Showing 96001 words to 99000 words out of 355604 words
ta dawo yi masa, tun da magana yaki fitowa.
Da hannu ta nuna masa in da Ayla take, cikin sauri ya riƙo hannunta suka karisa wajen, gaba ɗaya jikin Ayla ya ɓaci da jini, saboda juyawa da ta rinƙa yi.
Shiru matashin nan ya tsaya, ya rasa ta ina zai fara taimaka musu, shi bai san komai game da period ba, ita Rimsha ta san yadda mai haila ya kamata ta kasan ce idan tana yi, ta karanta, sai dai kuma bata san ya mace ke fara yin hailar ba, ta san dai ance ya mace zata yi jini duk wata.
(Tofa yau ake yinta)
Miƙawa Rimsha ledar hannun sa ya yi, ya ce musu yana zuwa, karɓar ledar Rimsha ta yi tare da tsugunnawa kusa da Ayla tana hawaye.
Suna wajen har matashin nan ya dawo tare da wata bayarabiya, da kallo ɗaya ta yi wa Ayla ta gane matsalar, sai ta ce da saurayin ya saya mata always bari ta taimaka wa yarinyar suje gida ta wanke jiginta, ina ne gidan su?.
Kallon Rimsha ya yi, dan shima bai san gidan su ba, girgiza masa kai Rimsha ta yi, alamar ba su da gida.
Matsowa kusa da ita sosai ya yi ya ce "Kanwata kwata-kwata baki iya magana ne? Ko kaɗan ba zaki iya ba? Na zaci bebiyace ke ai ba kurma gaba ɗaya ba".
Cikin sauri ta ce masa "A'a ina iya magana" jin maganar ta na fita a hankali-hankali ne ya sanya ya matso da kunnensa kusa da ɗan bakinta dan ya ji me take faɗe, nan ta sanar masa tama magana.
Cikin sauri ya ɗago ido ya kalle fuskar ta, yadda ya ji zazzakar muryarta, ba karamin daɗi ya masa ba. "Wow beautiful girl and sexy voice" ya furta a zuciyarsa. Sake jefa mata tambayar ina gidan su yake ya yi, sannan ya mai da kunnansa kusa da bakinta. Nan ta gaya masa su yan Katsina ne, basu da gida a nan.
Ɗago ido ya yi yana kallonsu dukkan su biyu, lokacin guda ya ji yana son taimaka musu, dan haka sai ya ce da matar nan white house zata kai su, cikin sauri matar ta kalle shi.
Da yaren yarabanci ta ce "Haba Ahmad me yasa zaka lalata wa yarannan yaruwarsu? White House fa? Bai kamata ka ɗauki yara kanana kamar wayan nan ka kai su hotel ba".
Zaro idanuwansa waje ya yi, dan shi kwata-kwata bai kawo hakan a ransa ba, shi ba mazinaci bane, kawai sauƙa ya yi a white house ya kama ɗaki, dan ba shi da yan uwa a nan, amma bayan haka ba wani abin da yake yi a hotel, yana son taimaka musu sai dai ba shi da kowa, ya zamar masa dole ne ya kai su masaukinsa, in dai zai taimaka musu.
Da yarabanci shi ma ya ce mata "Iya kin san halina, yau shekara uku kenan ina zuwa garin nan, duk da baki san daga in da nake ba, amma ai ke da kanki kina yabon halina, bani da wani shagon da nake sayan kaya, sai shagonki, ke da bakin ki kike cewa Allah ya yi wa iyayena albarka, sun bani tarbiya, to ina son ki sani, ni ba mutumin banza bane, wayen nan da kike gani kanne nane, ba wai wasu bare bane".
Cikin sauri Iya ta fara bin fuskokin su Rimsha da kallo sannan ta kalli Ahmad ɗin, kasan cewar Hausa fulani duk in da suka shiga kamannin jini baya ɓata ɓuya, sai Iya ta ga kamanin Ayla da wannan matashin.
Yar murmushi ta yi sannan ta ce "Ahmad na yarda, ga wannan mara lafiyar kamannin ku ɗaya sosai da ita, mu je to ka yi mana jagora zuwa room ɗin naka, amma gaskiya wannan tafiku kyau sosai, ita ta yi kama da indiyawa, kila da babanku ta ke kama". Ta kai karshen maganar tana kallon Rismha.
Shi dai Ahmad burinsa kawai ta taimaka ta kai masa su ɗakin shi, dan yana son yaje wajen wani abokinsa ɗan school na su.
Haka matar nan ta saɓi Ayla a kafarɗar ta, kasan cewar kakkarfar mace ce, kun san yadda matan yarabawa suke ba sai an tsaya ɓata lokaci wajen zayyana muku yadda suke ba.
Allah sarki tana da kirki matar, bata ji kyamar jinin jikin Ayla ba, haka ta ɗauke ta suka tafi izuwa white house.
White House wani tampatsetsen hotel ne mai girma, wadda yake ɗan gaba da su kaɗan, dan haka ba su yi wani tafiya mai nisa ba suka isa wajen.
Ahmad ya musu jagora har zuwa Room na shi. Bayan sun shiga ɗakin, banɗaki Iya ta wuce da Ayla, ita kuma Rimsha zama ta yi saman bedside drawer tana ta bin ɗakin da kallo, rabonta da ganin ɗaki mai kyan wannan tun gidan su na Abuja, shiru ta yi tana jin yadda sanyin Ac ke ratsa mata jikinta, nan take ta fara rawar sanyi, dama already da zazzaɓinta a jikinta.
Ganin haka yasa Ahmad ya kashe Ac sannan ya ce mata yana zuwa bari ya sayo abin da Iya ta ce ya sayo wato always, da kyar Rimsha ta gyaɗa masa kai, duk ta takure taki sakin jikinta.
Har ya kai bakin kofa zai fita, sai kuma ya juyo ya ce da ita, "Ki hau gadon ki kwanta mana? Kada ki damu yar uwarki zata samu lafiya" girgiza masa kai ta yi alamar bata son hawa gadon. Shiru ya mata bai sake magana ba, dan bai son takura musu.
Ya juya zai fita muryan Iya ta katse shi da cewa "Ahmad har da pant zaka sayo mata" sai lokacin ya gane me ke damun Ayla, shi kan shi kunya abin ya bashi, satar kallon Rimsha ya yi, ita ma ta sunkuyar da kai tana satar kallon shi dan ta ji iya ta ce pant, duk sai kunya ya kamata.
Ganin hakan yasa ya wuce da sauri ya fice daga ɗakin. Yana fita Rimsha ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya sannan ta ajiye masa ledarsa da ya bata ajiya awaje.
Ta yi shiru tana tunanin rayuwa, daga wannan sai wannan kullun cikin jarabawa suke.
Iya baiwar Allah, da kanta ta yi wa Ayla wanka, sannan ta ɗauki towel dake cikin toilet ɗin ta naɗota a ciki suka fito waje, Alhadulillah yanzu ciwon cikin Ayla ɗin ya ɗan ragu, yanzu kaɗan kaɗan take jin ciwon nata.
Kusa da Rimsha tazo ta zauna, suka takure waje guda, yar dariya Iya ta yi kafin ta ce "Me yasa kuke takure jikin ku wajen guda? Ku da ɗakin yayan ku? Ko dan kun ganni ni bakuwa ce? Tom ku saki jikin ku, ni da yayan ku mun jima muna tare, kullun yazo garin nan a shagona yake sayayya, sai dai ban taɓa sani daga ina yake zuwa bane, ban san gidan da yake sauƙa ba sai yau". Cikin harshen yarabanci ta yi maganar, kasan cewar ba wani jin yaren suke yi sosai ba, sai basu gane zancen nata ba, dan haka sai basu kulata ba.
Gefen gadon tazo ta zauna suna jiran Ahmad.
A haka ya dawo ya same su, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo cikin ɗakin, bakar ledar hannun sa ya miƙawa iya sannan ya fita wajen.
Riƙo hannun Ayla iya ta yi, suka koma cikin toilet ta nuna mata yadda ake amfani da komai, sannan ta fito ta musu sallama ta fice waje.
A waje ta isko Ahmad yana tsaye daga sama yana kallon garin da yadda yake.
"Ahmad it seems like wayan nan ba yan uwan ka bane" cikin sauri ya juyo yana faɗin "Like how Iya?" Yar murmushi ta yi kafin ta ce "The way na ga suna kame jikin su, basu saki jiki da ɗakin naka bane, sai wani ɓoɓɓoye kansu suke cikin jikin juna, kamar basu yarda da ɗakin ba".
Girgiza kai ya yi yana faɗin "No Iya kawai dan basu taɓa zuwa hotel bane shiyasa, amma yan uwana ne, kuma ai kema baki taba ganin na zo da su ba ko?" Gyaɗa masa kai ta yi alamar ne "To kin gani basu taɓa zuwa hotel bane, shiyasa suke tsoro, yanzu ma akwai dalilin da ya sanya na zo da su garin nan, amma idan ba haka ba, basa fita kullun suna gida".
Shiru Iya ta ɗan yi kafin ta ce masa to shikenan ita ta wuce, godiya ya mata sannan ya ciro 10k ya bata, ta karɓa ta yi masa godiya, sai mamakin irin karyar daya zuba yake yi, shi ba ma'aboci karya bane, ya sha mamakin ya akayi ya zuba karya son ranshi yau, ya ma akayi ya iya tsara karyar haka.
Ya ɗan jima tsaye a wajen kafin ya koma cikin ɗakin, zaune ya same su saman drawer ɗaya sun takure jikinsu waje guda. Kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa gefe saboda Ayla bata da kaya a jikinta, towel kawai ta ɗaura, rigar tata duk ya ɓaci da jini.
Kasa magana ya yi sai ma juyawa ya yi ya fice daga ɗakin yana tunanin kyan Rimsha.
Kasa gaba ɗaya ya sauƙa, har ya sauka sai kuma ya sake haurowa sama ya koma cikin ɗakin, a gefen gadonsa ya ɗauko key ɗin mota mai bala'i kyau, sannan ya fito.
Kai tsaye wata dankareriyar mota ya nufa kirar *McLaren solus GT.* Launin baki, sai kyalli motar ke yi, ciki ya shiga ya kunna motar ya ja ya fice daga hotel ɗin. Yana fita kai tsaye cikin Ilorin ya nufa.
Su Rimsha kuwa, dukkan su sai kugi cikinsu ke yi musu, yinwa suke ji sosai, Rimsha ga zazzaɓi Ayla kuma ciwon mara.
Suna zaune a wajen, har bayan awa ɗaya basu tashi ba, haka ba wanda ya yi wa ɗan uwansa magana, haka Ahmad ya dawo ya same su, hannun sa riƙe da manya-manyan ledoji guda biyu, irin ledojin shopping ɗin nan.
Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, Ayla ce ta amsa masa sallamar tasa, haka kawai Ahmad yake jin tamkar yana da wata alaka da su, shiyasa ya zage yake taimaka musu, yana jin kwanciyar hankali tarayyar sa da su.
Kusa da su ya ajiye ledojin sannan ya juya ya nufi waje yana faɗin "Kayan sawa ne a ciki, ku shirya ina zuwa".
Ayla ce ta miƙe bayan fitarsa ta buɗe ledojin, kayane masu kyau da tsada, abayas ne da hijabai.
Abaya ɗaya ta zara ta sanya a jikinta, ita ma Rimsha daga baya Miƙewa ta yi ta shige toilet, wanka ta yi sannan ta fito.
Itama abaya ɗaya ta ɗauko ta shirya cikin shi, ba karamin kyau ya mata ba, kayan sun karɓi jikinta sosai, ga shi Abayan launin sky blue ne, abin ba'a cewa komai.
Yafa mayafin abayar ta yi a kanta, sannan suka kwashe kayan da suka cire, suka zuba cikin ledar suka koma mazauninsu suka zauna.
Kasa kasa Ayla ta ce "Rumsha kin san me?" Girgiza kai Rimsha ta yi alamar bata sani ba.
"Wai haila na fara yi". Zaro ido Rimsha ta yi tana faɗin "Waye ya ce miki haila ce?"
Kara kasa da murya Ayla ta yi, sannan ta ce "Ba kin ce mensuration shine haila ba?" Gyaɗa mata kai Rimsha ta yi alamar eh. "To matar nan da tana mini wanka, shine take gaya mini da yarabanci, da na ce mata bana jin yarabanci, sai ta faɗa mini da turanci wai mensuration na fara yi sai na fara kula da kaina sosai".
Zaro ido sosai Rimsha ta yi tana tunanin dama haka haila take da bala'i zafi kamar mutun zai mutu, to ita kam gaskiya bata son hailar nan, ga shi kuma mum ta ce mata wata mace sati take yi, wata kuma kwana huɗu, kenan kullun idan jinin zai zuba sai an yi ciwo kamar a mutu, wayyo ta shiga uku.
Ganin sai zazzare ido take yi yasa Ayla ta dafa ta tana faɗin "Rimsha lafiya? Me yake damun ki?" Kara zazzaro sleeping eyes nata da suka fara washewa zuwa asalin kalarsu wato farare tas ta yi, yanzu muryar ta ma ya fara komawa normal. Kasa kasa ta ce "Ayla wlh ni kam bana son hailar nan, ki taya ni da addu'a Allah yasa kada na yi, kuma na ji mum ta ce ko wace mace tana yi, wlh ni kam bana so".
Ayla ta rasa me zata ce mata, dan ita dama ba wani ilimi ke gareta a kan haila ba, tana dai da ilimin Alkur'ani mai girma wadda mamanta ta koya mata, sai kuma addua'o'i da ba'a rasa ba, amma bata wani karanci littattafan musulunci ba.
Rimsha zata sake yin magana, Ahmad ya shigo, bakin sa ɗauke da sallama, har suna haɗa baki wajem amsa masa, tun da ya shigo ya kasa kawar da kallonsa da ka kan Rimsha.
Saman bakin gado ya zauna tare da jawo ledar da ya bawa Rimsha ta riƙe masa ɗazun a waje.
Buɗe ledar ya yi ya fito da takeaway guda ɗaya sai shawarma shima ɗaya da coca colar ɗaya, da ruwan shabram.
"Ku sauƙo ku ci abinci kun ji? Dama abinci naje na sayo zan ci sai Allah ya haɗa mu, to ku sauƙa ku ci ni zan sayo wani".
Har suna haɗa baki wajen cewa sun koshi.
(Oh ka ji yara da gulma yanzu suka gama kukan yinwa fa🤔)
"A'a banyarda da kun koshiba, ku sauƙo ku ci, ina son ku saki jikin ku, ku sani Allah ne ya haɗa ni da ku, domin ni tun da nake zuwa garin nan ban taɓa fita ba tare da motata ba, ban taɓa hawa taxi ba sai yau, kuma sai yanzu na gane dalilin da ya sanya, Allah ya sa naji sha'awar fita ba tare da motata ba, dan na haɗu da kune shiyasa, kuma karin abin mamaki, wlh lungun nan da na biyo ban taɓa bi ba, kawai dai daga wajen balcony ɗaki nan ina hangen hanyar ne, shiyasa yau dana hau taxi ya sauƙe ni a bakin wancan titi sai ya biyo lungun dan na iso da wuri, kuma kunga a bakin hotel ɗin nan akwai titi, amma nace mai taxi ya sauke ni a can, to dan haka ku saki jiki ku ci abinci ku koshi sai ku gaya mini me ya kawo ku wannan gari". Ya kai karshen maganar yana tura musu abincin kusa da su.
Shiru suka yi ba wanda ya iya magana a cikin su, ita Rimsha tsoro take ji kada ya yi musu wani abin, dan kullun mum ɗin ta tana gaya mata a duniyar yanzu ɗan Adam ba abin yarda bane, ita kuma Ayla ganin Rimsha ta ki ci ne yasa bata ci ba, Rimsha ta kasance kamar madubin Ayla haka suke.
Sai lallaɓa su Ahmad ya ke yi, har da basu labarin abin dariya, duk dan suci abinci. Da kyar ya samu suka sauƙo kasa suka buɗe abincin, jolof rice ne da kirjin dankwaleliyar kaza, ga shi abincin ya ji kayan haɗa su green beans carrot da sauransu, sai kamshi ke tashi.
Shiru suka yi saboda spoon ɗaya ne a wajen, waye zai ɗauki spoon ɗin a cikin su.
Shi kuma Ahmad ya mance da cewa spoon ɗaya ne a cikin abinci, sai ce musu yake yi su ci mana, su kuma sun kasa gaya masa spoon kwara ɗaya ne, kuma suna kunyar tsunduma hannunsu a cikin abinci.
Cikin zolaya ya ɗauki spoon ɗin yana faɗin "Bari to na baku a baki wata kila zaku ci" ya kai karshen maganar yana miƙawa Rimsha spoon ɗin, karɓa ta yi sannan ya mai da hannun sa cikin ledar da niyar ya ɗaukowa Ayla spoon ɗin ita ma, sai ya ji wayan, ya mance abincin mutun ɗaya ya saya. Ɗan shafa kansa ya yi yana murmushi, a hankali ya ce "Sorry bari na duba wajen masu saida abinci a hotel ɗin na karɓo muku wani spoon ɗin, dan ni duk abincin da nake sayowa jefar da takeaway ɗin nake yi idan na gama, kuma bana sayen abincin hotel ɗin nan dan ba shi da daɗi ko kaɗan".
Satar kallon sa Rimsha ta yi ta kasar ido, a ranta tana faɗin "Ko akwai wanda ya tambaye shi abincin hotel ɗin da daɗi ne ko babu, sai shegen surutu".
Muƙewa ya yi ya fito dan ya je ya karɓa musu spoon.
Yana fita Ayla ta dumbuza shinkafar ta danna a bakinta, ta cika baki taf, dariya Rimsha ta kwanshe da shi tana faɗin "Allah yasa akwai camera a cikin ɗakin nan, idan ya dawo ya ga kalar abin da kika yi".
Baki cike da abinci Ayla ta ce "Ba sai ya gani ba, hauka nake zan tsaya har sai ya kawo spoon, kin san yinwar da nake ji kuwa? Ni spoon ɗin ma sun mun kanana ne".
Kara faɗaɗa murmushita ta Rimsha ta yi tana faɗin "Eye lallai Ayla yanzu na gasgata zancen Kausar da take cewa muna cinye musu abincin gida, ashe dai ke ce mai cinyewa".
Yago fatar saman namar kirjin Ayla ta yi ta sunkuma a bakin ta tana faɗin "Ai da kika ce masa mun koshi da abincin nan, ji nayi kamar na shake ki dan haushi, ashe shima ɗan Albarka ne, ya yi kyan kai da ya matsa sai munci". Banda dari ba abinda Rimsha take yi, bayin Allah sun samu natsuwa yanzu kam.
Jin alamar motsin shi yasa Ayla ta yi maza ta goge bakin ta da bayan hannun ta, ta sunkuyar da kanta kasa tana ɓoye fuska, bata gama tauna abincin ba ta haɗiye ji kake gwat, ita dai Rimsha ta kasa daina murmushi, dariyar ma da kyar ta tsagaita shi.
Ahmad na shigowa bai san lokacin da spoon ɗin hannun sa ta suɓuce ta faɗi kasa ba, saboda bala'i kyau da ya gani, Rimsha na murmushi ga dimple na lotsawa, ga open teeth wow Masha Allah ya faɗa a ranshi.
(Niko nace dan ma bakaga lokacin da take cikin jin daɗi tana tare da daddy bane, yanzu ai duk ta rame ta kara duhu saboda wuya, ba ta samun lotion masu kyau da kayan kyaran jiki, fatar ta ya fara canzawa)
Sai da Rimsha ta ɗago sleeping eyes nata ta kalle shi sannan ya farga, cikin sauri ya duka ya ɗauki spoon ɗin ya kariso cikin ɗakin.
Tun bai zauna ba yake faɗin "Zan iya sanin me ya sanya wannan tauraruwar gimbiyar wannan murmushi mai kayatarwa haka?". Jin haka yasa Rimsha ta yi saurin kame kanta, ta dakatar da murmushi da take yi.
A ɗan ruɗe ya ce "Haba gimbiya menene abin ɓata rai kuma? To shikenan ki yi hakuri yanzu dai ku ci abinci kun ji? Ni