Showing 216001 words to 219000 words out of 355604 words

Chapter 73 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2766

akan maza, ita kam Rimsha kunya kamar zata nutse cikin kasa, sai wani yan kame-kame take, tana gyaran kayan miya, ɗan zungurar ta Akila ta yi tana faɗin "Ai ina gaya maki ne yadda zaki shawo mana kan mijinmu idan Allah ya kaddara, ki rikita mana shi, sai ya fara kuka yana baby ina son ki, kin san nifa Hajiya Batula mummy'n Aunty Abla ta gama gaya mani abubuwan gyran jiki idan na yi aure, kuma ina karanta wani book na Princess Teema, so nasan abubuwa da dama, dan haka ku kasa kunne ku saurare ni, ga shi ma Hajiya Batulan ta ce zata zo biki gidansu wannan Dr Nawid da ya zo jiyan, da muka yi waya da ita da safe ta ce mani zata zo biki a gidan, zata kawo mani ziyara duk da cewa Ammie bata son ta, amma zata zo, kanwar Abba ce fa, yar autan su, ina matukar kaunar ta, idan ta zo sai ta kawo mani dilka mai bala'in kyau da gyara jiki, da kuma su humra masu bala'in kamshi, a mai duguri take aure, wayyo Allah idan aurena ya zo, zaku ga gyara, akwai abubuwa, sai dai babu mijin, sai tarin wayan nan samari marasa lissafi akai, (🤣) duk ba su yi mani ba, shiyasa bana kula kowa, ni fa ina ji a jikina mijina wani shahararren sarki ne, irin shalele ɗan gatan nan, baby ina kake ne ka zo mu yi aure in tarairaya ka kamar yadda mummy Abla ta ke wa daddy Abla, ta ce habibi ga shuwayi (shayi) nan na kawo maka, ita fa mummy Abla bata kiran shayin ma kai tsaye idan zata gayawa daddyn Abla, wlh sai ta kara lanƙwasa shi ta wani ce suuwayi, sau biyu ina zuwa gidan ta, na ga abu iya ganin ido na, yaya Imran ya yi wa Ammie wayo ya kai Ni, nima yanzu ina son babyna ya zo mu yi aure na fara lanƙwasa sunan shayi". Ta kai karshen maganar tana kwashewa da dariya ita da kanta.

Sake baki Umaisha ta yi tana kallon ikon Allah wajen Akila, Akila ta fi karfinsu, wai shuwayi kai jama'a.

Ita kuma Rimsha yar dariya ta yi kafin ta ce "Aunty Akila ni fa ba ni ba zancen aure kawai ki kyale ni".

"Uhm shi kuma fa? Ina zaki kai mana shi, kuma wlh kin ji na gaya mani irin mijin mun nan sai da lanƙwasa sunan shayi, idan ba haka ba, kina ji kina gani za'a kwace maki shi, dan ma sa'an ki ɗaya baya kula kowa, da mazan da matan duk ba su ishe shi kallo ba, amma fa ki sani wlh sai kin dage, ta fannin gyara bani da matsala da ke, kina yi sosai, sai dai sauran harka, shi kuma karki ji komai zan gayawa mummy Abla zata ɗaura ki a network, zaki rikita mana oga da salon soyayyar ki". Umaisha kam ai tuni ta fara ɗibar lecture saboda ta ga abin fa e yana da amfani dan jiya taga amfaninsa iya ganin idonta.

Sai zuba masu zance Akila take yi, da yake bata san da zancen ɓatar A'afia ba, kuma Akil ne ya kara gayawa su Irfan akan kada a gayawa Akila da Umaisha za su shiga tashin hankali sosai da sosai, hakan yasa ba'a gaya masu ba.

Suna tsaka da aiki ruwan sama ya ɓalle, da gudu Rimsha ta fita zuwa cikin ruwan nan, sai mamaki su Umaisha suke yi, suka tsaya a bakin kofar palo suna ta kallonta.

Daga karshe dai Akila ma shiga cikin ruwan ta yi dan abin ya kayatar da ita sosai, haka suka rinƙa wanka cikin ruwa.

A ɓangaren su Lion kuwa.

Su Tga sun sami isowa Nigeria, sai dai ba su shigo da wuri ba, saboda sun ɗan tsaya a Spain na ɗan lokaci dan karɓar wani saƙon na Lion, sai wuraren karfe 3 na yamma suka shigo.

Motar da Lion yasa aka kawo mashi daga gidan gwamnan Kaduna yasa sojan dake yi masu girki ya je da motar Airport ya ɗauko su, kunna map sojan ya yi ya tafi ɗauko su

Tun da ya ɗauko su a hanya suke karewa Nigeria zagi har suka iso gida, kai tsaye parking space sojan ya wuce da su, Tga ne da Tyrone, yana kashe motar suka fito waje suna karewa gidan kallo.


A harabar gidan daga ɗan gefe can Tga ya ga wayan nan yan kwacen wayar da Lion yasa aka shigo da su, da alama kuma Lion ɗin ya mance da su, dan suna ta ɗan gefe sun yi kneel down a cikin rana, abin da ya sa Tga ma ya gansu saboda da suka fito daga cikin motar, ya tsaya kewaye gidan yana kwaɓe fuska kamar wadda ya ga kashi, wai gidan kwata-kwata bata wuci lambun daddy ba, kewayen da yake yi ne yasa ya gansu, ai kuwa ba ɓata lokaci ya tambayi sojan dake a bakin gate me suka yi? Nan ya gaya mashi abun da suka gaya mashi da bakinsu sun aikata, ɗaure fuska sosai ya yi yana kare masu kallo, kamar wasu almajirai yan datti da su, duk sun yi Tsuru-tsuru da su, da alama yunwa ya ci ganiyarsu sosai ne.

"ka ajiye mani su ina zuwa, bari na yi wanka na ɗan huta, zan zo in basu horo, dan dama hannuna yana ɗan yi mani kaikaiyi ga shi kuma ba za mu sami damar isa ga James yau ba sai gobe zamu yi masu diran safiya, yanzu dare ya yi ba mu shigo da wuri ba, hannuna na kaikayi sosai zan zo na sosa akan su" Cewar Tga kenan, kamar dai yadda kuka sani ne ya yi magana cikin harshen turanci, yana kai karshen maganar kuma ya wuce cikin gida.

(Yan kwacen waya Allah ya jiƙan ku😭)

A palo ya isko Tyrone yana tsaye yana yan kalle kalle "What are you waiting for?" Tga ya tambaya yana nufar staircase ɗin, bin bayan sa Tyrone ya yi yana faɗin "You am waiting for".

A tare suka haura sama, suma dai kamar Imran da kamshin perfume ɗin nasa suka gane ɗakin da yake.

Suna ƙoƙarin shiga cikin ɗakin, shi kuma Imran na fitowa, karo suka yi da shi, ya ɗan yi baya yana faɗin "Sorry".

Wani wawan damka Tga ya yi mashi a wuya, rai a ɓace ya ce "Who are you?!".

Allah sarki Imran ya ji shaƙar manya ya kasa magana, sai zare ido yake yi kamar zai mutu, kara matse mashi wuyar da karfi Tga ya yi dan mugunta, kuma abin da yasa ya yi mashi hakan kawai dan ya ganshi ne da kayan Hausawa wato shadda, hakan yasa yasan cewa shi musulmi ne, kuma ko ban faɗa ba kunsan kiyayyar musulmai dake a zuciyarsa.

Da gaske kashe Imran ya yi niyar yi, ya shaƙesa sosai, sai zaro ido waje Imran yake yi yana ƙoƙarin cire hannun Tga ɗin daga wuyarsa, amma ina ya kasa, saboda ba riƙon wasa ya yi mashi ba.

Kamar daga sama suka ga Lion ya damki hannun Tga ɗin, tun bai yi kokarin ɓanɓareta daya wuyar Imran ɗin ba, Tga ya yi maza ya saki Imran ɗin, ya buɗe baki zai yi magana kenan Lion ya kai mashi wani irin wawan duka a gefen kumatunsa, wadda yasa nan take ya zube kasa akan gwiwowinsa jini ya fara zuba daga bakinsa ciki kuma har da hakwaransa guda biyu da suka fita, idan baku mance ba dama Lion yana jin haushin abin da Tga ya yi wa Musharraf, saboda shi ma a yanzu musulmi ne, ba zai so a taɓa musulmai ɗan uwansa ba, to shima da biyu ya yi wa Tga wannan dukar, na daga ɗaya ba ƙari.

Imran na tangal tangal yana kokarin faɗuwa Lion ya riƙoshi tare da ɗan manna shi da jikinsa ya sanya hannu yana ɗan shafa masa wuyar tasa, ya ji wuya sosai.

Dawo da kallonsa kan Tyrone ya yi da wayan nan dara daran blue eyes ɗin nasa, tun bai yi magana ba Tyrone ya wuce da sauri ya koma palo ya ɗauko mashi ruwa mai sanyi ya kawo.

Karɓa ya yi ya buɗe tare da kafa wa Imran ɗin a saitin bakinsa, sosai ya karɓi ruwan ya fara sha.

Bayan ya sha ya samu natsuwa ne Lion ya sake shi tare da wucewa ciki abinsa.

Wucewa Imran ya yi ya fita ya nufi in da za shi yana mai kara waigo Tga, yau ya ci bakar wuya, ya ji kamshin lahira, daga yin karo a rashin sani kawai sai yunkurin kisa, tab lallai wannan akwai bakar zuciya.

Tga dai ya ɗan jima a haka kafin nan ya ɗan wastsake ya yi ƙoƙarin miƙewa, sai da Tyrone ya dafa mashi sannan ya miƙe suka karisa cikin ɗakin.

A balcony suka isko Lion yana tsaye yana kallon gari. Ɗan gefensa suka tsaya har suna haɗa baki wajen cewa "Good evening sir".

Ya ɗauki lokacin da akalla zai kai 10mins kafin ya fara magana gently in a cool voice ba tare da ya kalli in da suke ba "What Imran did to you da har kake kokarin kashe shi?" Murya na sarkewa ya ce "Ya buge ni ne".

"General ina hana ka zalinci amma baka son daina wa ko? I want you to know something, shifa zalunci baya ta ɓa kai mutun ga nasara, I knew ba wai dan ya bugeka ne yasa ka yi kokarin kashe shi ba, kai kasan dalilinka so as from now babu ruwanka da shi, kome ya yi maka ka gaya mani, sannan ka sanar da sojojin nan su canza position daga wajen da suke ɗin nan, su matsa zuwa gaba" To Tga ya amsa da shi sannan ya ciro wayar sa daga aljihunsa, ya kira Captain ɗin da ya jagoranci sojojin da suka zo da su ɗin.

Da sojoji 10 kawai suka zo, saboda sun ce gaba ɗaya state ɗin da James yake a ciki ma su kaɗai sun ishe state ɗin, bare ma iya wajen da yan ta'addan suke zasu yaƙa, hakan yasa suka ɗauki sojoji kaɗan, suma dan sun san ba shakka sai sun yi musayar wuta ne da yan ta'addan shiyasa.

A takaice dai yau su Tga a Naija suka kwana, tun da ya zo ya yi wanka ya cire riga ya fara yawo haka, dama kunsan halinsa baya son zafi, daga shi sai Three quarter yake yawo, haka ya je ya kama wayan nan yan kwacen wayar ya rinƙa azabtar da su, yasa sojan dake girkin nan ya saka mashi wani karfe a wuta ta yi jawur ya rinƙa sanya su suna danme karfen da hannunsu, sun sha azaba sai ihu suke yi, sun gwammaci mutuwar su akan azaban da Tga yake yi masu.

Lion kuwa lokacin sallar mangariba suka fita shi da Imran kamar yadda suka saba zuwa masallaci, Tga bai ma san sun fita ba, yana wajen azabtar da yan kwacen waya, shi kuma Tyrone yana zaune da sojan dake a bakin gate suna hira.

Sai da aka yi sallar isha Lion ya dawo gida, shi kuma Imran ya nemi iznin zuwa gidan Abbi dan ya ji ya ake ciki batun case ɗin Aafia, bai dai gayawa Lion abin da ke faru ba, ya dai ce mashi zai je ya gaishe da uncle ɗin sa, da haka suka yi sallama.

Tga kuma sai da ya tabbatar ya gama gashewa yaran nan hannayensu sannan ya musu azabar da sai da suka fita hayyacin su kafin ya kyalesu zube a wajen, ya shige cikin gida, yana zuwa ya yi wanka ya fito ya ci abinci ya shige ɗakin kasa ya kwanta abinsa ,sai barci dan gobe akwai babban aiki a gabansu.

Shi kuma Tyrone tare da sojoji biyun nan ya kwana, Imran kuma karfe 9 daidai kamar yadda suka yi da Lion haka ya dawo.

Yayi mamakin ganin Lion ya yi barci tun karfe 9, abin ya bashi mamaki sosai, wanka ya yi ya shirya shirin barci ya kwanta a gadonsa.

Har ya fara barci sai kuma ya tuna da abin da ya faru tsakaninsa da Tga ɗazun, cikin sauri ya miƙe ya zo ya sanyawa kofarsa Key abinsa, ya koma ya kwanta ya yi barci.

(Asuba ta gari mutane na!!🥰🤗)

Washigari, cikin zumuɗi Rimsha ta shirya yaya Akil ya kaita school, bayan sun yi girki sun ci sun ƙoshi kenan, sai daɗi take ji.

A ɓangaren Aafia kuwa, lokacin da ta ɗan farfaɗowa ta basu number yaya Irfan dan taci bakar azaba, kuma har lokacin jinine ke zuba daga jikinta, Sani ne ya karɓa ya kira, lokacin da kiran ya shiga Irfan na wanka daddyn Jelly ne ya ɗauki kiran, nan suke gaya mashi su suwaye ga kuma wadda suka ɗauka sannan suna bukatar kuɗin fansa naira million 50, daddy'n jelly bai wani damu sosai ba, tun da ya ji idan sun bada kuɗin za'a sake ta, lafiyarta kawai ya fara tambaya tare da gaya masu su kula da ita, tsabar rashin Imani sai cewa Sani ya yi ai tana nan cikin ƙoshin lafiya da aminci, daddyn Jelly bai yarda ba ya ce abata waya, ba musu suka bata wayar.

Muryar ta ya dashe sosai saboda kuka da ta rinƙa yi ga kuma bakar azaba, da kyar ta iya fara magana, ba karamin tashin hankali daddyn Jelly ya shiga ba jin yadda muryar ta ya yi, rai a matukar ɓace ya ce "Me suka yi maki? Sun dake ki ne?" Cikin kuka take faɗin "Mutuwa zan yi yaya Irfan, zan mutu!" A tunaninta Irfan ne, bala'i yasa bata iya gane murya ba, nan take daddyn Jelly ya fara hawaye yana faɗin "Ba zaki mutu ba zaki dawo yau ɗin nan zaki dawo gare mu".

A haka Irfan ya fito ya same shi, cikin sauri ya ce "Bappa Maik me yake faruwa ne?" Ba ɓoye ɓoye daddyn Jelly ya gaya mashi abin da yake faruwa, karɓar wayar ya yi suka fara magana da Sani, nan ya ce Millon 50 ya yi yawa basu da shi amma za su bada millon 3, ƙoƙarin hana shi daddyn jelly ya yi dan yana tsoron kada suce za su nemi ragi suje su kashe Aafia a banza, gara kawai a basu abin da suke so.

Da Irfan ya ga daddyn Jelly zai ja masu bala'i millon 50 sai ka ce hauka sai ya fice daga Palon ya shiga ɗakinsa ya rufo kofa ya sa key, sai bugawa daddyn Jelly yake hankali a tashe, kin kulashi Irfan ya yi ya cigaba da magana da su.

Daga karshe dai suka shirya akan millon 5 suka ce anjima da daddare ya kawo kuɗin dajin gabashin birnin gwari, to Irfan ya ce mashi tare da ce mashi ba ita kaɗai bace su biyu ne aka ce sun fita, da yake Sani ya san abin da ya yi mata, sai ya ce e su biyun dukka za'a fito maka da su bakin dajin ka ɗauke su, daga nan suka yi sallama, Irfan ya zauna yana tunanin me ya fitar da A'afia har suka kamata, ai na ma suka ganta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun , shi kuma daddy jelly yana tsaye a bakin kofa yana bugawa.

A ɓangaren su Tga kuwa, tun karfe 7 suka shirya tsab cikin fararen kaya, Lion ya sanyawa Tyrone wata yar karamar camera a botirin gaban rigarsa, dan ya samu damar ganin duk abin da zai faru idan suka je wajen.

Karfe 8 daidai suka nufi wajen da James yake, a cikin garin Kadunar ne, sai dai kwai ɗan nisa tsakaninsu, kuma cikin daji ne wajen sosai.

Diran mikiya suka yi wa wayan nan yan ta'addan, kafin sun farga sun musu rubdugu, kashe su kawai suke yi ba wasa, lokacin da yan ta'addan suka farga suka fara musayar wuta, sun yi nasaran kashe masu soja ɗaya, amma su kuma sun kashe su ba kaɗan ba, yan ta'addan suna da yawa, hakan yasa Tga ya yi amsani da kananan boma boman nan ya tashi wasu daga cikin ɓangarori na gidan, da kyar suka samu damar kutsawa izuwa cikin gidan.

Suna shiga asalin ɗakin da James yake suka ja burki babu shiri, duk abin da suke yi Lion na kwance saman bed nasa yana kallonsu.

Yan ta'addan sun ɗaure James a saman wata kujera a tsakiyar ɗakin, kamar ya mutu domin baya numfashi, ga kuma ogansu nan yan ta'addan yana zaune a saman kujera daga can gefe da James ɗin, fuskarsa ogan nasu sanye da mask baki, manya-manyan jiga-jigan yan ta'addan ne kusan su goma masu kirar basawa, suna kewaye da James ɗin a tsaitsaye, ɗaya daga cikin su ya sanya mashi wuƙa a wuya duk da ma baya numfashin, ɗaya kuma yana ruƙe da camera, ya yin da sojojin su Tga kuma suke waje suke ɓarin wuta.

Buga bed Lion ya yi ya furta kash da ɗan karfi, kasa-kasa ya fara yi wa Tyrone magana, da yake ya sanya Bluetooth headphones a kunnensa hakan yasa yake jin maganar da Lion ɗin yake faɗe dan sun yi connecting.

"Tyrone kada ka bari su sanyawa James Camera, suna yin yunkurin hakan ka harbi James ɗin!" Jinjina kai Tyrone ɗin ya yi alamar to.

Ai kuwa kamar sun ji me Lion ya ce sai suka fara ƙoƙarin kunna cameran ɗaya daga cikinsu yana faɗin, "Ka kunna mu nunawa duniya yadda zamu yi mashi yankar rago, mu za'a taɓa? Dole su ɗanɗani zafin kuna".

"Tyrone shoot James on his chest now" shine abin da Lion ya faɗa, kamar da gaske haka Tyrone ya ɗaga gun ɗin hannunsa ya sai ta James ɗin, nan take kuma ya ji ba zai iya ba.

"I can't sir I can't shoot James i can't!!" Ya kai karshen maganar tare da sauke gun ɗin nasa daga saita James ɗin da ya yi yana girgiza kai kamar zai yi kuka.

"Tyrone i said shoot him, idan baka harbe shi ba suka sanya mashi camera to zamu rasa shi har abada, domin kuwa CIA za su fasashi, ka harbe shi a chest nasa ta gefe wajen ɗan sama kusa da shoulder sa".

Kasawa Tyrone ya yi ya fara hawaye dan ba zai iya harbin James ba har ga Allah, dai dai lokacin kuma suka datse network dake a wajen.

A zafafe Lion ya diro kasa daga saman bed nasa, har wani tsuma jikinsa yake yi, dressing room nasa ya shiga, cikin yan mintocin da ba su fi 5 ba sai ga shi ya fito sanye da long coat da kuma wata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login