Showing 354001 words to 355604 words out of 355604 words
mata kafin ya yi mata sallama ya miƙe daga saman table ɗin ya nufi waje yana sallamar Areef.
Bayan Areef ya katse kiran ne ya ce mata "Ki je ki ɗauki abinci ki kaiwa Lion, ki kula sosai wajen zuba mashi abinci, nima ina nan zuwa bedroom ɗin nasa yanzu, baya cin abinci sosai, dan haka kaɗan zaki zuba mashi, yanzu dai ɗauko magani a cikin A box ɗin can bari na shafa maki a ciwukan naki".
To ta amsa mashi da shi sannan ta miƙe ta ɗauko ta kawo mashi, har zai shafa mata sai kuma ya fasa domin idan ya shafa mata ta je zubawa Lion abinci ya ji warin maganin nan to wata azaban zai sake yi mata, shi idan zai ci abinci ya fi son ya ji iya kamshin abincin ne kawai, idan ya ji wani kamshi a wajen bayan wannan da kuma perfume to za'a samu matsala, shiyasa sojojinsa suke matukar taka tsantsan akan kada wani kamshi ya saɓa dana abincinsa idan za su kai mashi abincin, haka zalika bodyguards suma suna taka tsantsan sosai wajen gani babu wani kamshi a tattare da su idan za su zuba mashi abinci, abin da suke wanke mashi kwanikansa ma abu ne na daban, Lion yana da bala'in tsarine a rayuwarsa wadda duk wanda zai zauna da shi to sai ya kai zuciyarsa nesa kamar nisan sama da kasa kafin ya iya zama da shi.
Jiki ba kwari zuciyarta sai bugawa yake yi, haka ta hakura ta yunkura zata miƙe, ɗan riƙota ya yi ya shiga kara mata karfin gwiwa akan zata iya kada ta sare. Bai kyaleta ta tafiba sai da ya ji ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya alamar ta samu kwarin gwiwa kenan, sannan ya kyaleta ta fito ta nufi Kitchen.
Mark ta samu a kitchen ɗin ya gama haɗa abincin Lion yana haɗa na Areef da na Imran, sannu ta yi mashi, bai amsa ba kuma ita ma bata damu ba domin dama ba wani son yi mashi magana take yi ba.
Wucewa ta yi zata ɗauki abincin, wani irin tsawa ya daka mata wadda ya sanyata dafe saitin zuciyarta take yi mata barazanar faso kirjinta ya fito waje tsabar bugawa da yake yi da karfi karfi.
"Ke mahaukaciyar ina ce da zaki ɗauki abincin oga ba tare da kin wanke hannayenki ba? So kike yi ki ja mani wata bala'in ko? Idan baki matsa mani a nan kin je kin wanke hannunki ba sai na ɗauke ki da marin da sai ya sanya ki ganin mutuwa ido da ido!!".
Duk wannan magana da Mark yake yi bai fa juyo in da take ba bare ya kalleta, ta wutsiyar idanunsa ya kalli zata ɗauki abincin, shi haka Allah ya yi shi, kusan irin Lion yake, idan yana abu baya ɗauke kallonsa a kan abin da yake yi, baya da yawan magana kullum gum kamar kurma, kamar dai ogan nasa, haka zalika baya shiga shirgin kowa, aikin gabansa kawai yake yi, sai dai idan kai ne ka shigo gonarsa, sannan ne fa zaka yabawa aya zaƙ, idan baku manta ba na gaya maku Mark renon Romeo ne, to fa shima sai a hankali kusan irin ogan nasa ne, sai dai ko rabin ogan bai kai ba a iya tsari, izza, izaya, ka'ida, da nuna isa akan koma waye.
Wucewa ta yi ta je ta wanke hannunta fes, sannan ta dawo ta ɗauki abincin, yau ma da kyar kamar zata faɗin saboda nauyin tray ɗin, Allah sarki bata saba ba. Ba'a kayan abincin jiya aka zuba mashi abinci ba, wasu sabbine launin sky blue, kayan abincin jiya ma a ɗakinta ta barsu Imran ne ya fitar da su, kuma da ya fitar zai mayar Kitchen ɗin sai ya manta ya barsu a saman table na palon sama.
Tun da ta doshi kofar ɗakinsa gabanta ya kara tsananta bugun da yake yi, ziciyarta tamkar zata fito waje saboda tsoro.
Sallama ta yi mashi a bakin kofar ɗakinsa, kamar dai jiya shiru bai amsa ba, yana zaune saman sofa set dake a cikin ɗakin, ya yi shiru yana latsa wayarsa, jikinsa na sanye da three quarter launin Ash color, daga ta sama kuma yau army t-shirt ne a jikinsa, ba ƙaramin kyau ya yi wa kayan ba, ya saki dark black curly hair ɗin nan nasa har kafaɗarsa, kamar dai kullun sai tashin fitinannen kamshi yake yi, da alama kuma yau sarautar tasa ma ta fi ko yaushe, da alama dai akwai abin da ya faru, ko a gidansu na Washington DC ko kuma a wajen aikinsu, domin ya sanya a rufe mashi TGA a cikin ɗaki na tsawon kwanaki ana hora shi, dan Tga ya shiga gonarsa sosai a ƴan kwanakin, to yau da safe ya sanya a fitar masa da Tga ɗin domin dole ko da yana cikin rashin lafiya na horon da ya sha dole ya jagoranci tawagar da za su dimfari G.M.A jibi Friday, sannan ya sanya sojojinsa zarata mada katti guda biyu a kofar gidan Josephine akan su tsareta ko nan da kasuwa bai yarda ta je ba, da yake tasan halin ɗan nata, sai bata yi gardama da sojojin nasa ba, ta hakura ta zauna a gida, dan ta san ba ƙaramin aikin sa bane ma ya sanya a ɗaureta da sarka, kuma dole ta ɗauru tun da ta riga da ta zubar da girmanta na uwa a idanunsu, hakan yasa kawai ta hakura take bin ɗan nata sau da kafa kamar rakumi da akala.
(Kai gaskiya Lion duniya ne, anya akwai biyunka kuwa? Yanzu duk wannan bala'i da zafin rai na Josephine ka sanyata natsuwa bata shirya ba, shiru kake jin Josephine, kada ku mance labarinta da daddy ya bada lokacin da suke school, kunga kuwa mafaɗaciya ce sosai tun da har ta iya marin William a lokacin, sannan duk tsagerancin da Dangerous Boss wato William ya yi amma Lion ya nitsar da shi yanzu kamar ba dangerous Boss ba, Allah ku yarda da maganata, Lion ɗan duniya ne na bugawa a jarida, ko da yake hakan ma ya fi tun da su suka riga da suka zubar da girmansu na matsayin iyaye a idanun yaran nasu, kuma dama mafi yawa kun san turawa haka suke da ƴaƴansu, wasu ma ƴaƴan suke komawa iyayen suna bawa iyayen nasu umarnin tare da controlling ɗinsu, bare kuma abu ya haɗu da Kristanci, ai sai dai muce Allah dai yasa mu dace)
STORY
Da yake jiya taga bai amsa mata sallamarta ba, sai ta yi tunanin yau ma bari kawai ta shiga ɗakin nasa kai tsaye.
Wani irin sanyi ta ji ya ratsa dukkannin ilahirin jikinta lokacin da ta sako kafarta a cikin ɗakin, ko'ina na ɗakin fes saboda Imran ya zo ya gyara mashi tun kafin ta tashi barci, da alama kuma sai ya hukunta ta na tsallake aikinta da ta yi na gyaran ɗakin nasa, domin time da Imran ya gyara ɗakin baya nan yana cikin toilet, da ya fito kuma sai da ya ce da Imran ɗin aikinsa ne da zai yi, kunga kenan zata karɓi hukunci domin duk abin da ya yi magana akai to ta shafe shi ne.
Yau daki kallon in da yake dan tana tsoron ya kamata tana kallonsa tun da baya son kallo, kuma da yake ya haɗu ne ma da yau yana saman sofa ne suna kusa, dan sofar kusa da carpet ɗin da take ajiye abincin, shi ne ma ya kara sawa taki kallon nasa.
Tazo daidai zata wuce shi ta je ta ajiye mashi abincin ne, ya daka mata ƴar tsawa na cewa ya ce mata yana da buƙatar abinci ne, ko an gaya mata ana kawo mashi abin da bai bukata bane?.
Wannan tsawa da ya yi mata ne ya yi sanadiyar mugun tsoratata da har ta saki tray ɗin abincin ya faɗi kasa komai na ciki ya tarwatse. BABBAR MAGANA.
Gaba ɗaya fruits dake a ciki sun watse, wani apple ne ya yi tsalle ya dake shi a kirjinsa kafin ya dawo ya bugi screen ɗin wayar hannunsa, da yake ba wani riƙe wayar ya yi sosai ba sai wayar ta faɗi kasa a saman carpet dake tsakiyar set ɗin.
Gaba ɗaya abincin sun zube kaza gudarta tana kwance mashi a tsakiyar ɗaki, ga shi jikin kazar duk kayan haɗi da akayi baking nata da shi. Tiles nasa fari tas sai kyalli yake yi duk ya ɓaci jaga jaga da miya.
Jikinta wani irin mugun kerma yake yi, ta kasa tsayawa akan kafafunta a in da ta durkushe a wajen domin tasan ba makawa zata hukuntu ba kaɗan ba, jiya ma da ba wani abin ta yi mashi ba ya azabtar da ita har haka, ina ga kuma yau da ta ɓata mashi ko ina na ɗaki, bayan haka kuma ta sanya apple ya dake shi a kirji sannan ya patale mashi wayar dake a hannunsa, ya ilahi ya lillahi, ita wlh ko da faɗuwar gaba da tsinkewar da zuciyarta keyi tare da bugawa ma kawai ya isa ya kasheta ba tare da wani hukunci nasa ba. Shi ne ta gudu ne ko ta tsaya? Idan ta gudu ma ina zata je a duniyar nan ta tsirawa hukuncinsa? Ya ilahi ya lalliahi!..
A zafafe ya ɗago kansa ya.................
Alhadulillah Alhadulillah Alhadulillah, Allah na gode maka da ka bani iko da dama na kammala book 2 na wannan littafin, kuskuren dake a ciki Allah ka ya fe mana, gyaran dake a ciki kuma Allah kasa mu yi amfani da shi, Allah ka ba mu dace wa, nan na kawo karshen book 2 sai mun haɗu a book 3 idan Allah ya kai mu nan ba da jimawa ba dan jin yadda wannan cakwakiya zata warware. Keep praying for me My people's, one love 💗 💘
SSG Palace Gujungu