Showing 279001 words to 282000 words out of 355604 words
fa Abbi ya ce a'a sai dai ya tafi ya bar Rimsha domin ita ta zo kenan.
Dawo da kallon shi kanta ya yi, kamar zata yi kuka ta yi kasa da kai, Imran ya rasa ya zai yi sai ya ce "Bappa kayi hakuri gobe zan tattarota da kayan ta dukka na dawo da ita, amma dan Allah yanzu ka barmu mu kowa a tare kamar yadda muka zo, kuma dan Allah kada ka tambayi dalilin".
Kallon Rimsha Abbi ya yi domin ya tambaye ta ko tana son ta bi Imran, bai kai ga tambayar ta ba, sai ya kalli tsantsan kaunar hakan a kan face nata, dan haka sai ya ce tom su tafi, domin baya son su yi mata abin da ba zata ji daɗin sa ba, kuma a tunaninsa, ai a gidan Abba suke, wato dai gidan su Imran ɗin, hakan yasa bai damu ba ya ce su tafi.
Riƙo hannunta Imran ya yi suka fice daga palon suna yi masu sallama.
Yana fita ya kira daddyn Jelly a waya akan ya fito su yi sallama za su koma, daddyn Jelly ya so hana su komawa, ya so suma su kwana cikin ƴan uwansu, amma sam Imran ya ki yarda, domin yasan tabbas Lion yana kewarsa, kara kawai yake yi mashi yasa bai kira shi a waya ba, kuma yasan ita ma Rimsha tana kewar Lion ɗin, kunyarsa kawai take ji yasa bata ce mashi su koma gida ba.
Haka daddyn Jelly ya hakura ba dan ya so ba, ya ce masu baya gida kuma yana da ɗan nisa da gida, su je kawai sai sun sake haɗuwa.
Da tom Imran ya amsa da shi sannan ya katse kiran ya shiga mota suka bar gidan.
Su Abbi kuwa bayan sun kammala cin abincin, saman sofa suka dawo suka zauna aka dasa hira daga in da aka tsaya.
Yanzu Imran ya tafi Akil sai abin da ya cigaba a pagen nunawa matarsa kauna, dama baya son jefa ɗan uwan nasa a cikin damuwa ne yasa ya daure baya tumurmusan soyayyarsa, yanzu kuma Imran ɗin baya nan.
Kusa da Wife ɗin sa ya zauwa dama suna cin abinci ta yi ta yi mashi tsiya ta hanyar taɓa mashi gaba, so a kusa yake, shi hiran nan ma da suke yi ba hakan yake so ba, so yake kawai su shige cikin ɗaki da abarsa su murji juna son ransu, amma yanzu su Abbi sun takura masu.
Akila da Irfan kuwa sai hira suke yi, amma kuma ga dukkan alamu kaso 80 cikin ɗari na hankalinta yama a kan wayar tane, tana ta fama da saƙon ɓoyayyen masoyi, duk wani motsinta yana gani, kanta ya kullu, ga shi ta kasa gayawa wani wannan magana, tabbas ba yaya Irfan bane, kuma ma ba ɗaya daga cikin ƴan gidan nan bane, to waye ne?.
Ta shiga ruɗani abin ya kuma ƙulle mata kai sosai, lallaɓawa Irfan ya yi cikin dabara ya kirata akan ta zo su je waje.
Cikin dabara suka zame zuwa waje abinsu.
Suna fita ya riƙo hannayenta yana tambayarta me yasa bata bashi abinci a baki ba, kashe wayar tata gaba ɗaya ta yi dan ma kada saƙon ɓoyayyen masoyi ya sake shigo mata waya ya raba mata hankali gida biyu.
Bayan ta kashe sai ta tattara hankalinta gaba ɗaya izuwa kan ɗan uwan nata, cike da kulawa ta ce "Yaya Irfan ai dan su Abbi sunanan ne, badan haka ba da na baka ai".
Jin ƴadda take magana ne yasa shi ƴin murmushin, domin tun ɗazun rabon da ta yi mashi magana haka, amma da yake yanzu dare ne kuma sun fito wajen da akwai ɗan duhu duhu sai ta saki jiki ta fara yi mashi hira, dan baya samun ganin face nata sosai.
Abin mamaki kuma abin al'ajabi sai ta ga wayarta ta kunna kanta da kanta.
Wayar na kunnuwa kuma saƙon ɓoyayyen masoyi ne ya shi go, a wannan karon da turanci da kuma hausa ya rubuta mata saƙon, ba gaba ɗaya hausa ya yi mata ba.
"Meyasa kika kashe wayarki? I don't like that, so ki kula, yanzu dai na kunna abata" ɗago idanu ta yi ta kalli Irfan dake a tsaye ya zuba mata idanu, kallon hannunsa ta yi kwata kwata ma babu waya.
A tsorace ta ce "Yaya Irfan ina wayarka?" Hannu ya sanya a aljihunsa tare da ciro wayar ya mika mata yana faɗin "Ga shi nan, ya naga kamar yanayin ki ya sauya?".
Girgiza mashi kai ta yi alamar ba komai, amma wannan lamari ya fara sakata a cikin ruɗani, ta yaya za'ayi ta kashe wayarta kuma a kunna mata? Wannan wace irinyar abu ce.
Bincike ta fara yi a wayar Irfan, bawan Allah kwata kwata ma bai taɓa turawa mutun saƙo ba, yanzu ta ma dai na zarginsu, domin ba ta yadda za'ayi ta kashe wayarta tana ruƙe da shi a hannunta kuma ace mutun ya kunna mata ba tare da ya karɓi wayar ba, ba zai yi wu ba dole wannan aiki sai dai Aljani.
Miƙa wa Irfan wayar sa ta yi tare da kakalo murmushin dole tana son tasa kada ya kawo zargin komai a ransa.
Ta kuma yi sa'a bai kawo komai a ransa ɗin ba, suka cigaba da hiransu.
Ɓoyayyen masoyi dai bai kyaleta ba sai da ya sake yi mata saƙo akan kada ta rinƙa yi wa ɗan uwan nan nata murmushi, shi kaɗai zata rinƙa yi wa murmushi, sannan shi ba zai hana ta kula kowa ba, shi zai kwata wa kansa ƴanci ta yadda ita da kanta ba zata sake yarda da kula kowa ba, so yanzu ta yi hiranta da koma waye, yana nan tafe ya ɗauketa kowa ya huta. BABBAR MAGANA.
Wannan saƙon ya razana ta sosai kenan wai duk abin da take yi yana kallonta? Yanzu ta gama saddakarwa gamo ta yi wlh.
Jikinta har kerma yake yi ta ce "Yaya Irfan mu koma cikin gida sanyi nake ji" mamaki ne ya bayyana akan face nasa, sanyi kuma, ya tambaya yana kare mata kallo.
Ganin yadda jikinta ke kerma ne yasa ya yarda e sanyi take ji, amma ya yi mamakin hakan domin yau garin kwata kwata ba bu sanyi, sai ma zafi da ake yi dan an kwana biyu ba'ayi ruwan sama ba.
Bai wani damu sosai ba, ya riƙo hannunta suka nufi cikin gida, amma ya sha mamakin ganin yadda jikinta yake ta faman kerma a lokaci guda.
Suna isa bakin kofar palo ya saki hannun nata ya juya ya nufu part nasa yana faɗin "ki je ina zuwa" to ta amsa mashi da shi sannan ta wuce da wuri.
Binta da kallo ya yi yana mamakin sauyawar ta a lokaci guda haka, to me yake damun tane? Ya tambayi kansa da kansa, tambayar kuma da bashi da amsar ta.
Jikinsa a mace ya juya izuwa part nasa dan ya yi wanka yana jin zafi, abin da ya kara bashi mamaki kenan, shi yana jin zafi yana son ya zuba ruwa a jikinsa, ita kuma ta ce sanyi take ji, wannan abin abin dubawa ne.
Ita kuwa tana shiga palo da kyar ta iya yi wa su Abbi sannu sannan ta wuce sama, sai sauri take zubawa, basu kawo komai a ransu ba, sun yi tunanin fitsari ne yasa take sauri hakan.
Tana shiga bedroom ɗin nasu ta haye saman bed tare da jan bargo ta shige tana mai da numfashi, yau ta ji abinda ya girmewa shekarunta.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, tana tsaka da tunani ta ji shigowar saƙo wadda ko bata duba ba ta san shi ne ɓoyayyen masoyi ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun ta fara furtawa Baiwar Allah, kin ɗaukar wayar ma ta yi bare kuma har ta duba saƙon, gaba ɗaya ji take yi kamar ta yi ta kurma ihu har sai muryarta ta daina fita ko zata ji sauƙi.
Kiran wayar tata aka fara yi, a hankali ta kai kallonta kan wayar, wannan number dai ta unknown ita ce ke kiranta, dafe kanta ta yi tare da fara hawaye.
Har kiran ta kashe bata ɗauka ba, wata kirar ne ta sake shigowa, ita ma ta kashe, sai a karo na uku ne ta ɗauki kiran murya kamar zata yi ihu ta ce "Waye ne dai Allah?" Daga ɗayar ɓangaren wata zazzakar murya wadda tana da tabbacin da wuya asami mai irin muryar nan a cikin mutane, a nutse ya amsa mata da "Heartbeat da farko dai sai dai in ce maki am so so sorry, na tuba ba zan kara ba, na sanya my angel cikin damuwa, ayi mani afuwa na tuba ba zan kara ba".
"Waye kai?" Ta faɗa tana matse kwallar da ta taru mata a cikin idanunta.
Daga ɗayan ɓangaren a nutse ya ce "Masoyinki na gaskiya, ni ban zo wajen ki da nufin na cutar da ke ba, dan haka ki saki jikin ki, ki yi hakuri ki daina tsorona hakan ya isa".
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "Amma da gaske ka bani tsoro, to dan Allah ta ina kake ganina har kake ganin duk abin da nake yi?".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Kada ki tambaye ni please kin ji? Ba zan iya yi maki karya ba, kuma bana son na gaya maki gaskiya yanzu, abin da nake so dake kawai ki saki jikinki ki dai'na damuwa kin ji ko?".
To ta amsa mashi da shi. "Ina ɗan yin wani aiki ne, idan na kammala zan kira ki kinji ko? Idan ma ban kira ki ba zaki ga saƙona saboda ba ko da yaushe na cika kiran mutane mu ƴi magana ba, yanzu ma dan na ga kin shiga damu sosai ne, hakan yasa na kira ki, ki kula mani da kanki sosai and then ki daina tunanin cewa waye yake maki kaza waye yake yi maki kaza, dukka nine mai yi, ni nake controlling na wayar ki, so ki daina damuwa, sai an jima".
Yana kai karshen maganar ya katse kiran ba tare da ya jira amsar ta ba, miƙewa ta yi tana tunanun wannan zazzakar murya, anya akwai irin muryar nan a cikin diniyar mutane kuwa? Ta tambayi kanta, ga shi kuma a nutse yake magana ɗaya bayan ɗaya yake fitar da duk wani word, ga voice ɗin nasa kamar na yara.
A zahirin gaskiya muryarsa ya tafi da ita sosai, yana da zakin gaske, kuma daga ji koma waye ne, inma mutun ko aljani yana da kamala da natsuwa sosai.
Akila tafi danganta shi da Aljani, domin abubuwan da yake yi ɗan adam ba zai yi shi ba, lokaci guda ta ji wani irin azababben son shi ya shigeta, tunani ta fara yi akan massages nasa da yake cewa shi ba zai hana ta kuka kowa ba, amma zata dai'na kula kowa dan ra'ayin kanta, abin da kawai yake so shine ta dai'na yiwa kowa murmushin nan nata mai kayatarwa baya son gani, shi kaɗai yake so ta rinƙa yi wa murmushi.
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi, abin ya ɗaure mata kai, baiwar Allah ta sami shigar soyayyar farat ɗaya, wannan lamari ya zata kaya.
KADA KUGA LAIFINTA DOMIN FAƊA DA ALJANI BABU RIBA, DUK ABIN DA BAKA IYA GANINSA ZAKA IYA DANGANTA SHI DA ALJANI, TO BATA GANIN SHI BATA SAN WAYE BANE, MAI YI WU WA ALJANI NE DA GASKE, KUMA KO NI NA JI WANNAN ZAZZAKAR MURYA DOLE NA FAƊA TARKON KAUNA,🤨🤣 ITA FA ZUCIYA BATA DA KASHI🙄😒 DA ZARAR KA YI MATA ABIN DA TAKE SO ZATA KAMU DA SON KA CIKIN ƘANƘANIN LOKACI, TO DAGA KARSHE SAI DAI IN CE JUSTICE FOR ƊAYA DAGA CIKINSU KO MA DUKKANSU, JUSTICE FOR IRFAN OR MASOYIN ƁOYE OR DUKKANSU.
Ta jima zaune a saman bed ɗin kafin ta diro kasa sai murmushi take yi ita kaɗan, ta sami kwarin gwiwa da jikinta baki ɗaya, voice nasa ya gigita ta sosai da sosai
(Dan baki ji voice ɗin yaya Saif bane our Lion da kince na ɓoyayyen masoyi babu daɗi😌)
Sai yawon voice ɗin nasa yake yi mata a cikin kunnuwanta, zan tukansa ne kawai yake dawo mata cikin kunnenta, ya iya tsara kalamai.
Kai tsaye palo ta fito kamar wata zautatciya sai murmushi take yi.
Tana zuwa ta faɗa jikin Akil tana dariya, da yake ya san abin da yake tsakaninta da Irfan kuma ya ganta da waya a hannu, sai ya yi tunanin cewa kila da Irfan ta yi waya yasa take wannan murmushi baki ya ki rufuwa har haka.
Suna zaune a wajen sun lula dunuyar hira sai ga Hajiya Hadizatu ta dawo, cike da kirsa ta yi sallamar tana wani taunar chewing gum, dama ita ba baya ba wajen cin chewing gum, yadda kasa dan ita akayi company chewing gum ɗin.
Jikinta na sanye da wani dandantsetsen lace maroon color, ɗinkin A shape ne, kayan sun zauna a jikinta sosai, kyanta ya kara bayyana, ga wasu shegun gwalagwalai da ta yi kwalliya a hannunta da wuyarta, ta je taya yar uwarta murnar bikin Nawid ne a can ta wuni, kafarta na sanye da wani kafurin plat shoe mai ɗan iskan kyau, Hajiya Hadizatu ba baya ba wajen kashewa kanta kuɗi da sayan abubuwa masu kyau da tsada dan ta yi kwalliya da su, shiyasa take ƴar caras da ita, ta kuma yi sa'a tana da kyan jiki ga shape kamar me, ta yafo mayafin nan kalar takalminta wato white color, ga wani haɗaɗɗe kuma tsadadden hand bag irin na ƴan matan nan, shi ta ratiyo abinta.
Da gudu Umaisha ta tashi ta nufita da nufin ta rungumeta, cikin sauri Akil ya ruƙeta yana faɗin "A'a ki yi mani a hankali, ko so kike yi ki jiwa kanki ciwo ki jefani cikin tashin hankali ne?".
Ɗaure fuska sosai Ommu ta yi, a walakance ta fara yi masu kallon walaƙanci.
Sai da ta kare masu kallo tsab kafin ta tsai da kallonta akan Akil ɗin, kallon sama da ƙasa ta yi mashi kafin ta ce "Kai kuma waye? Daga ina da har zaka damatar mani da ƴata ta cikina daga zuwa ta rungumeni?".
A takaice ya ce mata "Mamallakin ƴar a yanzu, kuma har zuwa illah Masha Allah".
Kara ɗaure fuska ta yi tare da daka mashi tsawa "Kai ɗan talakawa ka iya bakinka kuma ka sakar mani ƴa tun da kai a gidanku ba'a baka tarbiya ba, baka iya girmama manya ba".
Ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, to ko Abbi ai ba zai gwada mashi kuɗi ba shi kaɗai ma bare kuma ace hadda iyayensa, lallai rashin sani ya fi dare duhu, Ommu bata san waye Akil ba, shiyasa har take ce mashi ɗan talakawa, bata san cewa shi kaɗai ma yafi gaba ɗaya masu kuɗin family'n ta kuɗi ba.
A takaice ya ce "Wife ku je ɗaki" ya kai karshen maganar tare da sakin hannunta.
A tare suka miƙe da nufin su tafi ɗakin, "zo nan Umaisha" Ommu ta faɗa cike da gadara da nuna isa, rai a ɓace Akil ya daka mata tsawa akan ta wuce ɗaki, kun san halinsa ya tsani a nuna cewa an fishi a waje, kallon Abbi Umaisha ta yi kamar zata yi kuka, jinjina mata kai ya yi alamar ta tafi ɗaki ta bi umarnin mijinta.
Da gudu ta wuce ɗakin su Aafia suka bi bayanta
Miƙewa Abbi ya yi, kusan kuma a tare suka miƙe da Aunty, a nutse ya ce "Akil ku je part ɗin Irfan ka ji?".
A kule Akil ya ce "Bappa ni gida zan wuce domin already raina ya riga da ya ɓaci, ba zan iya kwana a nan ba" ya kai karshen maganar tare da haurawa sama.
Zuba mashi idanu suka yi suna kallonsa har ya kurewa ganinsu.
Jim kaɗan ya dawo ruƙe da hannun Wife wato Umaisha, bai bi ta kan kowa ba ya nufi hanyar fita daga Palon.
"Kai karamin mara kunya mara tarbiya ina kuma zaka kai mani ƴa? Ko dai ita ma ƴar taka ce?" Cewar Ommu kenan.
Yana matukar mutuntata tare da jin kunyarta saboda Umaisha da kuma Irfan, ba dan haka ba yau da sai ya tsintsin ka mata maruka, kuma yasan darajar iyaye domin shima ba zai so ayiwa tasa uwar haka ba, dan haka sai bai kula ta ba, ya fice abinsa.
Tana ƙoƙarin sake yin magana sai ga Aafia ma sun fito tare da da Akila da Hanan, Hanan zata yi masu raki za su koma, Akil zai mai da Akila gida sannan ya wuce da Umaisha da Aafia gidansa.
Cikin sauri Ommu ta biyo su waje tana faɗin "Ku wuce cikin gida Aafia ke da Umaisha".
Bayansu shima Abbi ya bi ya fito waje, ita kuma Aunty ta haura sama abinta dan bata son hayaniya.
Kallon Abbi Aafia ta yi wadda shima yanzu ya fito ya biyo bayansu.
Cike da nuna isa da izza Abbi ya ce "Wuce Aafia ki bi yayanki ku koma kamar yadda kuka zo". Da sauri Aafia ta nufi cikin motar dan ma kada Ommu ta sake yi mata wata magana.
"Idan kuka bi wannan marakunya yau sai dai ku nemi wata uwar ba dai ni ba". Cewar Ommu kenan.
A fusace Abbi ya ce "Ku tafi abunku dama ai ku baku da uwa, ko kun manta ne? Ita ce ta reneku? Dan haka kamar yadda ta tafi ta mance daku ta rufe babinku, kuma ku rufe tata, ni ubanku ina mai baku umarni ku tafi".
Da sauri Irfan ya fito daga part nasa jin hayaniya a harabar gidan, ganin Ommunsu a wajen yasa ya gane ba Alkhari ake yi a wajen ba, hakan yasa ya ji wani irin ɗaci tare da ɓacin rai ya lulluɓe shi, zuciyarsa na mashi zafi tamkar zata fito waje hakan ya ke ji, har wani irin jiri mai karfi yake ji tana ɗebarsa, tunani ya fara yi akan yaushe Ommunsu zata yi hankali ta fara yin abubuwan Alkhari ne? Cike da karayar zuciya ya juya ya kowa cikin ɗakinsa, yasan ba zai iya tunkarar wajen ba, zuciyarsa zata iya bugawa, domin gaba ɗaya familyn su haka suke, suna sa zuciya sosai da sosai, sai dai na wani ya fi na wani, amma duk wanda ka taɓa a cikinsu ba baya ba wajen zafin kai da zafin zuciya, kuma hakan yasamo asaline na gadon shi da suka yi daga iyayensu, kakansu Abbi bafilatanin dajine mai bala'in zuciya, haka ita ma kakansu mace, akwaita da zuciya ba kaɗan ba, har suka zo suka haifi mahaifinsu Abbin shima yana da bala'in zuciya dan