Showing 105001 words to 108000 words out of 355604 words
Ayla hawaye.
"Allah sarki yanzu mama da baba suna can suna haukar neman ki" Ahmad ya faɗa yana kokarin ɓoye hawayen dake ƙoƙarin zubo masa. Allah sarki bai ma san Ayla kam bata da baban ba, maman nata ma bata da tabbacin tana raye ko ta mutu, Ayla bata ba shi labarin asalin taba, abin da yasa bata yi hakan ba kuma, saboda Rimsha ta mata faɗa ranar da ta gayawa su Iya asalin wace ce ita, Rimsha ta mata faɗa sosai a kan ta koyi ɓoye sirrinta, ba kowa bane daga haɗu zata gaya mishi ita wace ce, dan ba kowa ne zai riƙe ka tsakani da Allah ba, shiyasa yanzu bata gayawa Ahmad asalin tarihinta ba, ta dai ce masa aikan ta mamanta ta yi, ta fito kenan yan Daular Mutuwa suka sace ta.
Sun ɗan jima suna jimamin labarin da Ayla ta bada, kafin nan Ahmad ya ɗago ya kalli Rimsha "Ke kuma fa Queen of beauty? Ya akayi kika bar gida?" Haka ita ma ta datsi labarinta daga wajen da taje sayo ashana aka sace ta, daga nan ta bashi story har zuwa yau, bata ɓoye masa abin da ya sanya suka baro gidan su kausar ba, ta gaya mishi komai, dan tasan idan bata gaya mishi ba ma, zai tambayi me yasa suka baro gidan su Kausar ɗin, shiyasa ta gaya mishin kawai.
Sosai ya tausaya musu, kuma ya ji kunan rai sosai, na fyaɗe da Jami'u ya yi yunkurin yiwa Rimsha, abin ya ɓata masa rai sosai.
Shiru suka ɗan yi na ɗan lokaci sannan Ahmad ya ce "Ni ma ba ɗan nan bane, a Abuja iyaye na suke, karatu na ke yi a nan, ko in ce na kammala akwai abin da nazo gyarawa a nan ne, zan ɗauki sawon sati biyu kafin na kowa Abuja, amma ku ba zan ajiye ku a nan har tsawon wannan lokacin ba, gara ku koma gida dan nasan iyayen ku suna tsaka mai wuya, to gara ku koma ko zasu samu kwanciyar hankali, nima dai dole ce ta kawo ni nan, domin ba a nan kasar ma na yi karatu na ba, kawai wani course ne ya burgeni shine na nema, da farko Ahmadu Bello university na zaɓa daga baya na fasa na ce bari na zo University of Ilorin, ashe rabon na taimakawa rayuwar ku ne, ina matikar farinciki da hakan, yanzu ku gaya min yaushe kuke son komawa gida? Kuma da me kuke son komawa jirgi ko mota?".
Bayin Allah har suna haɗa baki wajen cewa "Yau muke son komawa, kuma ko da me aka mai damu mun gode". Murmushi ya yi yana kallon yadda Rimsha ta yi maganar cike da zumuɗi har kamar zata tashi daga mazauninta dan murna.
"Queen of beauty ai yanzu yamma ta yi, sai dai zuwa gobe da safe, zan yi waya da daddyna ya nema muku alfarma ku samu jirgin safe".
Kamar abin haɗin baki, a tare suka zamo kasa daga mazaunin su, suka zube gwiwowinsu a kasa, suna hawaye suka fara zuba masa godiya. Fuskarsa ɗauke da murmushin tsantsan farinciki ya ce "Ya isa haka kukan, ina jin ku tamkar yan uwana ne ku, musamman Ayla yadda ta yi kama da daddyna ji nake yi kamar kanwata Anisa, ba dan na san cewa Anisa na wajen mum ɗin ta ba wlh da na riƙe Ayla nace Anisa ce, dan sun yi kama sosai, ita ma Anisa da daddy take kama, bari ma ku ga hotonta, amma dai Anisa zata fiki shekaru dan yanzu haka tana 200 level a school, kin ga kuwa zata girme miƙi" ya kai karshen maganar tare da fito da hoton Anisa a wayar hannunsa, sannan ya miƙa musu wayar.
Karɓar wayar suka yi suna kallon matashiyar budurwa dake jikin hoton, tabbas kamaninta ɗaya da Ayla, ba abin da ya raba su, sai dai ita cikakkiyar budurwa ce ba yarinya kamar Ayla ba ce, zata iya kai 21 years.
Rimsha ce ta ɗago kai tana faɗin "Allah ta yi kama da Ayla sosai" "Ni kuma fa Queen of beauty? ban yi kama da ita ba ne" ya yi maganar yana tsare ta da ido. Kawar da kallonta daga kanshi ta yi tare da sunkuyar da kai kasa ta ce "Gaskiya muryan kane ya yi iri ɗaya dana Ayla, amma baku kama Sosai, ta fi kama da Aunty Anisa" murmushi ya yi, a zuciyarsa yana faɗin "tabbas Rimsha ta yi gaskiya shi kan shi lokacin da ya fara jin muryar Ayla da tasa muryar ta masa kama, sai daga baya daya saurara sosai sai ya ji tafi kama dana daddynsu.
Miƙa masa wayarsa Ayla ta yi, karɓa ya yi ya ajiye a gefensa yana faɗin "To yanzu idan kuka koma gida, idan na dawo Abuja ina son ganin ku a ina kenan zan ganku?" Cikin sauri Rimsha ta ce masa "Ni ai Katsina nake ba Abuja ba, ita kuma Ayla Kaduna take"
Zaro ido ya yi kafin ya ce "Kai to kenan ku da kanku ma idan kuka rabu baku da tabbacin zaku sake haɗu ko ba zaku sake haɗuwa ba, tun da baku san in da gidan juna yake ba, kuma bama gari ɗaya kuke ba".
Jin wannan magana tasa ta sanya gaba ɗayan su idanuwansu suka cika da ruwan hawaye, jikinsu ya yi muguwar sanyi, ɗagowa Rimsha ta yi tana kallon Ayla, a yayin da ita ma Ayla kallonta take yi, abin gwanin ban tausayi, kenan yanzu idan suka bar nan sun rabu kenan? A tare suka gefawa kansu wannan tambayar.
Ganin haka yasa Ahmad ya yi murmushi sannan ya ce "Ai ko dan ma wannan zumunci naku ya ɗore dole na saya muku waya, domin ku rinƙa kiran juna kuna gaisawa, sannan nima idan zan zo wajen ku na kira ku a waya ku bani address, kuma idan ɗaya na son zuwa wajen ɗaya kunga zaku yi ta waya kuna yiwa juna kwatance har ku samu ganawa".
Tsabar murna ji suka yi kamar su miƙe su rungume shi saboda daɗi, shi kuma abu uku ne yasa ya yi musu wannan babbar taimako, na farko saboda Allah, na biyu saboda ya kamu da matsanancin son Rimsha lokaci guda, na uku kuma yana jin Ayla tamkar kanwarsa, tamkar yar uwarsa ta jini, wannan dalili ya sa ya tsaya musu.
After some hours👌
Bayan sun yi sallar mangariba. Da sallama Ahmad ya shigo cikin ɗakin, ya dawo daga masallaci. Cike da kulawa ya ce "Ku shirya muje cikin gari mu sayi abinci daga nan sai na saya muku waya, sannan kuma daddy ya gaya mini jirgin Kaduna zaku hau, Queen of beauty, idan kin sauƙa a Kaduna zaki iya zuwa park ki shiga motar Katsina?" Shiru ta yi tana tunani ita da bata san ko ina ba, shima Katsinar tun da suka koma sau ɗaya ta fita, sai kuma ranar da aka sace ta shine rana ta biyu.
Ganin ta yi shiru yasa ya ce "To idan kuka sauƙa a airport zamu yi magana, zan kira ki a waya sai na gaya miki in da zaki je, sai ki tari mashin zuwa wajen, idan kin je wajen sai mu sake yin waya, daga nan zan gaya miki in da motocin Katsina suke, idan kin je wajen sai ki haɗa ni da driver a waya zamu yi magana da shi, dan nasan wannan shirun da kika yi ya tabbatar baki san ko'ina ba a Kaduna, bayan haka kuma dama nasan da wuya ki san wani wajen tun da ba garin ku bane".
Sunkuyar da kai kasa kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba.
"Queen of beauty kuma Queen of kunya, to dai yanzu ku shirya mu je mu dawo da wuri dan kuzo ku yi barci da wuri, saboda jirgin karfe 7 zaku hau". Yana kai karshen maganar ya juya ya fice daga ɗakin, dan ya basu damar shiryawa a nutse.
Hijabi kawai suka ɗaura saman Abayar jikin su, sannan suka sanya takalmar Kausar da suka zo da shi, domin a kayan da ya sayo musu babu takalmi. Har sun kai bakin kofar ɗakin zasu fita, sai Rimsha ta dawo da sauri ta ɗauki perfume na shi dake saman drawer mirror ta fesa, dariya Ayla ta yi, kasa kasa ta ce "Ɓarauniya, to dai shi turare ba'a satarsa". Wucewa wajen switch na ɗakin ta yi, ta kashe wutar tana faɗin "Anyi ɗin idan mutun shima yana da ra'ayi ba sai ya yi satar ba". Sai faman guntse dariya Ayla take yi ta ce "Allah yasa ma turaren makale mata ne, ki makale masa ki ce ba zaki koma ba".
A kule Rimsha ta ce "Bakar muguwa, to dai nariga ki na ce Allah, kuma ta Allah ba ta mutun ba!" tuntsurewa da dariya Ayla ta yi, daman dariyar ya ciwota sosai, wato ita dai Rimsha duk wani zance da zai kawo mata zancen kada ta koma gida bata son shi ko da wasa.
Haka suka fito waje sai faman guntse dariya Ayla ke yi, ita kuma Rimsha ta sha kunu ta murtuke kamar hadari fuskar nan ta zama, dama Rimsha ba baya ba wajen iya tsare gida, idan aka ɓata mata rai.
Tsaye suka same shi yana kallon gari ya juya musu baya. Sallama suka mashi, juyowa ya yi yana kallonsu da yake hotel ɗin akwai wuta, an tada gen, hakan ya bashi damar kallonsu sosai, Rimsha Queen of beauty tamkar ka sace ta ka gudu da ita saboda kyau, hijabin ya mata kyau sai dai bai karisa kai har kasa ba.
Sai murmushi yake yi ya ce "Muje ko?" Ya yi maganar yana nuna musu hanya, gaba suka yi ya bi bayan su, yana kallon yadda suke tafiya a nutse ɗaiɗai abin su, ba hayaniya ba hargaga kamar yan matan kauye, a nutse suke. Wani azababben son Rimsha ne ke kara ninkuwa masa a zuciyarsa, sai wani murmushi yake yi shi kaɗai, kamar ba lafiya ba.
Ya kasa daina kallon su har suka isa wajen mota, abin mamaki sai yaga dukkansu sun shiga gidan baya, ɗan ɗaure fuska ya yi kafin ya ce "Ni driver ku ne? Ku fito ku dawo gaba". Ba dan sun so ba suka fito suka dawo gidan gaba, sannan shima ya shiga ya tada motar suka bar wajen.
Challenge suka fara nufa, wato kasuwar wayoyi. Wayoyine iri daban-daban a wajen, gasu nan a zube kamar kyauta ake rabawa.
Wani katafaren shago suka shiga, kun san yarabawa da son kyawawan mata, duk in da Rimsha ta wuce sai sun kalleta sun sake kallonta, da yake ko ina a wajen akwai hasken wuta sosai, saboda business ɗin su.
Wani irin bakin ciki Ahmad ya ji, haushi ya kama shi yadda suke ta kallon Rimsha, ji ya yi dama bai zo da su ba, kuma yanzu in da suka yi parking na motar su akwai ɗan nisa, ga shi yana son su yi sauri dan su koma su yi sallar isha, haka ya hakura ya danne suka shiga cikin shagon.
Wayoyi yasa aka kawo musu kala, huɗu ya ce su saɓi dai ɗaya, duk ka kuma Samsung ne masu tsada, A72 ne da A 12 sai A10 guda biyu.
Kallon su ya yi ya ce "Ku zaɓi wanda kuke so a ciki" Mai shagon duk da baya jin Hausa ya fahinci zaɓi Ahmad ya basu ai kuwa ya yi maza ta cap ke da cewa "Wannan kyakkyawar yarinyar da A72 ta dace" ya yi maganar cikin harshen turanci ba yarabanci ba, ai kuwa Ahmad ya zo har wuya, cikin ɓacin rai ya ce ba za su sayi wayar a nan shagon ba sun fasa, sosai mai shagon ya rinƙa ba shi hakuri, amma ina ya murje idanuwansa ya ce ba za su saya ba.
Haka suka wuce zuwa wani shagon, a nan ya sai musu A12 guda biyu iri ɗaya har color ma ɗaya, sannan suka fito, ya saya musu sim card, sai ya wuce da su wani katon super market dake gaba da challenge ɗin kaɗan.
Ko da suka je wannan super market ɗin kuwa, saboda karfin hali irin na Ahmad har da cewa su zauna a mota su jira shi, dan tsabar kishi, haka suka zauna ya rufe su tare da kunna musu Ac, ya wuce ya je ya yi sayayyar da zai yi ya dawo suka wuce Item 7, a nan suka sayi abinci suka dawo gida.
Lokacin da suka dawo karfe 9:10. A hanzarce Rimsha ta yi alwala ta gaba tar da sallar isha, shi kuma Ahmad suna dawowa da ya rako su ɗaki ya juya ya fice, ita kuma Ayla saman drawer ta zauna tana kallon Rimsha.
Bayan ta idar da sallah ne, suka jawo ledar abin cin da ya basu kafin ya fita da nashi, sosai suka ci abincin, sannan suka haɗa da fruits da ya sawo ɗazun kafin su fita, dama kafin ya fita ɗakin sai da ya ce musu su sha fruits ɗin su ya sayawa.
Bayan sun gama, sun tattare komai tsab, sai suka yi kwanciyar su a kasa wajen da suka kwanta ɗazun.
Can kuma kamar wayan da a ka tsikara, haka suka ta shi suka kunna kallon a Tv dake ɗakin, suka kama tashar zee wold.
Sai karfe 10 daidai Ahmad ya dawo hannunsa ɗauke da kananan trolley guda biyu, kusa da nashi trolley ya ajiye sannan ya zauna saman dadduma suka ɗan yi hira kaɗan, zuwa karfe 10:30 ya ta shi ya sanya musu wayoyin su a charji bayan ya sanya musu sim card da ya sai musu, saboda suna sauri gobe zasu tafi hakan yasa ya saya musu sim mai register amma ya ce musu idan suka koma su yi register wani sim ɗin da kan su. To suka amsa mashi da shi, sannan ya musu sallama ya ce su rufe kofar da key ta ciki su kwanta su yi barci da asuba zai zo ya tashe su.
Ba karamin daɗi suka ji ba, dama suna ta tunanin ya za su yi su kwana da shi ɗaki ɗaya, ashe dai yana da hankali sosai. Yana fita Ayla ta haye gado ta baje kafafu tana faɗin ",Yau dai ba gadon Kausar zamu kwana ba". Ita kuma Rismha wuce wa ta yi ta rufe musu kofar ɗakin da key sannan ta shiga toilet dan yin wanka.
Bayan ta yi wanka ta fito ta shirya cikin ɗayar abayar da ta rage a ledar da ya kawo musu ɗazun, bayan ta gama ta haye gado tana faɗin "Ayla ki je ki yi wanka mana". Ina Ayla barcin gajiya ya ɗauke ta baiwar Allah, yau dai sun kwana cikin farinciki, ita ma Rismha tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Amma kafin ta yi barci sai da ta ɗan yi tunani a kan ya za'ayi su hau jirgi ba passport ba komai, ko dai private jet ne, ko kuma sai da safe idan sun je zai musu passport ɗin. Da wannan tunani a ranta ta yi barci.
(Uh su Rimsha yau ana busy kuma ana murnan komawa gida, ba'ayi tunanin masoyi GAR ba🤣 an samu freedom)
Asuba ta gari
Nima kuma na haɗa kayana zuwa gidan Abba, sai mun haɗu gobe dan jin yadda zata kaya a gidan Abba. Na barku lafiya da yar dan mai duka.
💖💖TRIPLET'S💖💖
E33-34
💖💖GIDAN ABBA💖💖
Yau ma kamar jiya Umaisha ta yi wuni mai cike da annashuwa da farinciki, sakamakon Rufee ta sake dawowa, tun karfe 7 na safe ta dawowa gidan, yau ko shara Umaisha ba ta yi bare kuma a kai ga su gyaran ɗakin Abba da Ammie.
Ita kuwa Ammie kwata-kwata bata shiga harkar Umaisha ba, kamar bata nan a gidan ita ma, ta yi shiru a ɗakin ta, saboda tana tsoron bala'i Rufee.
(Toh fa wannan shine gaba ma da gaban ta)
Su Imran kuwa, wannan zuwa Kano da suka yi, sun sallami su Zuwaira masu aikin gidan su Jelly, Imran ya ce musu idan komai ya daidai ta zai zo har kauye da kansa ya ɗauko su, sannan ya ɗauki dollyn Jelly dan su dawo da ita Kaduna, da suka ta shi tafiya, sun rufe ko'ina na gidan, duk wani kayan wuta dake jone a sucket sun cire shi, daga karshema Akil ya kashe wutar gidan gaba ɗaya suka wuce suka kama hanyar Kaduna rai a ɓace domin har wa yau ba su yi nasara ba, amma sun bar baba mai gadi a gidan basu sallame shi ba, sun ce ya cigaba da kula da gidan.
Shi kuma baban Muneer yana yawan zuwa neman daddyn Jelly sai dai Allah bai taɓa haɗa shi da su Imran ba, ba'a kwana biyu bai zo gidan ba, sai dai su Zuwaira su ce mashi daddyn Jelly ya yi tafiya, ya ci alwashin nan da wata ɗaya in har daddyn jelly bai bayyana ba, to zai saki wannan video wa duniya, a cewar sa daddyn Jelly ai ɓuya ya yi, domin Company sa na aiki, bai san cewa Imran da Irfar ke tafiyar da company yanzu ba, kuma yana zuwa har company ya tambayi Engineer Muhammad Imam shin ko Maik ya dawo, kullum amsa ɗaya yake ba shi shine a'a bai dawo ba, duk kuma mafiyawancin lokutan da baban Muneer ke zuwa, su Irfan sun bar company, kuma a zahirin gaskiya daddy'n Jelly bai gayawa kowa abin da ke tsakanin shi da baban Muneer ba, a cewar sa idan ya yi hakan ya tonawa kan shi da kan shi asiri ne, shiyasa ya rufe maganar kawai, ya yi wa su Imran karya.
Sai Misalin karfe 6 na yamma su Akil suka shigo gida, gaba ɗaya a gajiye suke, sai wani ɗaure fuska Akil yake yi, to da yake shi Akil part na shi a cikin nasu Ammie yake, shi kuma Imran daga waje harabar gidar part nasa yake ta gefe, bai haɗu da nasu ba, hakan yasa suka rabu da Imran a harabar gidan, Imran ya wuce part nasa hannunsa riƙe da dollyn Jelly, duk ta rame, saboda bata cin abinci sai su Zuwaira sun mata ɗure.
Shi kuma Akil ya nufi cikin gida. Yana shigowa babban palon su, ita kuma Ammie tana saukowa daga sama. Sauri sauri ya yi mata sannu da gida zai wuce part nasa, dan a gajiye yake sosai.
"Ina kuke yawan zuwa ne Akil?" Ammie ce ta jefa masa