Showing 225001 words to 228000 words out of 355604 words
ta yi na zaɓi ɗakin da nake son zama, gaskiya ina kaunar ta sosai sahibina, dole kuma na kula da ita" ta kai karshen maganar tana jan mashi dogon hancinsan nan.
Yau Aunty taga karuwanci da tsakar rana ido da ido, Allah sarki Abbi Hajiya Hadiza bata bari ya yi wani yunkuri ba, ta yi saurin saye bakin nasa da salon kirsan ta, ya sami wasu abubuwa da Aunty ke jin kunya bata yi mashi, irin wasa da sauransu, har wani jan hancinsa hanjiya Hadiza ke yi, tana wani langwaɓar mashi da kai kamar yarinya, nan take ta rikita bawan Allah nan.
Har yana haɗe words wajen ce mata "Khadija yaushe kika dawo?" Jin haka ya yi mata magana a nutse ba da faɗa ba yasa ta kara narkewa da kashe murya (kamar tsohuwar kwartuwa) tana zuba mashi kirsa da makirci, Aunty dai yau taga tsantsan bariki data ci uban na Rufee, har wani shafa mashi wuya Hajiya Hadiza take yi, da yake ta yi wa kayanta farin sani, ita kuma Aunty kunga bakuwa ce, ba komai ta sani ba, Hajiya Hadiza ta san lagonsa fes, tasan ta yadda zata bi da shi ta zautar da shi.
Da Aunty taga ana ƙoƙarin runguma a gabanta sai ta sa kuka ta juya ta koma ɗakinta. Ɗan waigawa ya yi ya kalleta yana faɗin "Me ya faru Halima?" Ya zauce da kirsan Ommu har baya son yin magana sosai.
(Mata bala'in ne wata zubin, kai kuji makirar mace tab🤔🥺)
Cike da kirsa da makirci ta ce "Sahibi ka je ka rarrasa mani kanwata ta yi shiru, tana da kirki bana son ta ɓata rai" tana magana tana rungume shi, shiru ya ɗan yi, shi kaɗai yasan me yake ji.
"Hadiza wai yaushe kika dawo ne?" Shine abin da ya iya faɗa, kara shigewa jikinsa ta yi tana shagwaɓe fuska tare da turo baki kamar yarinya ta ce "Sahibi wai meyasa kake tambaya ne? To koma me ka je wajen aiki ka dawo akwai wani abin dana tanada maka, sannan sai mu yi hiran ko rabin raina? Yanzu dai kafin ka tafi ka rarrashe mani kanwata ka ji?".
Bawan Allah nan ya rasa bakin magana, domin harshen Ommu karfi ke kareta kamar reza, haka ya juya ya karɓi umarnin ta zuwa wajen Aunty dan ya rarrashe ta.
Yana tafiya ta saki wani shu'umin murmushi kasa-kasa ta ce "Yarinya da Hadiza bage maganin maza kike yi, ke baki ma ji sunan ba, maganin maza, sai na dafaki ta hanyar da ba wanda zai taɓa yarda kina dafuwa, ke yau kika gani, mu kuma mun ga jiya munga yau har ma da shekaran jiya, ki jira ki gani, Hadiza bata zama da kishiya, nan gidana ne ni kaɗai". Ta kai karshen maganar tare da wucewa cikin ɗakinta tana ayyana yadda zata rikita Abbi da yamma idan ya dawo.
(Tofa Aunty gara maki Rufee da wannan hamshakiya, ba abin da za mu ce sai dai Allah ya kuɓutar da ke😭)
Kuka Abbi ya iskota tana yi, ta haye saman bed nata tana kuka, gefenta ya zauna yana faɗin "Halima lafiya kuwa?".
Cikin kuka ta ce "Haba Abbi akan me zaku ci mani fuska haka?" Yar dariya ya yi kafin ya ce "Haba Halima! Kefa kika bawa Hadiza dama ta zaɓi ɗakin da take son zama, bai kamata yanzu kuma ki dawo sheɗan yana zuga ki kice wani abin ba, kamata ya yi kema ki so ta kamar yadda ta so ki, kuma kamar yadda kika faro tun farko, ki duba ki gani fa yadda take yabon ki, baki ga matsa mani da ta yi akan lallai sai na rarrashe mata kanwarta kafin na fita ba, amma ki yi hakuri, idan na dawo zamu zauna mu yi magana kin ji ko?" Bai jira amsarta ba yana kai karshen maganar ya manna mata kiss a goshi ya miƙe ya fita.
KADA KU GA LAIFIN ABBI, MAKIRAR MACE BA WASA BA, KAWAI KU TAYA AUNTY ADDU'AR ALLAH YA KWACE TA, AMMA MAKIRAN MATA SUN WUCI TUNANIN MAI TUNANI, BA BOKA BA MALAM SUKE MALLAKE GIDA, SU KUMA JUYA DUK WANDA SUKE SO, KUNA DAI GANI TA HANA ABBI MAGANA, SAI WANI RUFE MASHI BAKI TAKE YI, DUK WANI ZAFIN NAMIJI SAI DAI IDAN BAI HAƊU DA MAKIRAR MACE BA, TUNI ZATA JUYA SHI, KO SHEƊAN TSORON MAKIRAN MATA YAKE YI BARE MUTUN, ALLAH DAI YA RABA MU DA IRIN SU
Yana fita aunty ta kara rushewa da wani sabon kukan tana faɗin "Ya Allah na wannan wace iriyar masifa ce, matar nan tun zuwanta ta ce bata so na, hasali ma bata kula ni ba, amma yanzu ta zo ta ce mashi wai tana so na, kuma zata kula da Ni, har da wani cewa nayi ɗawainiya da ita na bata zaɓin ɗaki, ta kashe ni ta gama da ni, Allah ka mani sakayya da gaggawa!!!"
KUNJI ABUN DA YA FARU DA AUNTY JIYA KENAN BA RI MU DUBA WAJEN SU IRFAN MU DAWO.
Daga karshe dai Irfan da ya gama waya ya buɗewa daddyn Jelly kofa tare da gaya mashi yadda suka yi da bandits ɗin, sannan kuma ya ce Akil ya ce zai bada kuɗin, zai cire daga Account nasa, sai su kai su ɗauko Aafia ɗin. Har wani nauyayyar ajiyar zuciya daddyn Jelly ya sauƙe dan ba karamin tashin hankali ya shiga ba, ƴa budurwa a hannun yan bandits ɗin nan, abin dole akwai tashin hankali.
ALLAH SARKI BA KU MA SAN AN GAMA LALATA MATA RAYUWA BA😭.
AFTER SOME HOURS👌
Aunty da Ayla ce zaune a palo suna hira, yanzu sun ɗan samu sauki a ransu tun da su Akil za su je ɗauko Aafia ɗin.
Sai hira suke yi Aunty na kara koya mata yadda zata zauna da mijinta, yadda zata yi da daddyn ta.
A wannan hali ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ya same su, saman sofar kusa da babynsa ya zauna yana faɗin "Sadiya me ya same ki naga idon ki sun kumbura sun yi ja haka?" Murmushi ta yi kafin ta ce "Babu komai yaya Maik".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Saboda A'afia ce?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba komai.
Dawo da kallonsa kai Ayla dake ta faman ɓoye fuska ya yi "Baby wai har Yanzu baki dai na jin kunya ta bane?".
"Ina wuni daddy" shine abin da ta ce mashi, hannu yasa ya ɗan buge mata baki, cikin sauri ta rufe bakin nata da hannun ta tana yin kasa da kanta.
Dariya Aunty ta yi kafin ta ce "Kun dai fi kusa ni bari ma na kawo maku abinci ku ci sai ku ji daɗin yin hirar" cikin sauri ya ce "A'a Sadiya ba sai kin kawo ba ni ba zan ci ba". Bawan Allah damuwar rashin A'afia da kuma halin da suka sami labarin tana ciki ne ya hana shi cin abincin.
"To idan ma ka ƙoshi ai babyn taka bata ƙoshi ba, taki cin abinci tun safe" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi dining table dan ta ɗauko mashi abincin.
"Baby baki ci abinci ba, me yasa?" Ɗan satar kallon shi ta yi, nan take kuma abubuwa da Aunty ke gaya mata akan abin da zata rinƙa gaya mashi, ya faɗo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, tuna haka yasa sai ta ce "Kai nake jira daddy muci tare". Ɗan waro dara-daran idanun nan nasa waje ya yi yana faɗin "Haba dai?" Ya yi maganar cike da jin daɗin furucin ta da kuma tsantsan kaunar ta. Gyaɗa mashi kai kawai ta yi yana murmushi.
A gabansu aunty ta zo ta ajiye mashi tray ɗin abincin tana faɗin "To aci lafiya" ta kai karshen maganar tare da hayewa sama ta ba su waje.
Ƙoƙarin fara zuba masu abincin ya yi, cikin sauri ta sauƙo ta karɓe shi tana faɗin "Daddy ka bari na zuba mana, ba aikin ka bane ai" ɗan leƙo fuskarta ya yi yana faɗin "Ya naga yau kin kara tsantsan kyau ne?" Hannu tasa ta rufe fuskarta tana dariya.
Riƙo hannayen nata ya yi, har yanzu ya kasa dai'na taɓa mata hannu saboda da haka suka saba, ya saba riƙeta, amma dai yanzu baya yarda ya rungumeta idan yana rarrashinta, sai dai ya goge mata hawaye kawai.
Janye hannun nata daga kan fuakarta ya yi yana faɗin "Ni da fuskar baby na ne zaki rufe Mani? Ina ruwan ki?" Zata yi magana kenan wayarsa ta fara kara, cikin sauri ya saketa tare da fito da wayar daga aljihunsa domin dama yana jiran kiran su Irfan dan ya fita zai je ya haɗu da Akil su je wajen yan bandits ɗin kai kuɗin.
Miƙewa tsaye ya yi tare da yin picking call ɗin yana kara wayar a kunnansa,.
A ruɗe Irfan ya fara magana cike da tashin hankali.
"Hello bappa, mun samu nasarar karɓo su Aafia sai dai kuma kamar fa ta rasu bata da rai, bata numfashi, amma dai mun nufi hanyar asibiti da su yanzu, ka same mu a can, kuma dan Allah kada ka gayawa Abbi, ka bari tukun nan sai mun ji me likitoci za su ce, dan ina ji a jikina doguwar suma ta yi" ai tun Irfan bai karisa magana ba daddyn Jelly ya fice cikin sauri.
Kai tsaye part nasu ya koma ya ɗauki key ɗin motar Irfan ɗin ya shiga da gudu ya bar gidan, yana tafiya a hanya ne Irfan ya tura mashi address ɗin asibitin, ba ɓata lokaci ya isa can.
Wani katafaren private hospital ne, yana isa kuma lokacin motar Akil ɗin ta danno hanci cikin asibitin, a tare suka yi parking na motocin a parking space na hospital ɗin.
Akil ya riga kowa fitowa, fuskar nan tasa babu alamar sauki ko kaɗan, yau a ɗaure take tamau, haka suka fito da Aafia da kuma Hanan, Aafia kamar babu rai a jikinta, fuskar nan ta yi wani Yellow kamar bata da jini, ita kuma Hanan bata suma ba, idon ta biyu.
Nasan zaku so jin ya akayi ya zama A'afia da Hanan, to ku saurara, Irfan ya gayawa yan bindigar su biyu ne ba ita kaɗai ba, shine da suka tashi fito da su bakin dajin, in da suka yi da Irfan zai kawo kuɗi ya ɗauke su, sai suka ɗauki Aafia da kuma Hanan a maimakon Rufee, abin da yasa kuma suka ɗauki A'afia da Hanan ɗin, domin Hanan ita kaɗai ta kula Aafia, lokacin da ta farfaɗo daga sumar da ta yi, ta rungumi Aafia suna kuka, hakan yasa bandits ɗin suka yi tunanin cewa tare suke, kuma a hannun Hanan ɗin Aafia ta yi wannan doguwar somar, Rufee kuma bata iya magana ma bare ta je in da Aafia take, maman Zahra kuma ta yi iya kan nata rarrashin sai suka kyale Aafia ɗin da Hanan shiyasa da suka tashi, sai suka ɗauke su a tare.
Hanan bata suma ba, amma bata a cikin hayyacinta sosai, saboda kiɗima da kuma tashin hankali da take a ciki, har yanzu tana ganin kisan da aka yi wa mamanta a cikin idonta ya ki gogewa, kuma abin ya ɗan taɓa mata kwakwalwa.
Gaba ɗayan su cikin hospital ɗin suka wuce da su, da farko anki karɓarsu saboda ana tunanin ƴaƴan malam Shehu ne, sai aka ki karɓar su, Dr's ɗin suka fara cewa aa sai sun bi layi sun yanki kati da sauransu.
Da yake daddyn Jelly ya san halin likitocin mu na yanzu, sai ya nuna masu fa e lallai akwai ruwan kuɗin, hakan yasa nan take suka karɓe su babu zancen bin layi bare kuma yankar kati, duk an mance wannan, suka karɓe su hannun bibbiyu zuwa ɗaki na musamman tare da fara duba su.
Sai zarya a bakin kofar ɗakin Akil da Irfan, daddyn Jelly suke yi, har wani zufar wahala ne ke tsastsafo ma bayin Allah nan, tashin hankali iya tashin hankali sun shiga, bukatar su kawai suji ke matsalar, kuma Aafia ɗin tana raye ne ko dai ta mutu da gaske.
Suna wajen har karfe 5 na yamma, sannan babban likitan ya fito yana faɗin "Sannunku" a ƙage Akil ya ce "Dr yaya me yasa me ta? Tana raye ko?" Ya yi maganar a ruɗe.
Jinjina kai Dr ya yi irin alamar akwai damuwa, a tsanake ya ce "Kuyi hakuri fyaɗen da aka yi mata ne yasa ta zubar da jini sosai wadda ya haifar mata da rashin jini har ya kai ta ga doguwar soma, sannan kuma wanda ya yi mata fyaɗen ya ji mata babban rauni wadda sai an dage za'a shawo kan matsalar, idan kuma ba mu yi Sa'a ba muna iya rasa ta ko kuma kwakwalwarta ta ɗan taɓu, koma ta haukace baki ɗaya....."
Wani irin Jiri Akil ya fara gani lokaci guda, nan take gaba ɗaya fuskarsa ya wanke da zufa, idan baku mance ba yana da bala'in zuciya, dafe kansa ya yi yana maimaita kalmar fyaɗe, shikenan sun lalatawa kanwarsa rayuwa, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, kafin su daddyn Jelly su farga ya zube kasa wanwar. Dama idan baku mance ba, ya gaya mata idan har ya bincika ta taɓa sanin Namiji to zai kasheta, tun daga wannan lokaci ya kama kusani cewa ba zai iya ɗaukar wannan musifar ba.
Da sauri su daddyn Jelly suka yi kansa, suna addu'ar Allah yasa ba haɗiyar zuciya ya yi ya mutu ba, ɗakin da su Aafia ke a kwance nan aka shiga da shi, akwai sauran gadon da ba kowa, a nan aka kwantar da shi, ba ɓata lokaci shima likitocin suka dukufa akan sa, dan ceto rayuwarsa.
Sosai zuciyarsa ke bugawa da karfi-karfi, Irfan da daddyn Jelly sunga tashin hankali iya ganin idon su yau, daddyn Jelly sarkin saurin kuka, to yau ya yi kukan har ya ga ji ya daina.
Da kyar suka iya zama saman kujera, a nan suka yanke shawara a kan su rufe maganar iya su ukun kawai, kada kowa ya ji, ko Abbi ba za su gaya mashi ba, sai dai su ce mashi dukanta yan bandits ɗin suka yi har ta suma, a kan wannan shawara suka tsaya.
A ɓangaren Jelly kuwa wato gidan Abbo.
Sai shirya shiryen bikinta da Nawid Hajiya turai take yi, yau saura kwana goma cikin wa'adin da ta ɗeba na time ɗin bikin, har kayan da jelly zata saka ranar bikin duk ta sayo, sai shiri take yi, Hajiya Batula zata zo daga Maiduguri dan gyara Amarya nan da kwana biyar masu zuwa, duk wani kayan bukata Ummi ta sayo su, a ɓangaren Abbo kuwa yana ta faman shirya ta yadda zai yi ya ɗauketa ya maidata gidan sa a Abuja, domin Ummi dai ta ce sai anyi wannan aure, kuma idan ya cika yin jayayya da ita asirinsa zai iya tonuwa, shiyasa kawai ya yanke shawarar ɗauketa ana gobe biki, daga ɓangaren ita kuma Hajiya Jelly bata da masaniyar duk wannan abin da ake yi, ita dai tana ganin mata suna zuwa yin aiki tukuru, na gyare gyare gida, su yin cincin da sauransu, ita dai banda cin kaza ba wani abin da take yi, idan mata ta yi mata wani gani ta wanke ta tas soso da sabulu, haka Hajiya Turai zata basu hakuri ta ce kada su yi mata wata magana, suna ji suna gani kamar yarinya take gaya masu magana haka suke hakura ba yadda za su yi.
a ɓangaren shi kuma Nawid yana can yana faman yadda zai shiga zuciyar Rimsha ya yi kane kane abinsa, ya yin da shima Ahmad yake ƙoƙarin kafa tasa gwamnatin a zuciyar Queen of beauty, sai dai kuma duk ba ta tasu take yi ba, yanzu ma dukufa ta yi akan karatun ta kawai, ta mai da hankali ga makaranta, idan ma sun kira waya Akila ke ɗauka, idan sun ce ta bawa Rimsha, sai ta ce masu tana barci ko wani abin, dan bata son abin da zai ɓatawa Rimsha rai, ta fi son ta ganta cikin farinciki, idan ta yi waya da Ahmad tana shiga cikin bakin kuma haka take wuni, shiyasa Akila ke shiga tsakanin su....✍️
Sai mun haɗu Monday idan mai dukka ya kai mu a gidan Abbi dan jin ya wannan al'amari zai kasance I'm waiting for Hot comments my yan Amana, JAMES Fans!!!
*
💖💖TRIPLETS💖💖
*Idan kun samu typing error amin afuwa 👏 keyboard ɗin tana bani matsala sosai kwana biyun nan, to na yau ma ya fi tsananta, sai na danna girki sai ya koma kirki 😭*
E 61-62
After one days🥰
🔥GIDAN ABBA🔥
A yanzu Rimsha ta goge ta zage da karatunta babu kama hannun yaro, kuma hakan bai hana ta mafarkin Lion da take yi ba, kullun tana mafarkinsa kamar yadda ta saba, sannan wayan nan hotuna da Imran ya turo mata sun zame mata kamar Tv, kullun tana manne da waya tana kallonsu, shi kuma Imran, duk time da ya sami dama yana fakon idon Lion ya ɗauke shi hoto ko video ya tura mata, hakan yasa ta tara hotonsa sosai da sosai.
Yauma kamar kullun tana zaune cikin ɗakinta, ita kaɗai misalin karfe 3, Akila bata dawo daga school, ta baza takardunta a gaba tana dubawa, da alama an basu assignment ne, hankalinta ya dukufa akan takardun nata, wayarta dake a gefen ta ne ya fara kara, tana dubawa sai taga yaya Imran ne kuma video call.
Wani kayatatcen murmushi ta saki kafin ta ɗauki wayar tare da yin picking na call ɗin, kamar dai yadda ya saba nuna mata Lion, to yau ma haka ne, sai dai yau ya sha bambam, domin yau kwance ta gan shi yana barci, ba ƙaramin burge Imra yake yi ba idan yana barci, hakan yasa ya kirata dan ita ma ta gan shi.
Kasancewar idanuwansa a lumshe, hakan yasa ta kurawa zara-zaran eyelashes nasa ido, suna da tsawo masha Allah, a hankali ta dawo da kallonta kan wannan lallausan red lips ɗin nasa, ga bakin nasa ɗan karami, laɓɓansa na sama design of heart ne, kuma yana da ɗan tudu kaɗan, while na kasan kuma ya ɗan ɗara na saman kaɗan, kuma shi na kasan yana da ɗan faɗi kaɗan, daga kasan Lips ɗin nasa kai ka ce an zana mashi wani abine aka fito da shape ɗin laɓɓan sosai, amma kuma haka suke, haka Allah ya halitta mashi su kamar an fito