Showing 351001 words to 354000 words out of 355604 words
a jikinta ba kama hannu yaro.
A ɓangaren gidan Abba kuwa yau ma kamar kullun Akila dai an zuba love da masoyin ɓoye fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma fa yau ma sai da ya saka ta kuka da salon soyayyarsa, haka kuma ya zauna ya zama mata kamar karamin yaro, yana zuba shagwaɓa yana rarrashinta har sai da ta yi shiru, sannan ya yi mata kamar jiya, ya ce ta bar wayar manne a kunnenta bari ya zuba mata zafafan kalamai har zuwa ta yi barci.
Haka kuwa akayi, ya kasheta da kalaman da sai da ta yi mafarkinsa, wani irin barci ta yi mai cike da nishaɗi tare da begen masoyin nata.
Idan muka koma gidan LION kuwa, a wannan dare dai Imran ne ya sake miƙe wa da kansa ya je ya yi sauran aikin Rismha da bata kammala ba, sannan ya dawo ya kwanta.
DREAM (Mafarki)
Misalin karfe biyu na dare, zaune take a cikin palonsu na sama, daga ita sai wandon jeans guntu zuwa santala santalan cinyoyinta, ta sama kuma wata yar riga ce mara nauyi wadda ta tsaya mata a iya cibiyarta, hannunta riƙe yake da wani tsadadden haɗadɗen cup mai shegen kyau wadda ke ɗauke da custard da spoon a ciki, a hankali take ɗeba da spoon tana kaiwa ɗan bakin nan nata, sai wani murmushi take yi tana cikin nishaɗi sosai.
Daga ta bayanta ta ji ya zuro mata hannu izuwa saman wuyarta, ko bata juya ba ta san wanene domin kuwa kamshin perfume nasa ya isar mata da saƙon wanene ɗin, ɗebar custard ɗin ta ta yi zata kai bakinta, cikin sauri ya sanya hannun nasa a bakinta ya rufe mata, a lokacin kuma tana gab da kai spoon ɗin cikin ɗan bakin nata, hakan yasa custard ɗin ta zuba mashi a hannunsa.
Ƴar kara ya yi mata a shagwaɓe, da sauri ta ajiye cup ɗin tare da riƙo hannun nasa in da custard ɗin ya taɓa ta lashe tas sannan ta cigaba da lasar hannun nasa.
Ɗaukar ɗayar hannunsa ya yi ya ɗaura a saman shafaffen cikinta yana shafawa a hankali,. Cikin nata a shafe tamkar bata taɓa zuba abinci a ciki ba.
Wani irin dogon numfashi ta ja tare da sauƙe wa a hankali, matso da ɗan bakinsa ya yi saitin kunnenta, kasa kasa ya ce "Meesha mu je ciki in baki wani abu mai daɗi kin ji ko?" Ɗan juyo da face nata ta yi da nufin ta yi magana, bata kai ga yin maganar ba ya manna mata kiss a kumatunta yana faɗin "Please mu je mana, abun daɗi fa zan baki".
Okey ta ce mashi tare da miƙe wa ta juyo suna fuskantar juna, wani irin ihu ta kurma da ganin cikin kwayar idanunsa, a razane ta farka daga barcin da take yi, sai haɗa wani uban zufa take yi tamkar ba gobe, da alama zazzaɓin nata ya sauƙa, jikinta har kerma yake yi.
Da kyar da addu'a da ambato sunan Allah ta samu ta mai da barci, domin ba zata iya tashi ta yi nafila ba saboda rashin lafiya da take a ciki, ta kasa tashi hakan yasa ta gwammaci komawa kawai ta kwanta zai fiye mata alkhari.
Da kyar ta samu ta iya mayar da barcin nata, cike da danasanin mafarkin Lion da ta yi a yau.
Washegari sai karfe 7 ta samu dama ta iya tashi daga barcin wahala da ya ɗauketa tun bayan sallar asuba.
Wayarta da Imran ya ajiye mata a saman bedside drawer ta fara dubawa, nan fa ta sami miss call na new number har kala uku, ko wani number kuma ya mata miss call zai kai guda biyar.
Shiru ta ɗan yi tana tunanin waye zata fara kira a cikinsu, daga karshe dai ta yanke shawarar bari ta kira ta farkon da ta fara kiran nata ta ji ko wanene.
Bugu ɗaya aka ɗauki kiran, cike da zumuɗi ta ce "Hello Rimsha". Duk da halin da take a ciki hakan bai hanata sakin cool murmushi ba, cike da so da kauna ta ce "Anaya ke ce dama?" Daga ɗayan ɓangaren ta ce "E Rimsha nice na ga jiya baki zo school bane shi ne yanzu na gama shiri daddy zai kai mu sai nace bari na kira number da kika bani na ji ko lafiya". Daga jin yadda take magana tana cikin matuƙar faricniki tare da jin daɗin samun Rimshan a waya.
Kara faɗaɗa murmushin Rimsha ta yi kafin ta ce "Anaya wlh kaina ne kawai yake ciwo Shiyasa ban zo ba, amma gobe zan zo In Sha Allah". "Subhanallah Allah sarki Rimsha Allah ya baki lafiya, to idan na dawo school zan ce daddy ya sanya driver ya kawo ni gidanku sai na duba ki ko? Wannan shine numberta ki yi saving kin ji?".
"To Anaya amma sai na fara gayawa yaya Imran zaki zo tukun nan, idan ya yarda to Shikenan sai na kiraki na gaya maki" to Anaya ta ce sannan suka yi sallama sai murmushi Rimsha take yi, baki ya ki rufuwa, haka ita ma Anaya ɗin, tana matukar Kaunar Rimsha sosai, ita ma Rimshan tana matukar kaunar tane sakamakon ta ce Anayar tana yi mata mugun kama da Jehan, tamkar ƴan biyun Jehan ce ita, harta shekarunsu kusan ɗaya ne, sai dai Jehan ta ɗan fi Anaya kaɗan amma bacin haka komai har tafiyarsu yanayin magana komai iri ɗaya, sai dai kuma Anaya tana dariya, ita kuma Jehan ba sai na sake faɗa ba, kunsan kwata kwata bata ma san me murmushi ba bare kuma dariya, wannan shine kawai banbancin Anaya da Jehan,. Kada ku mance JEHAN da Nawazudden take kama sosai.
ANAYA AZHARUDDEEN SALMAN SULTAN nasan daga jin sunan kun san wace ce Anaya a wajen su Rimsha, sai dai kuma ita Rimshan bata sani ba, domin bata san wanene Azharuddeen ɗin bama, daddynta kawai ta sani, sai kuma yanzu da ta san cewa su Imran ma ƴan uwanta ne.
To musan waye Azharuddeen kaɗan a tare, nasan daga jin karshen sunansa na SALMAN SULTAN kun fahimci cewa ɗan uwane ga NAWAZUDDEN SALMAN SULTAN, to Azharuddeen dai shine Hasan ɗin Nawazudden, Professor ne lecturer a jami'ar Ahmadu Bello University Zaria, sai dai mazaunin cikin garin Kaduna ne, a nan yake shi da family'nsa baki ɗaya, yana da gida a zaria a in da yake sauƙa ya kwana sai ranar Friday ya dawo cikin Kd wajen family'nsa, shararren mai kuɗi ne na bugawa a jarida, bayan Professor ne kuma yana da kampanoni da dama a faɗin kasar nan wadda take amsa sunan SALMAN SULTAN, ƴaƴan sa uku, babba namiji ɗaya mai suna Feroz shine babba mai shekara 18 yanzu a duniya, sai kuma Anaya mai shekara 15 a duniya, sai autarsu Zaira mai shekara 14 sana'ar Rimsha kenan, da yake matarsa babbar likita ce sai ta ɗauki hutun haihuwa tun daga kan Zaira ta ce ta yi auta ba ƙari.
Azharuddeen wato Hassan yana bala'in Kaunar ƴaƴan nan nasa fiye da tunanin mai tunani, hala zalika yana kaunar ƴan uwansa su Abbi, da su yake kwana da su yake tashi, yana yawan bibiyar lamuransu, shi ya rayu da su na tsawon lokaci, daga bayane ya zame kansa daga garesu, amma Daddyn su Rimsha tun yana yaro ya barsu, hakan yasa da wuya su iya gane shi a yanzu, idan dai ba shi ne ya ce masu shine wane ba, amma fa lokacin da ya fito takarar shugaban kasa sunansa ya fara yawo a duniyar Africa baki ɗaya, har gida PROF AZHARUDDEEN ya zo dan ya ganshi ido da ido domin ya tabbatarwa da kansa wannan kamanni dake a kan fuskokinsu, amma ko da ya zo Daddyn Rimsha ya ce sam ba shi bane Hosain, sunane kawai ta yi iri ɗaya wadda kuma ana iya samun hakan a cikin jama'a tunda dai duniya da faɗi take, Azharuddeen ya ji ne kawai amma bai yarda ba, abin da kuma yasa ya kyale daddyn ya tafi dan saboda kada ace sai yanzu da daddyn ya yi kuɗi ya zama wani shi ne za su neme shi, hakan yasa kawai suka kyale shi, amma ba su cire tuhumar akan cewa shine Hosain ba, haka zalika suma su Abbi sun tuhumeshi ne saboda sunansa, suma ya musa masu saboda wani dalili nashi da bamu sani ba, wata kila sai gaba za su buɗe mana komai mu sani. WANNAN SHINE TAKAITATCEN WAYE AZHARUDDEEN SALMAN SULTAN IN KIYA HASSAN A YANZU, SAI MUN SHIGA CIKIN LABARIN KUMA ZAMU SAN AINAHIN TOSHEN KAN ZANCE AKAN FAMILY'N.
Ajiye wayar ta yi bayan sun gama magana da Anaya, cikin sanyin jiki ta sauƙo kasa daga saman gadon ta nufi toilet, ruwa mai zafi sosai ta zuba ta yi wanka da shi, sannan ta fito bayan ta ɗauro alwala dan ita kullun cikin zama da alwala take.
Shiryawa ta yi cikin riga da wando kamar yadda ta saba, sannan ta sanya takalmin flat shoe mai shegen kyau, ta yi kyau sosai kamar ka sace ta ku gudu ka je ka ajiyeta kayi ta kallo dan kyau, sai wani kara cika take yi kwana biyun nan, tamkar ba ita ba, idan ta yi murmushi Yanzu wani irin lotsa dimple nata yake har wani irin rami yake yi saboda ta kara kumatu, har lokacin hannunta basu dai na yi mata zafi ba, hannun ya fi yi mata zafi domin dayawa ya zuba mata chemical ɗin a hannu, a kafa kuma ita ce ta zuba da kanta, so kaɗan kaɗan ta zuba, ba sosai ba, da hannu da kafar duk sun kumbura, kun san idan fatar mutun ta tsage dole wajen ya kumbura, a hakan ma dan daren jiya da tana barci Areef ya shigo ɗakin ya shafa mata magani, da yake jiya taci wuya sosai, da ta kwanta ko motsawa bata yi ba, wani irin barci mai nauyi ne ya ɗauketa, hakan yasa bata ma san time da Areef ya shafa mata maganin ba.
A hankali ta fito palon sama, kamar kullum babu kowa a palo, wuce wa ta yi ta nufi kasan benen dan ta je ta gaishe da Areef, sai tashin kamshi take yi abinta.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo cikin ɗakin, yau yana zaune ne a saman sofa set dake a cikin ɗakin, daga shi sai singlet fara tas da three quarter zuwa gwiwa, ya yi wanka, kai Allah ya yi wa TRIPLETS halitta, wani irin sihirtaccen kyau na musamman ne ke gare su, sai kallon shi take yi, yau ma kamar jiya cikin zolaya ya ce mata "Da gaske Lion ya fini kyau, amma dai jiya da nace maki kafarsa ya fi nawa kyau wasa nake yi maki, halittar kafarmu duk iri ɗaya, amma dai ya fini kyau sosai gaskiya".
A yau dai bata ɓoye fuska ba, sai ma ɗan ɗaure fuska da ta yi jin ya amfaci sunan Lion, ta tuna azaban da ta sha daren jiya ne.
Kamar dai ko yaushe, gefensa ya nuna mata ta je ta zauna yana faɗin "Dan Allah Rimsha ki yafe wa ɗan uwana, kada ki ce zaki dai'na son shi saboda abin da ya faru jiya, duk abin da ya ɓata mu zamu gyara, shi kuma zai biya ki amma sai gaba, ina sa ran haka, kiyi hakuri saboda mu kin ji ko?".
Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ta ji. Wayarsa ya ɗauko ya fara kiran layin Aseef video call, dama tun ɗazun Aseef ya takura mashi akan ya haɗa da RIMSHA ya ce mata sorry da abin da ya faru,. Allah mai iko wai yau family'n William jacop ne za su cewa wata sorry, sorry ma kuma ga mace, tab lallai musulci duniya ne, musulci daban take, idan Allah ya yo ka a musulmi to ko tabbata ka yi kana gode mashi baka biya shi ba, addini mai sanyi, mai sauƙi, tausayin na kasa, girmama iyaye, kamanta adalci, rashin wariya, kaunar juna, Allah mun gode maka da ka yo mu a musulmai.
Yanzu haka a yadda Lion yake nan Addinin Musulunci ta sanyaya mashi zuciya sosai da sosai, da lokacin da yake kristar ne Rimsha ta sanya shi amai, da sai dai muce Allah ya jiƙanta, dan ko bai kasheta ba, to wlh ba zata sake moruwa ba, amma da yake akwai sanyin musulci a ransa sai ya tsaya a iya chemical, yanzu ga shi saboda musulci Aseef ya ce a kira mashi ita ya bata hakurin abin da ɗan uwansa ya yi mata, yanzu sun san da cewa ba komai ne idan suka yi ya zama daidai ba, dole akwai abin da ba daidai ɗin ba, kuma idan sun san sun yi ba daidai ɗin ba, suna kokarin su gyara, idan wannan murɗaɗen ɗan uwan nasu ne ya yi wadda shi ya fi karfin ba da hakuri, kuma idan ka ce mashi hakan zaka karɓi hukun dan baya son wannan kalma ta sorry, to idan shine ya yi abin da ba daidai ba, su biyun suna kokari su gyara su kuma bada hakuri a madadinsa, BAYIN ALLAN.
Bugu ɗaya Aseef ya ɗauki kiran, yana zaune a saman table yana cin abincin, yau wani irin azababben kyau ya yi, idanunsa na sanye da wata shegiyar glasa mai bala'in kyau da tsada baka mai ɗan girma, jikinsa na sanye da high neck t-shirt maroon color da wandon jeans fara tas, bayan sarkar da Lion ya ba shi akwai wasu karkar zinari guda biyu a wuyar tasa, daga hannunsa ma akwai sarkar hannu masu bala'i kyau da tsada, yau ya yi wa gashin kansa penti, amma daga ɗan gefene ya sanya purple color ya tura iya gefen kunnensa, kunsan gashin nasa yanzu ta yi tsawo, kuma Musharraf ya ce kada ya aske, shine ya barta har kalata yake yi yanzu, ba karamin kyau ta yi mashi ba, sai tashin wani irin fitinannen kamshi yake yi, ga kwarjini bala'i a tattare da su, sannan ga farin jini na fitar hankali.
Cikin sanyin murya ta ce "Good morning yaya ASEEF". Maimaita kalmar yayan ya yi kafin ya amsa mata, sosai Rimsha take kallonsa saboda na gaya maku shi ya fi kama da Lion akan James.
Zubawa sarkokin wuyarsa idanu ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "Wannan sarkar ta so ta yi kama da nawa, sai dai kuma akwai banbanci sosai da sosai, nawa complete ne kuma nawa round ne ba mai Heart ba, amma nima nawa yana kyalli kamar haka".
Fuska ɗauke da murmushi ya ce "ina naki ɗin yake, kawo bari na gani". Okey ta amsa mashi da shi sannan ta ɗan yi kasa da wuyar rigarta ta fito da sarkar, ɗan murmushi ya yi kafin ya ce "Akwai bambanci da namu sosai, na farko naki ba real zinari bane, akwai miss, namu kuma zinari ne zalla, baki ga saman tambarin nakin baya wani kyalli sosai kamar igiyar ba ne? Kuma sarkar ma ba su yi iri ɗaya ba, cox kawai dai chain ɗin ne ya so ya yi kama, wannan sarkar mummy'n mu ne ta bamu, ina son shi sosai, na ki ma ya yi kyau sosai, in saya maki wani zaki sanya?". Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e
Shi dai Areef ido kawai yake bin su da shi ya wani riƙe masu waya kamar wani ɗan aikinsu.
"Tom shikenan zan sa Prof ya saya maki zinari mai shegen kyau irin namu sai ki saka, duk da na san da wuya a sami sak irin namu domin namu mummy da kanta ta je aka buga mata, ita ta zaɓi design da take buƙata da kuma time da date a jiki, amma dai ba za'a rasa mai kama da shi ba, da a ce ina free ma da na je da kaina company na basu nawa in ce a buga mani irin shi sai na zo maki da shi, amma dai yanzu ma ko an saya maki wani zan sanya a buga maki wani irin namu na zo maki da shi kin ji ko?".
Fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "E naji kuma ina godiya sosai da sosai".
Rimsha ya ambaci sunanta da wata iriyar murya wadda sai da ya sanya Areef kallonsa, ita ma dai ta yi mamakin yadda ya kwantar da muryarsa kasa kasa ya amsaci sunanta.
"Rimsha ki yi hakuri da abin da ɗan uwana ya yi maki kin ji ko? Kada ki riƙe shi a zuciyarki, ki yafe mashi dan Allah, shi haka yake, shi sarki ne, amma mu bamu son hakkin kowa ya kama shi, musamman ma hakkin ke ɗin nan, bana so ya kama shi, idan baki yafe mashi ba ina da tabbacin Allah zai bi maki hakkinki domin wannan a rubuce take, to dan Allah ki yafe mashi sannan kuma ina mai matukar farinciki da kika kasance ƴar uncle Hosain, na ji daɗi fiye da tunaninki, kuma ina matuƙar ji dake kema tamkar uncle, ki kula mana da kanki ƴar kanwar mu, banda rashin ji, ayi karatu sosai, daddynki yana can yana barcin gajiya, ni kuma zan tafi school yanzu ina da exams, yau zan yi na ukun karshe, so please pray for me kin ji ko gimbiyar TRIPLETS?".
Murmushi Areef ya yi, tana ƙoƙarin yin magana ya rigata da cewa "Aseef kana da sata fa, yanzu ina ruwanka da sunan da nake kiranta da shi da zaka sata mani? Kaima ka kawo naka sunan mana, daga na baka labari shikenan ka sace mani suna".
Kallon gefen ido ya yi mashi a yayin da idanun nasa suke a cikin glass. With full confidence ya ce "Ka gaya mani menene banbancina da kai? Idan ka gaya mani zan daina yin abin da kake yi". Hararar wasa Areef ya yi mashi kafin ya ce "Na fika kyau mana, kuma na fika karfi sannan na fika iya cin abinci".
Dariya sosai Aseef ya yi kafin ya ce "Kuma ka fini neman magana ba, ni ka bari Gimbiya ta yi mani magana zan wuce school time na tafiya". Kallonta Areef ya yi alamar ta yi magana Aseef na jiranta.
"Our Queen kin yafe wa ɗan uwana? Dan mu zaki yi ba dan shi ba kin ji ko?". Cikin sanyin murya, a nutse ta ce "Ni dama ban riƙe shi a zuciyata ba, na yafe mashi Allah ya ya fe mu tare". Wani haɗaɗɗen murmushi ya sakar