Showing 120001 words to 123000 words out of 355604 words
taɓa ɗaga ido ya kalli wata mace ba, saboda shi tun asalinsa in da yake tafiya nan kawai yake kallo, baya kalle kalle haka zalika baya son a kalle shi.
(Mu koma cikin labarin mu)
Sai kokarin cire wandon Michael yake yi, da kyar Tga ya dakatar da shi, amma shi ya dage sai fa ya ga me a wandorsa shi ma, tun da yau yaga zahiri, a saman wuya Tga ya ɗauke shi yana ƙoƙarin fara kewaye palon da shi dan ya lallaɓashi, kamar daga sama suka ji daddaɗar kamshin perfume nan, wadda mutun ɗaya ke amfani da shi.
Cikin sauri Tga ya sauƙe Michael gaba ɗayan su suka natsu, ban da daddy duk kan su sun kasa ɗaga ido su kalli saman benen, domin ganin fuskarsa a wani yanayin gara maka ka kalli fuskar Tiger a tsakiyar dokar daji, kuma dama ba ko wani lokaci suke iya kallonsa idan sun ji kamshin perfume nasa ba, domin idan ka sake ka kalleshi ka bari kuka haɗa ido tofa kai kam ka shiryawa hukunci, dan kwata-kwata baya son kallo a rayuwarsa.
Sai wani nuku-nuku suke yi, suna son sanin shin su yake kallo ne ko kuma dai ya aka ciki, shi John ya fi kowa shiga tashin hankali da ruɗu.
Michael zama ya yi yana turo baki, ɗan wannan hirar da ya yi a palo, tasa ya rage jin yunwa.
Lion ya jima tsaye yana kallonsu yana tunanin irin hukuncin da ta dace da su, bf kuma a gidan nan, abin ya ɓata mashi rai, yana kwance a saman bed nasa a ɗaki ya ga abin da suke yi a cikin Tv, amma hakan kuma da suka yi ya ɗan sa ya fahimci wani abin dangane da ciwon Michael, ya lura kamar sarrafa Michael ake yi, wasu abubuwa ba yin kansa bane, saboda yanzu zaka iya ganin Michael tamkar cikakken mutum anjima ka ganshi kamar a birkice, yau da Michael ya ce bai san asalin me a wandonsa ba, kuma bayan yana wanka abin ya ɗan bawa Lion mamaki, ya kuma kara darsa ayar tambaya a kan Micheal ɗin sosai.
Sun kwashe 10mins a haka kafin ya ce da Tga ya hukunta John yadda ya kamata, shi kuma Michael yazo su wuce ɗaki.
Cikin sauri Michael ya miƙe ya bi bayan sa, shi kuma Tga da yanzu ya gane me Michael ya kalla a wayar John sai ya fara da fasa wayar sannan ya ɗauki John a kafaɗar sa suka fice waje.
Yin hakan da John ya yi a wajen Turawa ba laifin bane, amma su a tsarin gidan su, laifi ne, domin ko Lion baya nan, Tga sai ya hukunta John, saboda su basa son ire-iren waɗan nan abubuwa, kuma Lion bai shiga hakkin kowa ba, ya ce duk mai son aure ya yi magana ayi mashi, kuma yana yin pastor ko in ce yana yin church da suke bi, basu yarda da ganin ire-iren su Bf ba, domin a Kristen ɗin ma, ko wani church da abin da suka fi bawa karfi, to su church nasu bai yarda da yin hakan ba, domin sun san biyawa kai bukata babbar illace ga lafiya, hakan yasa suka tsawata, bayan kuma an tsawatar a church daddy ma ya kara tsawatar musu a gida, da yake sun rena daddy shine shi John ya aikata.
Lion kuwa suna shiga bedroom nasa Micheal ya yi maza ya haye bed, domin yanzu ya fara mancewa da zancen yunwa da yake ji.
Dama Lion yana da aiki a gabansa, dan haka sai ya ɗauko laptop nasa, ya zauna a saman bed ɗin kusa da Michael, bayan ya kunna laptop ɗin ya gama komai ne ya ɗauko ɗaya daga cikin watch nasu na Triplets,
A hankali ya zaro memory's ɗin, ya ciri guda ɗaya ya sanya cikin system ɗin, videos sosai ya fara cin karo da su, kan vedio na farko ya fara dannawa ya yi Play, Michael na kwance a gefensa kamar a mafarki ya ji muryan James a cikin video yana faɗin "Idan ka je lahira ka sanar da su Roshan ni na kashe su" a sukwane Michael ya miƙe zaune yana kallon system ɗin, ya yin da shima Romeo ya kafe video da idanuwansa, James ne ke tsaye a gaban camera daya kunna da kansa, ya na riƙe da gashin wani dattijon Bature, wadda da ka gan shi ka san mutumin kirkine dan ya yi shigar mutunci, kuma da alama yana da mukami a gomnatance, sannan kuma ya tsufa dan zai kai 50 to 55 years haka, sai hawaye mutumin nan yake yi, ga shi ba halin ya yi magana domin James ya ɗaure masa bakin sa, sai dai hawayen sa kawai zaka gani, abin tausayi.
Babu tausayi babu imani da iya karfinsa James ya sanya wukar dake hannunsa mai bala'in kaifi ya yanka wuyar mutumin nan, sai jini ya fara feshi kamar fanfo. Ihu Michael ya kurma yana faɗin "No this is not my blood, wannan ba shi bane wani ne mai kama da James" Romeo kuwa ko a jikinsa dan kisan da ya fi wannan muni ma ya saba gani, shi ba ma James yake kallo ba wani tambari hoto dake bayan su yake kallo, yana son gane wace kungiya ce, ihu da Michael yake yi kamar zararre ne ya sanya shi juyawa ya daka mashi tsawa a kan ya yi mashi shiru, yana takura mashi yana aiki. Tsabar tsorata da tsawar ta sanya Michael sumewa a wajen.
Bayan James ya yanka mutumin sai ya ɗauko fake face na sa ya sanya sannan ya wuce ya kashe cameran. Video na biyu lion na sake yin playing, a nan ma dai James ɗin ne ke zaune a sansanin su na yan ta'adda, sai dai a wannan video da fake face a fuskar sa, yana zaune suna haɗa boma bomai, wasu gunguma gumguman yan ta'adda ne a cike a wajen, mai ɗaukar su video yana bin su ɗaya bayan ɗaya yana basu hannu suna dunkule nasu su bugi na juna.
Ko da yazo kan James ko kallon in da yake James bai yi ba, sai faman haɗa bom nasa kawai yake yi, ga tarin wayoyin lantarki a gabansa, idan ka kalli James a wajen, ya saje da su, barema da ya sanya wannan fuskar robar tasa, ba zaka taɓa cewa shi ɗin bane, ya shige cikinsu sun saje da juna, sai famar aiki yake yi, ba dan Lion ya kalli video na farko, ya kalli yadda James ya sanya fake face ɗin ba, da shima ba zai gane fuskarsa ba, sai dai ya gane shi da jikinsa.
Karewa mutanen wajen kallon Lion ya yi, suna nan kamar wasu yan yinwa, ya faɗa a ransa, kuma haka ne, a kaidar ta'addancin akwai kuɗi amma ba damar su iya zama suci kuɗin nasu, kullun suna cikin fargabar za'a kawo musu hari dan ɗaukar fansa, kullun tunanin yadda zasu farmaki waje kaza suke yi, dan su zama don a kasa, abincin kirkima basu iya zama su ci.
Fita daga video lion ya yi ya sake shiga wani, nan kuma James da kansa yake ɗaurawa kananan yara bom a jikinsu, yaran da basu fi 15 years ba, runtse ido Lion ya yi ya fita daga wannan video, gaba ɗaya ya zare Memory ya ajiye ya ɗauki ɗayar ya sanya, bayai ne a kan ta'addancin, da kuma kungiyoyin da James ya kai wa hari ya taɓa su, ya kashe musu mutane, jerin kungiyoyin Lion ya zubawa ido yana kallon, manya-manyan kungiya uku James ya kaiwa hari ya kuma kashe wasu daga cikinsu, kuma dukka mai gidansa ya sanya shi wannan aiki, shiru Lion ya yi yana tunanin dole a cikin wayan nan kungiya ukun ne ɗaya suka kama James dan ɗaukar fansa, to su waye?
Bashi da isashen lokacin da zai yi bincike a kan ko wace kungiya, hakan yasa ya yi watsi da su gaba ɗaya ya cire memory ma gaba ɗaya ya zube su cikin drawer, dan ba abin da za su kara masa sai zafin kai, dama idan baku manta ba, shi Lion baya karɓar taimakon kowa, aiki da ƙwaƙwalwarsa kawai yake yi, dan hakan yasa ya yi watsi da wayan can, a cewarsa faɗuwa ce ya karɓi taimakon wani, dan haka sai ya cigaba da aikin da nasa ƙwaƙwalwar kawai ba tare da ya dubi wani taimako daga wani wajen ba.
Michael kuwa ba shine ya farfaɗo ba sai karfe 7 nan ma Lion ya fito palon kasa ne ya cikaro da Tga a Palo, sai ya bashi umarnin a kan yazo ya zubawa Michael ruwa.
Yana farfaɗowa, da sunan James a bakinsa ya farfaɗo, sosai Tga ya rinƙa rarrashin shi yana lallaɓa shi, da kyar ya hakura ya miƙe ya nufi part nasa.
Nan ya isko Musharraf yana buɗa baki, zama ya yi a kusa da shi yana faɗin "Uncle ɗin James lokacin cin abinci ya ne?" Gyaɗa masa kai Musharraf ya yi sannan ya ce "Tun ɗazun na fita na nemeka a palo ban ganka ba, shine na haɗo tea da kayan fruits nace bari nazo na yi buɗa baki na".
Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita yana faɗin "Kazo muje palon kasa mu ci abinci mai kyau". Kasan cewar Musharraf yana son Michael sosai kuma bayan son ya ja baya da shi, hakan yasa ya amsa da to kuma ya miƙe ya bi bayan shi.
Abin mamaki yau zaune a saman dining table suka isko Lion, abin da ba su taɓa gani ba, Lion da cin abinci karfe 7 basu taɓa gani ba, har su kansu bodyguards ɗin sun sha ruwan mamaki, domin wani lokaci abincin dare sai karfe uku yake ci, wani lokaci ma haka yake kwana bai ci komai ba, barema yan kwanakin nan kwata-kwata baya wani cin abinci.
Musharraf bai taɓa zama a saman dining table nasu ba sai yau, ganin Lion ya sa ya sha jinin jikinsa, ji ya yi tamkar ya koma ɗaki, amma ba hali, domin sun riga sun fito idan ya koma Michael ba zai ji daɗi ba.
Kusa da Lion Michael ya zauna yana faɗin "Good evening Lion" tamkar babu shi a wajen, haka Romeo ya kasan ce, ko kallonsu bai yi ba, fruits kawai yake sha, cikin class da kwantatciyar hankali.
"Uncle ɗin James me zaka ci?" Cewar Michael, ɗan satar kallon Romeo ya yi, yana son cewa zai ci komai amma banda namar da Allah ya haramta idan suna ci, shi baya ci, amma kuma yana tsoron faɗin hakan, dan James ya ce masa kada ya yarda ya bari su gane cewa shi musulmi ne.
"Uncle ɗin James why kayi shiru talk now?". Musharraf ya rasa me zai ce, yana tsoron ya ce a bashi komai, azo a zuba masa abin da Allah ya haramata ya ci ba tare da ya sani ba, sannan yana tsoron ya ce kada a saka masa abin da Allah ya haramta ya jawo baban yaki a gidan.
Ganin haka yasa Michael ya ce da bodyguard ɗin su haɗa masa tea kawai, Lion na jin duk abin da suke yi, sai dai ba su isheshi kallo ba ne, dan kallonsu ma ɓata masa ido za su yi.
Bayan bodyguards sun haɗawa Musharraf sun miƙa mashi, shi kuma Michael ya fara ɗura fruits yana shan ruwa mai sanyi. Ya ji yunwa sosai bawan Allah.
Bai wani ci sosai ba ya fara kwarara amai a wajen kamar menene, cikin sauri bodyguards biyu daga cikinsu suka yo kansa, shi kuma Lion zame hannunsa ya yi daga kan fruits da yake sha, ɗaya daga cikin bodyguard ya miƙa masa tissue, ya karɓa ya goge ɗan bakinsa tare da hannunsa, sannan ya juyawa su Michael baya tare da ɗaukar wayarsa dake gefensa ya fara latsawa.
Cikin yan mintuna kalilan sai ga Tga, kusa da Lion ya zo yana faɗin ga shi nan, da hannu Lion ya yi masa nuni da Michael ba tare da ya yi magana ba, sannan ya miƙe ya bar wajen.
Da sauri Tga ya ƙarisa wajen Michael ɗin yana tambayar bodyguards ɗin lafiya me ya sami shi, cikin girmamawa suka ce suma basu sani ba, Musharraf yana son zuwa ga Michael amma yana tsoro, da farko saboda Lion na wajen yasa bai karisa wajen Michael ɗin ba, lokacin da Lion ya tafi kuma Tga ya zo, hakan yasa ya hakura kawai yana ganin Tga ya saɓi Michael suka wuce sama.
Kai tsaye toilet ya kai shi, sannan ya fito ya kyaleshi, da kyar ya iya yin wanka saboda ya galabaita sosai, yinwa ya ke ji over, ga shi ya zo ya sha ruwa mai sanyi da fruits shiyasa ya yi amai.
Ɗaure da towel a kugunsa ya fito bayan ya yi wanka, pajama kawai ya sanya a jikinsa, ya lallaɓa ya fito palon kasa.
Bai ga Musharraf ba, kuma bai damu ba, dan yasan ya tafi ɗakin sa ne, saman table ɗin ya sake komawa, domin yunwa yake ji, already bodyguard ɗin sun gyara ko'ina fes, sun goge amai ɗin sai tashin kamshi wajen yake yi.
Zama ya yi tare da basu umarnin su haɗa masa coffee mai zafi, cikin hanzari suka haɗa masa, yau ba shan salo da class, tun da ya kafa ɗan bakinsa a cup ɗin bai sauƙe ba har sai da ya shanye tas, wani daɗi ya ji, lokacin da ya ji cikinsa ta yi ɗumi.
Miƙewa ya yi dan ya kasa iya sake cin komai. Yana kokarin hawa saman bene suka haɗu da Tga yana sauƙowa, nan fa Tga ya ce ya wuce su tafi word room a duba lafiyarsa. Tirjewa ya yi ya ce shi lafiyarsa lou dan haka babu in da zai je, ba yadda Tga ya iya haka ya hakura ba dan yaso ba, sai dan baya son su yi jayayya, dan ya san Triplets gaba ɗayansu ba mai magana ya sauya, ɗan gara shi Micheal ɗin ma, idan abu ya zo da matsala yana iya sauya magana, amma Lion da James ko uban matsalane basu taɓa sauya magana sai dai ayi wace za'a yi, sai dai a mutu.
Wucewa Part nasa ya yi, kai tsaye bedroom ɗin Musharraf ya shiga. Sallah ya isko Musharraf yake yi, saman gado ya haye yana kallonsa.
Bayan ya idar ya yi addu'a ne ya ce "Michael sannu ko" dogon numfashi Michael ya ja tare da saukewa a hankali.
"Uncle ɗin James gobe zan saka John ya karo maka wasu kayan sawa, dan na lura wayan da James ya saya maka basu da yawa sosai" murmushi Musharraf ya yi yana zuba mashi godiya.
Saukowa kasa Micheal ya yi, ya zo ya zauna suna fuskantar juna, a nutse ya ce "Uncle ɗin James, idan kana yin wannan abin da ka yi yanzu yana burgeni sosai, ko zaka koya mini ne?" Cikin sauri Musharraf ya ce mashi "Sallah kake nufi?" Gyaɗa kai ya yi yana faɗin "Wannan abin da na shigo na sameka kana yi yanzu". Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Michael ba'a yin Sallah sai idan mutun ya kasan ce musulmi ne, azumin ma da kaga na barka ka yi saboda nasan kuma kuna yin shi ne, a addinin ku ya halakta, amma shi Sallah wanda ya musulta ya karɓi Kalmar shahada ne kawai yake yin shi".
Shiru ya ɗan yi kamar mai tunani, can kuma sai ya ce "To shi me ma kace? Idan za'a shigeshi kuɗi za'a bayar ne ko me?" girgiza kai Musharraf ya yi alamar a'a, sannan ya ɗora da cewa "Musulunci ba'a shigar shi da kuɗi, kyauta ne". "To ko ma da kuɗin ne ni ka shigar da ni ina so, kuma ina da kuɗi a account na sai na sanya a ciro maka, idan ma yanzu kake so sai na je ɗakin Lion na ɗebo maka, dan shi yana ajiye kuɗi sosai a ɗakin shi".
Tsabar daɗi Musharraf bai san lokacin da ya riƙe hannayensa ba, cike da farinciki ya ce "A'a Michael kyauta ake shiga musulunci, kuma yanzu zan saka ka, amma fa sai ka mini alkawarin ba zaka taɓa gayawa kowa ba, kuma ka yi mini alkawarin duk abin da na koya maka zaka ɗauka kuma zaka rinƙa amfani da shi, sannan ba zaka gayawa kowa ba".
Cikin sauri Michael ya amsa da ya yi alkawari zan rinƙa rike komai da za'a koya mashi, sannan kuma ba zai taɓa gayawa kowa a gidan ba, kuma zai rinƙa yin duk wani abin da Musharraf ɗin ya ce masa ya yi. Daɗi a wajen Musharraf ba'a magana, duk da cewa dama yasan Michael ba zai yi wuyar karɓar addinin musulunci ba, saboda a halin da yake ciki yanzu ƙwaƙwalwar sa babu komai na kin wata addini a cikinta, sai ma son mutane dake cikinta.
Babu tunanin me zai je ya zo, babu tunanin abin da zai iya fuskanta, ya mance gidan William jacop yake, a tunaninsa Michael zai iya riƙe sirrin, cikin sauri ya yanke hukuncin bawa Michael kalmar shahada, shi kuma Michael cike da murna ya karɓa ya maimaita, sau uku yana maimaita wa, ya ce kalmar ta mashi daɗi over.
(Babbar magana, yau ake yin ta, shin kuna tunanin Michael zai iya rufe wannan sirrin? Kuna tunanin Michael zai iya addinin musulunci? Zai iya Sallah sau biyar a rana? Ya batun tashi sallar asuba? Zai iya kuwa? Zai iya azumi? Sannan zai iya yin basaja, a cikin gida ya nuna musu shi Kristar ne a wajen Musharraf kuma musulmi? Kada ku mance Michael baya karya, bai iya ba kuma bai taɓa yi ba, in fact bai ma san yadda akayi ba, ya ya kuke ganin wannan cakwakiya zata kasance? Yau ake yin ta, ni dai sai dai na ce Allah ya jiƙanka Musharraf)
Farinciki yasa Musharraf ya ringume shi yana hawayen murna, shi Micheal bai ɗauka wani abin arziki ya yi ba, sai bai wani damu ba, mamakin farincikin da Musharraf yake yi ma ya yi.
"Michael daga yau na canza maka suna zuwa Aryan" turo ɗan bakinsa ya yi ya ce "Ni uncle ɗin James bana son Aryan, ba bu daɗi sunan, why zaka canza mini suna ma tukunnan?" Fuska ɗauke da murmushi Musharraf ya ce "Ai dole na canza maka suna, domin sunan ka ba na musulmai bane, kai kuma musulmi ne yanzu" jinjina kai ya yi yana faɗin "Okey tom ka nemo wani suna banda Aryan kam, dan Aryan babu daɗi" shiru Musharraf ya