Showing 252001 words to 255000 words out of 355604 words

Chapter 85 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2756

yi nasara, kin wahala sosai my sister, sai dai nace maki Allah ya bamu iko da nasara, Allah muka ruƙe kuma za mu yi nasara...."

Kiran wayar Imran da akayi ne ya dakatar da shi daga maganar da yake yi, suka yi shiru dan bawa Imran damar ɗaukar call ɗin sa.

Ganin sunan Saif ne a kan screen ɗin wayar ya bayyana bayan ya duba ne yasa ya miƙe ya ce yana zuwa ya nufi waje.

Cigaba da magana Areef ya yi "Me yasa kike saka irin wannan manyan kaya haka? Ga shi sai zufa kike yi" ya yi maganar yana nuna hijabin jininta.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe, cikin muryar kuka ta ce "Haka muke yi a nan Nigeria, a kasar ku ne ko musulma sai dai ka ganta ba ɗan kwali bare hijabi, masu imani sosai ne sai kaga sun saka ɗan karamin hijabi, mu kam a nan har kasa muke saka wa mu rufe jikin mu".

Jinjina kai ya yi yana faɗin "Good, amma dai ya kama ku rinƙa sassautawa kanku dan wannan wahala ne ai" Shiru ta yi tana ɗan ɗari ɗarin amsar da zata bashi kada ya ɓata mashi rai, amma da ta tuna gaskiya ce zata faɗa, daga ƙinta kuma sai ɓata, sai ta daure ta ce "A'a Yaya Areef, wannan shiga ita ce daidai, ita ce annabi Muhammad (S.A.W) ya koya mana, gaba ɗaya jikin mace al aura ce, ya kamata ta rufe ko'ina nata, iya fuska kawai aka yarda ta bari a buɗe, shima ai kaga akwai dalili mai karfi, wannan shiga tamu ta nan shine shigar musulci, annabi ya ce mace ta sanya dogon hijabi, ta baya yana taɓa kasa, ta gaba kuma, ya kai idon sahu".

Sosai ya ji daɗin bayanan ta, kuma shi kanshi shigar tata ba karamin burgeshi ta yi ba, kawai dai dan ya ga tana haɗa zubane yasa ya yi mata magana, zufar kuma ta samo asaline saboda kukan da ta yi.

Sakin hannun nata ya yi yana faɗin "Ki yi mani addu'a na sami lafiya muje ki raka ni yawo a sassan kasar ku, dan ina son yawace koina da ina kafin mu koma kasar mu, ina son ganin kasar nan taku sosai, dan a yan kwana biyu da na yi a freedom nan, ba ƙaramin daɗin garin na ji ba".

Zata yi magana kenan Imran ya shigo bakinsa ɗauke da sallama yana ruƙe da wayar Lion a hannunsa, sai mirmishi yake yi yana kallon screen ɗin wayar, da alama video call yake yi da wani.

Kusa da Areef ya zo ya zauna tare da miƙa mashi wayar yana faɗin "Aseef want to see your face". Fuska ba ya bo ba fallasa ya karɓi wayar.

Wani irin kayatatcen Mirmishi ne ya bayyana akan face nasa lokacin da ya kawo wayar sai tin face nasa. Ba komai ne ya sanya shi wannan murmushi ba face ganin Aseef da ya yi zaune cikin library ga takardu a gabansa, da alama karatu yake yi tukuru, shima cool murmushi ne ɗauke a saman face nasa.

"My blood Nigeria ya yi maka daɗi ko?" Aseef (Michael) ya tambaya. Gyaɗa mashi kai Areef ya yi kafin ya ce "Over my blood over, idan akwai abin da ya fi over ma to shine, I really like Nigeria and Nigerians, they are good people's sosai".

Shiru Aseef ya ɗan yi kafin ya ce "Okey i will join you In Sha Allah, but not now, I have exams next month, if am done, i will try to join you, am not happy at all, All of you kun tafi Nigeria kun barni, dan ma am together with uncle Musharraf yana ɗebe mani kewa, if not da kewa ya yi mani yawa sosai, a really missed guys".

Zuba mashi ido Areef ya yi na yan mintoci kafin ya ce "What is wrong with you?" Kara faɗaɗa mirmishi kan face nasa ya yi yana faɗin "Nothing blood".

"Am I your mate? Am i playing with you? I said what is wrong with you?" Ya yi maganar yana ɗaure fuska sosai.

Cikin dariya Aseef ya ce "You're my mate and you're playing with me, what is next?"

Dafe kai Areef ya yi Aseef ya san takan tsiya, idan ya bi shi da karfi ba zai gaya mashi me yake damun shi ba, ga kuma damuwa karara akan face nasa bawan Allah, dan haka sai ya ajiye duk wata zafa ya fara yi mashi magana kamar sa'annin juna, suka koma TRIPLETS ɗin kawai, tun da ya ga yanzu Aseef ɗin ya warke garau tamkar bai taɓa yin ciwo ba, yanzu dole su goga kafaɗa.

"My blood you knew i really love you, and you knew am worried about you? Please tell me what is wrong with you, if not you will put me in to bad mood"

Yar dariya Aseef ya yi kafin kuma ya ɗaure fuska sosai, nan take yanayin sa ya sauya, yanzu dai cike da shagwaɓa ya fara magana "My James Uncle T ne yake bawa uncle Musharraf wahala, everyday idan na tafi school, before na dawo sai ya bashi horon sojoji, idan na tambayi uncle Musharraf ɗin what is happened to him sometimes nake ganin face nashi da kuma bodynsa somehow, sai ya ce mani nothing, kuma i knew there is something behind between him and uncle T dan na taɓa kama shi yana sanya uncle Musharraf ɗaga gun Ak, kuma tana cike da bullet sosai, ranar har ciwo sai da hannun uncle Musharraf ya yi, ina son gaya wa Lion amma bana son wata matsala ta faru a gidan kuma, kasan Lion zai bawa uncle T punishment mai tsanani, hakan kuma zai ɗaga wa daddy hankali, ina da tabbacin Lion yana busy this two days ɗin nan, i think that is the reason why baya bincinkan camarorin gida, da kuma abin da yake faruwa Kum......."

Bai kai karshen ba Areef ya dakatar da shi cikin tsawa "What uncle did to Uncle T da har yake ba shi horon sojoji Kuma?". "My blood you already knew that gaba ɗaya yan gida they hate Muslim people's, so the reason why uncle T ke azabtar da shi kenan, because he is a Muslim".

Rai a matukar ɓace Areef ya ce "Ya zama dole uncle T ya karɓi hukuncin zalincin da yake yi, before na tafi sai da nace mashi ya sauƙe wannan rawanin zalinci dake a kansan nan ya ajiye, amma yaki, yanzu dai zan gayawa Lion please ya sanya a kawo mani uncle na nan kasar, idan na sami lafiya sai mu koma tare, in na dawo Allah sai na sanya uncle T ya kwance wannan rawanin zalinci dake a kansa ya ajiye...."

"My blood why zaka raba ni da uncle Musharraf, you know shi kaɗai nake gani yake rage mani kewar ku fa". Girgiza kai ya yi yana faɗin "No Aseef ya zama dole na ɗauki uncle, ko so kake na barshi uncle T ya cigaba da wahalar da shi ne?" Girgiza kai ya yi alamar a'a. "To ka gani, idan ka gama Exam ai kai ma zaka bi yo mu sai mu koma a tare, so kada ka damu, ka mai da hankali sosai akan karatu."

To Aseef (Michael) ya amsa da shi, daga nan suka cigaba da hira, sosai Areef ya bashi labarin Rimsha bai ɓoye mashi komai ba, dan dama haka suke, da James da Michael sirrin su kusan ɗaya ne, abin da ɗaya ya sani da wuya ka ji ɗaya bai sani ba.

Wani irin daɗi Aseef ya ji ya ce sam Areef sai ya nuna mashi a ina Rimsha ɗin take, ai kuwa bai hana shi ganin ta ba, da hannu ya yi mata alama da ta dawo gefensa ta saman pillow da yake kwance su yi magana da ɗan uwan shi, ba musu ta miƙe ta je.

Ba ƙaramin farinciki Michael ya ji ba, da alama ma ya fi Areef murna, dan har da dariya ne akan face nasa ba iya mirmishi ba.

Ita ta fara ce mashi good morning, sai daɗi yake ji, ga fara'a palala a face nasa, ya amsa mata gaisuwar tare da tambayar ya take, lafiya ta amsa mashi da shi, "My Name is Aseef what of you?" Farinciki yasa bakinta ya ki rufuwa "My name is Rimsha" ta bashi amsa.

"Wow Rimsha nice name, cos the way am seeing your face like you are under 15 years" Ya yi maganar yana tsareta da wayan nan brown eyes ɗin nasa, ba ƙaramin mamaki Imran ya sha ba, dan ya san halin Michael sarai lokacin da suke school, amma ya akayi yau yake magana da Rimsha haka? Abin da bai sani ba shine ƙwaƙwalwar Michael ta da da ta yanzu ba ɗaya hace, da kamar ma za'a ce ba shi bane, yanzu kuwa shine, cikakken mutun mai imani da natsuwa, yanzu ne ainahin wanene shi ta bayyana.

"Yah Yaya Aseef am under 15 years, am 14 by age" Shiru ya yi yana tunanin shekarun Lion da nata shekarun, anya kuwa hakan zata yi wu kuwa? Ya tambayi kansa, Areef ne ya katse shi da cewa "What are you thinking?".

Ɗaga kai sama ya yi tare da juya manyan idanun nan nasa, kai a ɗage ya dawo da kallonsa kan Areef ɗin, ya kashe mashi ido ɗaya tare da ɗaga gera ɗaya kamar wasu munafukai, Areef bai san time da dariya ta suɓuce mashi ba, dan ya gano hanyar da Aseef yake, wato idan Allah ya ƙaddara abin da suke fata, na Lion ya yarda ya auri Rimsha zuwa ɗaya zai yi mata ba dawo sai dai a ɗauki gawarta, wato ta yi mashi karama, hakan yasa Areef satar kallon ta, ita kam ba abun da ta gane, tama yi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.

Dawo da kallonsa kan Aseef ɗin ya yi har lokacin yana ɗage da kai sama yayin da idanunsa kuma suke a gefe yana kallon Areef ɗin, da larabci Areef ɗin ya fara magana bai san cewa Rimsha tana jin larabci ba, ba kuma ya son ta ji abin da suke cewa ne, shi James yana jin yaren china amma Michael baya ji, larabcin ma James ɗin ya mance ne Michael baya ji, sai yana yi mashi kamar tare suka koyi komai.

"Kai Areef baka da kirki, me yasa zaka yi wannan tunani, ai zata girma...." Bai karisa maganar ba Aseef ya dakatar da shi da cewa "Which kind of language is this?".

Shafa fuskarsa ya yi sai lokacin ya tuna ashe Aseef fa yanzu yake koyan karatu, hakan yasa ya dawo magana da English ɗin kawai, tun duk wani baƙon yaren da yake ji Aseef baya ji sai English.

"My blood tayi ko? Kana ganin ta dace da Lion?" Cikin sauri Aseef ya jinjina kai yana faɗin "Yah sosai ma, saboda shi is so beautiful and she have innocent face, the way am looking at her like she is so silent, zata iya hakuri da mu, you knew yanzu wadda zata iya hakuri da mu ne muke buƙata, but seriously i pity her more than your expectations, saboda magana ta gaskiya you knew mu da muke TRIPLETS nasa ma, bamu taɓa gane ina ya dosa, kullun a murɗe yake, yana cikin gindayar da mutane, duk duniya ba wanda yake iya cankan ga abin da zai yi ko wanda ba zai yi ba, sai kana zaton shi a nan sai ka ga ya ma wuce nan, to be honest zata sha bakar wuya, ni for my on bana ji a jikina Lion zai bari ta zauna kusa da shi ma, bana jin wannan abin zai yi wu, amma anywhere shawarar da zan baku dai a nan ita ce, kada ku sanya yarinyar nan ta je kusa da shi ya yi mata kisan farat ɗaya, ku ɗauki alhakinta banza, wlh ni na sani idan ba wani kwakwaran dalili, kai in jin ko harbina da bindiga aka zo yi ta tare mani Lion ba zai barta a kusa da shi ba, ba zai yarda da ita ba, ko me zata yi mashi, amma zan taya ku thinking na wani solution ɗin wata kila mu dace, kuma ku yi tunani mai zurfi kada ku zo ku yi dana sani, for my on choice yarinyar ta yi sosai" dawo da kallonsa kanta daga kan Areef ya yi ya cigaba da cewa "My sister kin dai ji abin da na faɗa, iya gaskiya na gaya, ni bana karya, so is better for you ki iya takunki, ki ɗauki action mai kyau, dan bana son mu rasa wannan innocent face ɗin naki, ina ga ko daddy bai yi wa Lion irin sanin da ni na yi mashi ba, saboda ni nafi zama tare da shi, ko Areef ba zai gaya mani asalin wanene shi ba, duk da cewa nima ban san shi ciki da waje ba, dan ba komai zaka iya ganewa a tattare da shi ba, amma na san abubuwa da dama shiyasa kika ji na faɗi haka, so ki kula, idan da son samu ne ma, ki yi zaman ki sai na zo Nigeria sai mu san abin yi".

Areef ne ya tari numfashinsa da cewa "Yah Aseef abin da ka faɗa dukka gaskiya ce, ni kaina da abayane kace mani zan iya zama da mace haka mu yi hira, wlh zan ce karya ne kuma never in my life, so amma musulci ba wasa ba, In Sha Allah Lion zai so ta, ya yi aure muma mu yi aure, mu cika addininmu, amma na san ba nan kusa bane, yanzu ma abin da muke so ai ba zai ko kusan samuwa ba, shiyasa nace mata kada ta bari hanya ya rinƙa haɗa su, ta bari sai na sami lafiya, idan na sami lafiya shikenan, zan iya shiga ɗakin sa na kwanta kuma na kirata ta kawo mani abu, ko ta zo kuma ba zai ce komai ba, saboda kasan baya shiga abin da bata shafe shi ba, idan muna tare zan iya kiranta ba zai yi magana ba, amma yanzu dai bari na sami lafiya first".

Jinjina kai Aseef ya yi yana faɗin "Shawara mai kyau, hakan ma ya yi, kuma dama shiyasa nace ta bari sai nazo Nigeria, Lion baya kallon mutane da abubuwa, abin da yake gabansa kawai yake yi, amma ina da tabbacin idan tana yawan zama kusa da mu, wata rana dole zai so ganinta, kuma dole zai samu kwanciyar hankali a tattare da kasancewar a gidan, saboda idan ya ga muna tare da ita, zai ce e lallai tana da kirki, kuma zai so sanin wace ce ita da har muke tare da ita haka, zai yi bincike a kanta ko da bai gaya mana ba, kuma ina fatan daga nan shima zuciyarsa zata aminta da ita".

Jinjina kai shima Areef ya yi alamar gaskiya Aseef ya faɗa.

Kada ku mance duk wannan magana da suke yi, suna yi wa Rimsha kallon a matsayin kanwar Imran uwa ɗaya uba ɗaya ne fa, to ya kenan idan suka ji cewa shima Imran tsintota ya yi? Ba abin da ya haɗa su kuma bai san ina ƴan uwanta suke ba, kuna tunanin za su yarda da ita kenan? Kuna tunanin za su bari ɗan uwansu ya aure ta? Saboda fa kirkin Imran yasa suke sonta, dan kun ji sunce Imran mutumin kirki ne, suna son shi fiye da tunanin mai tunani, a cewarsu dukka family Imran mutanen kirki ne kamar shi, BABBAR MAGANA.


Miƙewa Imran ya yi ya nufi waje dan Akil ya kira shi yana kofar gida ya kawo kayan Rimsha.

Bayan ya karɓo ya dawo ne ya zo ya ce mata ta tashi ta je ta shirya zuwa school, to ta amsa mashi da shi, tare da yi wa Areef sallama da fatan samun lafiya sannan ta wuce ta barshi suna hira da Aseef nasa.

A gurguje ta yi wanka ta shirya cikin abaya blue color tare da hijabi ba mayafin rigar ba, time ya tafi almost 8:5 yanzu, sun zauna hira da su Areef, Imran ma bedroom nasa ya wuce dan ya yi wanka ya shirya ya zo ya kaita school.

Bayan ta gama shiri ne ta fito palo, wani irin nishaɗi ta ji lokacin da hancinta ya shako mata daddaɗar kamshin perfume nasa, da alama ya wuce a palon, zama saman sofa ta yi tana rataye da hannu ɗaya na school bag ɗin ta a kafaɗa, ga hijabinta har kasa launin blue kalar rigarta, ta yi kyau sosai, ba wani make up ko kaɗan a face nata, soft skin ɗin nan nata sai wani sheki yake yi, colan skin ɗin nata ya kara fitowa sosai, sai wani murmushi take yi ita kaɗai zaune shiru, idan ta tuna maganganun Aseef in da yake cewa mawuyacin abune Lion ya barta ta matso kusa da shi, sai ta ji gabanta na faɗu wa, me yasa kowa a cikin shawarar da zai bata sai ya ce mata kada ta haɗa hanya da shi? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.

Bata kai ga samin amsar tambayar ba Imran ya fito yana faɗin "Let's go". Shirye yake cikin manyan kaya na wani haɗaɗen yadi mai kyau coffee colar, kayan sun mashi kyau sosai, shima yana da kyakkyawar saje irin na daddyn Jelly, daga wajen bakinsa kuma akwai kewayayyen gashi mai kyau sosai a wajen, kamar dai daddyn Jelly.

Gaba ya yi ta bi bayansa, a palon kasa suka hango Lion saman dining table yana latsa laptop ga kuma kayan abinci a gabansa, amma bai fara ci ba, sojan dake yi masu girki ne tsaye akansa yana jiran umarni kawai ya zuba mashi abincin. Shirye yake cikin wasu shegun tsadaddun kaya, wandon jeans ne ask color mai bala'in kyau, daga ta sama kuma high neck t-shirt ne white color, rigar ta kama jikinsa sosai hakan yasa kakkarfar surar jikinsa daga ta sama ta bayyana, ya ɗaure kyakkyawar gashin kan nan nasa a baya, kamar dai kullun wannan guntu na gaban goshin nasa yana nan, while face nasa na sanye da black glass mai bala'in kyau, idan kaga lips ɗin nan nasa, sai ka rantse da Allah yasa lips stick, har wani kyalli suke yi saboda yana ɗan ciza su time to time, gaba ɗaya kamshin perfume nasa ne ya gauraye gaba ɗaya cikin palon.

Rimsha da aka ce kar tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login