Showing 114001 words to 117000 words out of 355604 words
yi ya yi amma ina Michael ya ki yi masa magana kukan sa kawai yake yi, daga karshe Musharraf ne ya yi karanbani muryar sa na rawa ya ce "Kayi hakuri ka ji Michael?" Juyawa ya yi ya kwantar da kansa saman cinyar Musharraf ɗin yana faɗin "Uncle ɗin James my stomach am feeling hungry over".
"Okey tashi muje na baka abinci" cewar Tga. Dawo da kallonsa kan Tga ɗin ya yi "Uncle T I can't eat anything now" "Why?" Tga ya tambaya yana zaro ido
Michael zai yi magana kira ya shigo wayar Tga dake aljihunasa, kin ɗaukar wayar ya yi dan a cewarsa koma waye ke kiran shi yanzu dole ya hakura domin shawo kan matsalar Micheal ta fi masa komai a yanzu.
"Uncle T pic your call mana". Ya yi maganar cikin kuka, girgiza kai ya yi yana faɗin "No Michael ina son in ji me damuwar ka first tukun nan, kafin na ji na wasu kuma".
"To uncle idan Lion ko kuma James ne suka kira ka fa?" Jin haka yasa ya ciro wayar a sukwane, ai kuwa Lion shine sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, a zafafe ya juya ya fice daga ɗakin har yana haɗawa da ɗan gudu, dan yasan Lion baya kiran layin kowa haka kawai sai da kwakkwaran dalili mai karfi, bare kuma yanzu da suke fama da case ɗin James ai dole ma su kasance tare.
Yana shiga part ɗin Lion ya isko shi tsaye yana fuskantar balcony ɗakin nasa a cikin bedroom nasa kenan.
Sanye yake da kayan sanyi yau, saboda sanyin yau ya yi yawa over, ya yi wa kayan kyau sosai, dan shi, shi yake yi wa kaya kyau ba kaya ke masa kyau ba, ya zura hannayensa a cikin aljihun wandon, a yayin da ya sanya hular rigar a kansa, kayan suna da laushi sosai, jikinsu kamar jikin mage, kun san Lion da son kalar farin abu, to wannan ɗin ma hakan ne, fari ne tas kamar yanzu ya cirosu daga ledarsu.
Excuse Tga ya masa sannan ya tsaya daga ɗan bayan sa yana shakar daddaɗar kamshin perfume nasa dake tashi a jikinsa.
Sun kwashi tsawon 10mins a haka kafin nan Lion ya fara magana ba tare da ya juyo ba.
"General na karawa wayar James tsaro saboda bana son mutanen da suka kama shi su iya shiga cikin wayar nan, a yanzu sun kama shi ne saboda ya kashe musu mutane a takaice dai alakarsu na ta'addanci ne, idan kuma suka iya shiga cikin wayarsa suka yi bincike za su gane cewa ɗan uwana ne, daga nan za su masa hukumci biyu, bana son hakan ta faru saboda ina bukatar James a raye, da kai na nake son yi masa hukunci, gudun ire-iren wannan abin yasa nake sanya wa wayoyin gaba ɗaya yan gidan nan tsaro, ta yadda ba wanda zai iya bincikar wayoyin naku, zan yi tafi next week ka kasan ce cikin shiri a ko wani lokaci zan iya kiranka ka buɗe mini wayar James, kafin na tafi zan tabbatar na kutsa cikin nasu tsaron da suka sanya wa wayar, yanzu ku tashi kungiyar su dake India yau ɗin nan, na gama komai" yana kai karshen maganar ya juyo ya nufi hanyar shiga cikin balcony ɗin.
Mamaki ne ya kama Tga, tunani yake yi ashe Lion ne yake rufe musu wayoyinsu ta yadda babu wanda zai iya bincikar wayar, lallai ma to a yaushe ya aikata hakan oho, yanzu ga shi ya rufe wayar James ba mai iya bincike a cikin wayar, su kuma wayan da suka kama shi sun ɓuye layin daga hanyar sadarwa ma gaba ɗaya, dan kada a gane location ɗin da suke a kama su.
(Lallai akwai cakwakiya, ni dai na haɗa kayana zuwa wajen su Rimsha wato kasar Yarabawa)
💖💖Ilorin State💖💖
Kamar yarda Ahmad ya yi alkawari haka ya zo da asuba ya tashe su, Already ita Rimsha ta tashi tana zaune kan dadduma bayan ta ɗauro alwala, ta kwana tana sallah tana yi wa Allah godiya daya sanya zata koma gida.
Bayan sun yi komai, sun shirya cikin abaya da hijabi, sun kuma ɗauki kayan su, har da takardun girkin Rimsha ba abinda ta bari, shi kuma ya ɗauki trolley guda biyun da ya kawo, ya sanya a bayar motarsa. Misalin karfe shida ya fita da su a motarsa zuwa airport.
Suna isa airport ya yi musu passport da yake yana da goyon baya, ya samu alfarma sai aka yi musu komai cikin sauri, wayannan kananan trolley da ya shigo da su da daddare, su ya fitar daga bayan motarsa ya bawa ko wacce ɗaya.
Har hawaye suka yi masa wajen nuna matukar godiyarsu a gare shi, murmushin kawai yake yi musu, amma shima a cikin zuciyarsa ba daɗi yake ji ba, domin ji yake yi tamkar zai rabu da wani sashe na rayuwar sa, kamar sun yi shikaru a tare.
Sai da ya shigar da number wayarsa a wayoyinsu, sannan ya ɗauki number ko wacce ya tura musu kati daga Account ɗin sa, bayan ya gama ya basu wayoyinsu ya ce suyi saving numbersa da kansu, sai murna suke yi za su koma gida.
Zama suka yi a ɗaki na musamman da aka basu suna jiran lokaci ya cika, dan an ɗaga tashin jirgin sai karfe 8 daidai, haɗaɗen abinci yasa aka kawo musu dan yin breakfast.
Da farko sun ki cin abinci saboda tsabar murnar za su koma gida, ko yinwa basu ji, sai da ya matsa musu ya nuna ya ɓata rai sannan suka ci, fried rice ne ya ji kayan kamshi da kayan haɗi, sai ta shin kamshi yake yi.
Kaɗan suka ci abincin sannan Ayla ta sha coca colar da aka kawo musu, ita kuma Rimsha ta sha ruwa kawai.
Bayan sun kammala ne ya tsare Rimsha da ido yana kallon ta, sai faman sunkuyar da kanta kasa take yi tana wani ɗaure fuska, dan bata son kallon nan da yake yi mata, tun jiya da ta fahimci hakan bata sake yin murmushi a gaban shi ba.
"Queen of beauty idan kika koma wajen mama zaki tuna ni kuwa?" Ya jefa mata tambayar yana mai do da kallonsa kan dogayen yatsun hannunta masu ɗauke da kyawawan kumba (farce) farare tas.
"E zan tuna ka" wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya ce "Amma idan ba damuwa ina son ki bani wannan sarka da na gani a wuyarki jiya, dan Allah ina son in samu wani abu da ya kasance daga wajen ki yake, dan na riƙe a waje na na rinƙa tunaki da shi".
Wani dum-dum ta ji gabanta ya bada bugu, domin kuwa idan ba mutuwa ba bazata iya yarda wani abu ya rabata da wayan nan sarkokin ba, guda biyu ne a wuyarta, yan sirara, ɗaya na zinarin da gwaggo ta bata ɗayar kuma mum ɗinta ta bata, ba zata iya rabuwa da ko kwaya ɗaya ba.
Ganin ta yi shiru ya sa ya fara rokarta da Allah, hawaye ta fara yi, yau ga wanda ya ceci rayuwarsu, kuma zai haɗa su da iyayensu, ya musu babban taimako arayuwa, yau yana bukatar wani abin a gare ta da ya kasance ba zata iya rabuwa da shi ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Murya kasa-kasa ta ce "Yaya Ahmad ka zabi duk wani abin da kake so a tattare da ni, zan baka amma banda wayan nan sarkan".
Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali "Kome nake so kin yi alkawarin zaki bani?" Gyaɗa masa kai ta yi tana faɗin "E matukar bai saɓawa Allah ba".
Ita dai Ayla ido kawai take binsu da shi.
Murmushi ya yi kafin ya ce "Ki yi mini alkawarin zaki kaunace ni, ki yi mini alkawarin zaki bani soyayyar ki, kiyi mini alkawarin idan kin koma gida zaki sanar da su mamaki ina son ki, kiyi mini alkawarin ba zaki kula ko wani ɗa namiji ba, kada kuma kice mini a'a domin kece kika ce kin yi alkawarin na zaɓi ko me nake so zaki bani, to wannan shine abin da nake so". (Babbar magana)
Kasan cewar batasan illar yin hakan ba, bata ma san menene soyayyar da yake magana a kai ba, kuma batun kula maza dama ba ta kula kowa, kananun shekarunta ya sata ta yi wani kuskuren da ba zai yi mata kyan gani ba gaba, haka ta buɗe baki ta ce masa "Na yi maka alkawari hakan" (Tashin hankali)
Bata san wanene Ahmad ba, bata san daga ina yake ba, bata san shin mutune ko aljaniba, bata san cewa idan ya kasance aljani bata isa ta warware wannan alkawarin ba, bata san cewa ko mum ɗinta ta ji abin da ya faru ba makawa sai ta bawa Ahmad aurenta ba, a kananun shekarunta bata san duk wannan kuskure ta aikata ba, ita kan ta Ayla dake zaune tana kallonsu babu abin da ta sani game da hakan.
A haka har lokacin tashin su ya yi, suka wuce ya raka su suka shiga cikin jirgi, yana ɗaga musu hannu har suka tashi, suna tashi ya canza mata sunan da ya sanya a number ta, daga Queen of beauty zuwa My wife.
(Yau akeyin ta, *TRIPLETS* yanzu zai fara ɗaukan zafi, ku gyara zama dan jin yadda wasan zai kaya, yanzu muka fara ɗan kutsa kai cikin labarin. Ma'assalam, na barku lafiya sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu a airport na Kaduna)
💖💖TRIPLET'S💖💖
35-36
💖💖RIMSHA💖💖
Tun da suka shiga jirgi waya suke yi da Ahmad, domin jirginsu na tashi ba jimawa bayan ya koma gida ya kirata a waya, haka ta ɗauka sai surutu yake zuba mata, ban da E da a'a ba wani abin da take ce masa, da yake ya san halin ta ɗan zaman da suka yin nan, sai bai wani damu ba, ya cagaba da janta da hira har Allah yasa jirginsu ya sauka a airport lafiya.
Suna sauƙa ya gaya mata in da zata tari mashin tace a kai ta, to kawai ta amsa mashi da shi, sannan ya bata daman sararawa wajen katse kiran.
Bayan sun sauƙo suka rungumi juna da Ayla suna kuka amma haka kowacce ta ɗauki trolley ta, za su tafi sai suka ji magana daga bayan su.
Cikin sauri suka juya ɗaya ne daga cikin ma'aikatan dake wajen, sannu ya musu suka amsa sannan ya ciwo kuɗi daga aljihunsa, ya kirga naira dubu ashirin-ashirin ya basu, kin karɓa suka yi saboda basu san shi ba, hakuri ya basu sannan ya kira Ahmad a waya ya haɗa su da shi.
Rimsha ce ta karɓi wayar suka gaisa, Ahmad ya ce mata ta karɓi kuɗin mancewa ya yi bai basu ba, amma tun jiya ya ciro kuɗin a kan zai basu sai da suka zo tafiya ya manta, shiyasa ya kira waya airport ɗin domin a basu.
Jin haka yasa suka karɓa suka yi godiya sannan suka sha kukan rabuwa da juna suka tafi.
Ita Ayla ta hau mashin zuwa gida, ita kuma Rimsha zuwa tasha, Ayla taso Rimsha tazo su je gidan su, ko da a tsaitsaye ne Rimsha ta ga gidan su, amma ina Rimsha taki yarda burinta kawai ita ma ta isa ga nata iyayen, hakan yasa Ayla ta hakura suka yi bankwana.
Lokacin da Rimsha ta je tashar kawo sai da ta tambayi ina ne wajen motar Katsina, wani bawan Allah ya nuna mata.
Ganin yadda ake ta kallonta ya yi mata yawa ne yasa ya sayi face mask da ake saidawa a wajen, ta saya ta sanya a fuskarta.
Lokacin da taje wajen motocin Katsina, ta yi Sa'a mutun biyu ya rage ake jira, Ahmad ya kirata a waya, shine take gaya masa saura mutun biyu mota ya cika, sai ya umarce ta da ta bawa driver wayar, ba musu ta nemi driver ta ba shi wayar.
Nan suka yi magana da Ahmad ya ce da driver a tashi motar yanzun nan zuwa Katsina, ya kama mata kujeran gaba dukka ita kaɗai, ma'ana zai biya kuɗin mutun biyu dukka, to driver ya ce, sannan Ahmad ya rufe da cewa ya turo mashi account number sa bari ya sanya mata kuɗin motar, to ya ce sannan suka yi sallama.
Miƙa mata wayarta driver ya yi ya ce ta rubuta Account number sa, yana karanto mata tana sanyawa, abin mamaki shine sunan GAR Rimsha ta sanya a matsayin password na wayarta, haka ta rubuta account number ta turawa Ahmad sannan driver ya buɗe mata gidan gaba na motar ta shiga ta zauna, ba ɓata lokaci a ka loda kaya, passengers suka shiga.
Bai fi minti ashirin ba da zuwanta motan su ya tashi zuwa Katsina, lokacin da motan su zai tashi Ahmad ya kirata, suka fara hira.
Haka zalika lokacin da motarsu ya tashi bai fi da minti biyarba, Ayla ta shigo park ɗin da sauri tana neman Rimsha tana kuka.
Wani bawan Allah ne ya gaya mata motar Katsina ta tashi bai fi minti biyar da suka wuce ba.
Zama tayi saman wani dakali a wajen ta kifa kanta da gwiwowinta ta ci kukanta mai isarta, ga kuma trolley ta a gefenta, kuka ta yi har na tsawon minti goma, sannan ta ɗago ta goge hawayen ta, ta fito da wayarta tana kokarin kiran Rimsha, sai taga ashe sun mance basu karɓi number juna ba.
Tana hawaye ta kira layin Ahmad dan ya tura mata number Rimsha ɗin, shima Ahmad ɗin da kyar ta iya kiranshi, dan ba wani sanin kan waya ta yi ba, yanzu ma Rimsha ce ta koya mata wasu abubuwa kaɗan a cikin jirgi kafin su sauƙo.
Lokacin da ta kira Ahmad yana waya da Rimsha kiran bata shiga user busy yake nuna mata, ta gwada yafi sau goma, daga karshe dai ta hakura ta miƙe sai kallonta jama'a ke yi, haka ta ja trolleynta ta fita daga park ɗin.
Tana tafiya tana hawaye har ta hau kan titi ba tare da ta sani ba.
Ji kake wani irin kara mai sauti ya tashi, wata mota ce da ta yi kokarin taka wani irin mahaukacin burki dan kada ta taka Ayla, amma duk kokarin da mai motarnan ya yi wajen taka birki, sai da motar ta ɗan bugeta kaɗan, Allah ya tsare ba wani ciwon da ta ji, faɗuwa dai ta yi kasa ta ɗan buga kanta da jikin bambam motar, trolley ta da wayarta suka faɗi kasa, ɗan gefe da ita.
Kan kace me jama'a sun taru a wajen, mai motar ne ya fito cikin sauri yana faɗin "Ya subhanallah" daddyn Jelly ne da kuma Irfan, sune a cikin motar, daddy'n Jelly ke tuka motar, suna tafiya suna hira, amma hankalinsa yana kan tunanin in da jellyn sa take, bai ankara ba sai ganin Ayla suka yi a gaban su za su taka ta, Allah ya tsare daddy'n Jelly tsohon hannune a jan mota, ya yi kokari wajen taka birki.
Sannu suka yi mata ta ɗan bugu, ta kasa yi musu magana, saboda wani jirijiri da take gani.
Irfan ne ya fara tsugunawa a gaban ta yana faɗin "Kina cikin hayyacin kuwa?" Kasa magana ta yi, sai ido kawai da take binsu da shi, ga idanun nata cike da kwalla.
Ɗagowa Irfan ya yi ya kalli daddyn Jelly "Bappa Maik ina ganin mu kai ta asibiti, da alama ta ɗan bugu, dan bata cikin hayyacin ta" cikin sauri daddyn Jelly ya ce tom ya ɗauko ta.
Kamar yar baby haka Irfan ya ɗauke ta, daddyn Jelly ya buɗe masa gidan baya na motar ya sanya ta, sannan ya dawo ya ɗauka mata trolley ta, sai dai babu wayar har an samu masu dogon hannu sun yi gaba da shi, da yake su Irfan basu san da zancen wayarta ba, sai basu wani damu da duba wayar ba, suka tashi motar suka bar wajen.
"Suna tafiya a hanya ne Irfan ya sake jarraba yi mata magana "Sannuki, ya sunan ki?".
Da kyar ta iya buɗe baki saboda sara mata da kanta yake yi "Sunana Ayla". Ruwan faro dake gabansu ya ɗauka ya miƙa mata yana mata sannu.
Ba musu ta karɓa ta sha, ba su kai ga isa asibiti ba, ta warware ta fara magana sosai.
Koda suka je asibitin ma, lafiya lou da a ka dubata, ba wata matsala, sai dai yan magunguna da ba'a rasa ba, aka rubuta mata, Irfan ya sawo mata.
Bayan sun koma cikin mota ne, daddy'n Jelly ya ke tambayar ta ina ne gidansu su mai da ita gida su bawa iyayenta hakuri.
Jin wannan tambayar tasu bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, juyowa suka yi a tare suna kallonta.
Irfan ne ya fara tambayar ta lafiya take kuka, kasa magana ta yi, yana kokarin sake tambayar ta, daddyn Jelly ya dakatar da shi, ta hanyar ɗaga mashi hannu, shiru ya yi yana kallon yadda take kukan.
Shiru suka yi suna kallonta, basu yi mata magana ba, kuma basu tada motar sun ta fi ba, tsawon minti talatin sannan fa, daddyn Jelly ya fara rarrashinta yana faɗin "Ya isa haka, kinga ai mun barki kin yi kukan ko, to yanzu ki huce haka, zuciyar taki ta ɗan sauka ki gaya mana me yake faruwa?".
Sai da ta kara minti goma sannan ta iya buɗe baki ta gaya musu cewa, ita bata da kowa, kallon juna suka yi sannan suka dawo da kallonsu kan kayan da yake jikinta, gata tsabtsab, ga kaya mai tsada a jikinta, kuma ta ce bata da iyaye to fa, shi kam Irfan har da kallon trolley ta dake gefenta.
Sake tambayar ta daddyn Jelly ya yi a kan ta natsu ta gaya musu ina ne gidan su.
Ba wani ɓoye ɓoye ta basu labarin tun ranar da aka sace ta har zuwa yau da ta koma gida, bata ga mamanta ba, gidan ma an rushe shi ana sake yin wani ginin, ta tambayi mutane da dama a unguwar amma sai su ce mata su ma basu san in da maman nata ta yi ba, wasu suce ta haukace wasu suce ta mutu.
Daddy'n jelly sarkin saurin kuka, tun da ta fara bada labari yake yi mata ruwan hawaye, har ta kammala. Domin su tabbatar da zancen ta sai suka wuce anguwar ta su, ai kuwa sun gani da idanuwansu, har gidan su Ayla da aka rushe sai da ta kai su suka gani da idonsu, sannan sun tambayi mutanen layi, abin da ta gaya musu