zubur ya yi zaune a tsakiyar gadon, nan take zufa ta fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa, a ruɗe ya furta "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun wannan wace iriyar bala'i ce" ko kallon in da yake Lion bai yi ba, kamar ba shi a ɗakin.
Sosai ya rinƙa bawa daddy hakuri yana bashi baki.
Bayan sun gama wayar ya zauna shiru ga zufa sai kara tsastsafo mashi yake, fuskarsa ta yi sharkaf, gaba ɗaya jikinsa ya yi la'asar, dama akan wannan dalili Jellyn sa ta bar gida? Ya ilahi ya lillihi, nan take ya fara ganin jiri, ɗakin na juya mashi, haka idanuwansa ma suka fata juya mashi kamar fanka, dafe kansa dake matsanancin sara mashi kamar zai fashe ya yi yana ambato sunan Allah.
Ba tare da ya ɗago ya kalle shi ba ya kyasta mashi wayan nan fareren dogayen kyawawan yatsu nasa a fuska, gently ya ce "Prof be a man mana, why ka ke yin abu like Asif? Even Asif ba zai yi hakan ba? Tell your uncle da ya turo mani da number guy ɗin, zan duba case ɗin because of you".
Saboda farin ciki Imran bai san time da ya kurma ihu ba, kallo ɗaya Lion ya mashi ya haɗiye ihun yana faɗin "Wow thank you so much, i really appreciate, i really like this my uncle, yana da...."
Bai kai karshen maganar ba Lion ya ɗaga mashi hannu alamar ya ishe shi haka nan, baya son surutu.
Bai wani damu ba tun da Lion ya shiga case ɗin ya san 2 hours ya yi yawa za su damko baban Muneer kuma ya sha bugun maza, domin duk abin da daddyn Jelly ya faɗa Lion yana jin su, hakan yasa ya ce zai shiga case ɗin, domin daga maganar mutun yake gane mai gaskiya da kuma mai karya a cikin su, yana aiki da ƙwaƙwalwarsa sosai, da ƙwaƙwalwa yake tace abu, so ya gane daddy jelly yana da gaskiya daga cikin maganar tasu.
Sai zumuɗi Imran yake, ya kira daddyn Jelly ya ce ya tura mashi number baban Muneer, kin tura mashi daddyn Jelly ya yi dan yana tsoron kada Imran ɗin ya kira shi ya ce zai zage shi ko wani abin, shi kuma ya ji haushi ya saki Video wa duniya, hakan yasa ya ce shi ba shi da number a kansa, bai san cewa mai gayya mai aiki ne na shiga case ɗin ba.
Daga jin maganar daddyn Jelly na bai da number a kansa Lion ya san karya yake yi, abin kuma ba karamin haushi ya bashi ba, dan bai son mutun makaryaci, dan haka sai ya ce da Imran ya kyale shi ba zai yi aikin ba, Imran kamar zai yi kuka ya ce kada ya damu zai samo mashi number a hankali, shiru ya yi bai sake magana ba, daga haka Imran yasan cewa e fa ba zai shiga case ɗin bane, domin baya magana biyu.
Tsabar takaici har sai da idanuwan Imran suka cika da hawaye, ko ajikin Lion sai ma miƙewa da ya yi ya shiga toilet dan yin wanka.
Yana shiga toilet Imran ya fara zubar da hawaye, kafin Lion ya fito ya sha kukansa dan bakin ciki.
Shiryawa ya yi cikin wata kyakkyawar tsadaddiyar jallabiya fara tas, ya feshe jikinsa da wannan fitinanniyar perfume ɗin nasa, sannan ya gyara dark black curly hair sa tare da sanya black face mask a face nasa, ya dauki wayarsa ya nufi waje yana faɗin "Remain 20mins ayi sallar mangariba ka same ni a masallaci" daga nan ya fice abinsa.
Da kyar Imran ya iya miƙa wa ya fito ya nufi nasa ɗakin, wanka ya yi ya shirya shima cikin jallabiya fara, sauri-sauri ya fito dan har an fara tada hiƙama da yake akwai masallaci a unguwar tasu, suna ji ta lasfiƙa.
Duk wanda Lion ya wuce shi sai ya juya ya kallesa dan ya ga waye mai wannan kamshin turaren, perfume ɗin tana da karfi ne sosai.
Bayan sun yi sallar mangariba da isha ne suka fito zuwa gida, yau Imran kamar wadda ruwa ta cinye shi haka ya zama, so silent, shi kuwa Lion ko a jikinsa, dan dama shi zaman shiru ita ya fi kware wa, bai iya magana ba, baya ma zama a in da ake surutu.
Suna tafiya kamar gumaka, daidai za su shiga kwanar da zai sada su da gida, dan da kafa suka fito, Lion ya sa an kawo mashi mota kirar *Bugatti cantodieci* daga gidan gwamnar Kaduna, sanna ya sai wata sai dai ita bata iso bane, amma idan zai je masallaci da kafa yake tafiya dan saboda samun lada, kuma masallacin ba nisa, ya san cewa idan mutum ya je masallaci da ƙafarsa, iya adadin kurar da ta hau kafarsa iya ladar da zai sa mu, kuma sunnar annabi ne ma zuwa masallaci da kafa, hakan yasa kawai ya zaɓi zuwa da ƙafarsa ya bar motar.
A daidai wannan kwanar wasu yan jagaliya suka tare su, irin matasan nan ne masu shaye-shaye yan kwacen waya, da yake darene sai Allah yasa suka tare gamonsu.
Duka duka tsawon dogon cikinsu ma bai wuci a kirjin Lion ya tsaya ba, shi ma Imran ɗin da kaɗan ya haura kirjin Lion ɗin da tsawo, wasu yan guntaye a gabansu amma a haka suka zaro wasu ruɓaɓɓun wuƙaken su suna cewa su Lion su kawo wayoyin hannunsu da kuɗi.
(Kwacen waya ko ina, Kasata!! Kasata!!😭😭 Allah ka kawo mana sauƙi)
Hannu Lion yasa ya buɗa su daga kan hanyarsa zai wuce, ma'ana yasa hannu ya matsar da su daga kan hanyarsa, dan ya san idan ya ce zai dake su to wlh duka ɗaya zai yi masu ba za su sake moruwa ba, wasu ruɓaɓu da su, shi kuma yau bai fito da niyar dukan kowa ba, hakan yasa ya buɗa su zai wuce.
Da gaske wannan yaron babba mai ɗan tsawon cikin nasu ya yi yunkurin caka wa Lion wukar hannunsa a ciki
Wani wawan damka Lion ya yi wa hannun yaron tare da murɗeta baya, ji kake kass kashin ta ɓalle, tuni yaron ya saki wukar ta faɗi kasa yana kurma ihun azaba, da hannu ɗaya Lion ya yi wurgi da shi kefe guda, a guje sauran suka juya za su gudu, a zafafe Lion ya damko biyu daga cikinsu ya haɗe kansu ya buga da karfi suka yi gwarel, sai ga jinin ya fara malala daga goshin su. Yunkurin yin ihu suka yi, ya toshe masu baki tare da yin wurgi da su gefe, nan suka sume a wajen
Da farko bai yi niyar dukansu ba, amma da ya ga da gaske suna iya cakawa mutun wuka a kan yar waya shiyasa ya musu duka ɗaya ba tashi, kwata-kwata bai ɗauka haka abin yake ba, bai ɗauka za su iya kashe rai akan yar waya ba.
Biyun da suka gudu ma, taku biyu ya yi ya damkosu, dukkan su duka ɗaiɗai ya musu suka sume a wajen, ganin jama'a sun fara taruwa a wajen ne saboda ihun da yaro na farko ya yi, dan ma dai sauran ya toshe masu baki, hakan yasa suka wuce cikin gida, shi kam Imran ko ajikinsa, domin hukuncin da ya fi haka ma yasha ganin Lion yana yi.
Suna shiga cikin gida Lion ya bawa wannan soja mai gadi umarni akan ya tattaro mashi sumammun masu kwacen wayar ya kawo su cikin gida, dole ya koya masu hankali da har za su iya kashe rai akan waya, dole su fiskanci hukunci.
Da haka ya wuce izuwa cikin gida, kai tsaye ɗakin Lion ɗin suka wuce, yana shiga ya cire jallabiyar jikinsa, ya rage daga shi sai Short da singlet farare tas kamar yanzu ya cirosu daga ledarsu.
Saman gado ya hau ya kwanta yana tunanin yadda zai je ga James gobe.
Shi kuma Imran saman bedside drawer ya zauna yana tunanin daddy'n jelly.
Ni kuma na haɗa kayana zuwa wajen bandits😭
😭💔BANDITS😭💔
Su Aafia suna nan a wajen cike da tashin hankali da damuwa, sun yi kuka har sun gaji, daga ƙarshe suka hakura suka fawwalawa Allah komai.
Ɗaya daga cikin bandits ɗin ne ya zo ya damko wuyar hijabin jikin Hanan ya miƙar da ita da nufin ya tafi da ita, da sauri mamanta ta tashi ta riƙotana tana kuka da hawayenta tana faɗin "Ina za ku kai min ita? Na shiga uku na, dan girman Allah ku yi hakuri, ku rufa mani asiri, ku tausaya mani, ku kyale mani ita".
Kafa ɗan bandit ɗin nan yasa babu tausayi bare imani ya dake maman Hanan ɗin ta faɗi kasa tana kuka, ƙoƙarin kwacewa ita ma Hanan ɗin ta yi dan ta