Showing 249001 words to 252000 words out of 355604 words

Chapter 84 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2832

yi mafarkinsa?".

Jan dogon hancinta Malika ta yi tana faɗin "A lokacin da kike gayawa Ayla mana, kin san me nake so da ke?" Girgiza kai ta yi alamar a'a. "Good, abin da nake so dake shine kibi shawarar da Imran ya baki akan Saif kada ki yi mashi shisshigi, idan ba haka ba, zai iya halakaki, ni ba zan iya shiga jikinsa ba, kuma ba zan iya kwatarki a hannunsa ba idan yana baki a jikinki, domin ya fi karfin mu, yana da ayoyin da duk musulcin aljani matukar zai cuci wani to yana tsoron su, kin san akwai ayoyin da koda aljani musulmi ne zai ji tsoron su, Al Qur'ani mai girma maganin komai da kowa ne, sannan magana ta gaba akwai ciwo sosai a rayuwar shi ko in ce maki a rayuwarsu su ukun dukka, ki kula sosai, dan kamar yadda Imran ya gaya maki Saif ya wuci gaban tunanin ki, to haka ne, dan haka ki kula, bana son wannan kyakkyawar face ɗin naki ta saɓa kammani, dan idan ya yi maki mari ɗaya ba zaki ganu ba". Ta kai karshen maganar tana murmushi.

Murmushi ita ma Rimsha ta yi tana ƙoƙarin yin magana sai ta ga Malikar ta ɓace ɓat, hakan kuma ya yi daidai da shigowar Imran cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.

Da fara'a a kan face nata ta amsa mashi sallamar tare da ɗaga mashi gaisuwa, amsawa ya yi tare da tambayarta ta kwana lafiya. Da lafiya ita ma ta amsa mashi sannan ya ce ta tashi suje ta gaisheda Areef, to ta amsa da shi sannan ta miƙe, ya yi gaba ta bi bayansa.

Da sallama suka shiga ɗakin, idonsa biyu yana askar, lokacin kuma karfe 6 tayi.

Gefensa Imran ya zo ya zauna tare da miƙe mashi hannu akan su yi musabaha, hannu shima Areef ɗin ya miƙa mashi suka gaisa, Imran ya tambaye shi ya ji, Alhadulillah ya amsa da shi.

Daga ɗan gefe Rimsha ta tsaya tana faɗin "Ina kwana yaya Areef?" Sai lokacin ya kai kallonsa kanta, lafiya ya amsa mata da shi tare da dawo da kallonsa kan Imran yana faɗin "Ki zo ki zauna kusa da yayan ki mana, dan na san ko ba'a faɗa ba ke kanwar Prof ce tun da na ganku a tare" Duk wannan magana suna yin shine cikin harshen turanci, abin da yasa kuma ta gaishe shi da turanci dan ta ga Imran turanci ya yi mashi, hakan yasa ta gane kwata-kwata basu jin Hausa.

Juyowa Imran ya yi yana kallonta ya ce "Rimsha ki zo ki zauna mana?" To ta amsa da shi tare da karisawa kusa da shi ta zauna tana tambayar Areef ya jiki? Alhadulillah nan ma ya ce mata, daga nan suka shiga hirar duniya shi da Imran, ita kuma sai satar kallon shi take yi dan jini ba wasa ba kallon kamannin Lion take yi mashi.

Suna tsaka da hira sai ga Lion ya shigo dakin bakinsa ɗauke da sallama, time na yiwa Areef allura ya yi, miƙa mashi hannu Imran ya yi suka yi musabaha, ita kuma Rimsha sai kallon shi take yi, amma bata yi mashi magana ba, dan ta ji zancen Imran sosai. Yana sanye da wando three quarter fara tas da Round neck polo shirt mai bala'in kyau, ya ɗaure dark black curly hair san nan a baya, wannan guntu na gaban goshin ya sake ta, da alama kuma ya kara rage mata tsawo, domin yau bata wuce mashi iya sajensa ba, saɓanin kwana biyu da suka wuce ya kai mashi har gemu, kamar kullun sai tashin wannan fitinannen kamshin perfume nasan yake yi.

Hannun ta Imran ya kamo suka koma gefe saman sofa dake a cikin ɗakin suka zauna dan su bashi waje ya yi aikinsa ya fita, baya son ɓata lokaci.

Sai kallon shi Rimsha keyi, zafi zafi cikin zafin nama ya yi abin dake gabansa, bayan ya kammala ne ya ɗan zubawa Areef ɗin wayan nan dara-dara blue eyes ɗin nasa na yan mintoci kafin ya ce "How are you feeling now?" Jinjina kai Areef ya yi kafin ya ce "Alhadulillah am felling better" daga nan bai sake magana ba, ya ɗebo magunguna ya fara buɗesu yana tarawa a hannunsa, bayan ya kammala ya buɗe fridge dake a wajen ya fito da ruwa mai sanyi ya miƙawa Areef ɗin ya sha. Sai da ya tabbatar ya yi mashi duk abin da ya dace sannan ya nufi waje akan anjima zai zo ya kai shi toilet ya yi wanka. Magana ta gaskiya Rimsha dai daurewa kawai ta yi, amma har fitsari take ji saboda tsananin rikitata da kwarjininsa ya yi, ta ruɗe sosai, ga shi ko ta kansu bai biba, bayan gaisawa da Imran da ya yi, shima gaisuwar yana yi hankalinsa na a kan kirjin Areef in da ya harbe shi da gun ranar, yana tunanin za ayi wa wajen tiyata gobe ko jibi, dan ya na ji tamkar akwai wani abin a wajen.

Yana fita Rimsha ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya wadda ya sanya Areef da Imran ɗagowa da kallonsu kanta lokaci guda. Da hannu Areef ya yi mata alama akan ta zo, ba musu ta je kusa da shi ta tsaya, nuna mata in da ta zauna ɗazun ya yi akan ta zauna, nan ma ba musu ta zauna tana kallon Imran da yake jinjina mata kai akan ta zauna ba wata matsala.

"What is your name?" Shine abin da Areef ya fara tambayarta. "My name is Rimsha" ta bashi amsa.

Jinjina kai ya yi yana faɗin "Good nice name" ya yi maganar tare da ɗan yin shiru kafin kuma ya sake cewa "Do you love my brother?" Zaro ido suka yi daga ita har Imran a lokaci guda, girgiza kai ta fara yi alamar a'a.

Murmushin kaɗan ya yi kafin ya fara magana a nutse "Ni fa jami'in CIA ne, da kallo ɗaya wadda bai fi sakan uku ba nake gane abu, na samu horo ta ɓangarori da dama ta yadda kallo ɗaya zan yi wa mutane ɗari na fitar da ɓarawo da kuma mai gaskiya a cikinsu, mara ƙwaƙwalwa da tunani bai isa ya tunkari CIA ba ma bare ya shiga cikin ta, Jami'ai ne dake amfani da zallar kwakwalwa da basira, ko mai shara ba zaka iya zama a hukumar CIA ba har sai idan zaka iya gane ɗan ta'adda a cikin miliyoyin mutane, wadda yake share mana office namu ya goge, daidai yake da D.O.P na yan sanda a wajen iya aiki, to ni kuma ina matsayin DOA mutane biyu ne kawai a samana a cikin hukumar, kin ga kuwa ai na wuce duk yadda kike tunani, tun da Lion ya shigo ɗakin nan kike kallonsa, acikin kwayar idon ki akwai tsantsan Kaunarsa, abin da ya sa na tanka maki saboda da kallo ɗaya da na yi maki na fahinci da iya gaskiyar ki kike son shi, akwai mata da dama da suka yi mashi abin da ina da tabbacin ya fi wadda kika yi mashi na soyayya, sun mutu a kanshi, akwai masu cewa idan bai ce yana son su ko da sau ɗaya bane sai sun sha guba sun mutu, wa su sun sha da gaske an kai su asibiti, wasu kuma ba su sha ba, shi kuma ko kallo basu ishe shi ba, akwai wadda lokacin muna school Prof bai gaya maki bane? A gabansa ta zo ta tsaya da poison a hannunta, wai idan bai ce yana son ta ba zata sha, a zafafe ya miƙe ya damki wuyarta da hannunsa ya ɗura mata gubar gaba ɗaya abankinta tare da toshe mata hanci, ranar da kyar na kwaci yarinyar a hannunsa, na miƙata aka kai ta hospital, tun ba mu kai haka ba, tun muna school ake mutuwa akanshi bare kuma yanzu, cos ban taɓa kula ko da mace ɗaya masu masa irin wannan haukar son ba, saboda nasan ba dan tsakani da Allah suke son shi ba, kuma mu mace ta yi mana babbar illar da yarda da ita zai zame mana abu mawuyaci a rayuwar mu, ban san me yasa nake jin a jikina matan Nigeria sun fi matan mu amana da mutunci ba, da kallo ɗaya na yi maki na gane da iya gaskiya kike son Lion, ba dan wani abu nasa ba, kuma ina da tabbacin ba zaki cutar da mu ba, saboda Imran mutumin kirki ne sosai, sanadiyarsa ni da Lion muka musulunta

Muna matukar kaunar prof fiye da tunanin ki, da Lion da Michael sun azabtar da zuciyoyin masu son su da dama, ni bana cutar da zuciya, idan mace ta ce tana so na, bana wulakantata duk da cewa sun mana illa, na kan nuna mata ne cewa ni bana da damar yin soyayya ta yi hakuri, da lalama da kuɗi muke rabuwa, mu matan mu mafi yawanci kuɗi suke so ba mutun ba, hakan yasa nace maki da wuya a kasar mu a sami mai yi mana son gaskiya, so koma dai me ni bana cutar da zuciya saɓanin Lion da Michael, ga mu da farin jini bala'i, duk in da muka shiga sai an so mu, amma haka Lion da Michael suke cin uban duk zuciyar da take son su, in ma mace ko namiji, basu cire ko ɗaya ba, yanzu haka zaman da kika yi a cikin gidan nan, da a baya ne baki isa ko kusa da gidan nan kin zo ba, amma da muka musulta muka san cewa laifin wani baya shafan wani shiyasa Lion ya rage tsana da ya yi wa mutane, wlh ina da tabbacin da a baya ne, ko mutuwa kike yi sai dai ya sanya bindigarsa ya karisa ki gaba ɗaya, ba dai ki zo mashi gida ba, ko da kuwa tare aka haifeku rana ɗaya da prof bama kanwa ba, cos yanzu gaskiya ya sassauta, ko in ce maki mun sassauta, addinin musulunci addini ne mai sauki, laifin wani baya shafan wani, a da lokacin da muke kan mummunar hanya muna ganin komai daidai ne, hakan yasa muka yi wa mata kallon ɗaya, amma yanzu Alhamdulila mun rabe ku, na yi maki alkawarin cewa zan taya ki yaki akan abin da ki ke so, sai dai fa akwai matuƙar wahala, dan Lion tun muna yara baya tanƙwaruwa, sannan zuciyarsa kamar dutse take baya juyuwa, amma fa yana da zuciyar zinari sosai, kawai dai shi na saban ne, ina son ki da ɗan uwana, dan tabbas matan Nigeria kuna da kirki, yanzu dai ina son ki daina yawan kallon shi da kike yi, dan in ya kama ki wlh mai kwatarki ma ina ji sunan sa gawa, ni dai kinga yanzu ba lafiya ke gare ni ba bare nayi yunkurin kwatarki, na biyu kada ki rinƙa bari hanya ta haɗa ku, a hankali za mu san ya zamu ɓullowa abin ni da Prof, idan kika cika haɗa hanya da shi wata rana za'a iya ɗaukar gawarki na gaya maki" Shiru ya yi yana jan numfashi yana ɗan hutawa.

Ita kuwa ta yi kasa da kanta tana hawaye, wai yau ita ce ta zauna da ɗaya daga cikin yan uwan GAR suna magana haka cikin mutunta juna, kai wannan abin ta rasa taya zata kira shi, lallai Areef ya cika cikakken musulmi mai imani, mutumin kirki ne sosai da sosai.

Ban so dagatawa a nan ba, naso kai karshen tattaunawar Areef da Rimsha tare da Imran, dan jin yadda zata kaya, Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💖💖TRIPLETS💖💖





E 67-68



Ita kuwa ta yi kasa da kanta tana hawaye, wai yau ita ce ta zauna da ɗaya daga cikin yan uwan GAR suna magana haka cikin mutunta juna, kai wannan abin ta rasa taya zata kira shi, lallai Areef ya cika cikakken musulmi na kwarai mai imani, mutumin kirki ne sosai da sosai.

Imran ne ya sanya hannu yana goge mata hawayen dake a kan face nata. "Ki yi shiru Rimsha ki dai'na zubar da hawayen ki, haka Allah yake lamuransa". Juyowa ta yi da kallonta izuwa kan Imran ɗin ido cike tab da kwalla murya a dashe ta fara magana

"Yaya Imran ba bu wanda ya taɓa fahimtata irin yadda yaya Areef ya fahimceni lokaci guda, ko Jehan da muke uwa ɗaya uba ɗaya, kai ba Jehan ba, ko daddyn mu ya kasa fahimtata akan kallon video yaya Saif da nake yi a Tv, har hana ni sai da daddy ya yi, ni ban san ta ya ya zan gaya maka ba, amma dai abin da na sani shine ina son shi, ban taɓa ganin fuskarsa ba before ya zo nan, amma a haka nake kwatatan ta yadda zai iya kasancewa a zahiri na zana shi, kuma kai da kanka ai kaga zanen, kai da bakinka ka ce shi na zana, amma ba tare da na sanshi ba na zana shi kuma ya fita daidai yadda na zana, har mahaukaciya Jehan take ce mani akan shi, ta dake ni ta zageni dukka akan shi, amma ko sau ɗaya ban taɓa jin na dai'na son shi ba, ka san cewa mutun baya sanyawa kan shi soyayya ko?" Gyaɗa mata kai ya yi alamar e, shima idanunsa sun cika da kwalla, wannan irin jarabawa Allah dai ya bata ikon cinye shi, amma akwai wahala, abune mai matukar wahala, wannan shine faɗa tsakanin mutuwa da rayuwa, domin idan Lion bai so ta ba, tana iya mutuwa yadda ta kamun nan, shi kuma mawuyacin abune ya so ta gaskiya. To fa yau ake yin ta.

"Yaya Imran ni nasan da cewa Allah ne ya jarrabeni ta wannan hanyar, ina kuma fatar na ci wannan jarabawa".

Jawota ya yi jikinsa yana rarrashinta dan kukan da take yi ya yi yawa, ita kuma ta jima ne tana son ta sami wadda zata amayarwa abin da ke cikin ta na yadda take ji akan Lion, Akila yarinya ce, kansu kusan ɗaya ko da ta bata labarin yadda take jin Lion a ranta ba ta wani fahimci yadda take ji ba, amma yanzu da ta samu ta gayawa su Imran kuma suka fahinceta, ta ji sauƙi a ranta, baiwar Allah shine silar kamuwarta da cutar da Dr ya ce yake damun ta, ta azabtu sosai da soyayyan bawan Allah nan, tun tana da shekara 9 a duniya take fama.

Areef da ba jin hausa yake yi ba sai bai gane me suka faɗa ba, kawai dai yana ganin suna magana, amma yadda ya ga tana hawaye ga Imran shima idonsa ya ciko da kwalla, sai ya fahimci koma me akan Lion suke magana, kuma tana bashi labarin irin son da take yi wa Lion ɗin ne, dan haka sai ya tambayi Imran ɗin akan ya faɗa mashi me ta ce.

Ai kuwa Imran bai ɓoye mashi komai ba ya zayyana mashi duk abin da ta faɗa.

Hannunsa da bai ji ciwo sosai ba ya sanya ya riƙo nata hannun, da yake shi ba laifi yana da tausayi, cikin harshen turanci ya fara yi mata magana a nutse.

"Me yasa kike son Lion har haka? Kuma me yasa yanzu kike yin kuka? Ya kamata ki daina yin kuka ki yi godiya ga Allah, bari ki ji wani abun al'ajabi da mamaki, daga ni har su Lion ba wanda yake kaunar Africa da yan cikinta abaya, bamu son bakaken fata fiye da yadda baki zato, a baya da zamu haɗu da bakin fata ko a rashin sani ya ɗan taɓa mu, to muna iya kashe shi, dan ba mu son su, amma haka kawai na tsinci kai na da kauna shiga hukumar CIA, daga nan na yi wa kaina alkawarin shafe yan ta'addan dake kewaye da mu, sanadiyar haka na zo Nigeria, sanadiyana kuma Lion ya zo Nigeria, har gobe ina mamakin ya akayi muka yarda da Prof lokaci guda duk da yana bakin fata, amma dai na san Allah ne ya so mu da rahma shiyasa ya haɗa mu da shi kuma ya sanya mana kaunarsa har muka musulta, mu ko turawa yan uwanmu bamu yarda da su ba, kwata-kwata ba mu son kowa sai mu kaɗai kan mu, gidan mu ko shekara goma zaki yi a ciki ba zaki taɓa ganin baƙo ya zo ba, dan bamu so, amma a haka muka yi accepted na Prof harma muke kaunarsa fiye da uncles ɗin mu, time da Prof ya gaya mani Lion ya yabawa yan Nigeria, wlh ba dan nasan waye Prof ba da ba zan yarda ba, na san cewa ba zai yi mani karya ba, shiyasa na yarda, amma nayi mamaki, nima kuma yanzu ga shi haka kawai naji ina son ƴan Nigeria, ina son zama cikin kasar ku, akwai daɗi kuma ina son ki kasance matar ɗan uwana, saboda ke yarinya ce, na farko baki san yaudara ba, babban abin da yasa ma na aminta dake kenan, yara duk abin da za su gaya maka daga cikin zuciyarsu kai tsaye yake fitowa, inma karya ko gaskiya, daga karkashin zuciya yake fitowa, duk abin da zai fito da ga karkashin zuciya kuma ai kinga ba batun dogon bincike akan shi dan hakan yake, sannan yanzu ke baki ma san cewa ki so Lion dan kuɗin sa ko kyansa ba, ɗan gara kyau ma yara suna son abu mai kyau, amma ke tun ma baki san face nasa ba kika fara son shi, kuɗi kuma a yanzu yadda kike ɗin nan me zaki yi da kuɗi bare ace dan kuɗi zaki so shi, sai Maganar mukami, ina da tabbacin a wayan nan ƴan shekarun naki baki ma san me THE GENERAL OF THE ARMY'S yake nufi ba, yanzu ke ina da tabbacin duk wani soja mai kaki ajiki kallon abu guda kike yi masu, saboda bama ki san mukami ba bare ace dan shi kike son shi, duk wace zata so Lion to fa abayar ki ce ina da wannan tabbacin, ba zai taɓa samun mai yi mashi son tsakani da Allah kamar ke ba, ni abin da baki sani ba ma shine, da shekarunki nayi amfani na san cewa e son gaskiya kike yi wa ɗan uwana, In Sha Allah yadda kika sha wahala akan shi, Allah ba zai bari wuyarki ya tafi abanza ba, za mu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login