Showing 99001 words to 102000 words out of 355604 words
bari na je wajen wani abokina, sai karfe huɗu idan nayi sallar la'asar zan dawo, idan na dawo sai ku faɗa mini me ya kawo ku nan, kada ku fita ko'ina fa, dan kunga nan hotel ne akwai mutane kala-kala na banza dana kirki, dan haka ku kula" yana kai karshen maganar ya miƙa wa Ayla spoon ɗin sannan ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice daga ɗakin ya ja musu kofat ya rufe, amma bai sa key ba.
Yana fita suka fara ɗura abinci, hannu baka hannu kwarya, Ayla kam tana ci tana korawa da coca colar, ita kuma Rimsha ruwar shabram dake wajen take korawa da shi.
Tas suka cinye abinci har da lashe takeaway ɗin, kamar basu koshi ba, a ɓangaren nama kuwa har da kashin suka taune abinsu.
Bayan sun gama a tare suka tattare wajen, sannan suka kwanta a kasa, sun ki yarda su kwanta a gadon, sai ajiyar zuciya suke sauƙewa.
Yar hiran duniya suka fara yi, tun Ayla na amsawa kasa-kasa har barci ya ɗauke ta, ita kuwa Rimsha ta jima kaɗan kafin ita ma barci ɓarawo ya ɗauke ta.
(Ni kuma na kwashe kayana zuwa wajen James)
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Wani irin gida ne wadda da ka ganshi kasan maɓoya ne ko na yan ta'adda ko kuma na matsafa, dan gidan bana tunanin a saman kasa yake, na fi tunanin a cikin kasa yake, sannan ginin gidan an yi masa wani irin tsari wadda ya fita daban da gidan zaman mutane, ba sai na tsaya zayyana muku yadda maɓoyan yan ta'adda yake ba, kun san dai yadda suke yin abinsu.
Wani katon mutumi ne ya fito daga wata ɗaki hannun sa riƙe da bokiti mai ɗauke da ruwa sanyi, gaba ɗaya jikin mutumin nan a rufe, ya sanya long coat zuwa gwiwarsa da wando dogo na jeans, launin baki, daga ta ciki riga mai godon hannu ne launin baki, kafarsa na sanye da irin takalmar waterproof ɗin nan shima baki, ya sanya hand gloves baki, fuskar sa akwai mask shima baki, a takaice dai baka iya ganin komai na daga jikinsa, ga shi kuma yana da tsawo da kuma ƙiba ba kaɗan ba.
Kai tsaye wani ɗaki mai girman gaske ya shiga, ɗaki ne mai filli wadda babu komai a cikin ta, sai wani bawan Allah da suka ɗaure a saman chair a tsakiyar ɗakin, daga gefe kuma wasu mutane masu dressing irin na wannan mutumin ne ke ta faman aiki a desktop computer dake gaban su, da alama wani binciken suke yi, ɗakin akwai manya-manyan Windows na glasai a cikin shi, wadda akalla Windows nan za su kai goma, duk kuma Windows ɗin a buɗe suke.
A tsakiyar ɗakin ya ajiye bukitin hannunsa sannan ya karisa wajen wayan nan mutane masu dressing irin na shi wadda baka iya ganin komai na su.
Cikin harshen turanci ya ce musu "Kun samu damar kutse cikin wayar? Kun iya gane wani kungiya ne suka turo shi?" Girgiza masa kai suka yi, cikin harshen turanci suma suka ce "No sir ba mu samu komai ba, da alama wayar nan tasa komai nata a datse yake, duk yadda akayi babbar kungiya masu amfani da kimiya yake yi wa aiki, domin ba zaka iya shiga komai a cikin wayar nan tasa ba, idan ma muka matsa sai mun shiga, wayar kashe kanta da kanta take yi, idan muka sake kunnata kuma sai ta ɗauki tsawon awa tana bamu hawala kafin mu samu ta buɗu"
Wani hucu wannan mutumi ya fara tare da juyawa ya koma wajen bokitin da ya ajiye, ɗaukar bokitin ya yi ya nufi wajen da suka ɗaure James, da karfi ya kwara masa ruwan cikin bukitin, daga kansa har zuwa kasansa, wani dogon numfashi James ya ja tare da sauƙewa a hankali, da kyar ya iya ɗago kansa, duk sun fasa masa fuska, sun masa dukan mutuwa, a takaice James bai san in da kansa yake ba, dan dukar da suka yi mashi ya fita hayyacinsa.
Damko dark brown curly hairsa wannan mutumin ya yi yana faɗin "Zaka sanar mana waye ya turoka ka kashe mu ne ko dai sai mu mun kashe ka?" Kada ku manta da turanci suke yin maganar.
Banda numfashi wahala mai sauti da James ke fitarwa ba abinda za ka ji yana ta shi a wajen, baya iya magana, bakin sa duk ciwoka, wani ciwon ma har ya fara bushewa, alamar sun kwana biyu da jimasa ciwon, wajen idanuwansa nan duk sun kunbura, da alama ma kunburin yasa baya iya buɗe idanuwansa, ba zaka taɓa cewa James bane saboda gaba ɗaya fuskarsa ta canza, har jikinsa ya kumbura ba iya fuska kawai ba.
Duk kuma wannan duka da suke yi masa, James bai taɓa gigin buɗe bakinsa ya yi magana ba, in fact ko muryarsa ba su taɓa ji ba, dan yaki basu haɗin kai, ya amsa musu magana. Dun kule hannu wannan katon mutumin ya yi ya kai mashi duka a fuska daidai saitin dogon hancinsa.
Wannan naushi da ya kai mashi hakan ya yi daidai da farkawar Romeo da kuma Michael daga barci. A razane Romeo ya miƙe zaune a tsakiyar bed nasa, duk da sanyin Ac dake cikin ɗakin shi zufa yake haɗawa, gaba ɗaya idanuwansa sun sauya zuwa ja sosai, alamar barci yake ji, amma bai isa ya kwanta ba, da ya kwanta zai rinƙa jin azaban zafi a jikinsa tamkar shi ake mawa azaba ba james ba, gaba ɗaya dark black curly hairsa ya watse, ya bazu masa har saman kyakkyawar fuskarsa, bin ɗakin nasa ya yi da kallo, ya rasa meke yi masa daɗi a duniyar nan, a takaice Lion ya fi James shiga tashin hankali da azabtuwa na zuciya.
A wannan hali Michael ya shigo ɗakin ya same shi, dama shi Micheal barcin wahala ya yi bawan Allah, ya sha gwarel da su Tga na rufe su a ɗaki da Lion ya yi, ya kuma sha kuka, da kyar ya samu ya yi barci bayan Lion ya buɗe su kenan.
Saman gadon ya hau yana hawaye ya ce "Lion please and please tell me where is James, ina ɗan uwana yake? Duk lokacin da na tuna shi ina jin zuciyata tana bugawa da karfi, zafi zuciyata take yi mini tamkar zata fashe ta fito waje, Lion zan iya mutuwa in dai James bai dawo ba, jikina na mini ciwo kamar ana dukana da wani karfe haka". Yana magana yana hawaye. Gwanin ban tausayi
Dafe kai Lion ya yi dan shima kan sa sara masa yake yi, kuma duk abin da Michael ya faɗa yana ji a jikinsa, hakan shima yake ji, ya kara tabbatarwa kansa James baya lafiya, domin tun suna yara haka suke, idan ɗaya bai da lafiya a cikinsu, to tamkar dukkansu ne basu da lafiya.
Sosai Michael ya kara sautin kukan nasa ganin Lion ya ki kula shi, jin kukan Michael na kara masa azaba a cikin zuciyarsa dan haka sai ya ce "Get out Michael". Zaro idanuwansa waje Michael ya yi yana mamaki, cak ya tsaya da kukan nasa, dan yasan Lion bai taɓa ce masa ya fita masa a ɗaki ba sai yau.
Sanin halin Lion baya magana biyu, yasa ya sauƙo daga gadon tare da cigaba da hawayen da yake yi ya fice daga ɗakin, shi kan shi Lion ji yake kamar ya yi hawayen ko zai samu sauƙin abinda yake ji a ransa, shi zafin ma ya masa yawa, ga daddy a gefe, ga Michael sannan ga bala'i da suke ciki na rashin sanin ina James yake, abubuwan sun taru masa, amma idan ka gan shi bazaka taɓa gane hakan ba, dan shi already dama a hakan yake, fuska a ɗaure kullun, ba'a gane murna bare bakin cikinsa.
A hankali ya mai da bayansa ya jingina da gikin kayin gadon yana tunanin menene A.E.A ke nufi, idan ya gane su zai iya gane in da James yake, sannan yana bukatar kutse cikin tsaron da a ka sanyawa wayar James, me yasa wayar ta kasance haka, wannan ma abin tambaya ce.
Ba wanda ya isa ya yi kutse cikin wayar James har ya yi bincike sai wanda ya kasan ce makura wajen basira da sanin kimiya na hanyar sadarwa. Haka shima wayar Lion take, ba zaka iya bin diddgin wayar ba, haka ba zaka iya datsar layin sa ba, sai dai wayar James, an ɓoye layin ne a karkashin wata tsaro na musamman, kuma a wannan tafiya da ya yi ne hakan ta faru. Maganar gaskiya kuma mutanen da suka kama shi ne suka ɓoye layin nasa a karkashin tsaro domin kada a bibiyi in da suke, saboda basa son kashe wayar suna son yin bincike a kanta, kuma sun san idan basu kasheta ba za'a iya bin diddigin su har a kama su, wannan dalilin yasa suka saka mata matakan tsaro ta yadda ba za a iya bin diddigin su ba
Ya jima a haka sannan ya jawo system nasa ya fara bincike a kan menene A.E.A a cewar sa idan ya gano ma'anar su sai ya fara kutse cikin wayar James dan sanin a wani location ɗaya yake.
(Toh fa aiki ya ganku, sai mun haɗu da ku a gidan Abbo gobe idan mai dukka ya kai mu)
💞💞TRIPLET'S💞💞
E31-32
Ya jima a haka sannan ya jawo system nasa ya fara bincike a kan menene A.E.A a cewar sa idan ya gano ma'anar su sai ya fara kutse cikin wayar James dan sanin a wani location ɗaya yake.
A ɓangaren Michael kuwa, yana fita part nasa ya koma. Yana shiga ya isko Musharraf yana Sallah saman Chinese carpet dake gaban katafaren bed nasa, saman gado ya haye ya ɗan kishingiɗa yana hawaye yana kallon yadda Musharraf ke sallah. Allah sarki Michael saboda son da yake yi wa Musharraf ya sa ya ce Musharraf ya baro word room ya dawo part nasa su zauna tare, kuma duk hakan ya samo asaline saboda son da James yake yi wa Musharraf ɗin.
Sai hawaye yake yi har Musharraf ya idar da sallah, hannu sama ya ɗaga ya jima yana addu'a sai kallonsa Michael ke yi, har ya dai na zubar da hawayen da yake yi ba tare da ya sani ba, ganin Musharraf na ibada yana sanya shi samun nitsuwa da kuma farinciki.
Bayan ya kammala addu'ar ne, ya miƙe ta hawo saman gadon yana faɗin "Michael what is wrong with you? Why are you crying?" Ya kai karshen maganar yana zama kusa da Michael ɗin, amma kafin ya hau gadon sai da ya yi bismillahi.
Shiru Michael ya ɗan yi mashi kafin ya ce "Uncle ɗin James me yasa idan zaka zauna kake yawan faɗin wannan kalmar da ka faɗa yanzu". Murmushi Musharraf ya yi yana faɗin "Wai bismillahi kake nufi?" Gyaɗa masa kai ya yi alamar e. Shafa kansa Musharraf ɗin ya fara yi yana faɗin "Ina koran sheɗan ne" miƙe wa daga kishingiɗar da ya yi ya yi, ya zubawa Musharraf brown eyes ɗin nan nasa, na ɗan lokacin kafin ya ce "Waye shi shaiɗan ɗin?"
"Sheɗan makiyi ne ga duk wani ɗan adam, baya son mutane, ya kuma yi alkawarin sai ya kai mutane dayawa wuta, sai wanda Allah ya tsarene kawai ba zai je wuta ba" Musharraf ya ba shi amsa. Shiru ya yi yana maimaita kalmar wuta, Allah, sheɗan da kuma makiyi.
Ganin ya yi shiru ne yasa Musharraf ya ce "Kai ma idan zaka zauna karinƙa faɗin bismillahi, dan ka kori shaiɗan daga kusa da kai, kuma ba iya shaiɗan kawai bismillahi ke kora ba, yana sanya Mala'ikun su kasance kusa da kai, sannan kuma idan aka maka wani sharri a wajen, Allah zai kareka ta sanadiyar wannan bismillar da ka yi".
Cikin sauri ya ce "To zan rinƙa yi". Wani daɗi Musharraf ya ji ya ziyarce shi lokaci guda. "Baka faɗa mini me ya same ka kake kuka ba?"
Tambayar Musharraf ta fama masa ciwon dake damun shi, nan take ya fara hawaye, "Subhanallah a'a Michael idan har baka son faɗa mini abin da ke damun kane ne ba sai ka sake yin kuka ba ka ji? Ka yi shiru ni na fasa ji ma" kwantar da kansa saman cinyar Musharraf ɗin ya yi, cikin kuka ya fara gaya masa halin da yake ci dan gane da James.
Sosai shima Musharraf ya ji wani irin kuna a zuciyarsa domin har ga Allah yana matuƙar kaunar James, cigaba da shafa kan Micheal ɗin ya yi yana karanto addua'o'i yana tofa masa, shiru Michael ya yi yana jin zuciyarsa tana masa sanyi, har cikin ransa yake jin sauƙi. Dama kuma tun da Musharraf ya dawo part nasa yau kwana biyu kenan, kullun sai ya karanto masa addu'a ya tofa ya shafa masa a jikinsa, haka idan ya yi barci sai ya masa addu'ar barci kafin nan ya bar ɗakin zuwa ɗayar ɗakin na kusa dana Michael ɗin, da yake bedroom uku ne a part ɗin, shiyasa Musharraf ke kwana a daya, amma fa barci ne kawai ke raba shi da Michael, domin kuwa ko da rana a ɗakin Michael yake zama, saboda yana son jan shi a jiki sosai.
Ya jima yana tofa masa addu'a kafin nan ya ce "In Sha Allah zan yi wa James azumi gobe, da izinin Allah zai dawo cikin koshin lafiya, kuma yau ma ba zan yi barci ba zan kwana ina yin Sallah ina rokan masa Allah daya tsaresa a duk in da yake". Allah sarki Michael ya samu nitsuwa sanadiyyar addua'o'i da yake samu daga wajen shi, a nitse ya ce "Uncle ɗin James idan kayi azumin James zai dawo?" Gyaɗa masa kai Musharraf ya yi yana faɗin "Da izinin Allah zai dawo lafiya".
Juyo da kallonsa kan fuskar Musharraf ɗin ya yi kafin ya ce "Uncle ɗin James ni ma zan yi azumin domin muyi dayawa don James ya dawo da wuri" kara faɗaɗa murmushinsa ya yi yana faɗin "To shikenan bari na gaya maka yadda ake yi, idan muka ci abinci da asuba ba zamu sake ci ba har sai rana ta faɗi..." Bai kai karshen maganar ba Michael ya katse shi da cewa "I already knew it through James friend, yana da wani aboki musulmi, a school ɗaya muke amma shi kamar ɗan Dubai ne ko Saudia ne na manta, kuma ai pastor a church ma ya gaya mana yadda akeyin azumi, so kaga na san yadda ake yi, kullun wannan friend ɗin James ɗin yana yin azumin Monday and Thursday".
"Tom shikenan My Michael Allah ya kai mu da asuba sai mu yi sahur ko?". Gyara kwanciyarsa ya yi yana faɗin "Tom me zaka ci da asuba ɗin sai na gayawa masu dafa abinci dan su tashi a kan time su dafa maka da wuri". Cikin sauri ya ce "A'a ni ruwan tea ma is okey for me, sai dai idan kai ne zaka ci wani abin" girgiza kai ya yi ala'mar shima baya son komai.
Shiru suka ɗan yi Musharraf sai tofa masa addu'ar Allah ya bashi lafiyar ƙwaƙwalwarsa yake yi, "Uncle ɗin James do you know what?" Lokacin Musharraf yana karanta addu'a bai kai karshe ba, hakan yasa ya girgiza masa kai kawai alamar a'a.
"Sometimes if am with you I feel like am with james". Hannu Musharraf ya sanya yana ɗan jan dogon hancinsa a hankali ba tare da ya yi magana ba, har sai da ya kai karshen addu'ar da yake karantowa a zuciyarsa, ya tofa masa sannan ya ce "Saboda ina son James ɗin sosai ne shiyasa wani lokaci nake maka kamar shine, kuma kaga James ya kasance tare da ni sosai mun saba shiyasa" "Yes Uncle, idan na ganka sai in ji kamar James nake kallo, saboda mafiyawancin kuna tare lokacin da yake nan".
Cike da tsoron abin da zai biyo baya, dan ya san wani lokaci Michael birkitacce ne, ya ce "Michael why are you not calling your mum on phone?" Abin mamakin da bai taɓa tunani ba, ya yi tunani Michael zai ɗauki zafi sosai, dan James ya gaya masa kada ya kuskura ya yi maganar mum ɗin su ga kowa a cikin gidan idan ba haka ba, to zasu kashe shi, amma ya ga akasin haka, dan kuwa Michael ce masa ya yi "Because i don't have her phone number that is why I'm not calling her". Zaro ido Musharraf ya yi dan bai yi tsammanin haka ba.
Kenan ƙwaƙwalwar Michael na baya ne bata son mum ko yaya? Kada ku manta yanzu ya fara sakun sauƙi yana kuma iya rabe daidai da ba daidai ba.
"To ka karɓi number nata mana, sai ka kirata ku gaisa zata ji daɗi sosai" ya yi maganar yana tsare shi da ido, turo ɗan bakin ya yi kafin a shagwaɓe ya ce "To kana da number ne ka bani?" Girgiza kai ya yi alamar a'a bashi da shi.
idan banda Michael da meman magana ta ina Musharraf zai samu number mum ɗin su, shi da yake bako.
"In je in tambayi Lion number?" Cikin sauri Musharraf ya ce "A'a kada ka masa maganar". Musharraf ya san cewa idan Michael ya yi wa Romeo wannan magana to za'a samu matsala, domin kuwa yasan Lion sai ya tambayi shi waye ya masa zancen mum, shi kuma Michael baya ɓoye abu, bai iya karya ba, sai dai idan saka masa magana a baki kayi, amma da kan shi kam baya karya, idan kuma ya faɗa cewa ga wanda ya yi masa zancen mum tofa yasan dole Lion ya hukunta shi, dan ya lura tabbas Lion bayason mum ɗin su, da gaske yake yi, shi ma James baya son ta, amma yana kokarin dannewa ne kawai ya kula ta, shi kuma Michael ƙwaƙwalwarsa ta baya ce bata son ta, na yanzu kuma babu tsanar kowa a cikinta, sai zallar soyayyar wayenda suke tare da shi, kowa na gidan Michael na son shi, har da daddy yake nunawa soyayyar da bai taɓa tunanin zai samu irin shi daga ɗaya daga cikin triplets nasa ba, amma sai ga shi Micheal yana nuna masa, hakan kuma ya faru ne yan kwana biyu da suka wuce, saboda addua'o'i da Musharraf ke yawan tofawa ƙwaƙwalwar tasa, hakan yasa Michael ya canza sosai da sosai, sai dai har yanzu ragwanta da shagwaɓa yana nan bai tafi ba.
Haka suka yi ta hira Musharraf na shafa lallausan brown hair ɗin Michael ɗin,