Showing 198001 words to 201000 words out of 355604 words
Ɓuye kanta ta yi a jikinsa tana dariya.
Sakinta ya yi yana faɗin "Tom ki cewa Sadiya daga yau ta rinƙa barin abincin Irfan zai zo ya rinƙa ɗauka, bana son ki sake zuwa nan, ba wai dan bana son ganin ki bane, a'a kawai dai ki zauna a part naku zan rinƙa zuwa mu yi hira a can, yanzu dai tashi ki je, an jima idan na dawo ina zuwa mu yi hira" ya kai karshen maganar tare da manna mata kiss a goshi sannan ya ce "I love you".
Shiru bata bashi amsa ba sai ma kokarin mikewa da ta yi daga jikin nasa, ɗan riƙo hannunta ya yi yana faɗin "Baki bani amsa ba, na ce maki I love you" "Ni ban san me zan ce ba daddy" hannu ya kai ya matse mata baki yana faɗin "Idan kika sake cewa daddy sai na...." Bai karisar da maganar ba ya yi shiru tare da sakinta ya miƙe ya nufi waje yana faɗin "Gobe dai zaki fara zuwa school" daga nan ya fice abinsa, ita kuma tattare kayan ta yi ta bawa Irfan kulan abincin da miya sai plate ɗaya da spoon ɗaya, ta ɗauki wanda suka ci zuwa cikin gida.
Yadda ta bar aunty haka ta shigo ta same ta, Kitchen ta shigar da kayan sannan ta zo ta zauna tana faɗin "Aunty daddy ya ce gobe zan fara zuwa school" sai murmushi Aunty take yi ta yi mata fatan alkhari daga nan suka shiga duniyar hira tana bata labarin yadda zata rinƙa yi wa daddyn Jelly da shawarin da suka dace.
A wannan Hali Abbi ya dawo ya same su, sannu da zuwa suka yi mashi, abin mamaki sai suka ga ya amsa da fara'a ya kuma ɗaura da cewa "Ina A'afia? Akil ya kirani a waya ɗazun da safe akan ta wuce ta koma kafin ya zo ya yi mata ɗan banzan duka".
Cike da murnan Abbi ya sauƙo Aunty ta ce "A'afia ai bata dawo nan gidan ba, tun fa kwana huɗu da suka wuce da ta tafi gidan su Umaisha akan za su yi kwana ɗaya sai suka yi biyu, to ni daga ranar ma dana tambaya sai Irfan ya ce mani ta koma gidan da zama" wucewa Abbi ya yi ya nufi sama yana faɗin "E a gidan take dama, ina ga yaune ta fita ta ce masu zata zo nan, shine Akil ɗin ya ƙirani akan ta dawo, to na kira layinta ma a kashe, yanzu haka bai wuce tana tare da su Rufaidah bane, amma dai bari na kira Irfan ya je gidan su Rufaidah ɗin ya ɗauko ta ya mai da ta gidan yayan". Da zumuɗi Aunty ta amsa da to sannan ta tashi ta bi bayansa suka shige ɗaki a tare.
💖💖Star Lady....✍️✍️💖💖
Ita kuma Ayla ta gyara kwanciyarta a saman sofa tana murmushi, idan ta tuna cewa daddynta yana sonta, kuma ya ce zai aureta sai ta ji wani mugun daɗi, baiwar Allah ita ma tana matukar son shi sosai da sosai.
(Uhm soyaya kenan, soyayya taburmar kaya, idan ka iya zama ka ji daɗi, idan kuma baka iya ba....😭💔)
A ɓangaren Rimsha kuwa.
Bayan Akil ya ɗaukota da ga asibiti tare da saya mata magungunan da ake buƙata. Suna zuwa gida bayan sun shiga palon Imran sun zauna ne, ya tambayeta ko akwai wani abin da take so, nan ta ce mashi school take son komawa, sosai ya ji daɗi sannan ya tambayi wani school take so, kuma a class nawa ta tsaya,. "Na gama primary 6 zan shiga Jss 1" ta bashi amsa, ba ɓata lokaci ya mata alkawarin nan da gobe zai gama mata komai domin harka ce ta kuɗi to kuma akwai su sosy, Akila bata san wainar da ake toyawa ba, dan ta shige cikin gida yin wanka, hakan yasa bata san me ake ciki ba, ta gama cin buri zata tafi Usa karatu, ga shi Rimsha ta ɓata mata komai bata da labari. Daga nan ya tambaye ta ko akwai wani abin da take so bayan school, a'a ta ce mashi sannan ya miƙe ya fita yana faɗin, anjima da daddare zai dawo ya bata magani ta sha a gabansa, to ta amsa mashi da shi.
Yana fita ya kira Imran a waya ya sanar mashi da duk yadda suka yi, to Imran ya ce sannan ya ce ya amince ya yi mata komai na school ɗin kamar yadda ta buƙata, ya ɗaura da sanya mashi albarka, sannan suka yi sallama, sosai Imran ya samu kwanciyar hankali, yanzu ya samu natsuwar zai iya zama da Lion ba tare da farkaba ko tunanin wani hali Rimsha ke a ciki ba, saboda Akil na kula da ita yadda ya dace.
Ita kuma Rimsha Akil na fita, ta miƙe zuwa cikin bedroom nata, wanka ta yi sannan ta shirya cikin riga da wando, wandon jeans irin palazon nan, sai riga T-shirt, da yake yau garin akwai iska mai sanyi sosai, sai ta ɗaura boyfriend jacket a saman kayan nata, ta gyara kanta ta fito zuwa kitchen, sai tashin kamshi take yi.
Bayan ɗan wani lokaci Akila ta shigo suka kama aiki tare. Sai karfe 6 suka gama, wanka kowacen su ta yi suka sake shiri cikin dogon riga abaya suka nufi palo suka zauna.
Zaman su ke da wuya Ahmad ya fara kiran layin Rimsha, ɗauka ta yi suka fara hira kenan sai ga Akil da Umaisha sun shigo, bata sallami Ahmad ɗin ba ta katse kiran dan kunyar yaya Akil take ji.
Zama suka yi suka fara hira kamar Kullun.
"Yaya Akil dan Allah ina son ka kai mu wajen gyaran gashi da kuma kunshi kaga nawa ya fara gogewa, kuma kaina ya ɗan yi datti" cewar Rimsha sarkin tsabta da son gyara kenan
Ba musu yace gobe da yamma za su je ya kai ta, nan fa Umaisha ta ɓata rai dan ta jima tana ce mashi ya kai ta gyaran gashi sai dai ya ce suje toilet ya wanke mata domin yana da kishi bai yarda wata ta kalle mashi gashin sa ba, haka zai tasa ta gaba ya wanke mata da kansa, ya gyara mata har da shafa mayuka, amma yanzu rana tsaka ya ce zai kai Rimsha gyaran gashi, wlh ba zai yiwu ba. Ita ma Akila wage baki ta yi tana murmushi ta ce ita ma zata je, to ya amsa da shi, ita kuma Umaisha da ta ce zata je sai ya ce a'a bai yarda ba, kuka ta sa mashi tare da tashi ta fice daga cikin palon.
Miƙewa shima ya yi ya nufi waje yana yi wa su Rimsha sallamar sai da safe dan ba zai dawo nan ba tun da Imran baya nan, sannan ya ce Akila ta kawo masu abinci ɗakin sa, to suka amsa mashi da shi.
Har ya kai bakin kofa kuma sai ya juyo ya kalli Rimsha ya ce "Rimsha anjima idan anyi sallar isha kina da baƙo" zaro ido waje ta yi tare da dafe kirji ta ce "Yaya Akil baƙo kuma?" Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "E baƙo, yaya Imran ya kira ni a waya ina gab da shigowa nan, ya ce mani Dr Nawid zai zo ku gaisa" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palo.
Kallon Akila ta yi ta ce "Aunty Akila kina ji dai ko?" Dariya Akila ta yi tana faɗin "To ni dai gaskiya ba zan yarda wani ya shiga gonar yaya Ahmad ba, dole na gayawa yaya Imran, yaya Ahmad ya riga kowa".
Miƙewa tayi daga saman kujerarta, ta dawo kusa da Akilar ta zauna. Hannayenta ta riƙo cikin nata, ta fara Magana cikin murya kamar wadda zata yi kuka "Aunty Akila ban taɓa haɗuwa da wata da nake bala'in kauna kamar ki ba, ko Jehan da take yar uwata ban yarda na gaya mata wani hali nake ciki ba, saboda ita ba kamar sauran mutane take ba, tana da zafi, ga faɗa, kuma bata tsayawa ta fahinci mutun take yanke mashi hukunci, idan bata son abu to ko mutuwa zaka yi ba zata taɓa fahimtar yadda kake ji akan wannan abin ba, hakan ce ta faru tsakani na da ita yasa ba zan iya gaya mata halin da nake a ciki ba, dan ba zata ɗauka ba, da ace tana nan yanzu ko me zai faru ba zan iya gaya mata ba, dan zata iya naɗa mani duka akan hakan ma.
Zuba mata ido Akila ta yi tana kallon yadda take maganar, daga muryarta har fuskarta duk shaƙe suke da matsananciyar damuwa. Ba ɓoye-ɓoye ba komai Rimsha ta bata labarin halin da take ciki da asalinta da komai da komai bata ɓoye mata ba, daga karshe ta rufe da ɗan jan rigarta kasa ta nuna mata zanen sunan Lion dake a saman kirjin tata.
Dogon numfashi Akila taja tana goge hawayen da suke gangaro mata a fuskarta, tabbas ta tausayawa Rimsha aihun ba kaɗan ba, kankame hannayenta ta yi a cikin tata, cikin shessheƙar kuka ta fara magana
"Gaskiya Rimsha akwai ciwo sosai a cikin rayuwarki, amma da izinin Allah tun da har kika yi istihara kuma kika yi sallar dare kika roƙi Allah ya zaɓa maki abin da ya fi zama maki alkhari, still baki daina mafarkin Lion ba kuma baki daina son shi ba, sai ma karuwa da son nashi ya yi a zuciyarki, to da izinin Allah shine zaɓin da Allah ya yi maki, kuma ba a banza Allah ya kawo shi Nigeria ba, In Sha Allah kafin ya tafi zai so ki, duk da yaya Imran ya gaya mani ya bar gidan nan, amma In Sha Allah zaku haɗu kuma zai so ki har ma ya zama mijinki, zan taya ki da addu'a kuma ki yi hakuri zan gayawa yaya Imran irin dagon soyayyar Lion da kika yi a zuciyarki, wata kila ya iya taimaka maki ta wani wajen, amma gaskiya sai kin jure, domin ganin Lion a Tv ma ni tsoro yake bani bare kuma a zahiri, ai jiya wlh ban san shi bane da na sume a nan, Allah Ubangijin ya kawo maki komai da sauƙi, yaya Imran ya gaya mani cewa ma ya yi tafiya zuwa Abuja, In Sha Allah yana dawowa zan gaya mashi batun soyayyar naki nasan zai taimaka maki, kiyi hakuri amma dai kin ɗauki dala ba gammo gaskiya".
"A'a Aunty Akila dan Allah kada ki gayawa yaya Imran ɗin kin ji? Dan Allah ki rufa mani asiri, saboda fa nasan da cewa idan na gaya maki ba zaki gayawa kowa bane yasa na gaya maki, dan Allah kada ki faɗa kin ji? kuma wlh ni ba son GAR nake yi ba, na gaya maki kawai yana burgeni ne, amma kinsan kema GAR ya fi karfi na, ina zai kai ni, ba ajinsa bace, ni kam kawai yana burgeni ne, a dama ji nake zan daina kallon videos nasa, amma dana ga cewa shi musulmi ne, sai nace to zan cigaba da kallon videos nasa ɗin, amma ba da nufin soyayya ba" ta kai karshen maganar cikin raunataciyar murya.
Jinjina kai Akila ta yi tana faɗin "To shikenan tun da baki so ba zan gaya ba, In Sha Allah zan rufe maki siririnki kin ji?" Gyaɗa mata kai ta yi daga nan suka tashi suka nufi cikin ɗaki dan gabatar da sallar mangariba, dan tun ɗazun aka yi sallah su suna zaune suna hira ga shi har isha ta kusa.
To bari mu koma wani ɓangaren tun da sallah za su yi.
💖💖Washington DC💖💖
Musharraf yana a wajen har wuraren karfe 4 na yamma, ya kasa motsawa, bawan Allah bai saba ba, kafafunsa duk sun kumbura sun yi jawur da su, har kwallah sai da ya yi.
Misali karfe 4:30 Michael ya dawo daga school, kai tsaye part nasa ya nufa, a gajiye ya dawo ga shi kuma lecture biyu zai rinƙa karɓa, dan abin ya zo mashi da sauƙi, idan ya yi karatu a school daddy kuma zai rinƙa koya mashi nasa a gida tun da shima surgical doctor zai karanta irin daddy ɗin, shiyasa abubuwa suka yi mashi yawa, idan ya dawo sai su zauna da daddy yana nuna mashi wasu abubuwa dan komai ya tafi daidai.
Wanka ya yi a gurguje ya shirya cikin wando three quarter fari tas da kuma riga mai karamar hannu launin sky blue, bai nemi Musharraf ba saboda yana tunanin yana barci ne, alwala yayi ya gabatar da sallar la'asar sannan ya fito Palon kasa.
A nutse ya ci abincinsa ya miƙe ya nufi waje dan ya je gym ya motsa jiki zuwa karfe 5:30 ya dawo su fara karatu da daddy.
Yana fita palon suka yi karo da Tga shi kuma ya dawo kenan daga wajen aiki, sannu Michael ya yi mashi ya wuce ya nufi gym ɗin.
"Michael I want us to discuss something me and you" shine abin da Tga ya faɗa, ba tare da ya juyo ba, kuma bai dakata daga tafiyar da yake yi ba ya ce "Not now uncle, ka bari sai dare because i don't have time now" ya kai karshen maganar daidai lokacin da yake ɗaukar hanyar gym ɗin, sai sauri yake yi abin shi.
Rai a matukar ɓace Tga ya bi bayan sa, sai wani huci yake yi.
Michael na shiga ya tadda Musharraf a zaune ya haɗa kai da gwiwa ga kafafunsa sun kumbura sosai bawan Allah, cikin sauri ya kariso cikin wajen yana faɗin "uncle ɗin James what happened? What is wrong with you? What brought you here?" Ya ruɗe ya jero mashi tambayoyin. A hankali Musharraf ya ɗago da kansa kamar zai yi kuka idanuwansa sun yi ja kamar wuta, da kyar ya ce "Nothing my Asif".
Michael zai sake yin magana muryar Tga ta katse shi da cewa "Ni ne na bashi horo yadda ya dace" A sukawane Michael ya juyo tare da miƙewa tsaye yana kallon Tga ɗin.
"Uncle T because of what zaka bashi horo? Me ya yi maka?" Ɗaure fuska sosai Tga ya yi cike da izza ya fara magana "Because of shi musulmi ne, kuma kai kasan...." Dakatar da shi Micheal ya yi ta hanyar cewa "And so what idan shi musulmi ne? Ko akwai wata doka da tace kada musulmi ya zauna a gidan kristen ne? Faɗa mani ina ji".
Zaro ido sosai Tga ya yi yana kallon Michael ɗin, hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba, jikinsa har wani tsuma yake yi, yau Michael ne da gaya mashi magana haka? Cikin tsawa ya ce "Michael are you heard what you said kuwa? Kana cikin hankalin ka kuwa?".
"Yes Uncle i heard what i said!, and so what dan na ce hakan?! look uncle be careful, ni bana shiga gonar kowa, dan haka bana son kowa kuma ya shiga nawa, ni dai na san uncle ɗin James ba mugu bane, ba zai taɓa cutar da mu ba, ina son ka sani ba wanda ya isa a gidan nan ya ce zai yi mashi wani abin na kyale shi, saboda James, dole zan riƙe wa James uncle ɗin sa, i knew James yana bala'in kaunar uncle Hosain (Musharraf) dan haka nima dole naso shi, please uncle T bana son yin sa in sa da kai, please and please mind your business!!" Ya kai karshen maganar yana mai duƙawa a gaban Musharraf.
Nasan kuna son sanin a ina Musharraf ya samu sunan Hosain, to kada ku ji komai, Hosain dai sunan shine na yanka, ya bawa Michael tarihin rayuwarsa ne yasa Michael ya dai na kiransa da Musharraf yake ce mashi Hosain kamar yadda yan uwansa ke kiran shi, idan muka nutsa cikin story a hankali zaku ji tarihin Musharraf ɗin kuma.
"Michael ni yau ka tsaya kake gayawa magana akan wannan banzan? Har kake cewa babu wanda ya isa ya yi mashi wani abin a gidan nan? To sai na gayawa Lion, kuma dole wannan ɗan ta'addan ya fita daga cikin gidan nan yau".
"Uncle T na gaya maka, kuma abin da ya fi haka zan gaya maka, in dai a kanshi ne, kuma na faɗa ko Lion bai isa ya ce zai yi wa Uncle Hosain wani abin ba, idan kuma ya ce sai ya yi mashi wani abin, to sai dai ya haɗa mu gaba ɗaya ya yi mana a tare, kuma da kake maganar Musulmai yan ta'adda ne, baga ɗan ta'adda ba nan muna tare da shi James, kai da kanka kasan da hakan, ka san cewa har musulmai James yana kashewa, ɗan uwana ne kuma ina matukar kaunar shi kamar raina, amma ya zama dole idan gaskiya ta zo a faɗe ta, dan samun zaman lafiya, hanyar da James ya ɗauka ba daidai bane, ya zama dole mu gaya mashi gaskiya, i knew everything akan da kai akayi bincike akan abin da James yake aikatawa, kasan abubuwan da ya yi dukka, yanzu ka gaya mani da James da uncle Hosain waye ɗan ta'adda? Ga Kristen ɗin ga kuma musulmin dukkan a gaban ka, sai ka banbance, bari ka ji uncle T da Uncle Hosain ɗan ta'adda ne da kai baka saura a cikin gidan nan ba, domin idan da kashe mu ya zo yi, yadda ya shiga cikin gidan mu ya zauna, da ya jima da kashe mu, ni bana son hayani idan kuma ka matsa mani zan iya sanya gun na harbeka idan Lion ya dawo sai ya haɗa ni da uncle Hosain ɗin dukka ya kashe mu kowa ya huta!!" Yau iya ɓacin rai ran Michael ya ɓaci, har wani huci yake yi, yana magana ne cike da izza na jinin William jacop.
"Michael ko kaso ko kada ka so musulmai yan ta'adda ne, gara maka ma ka rabu da wannan bakin mugun, idan ba haka ba, ta kanka zai fara, kai zai fara kashewa".
"Uncle T na yarda Uncle Hosain ya kashe ni, babu ruwanka da ni, kuma yanzu ina son ka gaya mani taaddaci ɗaya da musulmai suka yi, idan har ka gaya mani ka kawo hujjoji da na gamsu, na maka alwarin da kai na zan kashe uncle Hosain!!!" Ya kai karshen maganar tare da juyowa ya miƙe suna fuskantar juna.
Ba karamin razana Tga ya yi da ganin fuskar Michael ba, domin da ya ɓata rai sai ya koma sak fuskar Lion, jini ba wasa