Showing 48001 words to 51000 words out of 355604 words

Chapter 17 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2768

su kwana, Rimsha da Ayla suka yi wa kansu tambayar a tare a cikin zuciyoyinsu kamar abin haɗin baki, sai dai kuma ba su da amsar tambayar tasu.

Haka suka zauna a palon tare da su Jami'u, Rimsha kamar za ta yi kuka dan haushin zama da karti, haka ita ma Ayla. Ita kuwa Kausar sai faman wage hakwara take tana dariya kamar wata yar fari, sai murna take, ta wani zauna kusa da Jami'u suna kallon Yoruba film, ita kuma Iya ta ɓige da barci kwance saman sofa.

Sai misalin 11 na dare sannan su Jami'u suka wuce ɗakin su, wanda ya kasance kusa da ɗakin Iya ne, duk dai cikin rufi ɗaya. Tsoro sosai Rimsha ta ji lokacin da taga cewa a nan gidan su Jami'u za su kwana, ga shi ta lura da irin kallon ta da suka rinƙa yi mata.

Haka cike da tsoro suma suka wuce na su ɗakin, bayan Kausar ta tashi Iya daga barci, Iya ce ta kulle kofar falon da key da kuma sakata, sannan ta wuce ɗakinta ita ma. Rimsha dai ta tsorata sosai, gani take kamar za su zo su kama ta, shiyasa da suka shiga ɗaki ta riga su hayewa gado, ta tafi can karshen gado ta kwanta ta manne da bango, Ayla ce ta kwanta kusa da ita, sai Kausar a karshen gadon

To Rimsha mu Sarkin tsoro sai dai mu ce Allah ya tsare, na yi nan sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu.

Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode17-18🌹



Haka cike da tsoro su ma suka wuce nasu ɗakin, bayan Kausar ta tashi Iya daga barci, Iya ce ta kulle kofar falon da key da kuma sakata, sannan ta wuce ɗakinta ita ma. Rimsha dai ta tsorata sosai, gani take kamar za su zo su kama ta, shi yasa da suka shiga ɗaki ta riga su hayewa gado, ta tafi can karshen gadon ta kwanta ta manne da bango, Ayla ce ta kwanta kusa da ita, sai Kausar a karshen gadon. Suna kwanciya ba jimawa Kausar da Ayla suka yi barci, ita kuma Rimsha ta jima idonta a rintse amma ba ta yi barci ba har sai da dare ya tsala sosai tana ta tunani rayuwa, baiwar Allah har kusan asuba, sannan barci ya yi awon gaba da ita. Asuba ta gari.

💞💞Spain💞💞

Helicopters guda shida aka tasa tun kafin lion ya iso, sai kewaye cikin *Madrid* wato babban birnin Spain suke.

*Madrid* shi ne baban birnin Spain, birni ne mai girman gaske wanda a kalla Population nasu ya kai 3.3 million, birnin ya tsaru iya tsaruwa, ga dogayen gine-gine Turawan masu kyau da kawatuwa, ta ko'ina tsaf-tsaf, suna da wuraren shakatawa da yawon buɗe ido, ga wajen wasanni kala-kala, shimfiɗaɗɗun tituna masu kyau wadda suka ratsa ta cikin unguwanni lungu da saƙo, ga kuma manya-manyan gumakai na manyan shuwagabannin da suka suɗe, an yi guma kan su a tsakiyar garin, suna da manya-manyan teku wato koguna, masu ɗauke da ruwa mai kyau da karawa garin kyau, sannan akoi gumakan da irin na mace a keken doki, ko namiji ya ɗaga igwa zai sake wuta. Tsayawa zayyana muku yadda Madrid take ba zai yiwu ba, dan sai ya cinye mana wannan page ɗin ba mu kammala ba.

Karfe 12 na rana daidai, The General of the Army jet ya yi landing a *Madrid-Barajas International Airport,* har lokacin da suka yi landing helicopters suna sama suna shawagi, dan tabbatar da tsaro, kuma ba za su sauko ba yau a sama za su wuni har sai lion ya bar kasar.

Airport ɗin cike take makil da dubban sojojin Spain, dan tuni sun san da zuwan lion, sun karɓi umarnin daga sama, a kan su tarbo shi daga airport su tabbatar sun kai shi masauki lafiya, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon His Excellency mr President kakan su lion ya kira President na Spain ya sanar da shi zuwan jikan nasa, hakan yasa a ka kara tsananta tsaro sosai, ko'ina a cikin birnin sojoji ke yawo, duk ta in da ka juya sai ka ga sojoji, a kan titi ne, lunguna da sakon birnin ne, ta ko'ina.

Ko da jiragen suka sauka lion bai fito daga cikin jet ɗinsa ba, yana zaune tamkar bai san sun sauƙa ba.

Kasancewar sojojin Spain ba su san halinsa ba, labarinsa kawai suke ji, hakan sai ya dame su, rashin fitowar na shi ya dame su sosai, gani suke kamar ba lafiya ba, suna son tinkarar jet ɗin nasa dan su duba ko lafiya, amma babu dama domin jibga-jibgan sojojin Washington DC wato sojojin lion da suka zo a sauran jiragen sun kewaye jet ɗin, hannayen su riƙe da manya-manyan bindigu, hakan ya sa sojojin Spain ba su yi gigin tinkarar jet ɗin ba, dan sojojin Usa ba wasa ba, ba su da wasa a kan aikinsu, manya-manyan kasashen duniya tsoron su suke ji, saboda idan suka tinkari abu tofa basa juya baya komai wuya komai daɗi har sai sun cin ma abin da suke so, basu da imani ko kaɗan.

Wasu dankara-dankaran motonci masu numfashi His excellency president ɗin Spain ya turo su ɗauki lion. Motocin sojoji guda 6 sababbi gagal, sai kyalli suke, sai kuma wata dankareriyar mota wadda da ka gani ka san na musamman aka tanadawa lion, motar ta haɗu sosai kirar Bugatti cantodieci fara tas sai kyalli motar take kamar yanzu a ka ɓallota gal-gal.

Good 40mins lion ya ɗauka zaune cikin Jet ɗinsa ya jingina kai da jikin sofa da yake zaune, dara daran idon sa a lumtse sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakinsa. Sojojinsa dake tsaye a kansa, sai faman satar kallon sa suke, dan su kansu burge su ogan nasu yake, Allah ya masa wani irin sihirtaccen kyau, ga bala'i kwarjinin da farin jini masifa, duk in da zai shiga, za su so shi sosai amma kuma za su ji tsoron sa kamar su mutu, dan fusataccen fuskar sa ma kawai abun tsoro ne.

Yar kara wayarsa dake gefen sa ya yi, alamar shigowar sako, sai da ya ɗauki 5mins sannan slowly ya waro idanuwansa tare da ɗaukar wayar da system nasa ya miƙe tsaye. Cikin sauri sojojinsa dake tsaye a kansa, suka ɗaga hannu suka sara masa. Wucewa ya yi ya nufi waje.

Yana sako kafarsa wajen jet ɗin, sojojinsa da ke kewaye da jet ɗin suka ɗaga manya-manyan bindigun hannunsu suka fara sakin wuta a sama, gaba ɗaya karan harbi ya kewaye ko ina, nan take masu ɗaukan shi a hoto suka fara ɗaukan shi. Wucewa ya yi ya nufi wayan nan dankara-dankaran motonci da His Excellency ya turo, yana taku cike da izza da cikan gwarzon ɗa namiji.

Su dai sojojin Spain sun zama yan kallo, dan abin ya fi karfinsu duk yadda suke tunanin lion ashe ya wuce nan ba su sani ba, haka zalika yadda suke tunanin sojojin USA sun wuce nan.

Ji kake dip-dip-dip a guje direbansa na yanzu ya nufi motar da a ka tana da domin shi , jikin sa har kerma yake wajen buɗe kofar motar, dan lion ya kusa isowa wajen, idan kuma ya iso bai buɗe masa kofar motar ba to akwai matsala, shiyasa jikinsa sai ɓari yake wajen buɗe kofar.

Cikin zafin nama yake taku irin na jaruman maza har ya isa wajen motar, bai wani tsaya ɓata lokaci ba ya shige cikin motar kawai, yana shiga driver sa ya ɗaga hannu ya sara masa sannan ya rufe kofar motar, gaba ɗaya sojojin dake wajen har sojin Spain sai da suka ɗaga hannu suka sara masa, sannan sojojin sa suka nufi motoncin da a ka tana da musu, a guje suka haye saman bayan motoncin. Cikin zafin nama driver sa ya shiga gidan gaba na motar.

Kamar yadda suka saba a Washington DC, a nan ma haka suka yi a jere suka tashi motoncin suka bar Airport ɗin da gudun gaske, tun kafin su fita Airport suka saki jiniya.

Motoncin suna fita sojojin Spain suka yi saurin shiga nasu motoncin suka rufa musu baya.

Kai tsaye gidan His Excellency suka wuce, dan shi Romeo baya son kama hotel, ya fi son zaman gida, idan ka gan shi a hotel to dole ce ta sanya.

Kun san dai yadda gidan Turawa yake, mu samman gidan President kun san yadda gine-gine yake, ba sai mun tsaya nan ba.

Gaba ɗaya gidan His Excellency President ɗin Spain a cike yake da sojojin Spain da yan sanda, ga kuma manya-manyan baki masu faɗa a ji a kasar, duk sun hallara a gidan, dan tarban jika ga His Excellency Mr President of USA.

A tunaninsu lion mutun ne mai sauƙin kai, labarinsa kawai suke ji ba su taɓa zama da shi ko ganin shi ba. Yau sun ga asalin kalar halinsa, dan kuwa yana fitowa daga cikin motoncin nan ya wuce cikin gida, duk wayan nan manya-manyan baki dake tsaye a wajen domin shi bai kula kowa ba, ko kallo ma ba su isshe shi ba ya sa kai ya wuce abinsa. Babbar magana. Sun sha mamaki wasu daga cikinsu kuma sun ji haushi sosai, a ganinsu lion ya wulakanta su ya musu cin mutunci.

Tuni Lion ya san in da a ka tana da masa, domin sai da ya yi bincike a wajen kafin ya zo, sai da ya sauƙe sojojinsa sama da guda 15 wadda suka riga shi zuwa, suka zo suka bincike wajen tsaf, shi ya sa yana fita mota ya wuce wajen.

Jama'ar da suka zo domin shi, cike da jin haushin abin da ya musu suka koma cikin fadan His Excellency. Nan su ka shaida masa abin da lion ya mu su, hakuri His Excellency ya ba su tare da faɗa mu su haka halin lion yake, baya da yawan magana kuma baya son hayaniya, yanzu ma idan suka takura masa da hayaniya tofa barin gidan zai yi, idan kuma ya bar gidan nan, za su samu matsala da His Excellency mr President na USA, zai ce sun yi wa jikansa wulakanci, ba zai taɓa yi musu uzuri ba. Dole ba dan sun so ba, haka suka ja bakin su suka yi shiru dan kar su yi wani magana ya zamo musu matsala, dan sun san halin His Excellency Mr President of USA a kan family sa, kuma sun jin halin yaran William Jacop, suna ji a News, yanzu a kan haka lion zai iya sawa su rasa mukamansu ko rayuwar su ma baki ɗaya, dan sun san halin gwamnatin USA ba wasa.

A ɓangaren lion kuwa, yana shiga part na musamman da a ka ware domin shi, sai ya kara ɗaure fuska sosai da sosai, ya fito daga wajen, a cewar sa wajen yayi datti kuma abubuwan ciki sun masa local. A zahirin gaskiya ba laifi komai dake cikin wajen sabbi ne kal-kal a ledansu a ka fito da su, sannan an zuba komai da ɗan adam zai buƙata, kuma an share wajen sosai da sosai, shi ɗin ne dai ba'a iya masa, baka taɓa gane gabansa bare bayansa, yana da bala'i tsabta, ko datti kaɗan ya gani a waje to sai ya haɗe wajen gaba ɗaya ya ce akwai kazanta ba zai zauna ba, yanzu ma abin da ya faru kenan, kura kaɗan ya gani wajen mirror shikenan ya ce wajen akwai datti, sannan kuma bayan haka furnitures da ke wajen ba su masa ba.

Yana fita sojojin sa suka take masa baya, kai tsaye motoncin da suka kawo shi ya nufa. Da gudu wani soja ya zo ya buɗe masa motar gidan baya, ya shiga ya zauna. Cikin zafin nama sojojinsa suka haye saman bayan nasu motoncin, kusan a tare suka yi wa motoncin key. Jin tashin motoncin ya sanya His Excellency fitowa daga fadarsa. A hanzarce ya iso wajen yana tambayar lion ko lafiya, ina zai je.

Shiru lion ya yi na yan mintoci kafin ya sanar da shi wajen da suka tana da masa bai masa ba, sosai His excellency ya ji ba daɗi tare da yiwa lion alkawarin yanzu za'a canza komai zuwa yadda yake buƙata ya fito ya koma cikin fadar shugaban kasar ya zauna. Shiru ya yi na ɗan lokacin, kafin ya ba wa sojojinsa umarni a kan su tashi motonci su tafi, dan shi idan ya yi magana baya canzawa komai zai faru, sai dai ya faru, kai ko tunani ya yi a zuciyarsa zai aiwatar da wani abin to fa ba zai canza wannan tunani ba kome za'ayi.

_Kai jama'a wannan iri hali na Romeo ba mai iya shi sai daddynsu shi ya san halin kayansa, wai ta ko'ina ba sauƙi, gaskiya Lion ba dama._

His Excellency bai ji daɗi ba, domin ya san kakansu lion ba zai fahimce shi ba, kuma ba zai masa uzuri ba, zai ce da gangan ya wulakanta masa jika, sosai ya shiga duniyar tunanin ya zai yi da His Excellency, ya zai yi His Excellency ya yarda cewa shi bai wulakanta Lion ba, zancen zuci ya fara "To ma ni na isa in wulakanta Lion ne, mutumin da muke neman taimakonsa idan abubuwa sun fi gaban tunaninmu, dole a matsayinmu na tsofaffi sai mun nemi agajin sabon jini, dan zaren ba kalar yadin ba ne, kwakwalwar ma ba ɗaya ba kuma ko da gwaji ma ba za'a gwada ba, ni yanzu ya zan yi?" Haka ya tsaya sai zancen zuci yake, shi kuma Lion ya wuce ya bar gidan.

Yana fita su ka nufi *Westin Palace Madrid Hotel*, a karon farko da Lion ya fara sauƙa a hotel idan ya je wata kasar, ba ya son zaman hotel amma ya zamar masa dole ne ba yadda zai yi.

Katafaren Hotel ne mai girman gaske, wanda yake tsakiyar teku, a cikin ruwa Hotel ɗin yake, amma yana da shinfiɗaɗiyar hanya da zata fito da kai kamar gada haka, sannan Hotel ɗin yana da tsaro sosai, kasan cewar yana tsakiyar ruwa mai ɗauke da manya-manyan halittu irin su shak da sauran su. Duk da tsaron da wannan Hotel ɗin yake da shi, sai da jama'ar cikin ta su ka san da Lion ya shiga cikinta, saboda dubbanin sojoji da su ka kewayeta, ta ko'ina, hannayensu riƙe da manya-manyan bindigu masu aiki ba saɓa saiti.

A zahirin gaskiya ba kowa ke iya kama wannan hotel ɗin ba, domin hotel ne na manya-manyan mutane, duk kuma wanda ya sauƙa a hotel ɗin ya kwana, yana barin hotel ɗin masu hotel ɗin za su kwashe komai kama daga gadaje da sauransu, duk za su kwashe su zuba sabbi.

Ɗakin da Lion ya kama ba a magana ɗakin ya kawatu iya kawatuwa ya haɗu sosai, kana zaune daga cikin ɗakin kana kallon daga mahangar glass da ke a matsayin bangon gefe guda, zaka rinƙa kallon yadda ruwa ke juyi yana gudana ga wasu kananan kifaye suna tsalle saman ruwa, suna sake komawa, tekun na da girman sosai, girma da ba ka iya ganin karshensa, abin gwanin ban sha'awa ga masoya, shi kuwa Lion da bai san mene ne soyayya ba, ba shi da wani shauƙi, ko kallon wajen ma bai yi ba bare ya burge shi.

Driver sa ne ya kawo masa trolley sa ya ajiye masa a wajen da suka tanada dan ajiye trolley sannna ya fice daga ɗakin

Wanka ya fara yi, sannan ya shirya cikin kananan kaya, wando three quarter da riga marar nauyi duka farare tas, ya yi kyau sosai da sosai kamar shi ya yi kansa, dan shi a ko da yaushe shine ya ke yiwa kaya kyau ba kaya ke masa kyau ba, ya saki dark black curly hair nan nasa ba tare da ya ɗaure ba, sai tashin fitinannen kamshi ya ke, ya haye saman lallausan bed na Hotel ɗin tare da ɗaukan system da wayarsa ya fara aiki, yayin da jibga-jibgan sojojin ke zagaye da ɗakin nasa riƙe da manyan bindigu, dan tabbatar da tsaro.

_Wai Romeo wannan aiki haka ai sai kai ɗin mu bari mu koma Nigeria watakila kafin mu dawo abubuwa sun setu a nan._


💞💞Nigeria 💞💞

💞💞GIDAN ABBI💞💞

Sai washegari Abbi ya iya gane kansa, a nan ne kuma yake tambayar ina Aunty da Aafia? Mai aikin da ya kawo ke sanar masa da suna asibiti, ya sha ruwan mamaki sosai jin hakan, dan haka sai ya koma bedroom nasa, ya yi wanka ya shirya ya fito dan zuwa hospital ɗin, ya yin da shi kuma daddy Jelly har lokacin yana can bedroom nasa yana barcin wahala bawan Allah, ya fi Abbi jin jiki sosai da yake daman ba koshin lafiya ke gare shi ba.

Lokacin da Abbi ya isa asibiti da motar Irfan, dan already daman ya san asibitin da suke zuwa, shiyasa ya wuce kai tsaye. Ya kuwa isa a kan gaba domin ya isa lokacin da Dr ke cewa Aafia yana son ganin wani na Aunty ko baban ta ko kuma babban yayan ta, ko mijinta, dan haka Abbi na zuwa ya ce ga shi nan. Wucewa office Dr ya yi ya ce Abbi ya biyo shi.

Haka kuwa a kayi, da suka shiga office sosai Dr ya masa bayanin abortion ɗin da Aunty ta yi ya haifar mata da matsala sosai a mahaifarta, domin ta yi shine ba bisa ka ida ba, so yanzu sai an mata aiki, kuma ko anyi aikin ma ba lallai ta sake iya ɗaukan wani ciki ba. Tashin hankali a zabure Abbi ya miƙe tsaye bakinsa na maimaita kalmar abortion, lokaci guda zufa ya fara wanke masa fuska, sabon murɗawan ciwo cikinsa ya fara yi masa, kunnuwansa sun ki yarda da jin cewa Aunty ce da kanta ta yi abortion ji yake kamar a mafarki, ya kasa gaba ya kasa baya, komai ya tsaya masa cak, tunani yake "Yanzu da ma Halima za ta iya kashe min jinina? Da ma Halima ba ta kaunar kyautar cikin da Allah ya ba mu? Da ma Halima ba ta so na? Da ma duk ilimin addini Halima na banza ne? Kullun idan muka zauna wannan nasiha mai ratsa jiki da take mini ashe duka ta karya ce? Why Halima? Me ya sa za ki zama Musa a baki, Fir'auna a zuci? Me yasa za ki cutar da ni? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun". Dafe kansa da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login