Showing 276001 words to 279000 words out of 355604 words

Chapter 93 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2764

mashi, bai damu ba saboda ya san halinta ne rashin son magana, kuma yasan yau bata da lafiya, hakan yasa ma bai ja ta da hira sosai ba, kaɗan suka tattauna suka yi sallama, makudan kuɗi ya ɗauko ya bata, amma taki karɓar, ba yadda bai yi da ita ba, amma ta kafe ta ce bata so, haka ya hakura ya wuce da kuɗin, har lokacin kuma bai sami haɗuwa da daddyn Jelly ba, domin daddy dai barci ne mai nauyi ta kwashe su, bai farka ba sai lokacin da ake kiraye kirayen sallar Isha, a lokacin ya farka kuma A'A ya wuce Abj time ɗin.

Wanka ya fara yi kafin nan ya ɗauro alwala ya zo ya fata gabatar da sallar mangariba dake a kansa, bai tashi Ayla ba ya kyaleta tana barcinta abinta.

A ɓangaren Rimsha kuwa bayan A'A ya tafi sun yi sallama sai ta juya zata koma cikin gida, ido huɗu suka yi da Akil wadda ya fito yanzu, rai a ɓace ya ce "Waye kuma wannan?" Kasa ta yi da kanta tana ƴan kame kame, sake maimaita mata tambayar ya yi a karo na biyu.

Cikin in..ina ta gaya mashi waye ne, tsawa ya daka mata tare da yi mata gargaɗi akan idan ya sake ganin ta tsaya da wani namijin sai ya ƙaryata, wannan sam ba tarbiya bace, kuma ita yarinya ce bai yarda da hakan ba, ta tsaya ta natsu ta yi karatu, duk wadda yake son ta to ya zo ya same su, idan sun duba hankalinsa da yanayinsa sun san tushensa sai su bashi damar hira da ita, kuma hirar ma a cikin Palo za su yi, ba'a keɓe a harabar gida ba, dan idan ta sake yin gigin tsayawa da wani namijin sai ya yi mata duka.

Kasa ta yi da kanta tana bashi hakuri tare da gaya mashi cewa abokin yaya Imran ne, domin Imran ya gaya mata alakar dake a tsakaninsa da A'A.

Dakatar da ita ya yi cikin fushi kun san halinsa da zuciya dama, baya son abin da zai kaucewa Shari'a hakan ya sa ya ce mata ko da yaya Imran ɗin ne da kansa yake sonta sai ya fara neman izini daga manyanta dan haka shin dai ya gaya mata kada ta bari ko da sunan wasa ya sake ganin ta da wani namijin sun keɓe suna magana, baya son hakan.

Sosai ta rinƙa bashi hakuri tare da yi mashi alkawarin ba zata sake ba, sai cizan yatsa yake yi, ya so ace ya fito ya sami A'A da sai ya daka mashi warning akan kada ya sake kula mashi kanwa, idan aurenta yake son yi to ya bari sai ya sami izini daga wajen su Abbi bayan sun yi bincike akan waye shi ya halinsa yake, amma abin haushin A'A na barin gidan shi kuma ya fito, bai san suna waje ba da tun ɗazun zai fito.

Cikin natsuwa ya fara tambayarta menene yake damunta? Kin faɗa mashi ta yi tana ɓoye ɓoye, da ƴan kame kame.

Dabara ya yi mata ta hanyar amfani da ilimin da Allah ya bashi, ya ce mata ai sun yi magana da Imran to yana son ya ji daga bakin tane.

Jin hakan yasa ta gaya mashi gaskiya abin da yake faruwa, shiru ya yi yana nazari akan maganar.

A iya zaman da ya yi da ita ya fahimci ita mace ce mai addini ga ilimin boko da Arabia, sannan akwaita da gaskiya da amana, bata da hayaniya, yasan da cewa tabbas abin da ta gaya mashi hakan ne, kuma yasan da cewa sihiri gaskiya ce sannan kuma suma aljanu akwai masu gaskiya masu amana wayan da basu cutar da ɗan adam, idan ma suna tare da kai to sai dai su tallafa maka, ya san cewa Rimsha ba zata yi mashi karyar aljana ba, saboda Rimsha yarinya ce, kawai ma dan tana da tsawo da kuma dirarren jikine yasa ake yi mata kallon kamar ƴar 16 years alhalin 14 years ke gareta.

Sun ɗauki lokaci mai ɗan tsawo tsaye a haka kafin ya yi kasa da murya cikin natsuwa da ilimi ya fara magana "Duk abin da kika faɗa na yarda gaskiya ce, ina son idan wannan Malikar ta dawo ki tambaye ta wace ce ta bada wannan aiki, sannan ki tambayeta waye da waye aka yi wa aikin ko zaayi wa, babban abin da yasa na gasgata maganar ki, na san dai ke a ƴan shekarunkin nan baki ma san abin da ake nufi da aure ba, soyayya ma baki san ma'anar ta ba, ba zance baki yin soyayya ba, amma baki san menene ma'anar yinta ba a yanzu, so ba zaki iya zama ace ki tsara wannan karya ba, ta ya ma kika san kwanciyar aure da har zaki tsara hakan? Sam wannan ba karya bace gaskiya ce zalla, amma yanzu kin san me nake so da ke?".

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.

"Good, idan muka koma cikin palo yanzu, zan gayama Aunty kina son yin magana da ita, zan kuma gaya mata da ta ɗauki maganar da mahimmanci, idan kuka keɓe da ita ki gaya mata hakan ki ce na ce ta gayawa Abbi, idan kika yi hakan shikenan ƴar uwarmu kuma amaryar bappanmu zata tsira".

Ya kai karshen maganar yana riƙo hannunta dan su koma cikin gida, gaba ɗayansu kallon yarinya suke yi wa Rimsha, shiyasa basu wani damu ba suke ruƙeta, musamman ma Imran a yarinya kuma kanwa uwa ɗaya uba ɗaya ya ɗauke ta, hakan yasa har rungumarta yake yi.

A ɓangaren ita ma Rimsha ta ɗauke su ne tamkar ƴan uwanta, tasan ba zasu cutar da ita ba, musamman ma Imran da Akila sun fi shiga ranta, hakan yasa ta fi sakin jiki da su, shiyasa bata damu ba koda sun ruƙe mata hannu, kuma bata damuwa dan Imran ya rumgumeta, Akil ne da bata saba da shi sosai ba, kuma ta ga yana da zafin kai sosai, shine take ɗan ja baya da shi dan tsoro ma yake bata.

Zaune gaba ɗayan su a palo suka isko su aunty sai zuba masu tsiya take yi, kusa da ita Akil ya zo kasa kasa ya ce ta kira Rimsha suje ɗaki akwai maganar da za su yi, kuma ta ɗauki maganar da mahimmanci.

To ta masa mashi da shi tana murmushi, shi kuwa Imran hankalinsa na a kan wayarsa, Abbi da Irfan kuma suna hira, while su Umaisha ma suna tasu hirar ita da Akila da A'afia da Hanan, sun lula duniyar hira babu kama hannun yaro.

Miƙewa Aunty ta yi ta ruƙo hannun Rimsha suka haura sama, da ido kawai Abbi ya bisu yana tunanin ko dai ba lafiya bane, to me yake damun Rimsha ne? Ya tambaya acikin zuciyarsa tare da cigaba da hirar da suke yi shi da su Irfan, su Akila kuwa suna duniyar hira basu ma lura da Aunty da Rimsha da suka haura sama ba.

Kusa da su Akil ya zauna suka cigaba da hirar.

Wayar Akila dake a gefenta ne ya ɗan yi kara alamar shigowar sako, ɗaukar wayar ta yi tare da cire password ɗin wayar.

Tasha ruwan mamakin ganin saƙo da unknown number, ɗan taɓe baki ta yi tare da buɗe saƙon dan ganin me ya kuntsa.

"Assalamu alaiki warahmatullahi taala wa barkatuhu, barkar ki da dare ya bugun zuciyata, amincin Allah ya kara tabbata agareki tauraruwar mata ta duniya, gaskiya yau kin yi kyau sosai da sosai, kallon farko soyayyar farko, kada na cika ki da surutu na barki lafiya sai zuwa anjima zaki ga saƙona ya shigo, yanzu dai ina son ki san da zama ne, saƙo daga ƁOYAYYEN MASOYI".

Shine abin da yake rubuce a cikin saƙon, ɗago kai ta yi tare da kallon su Irfan dake a zaune saman sofa while su kuma dama suna kasa a tsakiyar carpet ɗin ne.

Hira kawai su Irfan suke yi, babu wanda yake ruƙe da waya ma a cikinsu sai Imran, shi kuma ya duƙar da kansa kasa yana kallon wayar da alma wani abin ya ke kallo ma, ba ma taɓa screen ɗin wayar yake yi ba bare kuma ta ce shine ya yi mata irin wannan wasa, ɗayar hannunsa ma tana ɗaure saman sofa da hannu ɗaya ya ruƙe wayar tasa, shi kuma Irfan wayarsa tana zaune kusa da shi bai taɓa ta bama bare kuma har ya kai ga rubuta saƙo, shi kam Akil wayar ma tana cikin aljihu, dawo da kallonta kan su Aafia ta yi dan taga ko dai sune suke yi mata irin wannan wasan.

Sai taga gaba ɗayansu babu ma wadda waya yake a hannunta, dukkansu wayoyinsu na a zaune a gefensu, to waye wannan? Ga kuma dai number unknown number ce bare ta ce, zata kira dan ta ji wanene, amma koma waye da alama ya yi mata farin sani ko kuma yana da alaka da ita, domin hausar da ya rubuta mata sak irin hausar Kaduna ce.

Tana tsaka da mamaki sako ya kara shigowa, cikin sauri ta duba, unknown number ɗazun ce dai, saƙo ne yake rubuce kamar haka.

"Haba heartbeat me yasa zaki wahalar mani da kanki wajen waige waigen neman waye ya turo maki saƙon, to ki daina wahalar mani da kan ki bana so, and then please ki ɗan yi mani murmushi zan ji daɗin hakan sosai kin ji my angel? Saƙo daga ƁOYAYYEN MASOYI". Babbar magana.

Cikin sauri ta sake ɗago kanta ko zata gane wanenen, kamar dai yadda suke ɗazun haka suke yanzu ma, shi Imran ma da alama wani news yake karantawa a wayar tasa, domin ya tattara hankalinsa kaf akan wayar, ya natsu yana kallon screen ɗin.

Kawar da kallonta gefe ta yi domin tasan Imran dai ba zan yi mata wannan abinba, suna uwa ɗaya uba ɗaya, to waye kenan?.

Kamar zata yi kuka ta sake mayar da wayar zata ajiye. Sake turo mata saƙo ya yi a karo ba uku kenan.

Da farko kamar ba zata buɗe ba, amma sai ta daure ta buɗe saƙon, saƙone kamar haka.

"Heartbeat ba nace ki yi mani murmushi ba? Amma shine zaki ɗaure fuska? Idan kika yi kuka sai na ɗauke ki mun ta fi dake duniyarmu, ba zaki sake ganin kowa na daga ƴan uwanki ba, ki yi mani murmushi kuma ki daina neman waye mai turo maki sako dan ba zaki ganni ba, yanzu dai ayi mani murmushi ko kuma na zo na ja wannan ɗan bakin mai kama da birro, na kuma yi maki caƙulƙuli".

Bata san time da kayatatcen murmushi ya kubce mata ba, wai bakinta kamar biro, shine abin da ya bata dariya, tana yin murmushin baafi minti 1 ba sai ga sakon shi ya kara shigowa.

"Gaskiya wannan murmushi ya tafi da ni my angel, kin iya murmushi sosai, wow rufe idanunki bari na baki hot kiss a kumatu mu gani ko na iya".

Cikin sauri ta ajiye wayar tare da tare kumatunta da hannayenta dan wai kada ya yi kissing nata, ai kuwa ji ta yi tamkar anyi kissed na kumatun nata, zaro idanu waje ta yi tana karanto duk wani addu'a da ya zo mata bakinta.

Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ta fara faɗe tana zare ido.

A ɓangaren su Rimsha kuwa, kamar yadda suka yi da Akil haka ya gayawa Aunty, ita ma Aunty da yake akwai ilimin addini, ta fahimci maganar sosai da sosai, hakan yasa bata ɓata lokaci ba wajen kiran Abbi a waya akan ya zo ɗaki, ita kuma Rimsha ta ce ta koma palo kada ta damu.

Abbi bai ɓata lokaci ba wajen zuwa ɗakin, ba ɓata lokaci Aunty ta gaya mashi abin da yake faruwa, sosai ya sha ruwan mamaki tare kuma da yi wa Allah subhanahu wata'ala godiya sosai akan Allah ya so su da rahma, Allah ya kaddara ɗan uwansa bashi da rabon shiga wahala a karo na biyu, dukkan su sun yarda da zancen Rimsha, domin wannan bama zance ce da za'ayi karya akan ta be, me riba idan akayi karya akan gakan? Me ribar mutun da daddyn Jelly ya yi dis virgin ɗin Ayla? Cos wannan ba magana ce ma da za ace karya bace. Amma Abbi ya yi alkawarin bayan komai ya lafa zuwa jibi dole ya kira babban malami a yi masu saukar Al Qur'ani mai girma a gidan, tare da yi wa gaba ɗaya ƴaƴan karatu a kansu domin Allah ya kara tsare su

Da haka Aunty ta ce Abbi ya kira daddyn Jelly ya turo mata Aylar yanzu, to Abbi ya amsa da shi tare da kiran layin daddyn.

Lokacin da kiran ta shigo yana kan dadduma ya idar da sallar mangariba yana jiran a tada kabbarar sallar isha ya je masallaci tun da an yi kira tun minti 7 da suka wuce.

Ganin Yaya Deen ne yasa ya yi saurin ɗaukar wayar, ba tare da nuna wasa ko wani abu makamancin hakan ba, Abbi ya ce ya turo mashi Ayla yanzun nan, sannan kuma idan suka fito sallar isha ya tsaya a bakin masallaci yana son yin magana da shi.

Tom ya amsa da shi tare da katse kiran ya miƙe ya haye saman bed ɗin.

Tana kwance kamar yadda ya kwantar da ita, sai zuba barcinta take yi cikin kwanciyar hankali, da alama barcin ya yi mata daɗi, dan yadda take sauƙe numfashi a hankali hankali.

Fuskarta ya fara shafawa a hankali hankali, can kasa kasa a saitin kunnenta ya fara kiran sunanta yana shafa face nata.

Cikin magagin barci a shagwaɓa ta ce "Uhm uhm daddy ka bari mana".

Bakinsa ya kai saitin tata yana faɗin "Uhm uhm daddy ba zai bari ba har sai kin tashi".

Jin voice nasa ya sa ta gane ba mafarki take yi ba, cikin sauri ta waro idanunta da suka yi ja saboda barci, karaf sai cikin nasa idanun, da sauri ya kawar da kallonsa, domin har ga Allah yana jin kunyarta, baya son su rinƙa haɗa ido, shi mutun ne mai kunya sosai.

"Baby ta shi ki je Abbinki yana kiranki, daga nan sai ki yi wanka ki yi sallah ki kawo mana abincin dare".

To ta amsa mashi da shi tare da yunkurawa zata miƙa, matsa mata ya yi dan ta miƙe.

Bayan ta miƙe sai da ya rungumeta tare manna mata kiss a goshi yana faɗin "Ki kula mani da kanki".

To ta amsa mashi da shi tare da cewa "Kai ma ka kula mani da kanka daddyna".

Wani irin daɗi ya ji ta rufesa, cike da murna ya diro kasa daga saman bed ɗin, da kansa ya sanya mata hijabinta tare da rungumota sosai a jikinsa suka yi sallama.

Cikin gida ta wuce while shi kuma ya wuce masallaci.

A palo ta isko Aunty tana tsaye tana jiranta, su kuma su Aafia sun haye sama dan suje su yi Sallah.

Tana shigowa Aunty ta riƙo hannunta suka wuce bedroom nata, wanka ta sata ta yi tare da gyare jikinta sosai, turatuka masu kamshi Aunty ta bata akan ta sanya, tsadaddun humrane masu shegen daɗin kamshi.

Ayla ta sha mamakin ganin hakan, amma sai bata wani damu ba, ta yi duk wani abin da Aunty ta ce mata, sababbin kayan barci masu kyau da tsada Aunty ta fitar daga cikin kayan lefenta ta miƙa mata akan ta sanya.

Ayla baiwar Allah bata musu da koma waye, to ne yake rabata da kowa, to ta ce tare da karɓa ta buɗe su.

Wani ɗan iskan rigane wadda ba zai wuci gwiwa ba, sai kuma pant nasa wadda dukkansu jikinsu yana da tsantsi sosai, sanann gaban rigar a buɗe ana iya ganin pant ɗin da kuma cibiyarta zuwa iya saitin kasan kirjinta tsagun rigar ta tsara, ta bayar rigar kuma an kwashe bayan sosai, daga kafaɗarta har izuwa tsakiyar bayanta walam ne, haka rigar take.

Cikin natsuwa ta sanya kayan, ba karamin kyau ta yi ba, sai tashin wani gigitatcen kamshi take yi.

Bayan ta gama ne Aunty ya bata hijabi har kasa ta ce ta sanya ta yi sallah, karɓa ta yi tare da sanyawa ta shimfuɗa daddumar Auntyn ta tayar da Sallah.

Ita kuma Aunty ta wuce kitchen dan ya shirya masu abinci mai daɗi.

After some minutes.

Dukkansu sun dawo daga masallaci sun haɗu a palo banda daddyn Jelly wadda kwata kwata ma bai dawo gidan ba.

Shirya masu abinci a saman table Aunty ta yi tare da cewa su zo su ci, sannan ta ɗauki na daddyn Jelly da amaryarsa wadda ta shirya masu na musamman ta ajiye masu a saman carpet dake tsakiyar palon sannan ta kira Ayla akan ta zo ta ɗauka.

Ba musu ta sauƙo kasa ta ɗauka jikinta na sanye da hijabi har kasa while kayan barcinta kuma na daga ta ciki.

Rimsha ta saki jiki sosai yanzu, domin Aunty ta karfafa mata gwiwa akan ta kwantar da hankalin ta a cikin daren nan komai zan daidai ta, to ta amsa cike da kunya, sai tsokananta auntyn take yi.

Su Abbi gaba ɗaya hayewa saman dining table suka yi, Aunty ne ta yi serving nasu dukkansu.

Kusan a tare suka fara cin abinci, Umaisha tana zaune kusa da mijinta, da yake darene kuma wutar wajen dining table ɗin blue light ne ba'a gani sosai, sai Akil ya zura hannunsa ta kasan table ɗin yana shafa cinyoyin matarsa yana cin abinci da hannu ɗaya, ita ma time to time tana shafa masa gabansa duk kuma suna cin abinci.

Shi kuwa Irfan ya zauna kusa da Akilarsa sai janta da hira yake yi amma taki biye mashi, domin zuciyarta tana can duniyar tunanin waye wannan masoyin ɓoyen?.

Duk wani motsi idan ta yi sai ya yi mata massage akan ta yi kyau da ta yi kaza ko kuma ta gyara kaza, to waye ne wadda yake iya kallon duk wani abin da take yi?, Abin ya yi mugun ɗaure mata kai ba kaɗan kaɗan ba.

Su A'afia kuwa abinci kawai suke ci, A'afia da bata da yawan cin abinci sosai ma yanzu zagewa take yi ta ci sosai dan idan bata ci ba zata sami matsala da Akil, duka zai yi mata, ya hana su wasa da cin abinci, akan haka har dukansu ya taɓa yi, shiyasa yanzu basa wasa da cin abinci, sosai suke bada himma.

Bayan sun kammala cine Imran ya miƙe tare da ce da Rimsha ta shirya su wuce.

Aunty da Abbi har suna haɗa baki wajen cewa ina kuma za su je, za su koma gida Imran ya basu amsa, nan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login