Showing 213001 words to 216000 words out of 355604 words
yadda daddy zai yanka monitor lizard nan kuma ya tashi, kayan Aiki daddy yasa John ya kwaso mashi, cike da kwarewa ya fara da yi wa monitor lizard ɗin allura na kashe zafi sannan suka ɗaure kafafunsa, ya gama gyara komai dai, sannan ya fara tiyatar.
Dukkansu zaba ido suka yi har da uncle Herry ga Tga a gefe suna kallon yadda wannan tiyata ke gudana, daddy yana yi yana yi wa Michael baya ni ta yadda zai fahimtar da kyau, badan okey sir ba abin da Michael yake cewa.
Haka daddy ya kammala ya ɗinketa kuma ta tashi, tafi suka sa suna faɗin "Well done, good job daddy" da yake shima daddy ba kasafai ya cika murmushi ba, baya murmushi sai ta ƙuƙe mashi, dariya kam shima ba'a magana baya yi kwata-kwata, da alama daddy ma boss ne lokacin da yake tashen sa.
"Michael a kawo wata monitor lizard ɗin mu sake gwadawa domin ka fahimtar da kyau".
Cikin sauri ya ce "No daddy ni ba sai an sake nuna mini ba, already na haddace komai, dan haka uncle T ya kwanta a bani wuka mai kaifi sai na fara gwada tiyatar cikin a cikinsa, shi kuma John zan gwada na zuciya a kansa, ni fa bana son wannan ɗan karamin wukar, kato mai kaifi za'a bani, kaga cikin uncle T akwai tauri"
(To fa tashin hankali)
Zaro ido John ya yi yana tunani yadda daddy ya yi wa wannan monitor lizard tiyata a gaban su suna gani, sannan yanzu Michael ya ce suma su kwanta ya yanka su haka, tab ba gwara daddy ba aikin sane ya saba, daya yanka monitor lizard ɗin ya ta shi, ya yi rai, Michael kuma fa? Yanzu yake karatun abin daga nuna mashi sau ɗaya wai ya iya, yazo ya yankasu shikenan su kasa tashi su mutu.
Shi kuma Jay bin su kawai yake yi da ido, yana mamakin iskanci irin na Michael, shi komai aka karantar da shi sai ya ce a kan uncle T da John zai gwada, wannan wace irinyar bala'i ce.
Uncle Herry kuwa, baya baya ya yi ya bar wajen dan shi iskancin Michael ya fi karfin sa, yaro da ankoya masa abu sau ɗaya sai ya ce shi lallai sai ya gwada kuma a kan su.
Tga ne ya ce "Michael are you mad? A cikina zaka gwada tiyatar ma kenan? To ni monitor lizard ne? Kai bakaga ko daddy da yake kwararren likita ma da dabba ya gwada bane? Kai ne shararre ɗan nema shine zaka ce sai a jikin ɗan adam zaka gwada? To baka isa ba, ni kaga tafiya ta ma, barin kasarma zan yi anjuma kaɗan, ka dai'na kallona ko ka huta, haba wannan bala'i dame ta yi kama" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya bar wajen.
Shi dai Michael ko a jikinsa suka cigaba da abin da suke yi shi da daddy, daddy'n yana lallaɓashi akan ya gwada da wata monitor lizard ɗin, da kyar ya yarda, da ya kafe sai dai akan John zai gwada, amma da daddy ya lallaɓa shi, sai ya yarda da zai gwada akan monitor lizard ɗin.
Haka aka kawo mashi wani monitor lizard ɗin ya kwanta ya fara yin komai kamar yadda daddy ya yi, an kuwa yi Sa'a akwai kaifin ƙwaƙwalwa yana ɗinketa sai ga shi ta tashi, sosai daddy ya ji daɗi yana faɗin "Dama na san zaka iya, jinin jacop Roshan babu jahili mara ƙwaƙwalwa, dukkan mu haka muke ba da bala'in kaifin ƙwaƙwalwa".
Uncle Herry da ya dawo yanzu ne ya karɓi zancen da cewa "Of course, blood of Jacop Roshan is not easy, ba wasa ba". Shi dai Michael haka kawai ya ji bai ma son Roshan ɗin nan, dan daga jin sunan shine bakin mugun family'n su, da alama shi Tga ya gado (To fa🤔)
"Daddy please stop talking about this Roshan, let's continue our practical" ba su wani damu ba dan ya ce bai son hirar kakansu Roshan, dan saboda har yanzu suna ɗaukar Michael kamar ƙwaƙwalwarsa bata dawo normal gaba ɗaya ba, hakan yasa ko ya ce baya son wani basa damuwa.
Haka suka ci-gaba da karatun har karfe 6:30 daidai, bedroom nasa ya wuce ya sake yin wanka ya shirya cikin kananan kaya masu kyau, full Jeans har kasa da kuma T-shirt kamar dai yadda ko wani cikakken musulmi yake dressing, yanzu ya daina yawan saka crazy ma, dressing nasa yake yi na cikakkun mutane masu cikakken hankali.
Bayan ya gama shirinsa ya feshe jikinsa da perfume mai daɗin kamshi, sannan ya fito, word room ya fara shiga ya duba Musharraf, har lokacin barcin wahala yake yi Bawan Allah.
Kan shi Micheal ya shafa yana faɗin "Allah ya saka maka uncle, In Sha Allah zaka samu lafiya" ya kai karshen maganar yana manna mashi kiss a goshinsa.
Daga nan ya wuce zuwa waje, kai tsaye parking space ya nufa, kamar yadda suka saba fita zuwa masallaci, haka yau ya fita shi kaɗai, duk sai ya ji babu daɗi, tunani yake yi anya zai iya rabuwa da Musharraf kuwa? Yanzu ma zuwa masallaci shi kaɗai ma ya ji wani iri, ba dan sallar farilla bane da ba zai je ba, amma haka ya daure ya nufi masallacin. Sai da ya yi sallar isha sannan ya dawo gida, lokacin su kuma Tga jirginsu ya ɗaga zuwa Naija, karfe 7 daidai suka tashi.
Sai da Michael ya kara shiga word room ya duba Musharraf sannan ya dawo palo suka ci abincin dare, lokacin kuma karfe 8:40, part nasa ya koma bayan sun kammala.
Yana shiga ya kwaso takardunsa na makaranta, kafin ya fara karatun boko sai da ya tusa karatun Alqur'ani mai girma suratul humaza da Musharraf ya gaya mashi yau da asuba, bayan ya tusa kaman sau uku sai ya rufe tare da yin addu'a kamar yadda Musharraf ya koya mashi, sannan ya buɗe takardun sa ya fara dubawa yana nazari akansu, abin da ya shige mashi duhu sai ya shiga goggles ya duba, idan ya duba bai gane ba ma sai ya kira Lion a waya akan ya mashi karin bayani, da yake Lion yana son ya yi karatun sosai haka zai zauna yana mashi bayani dalla dalla. Ta ko'ina Michael yana samun taimako a kan karatu, daga daddy har Lion, ga Musharraf shiyasa a take yake haddace duk wani abin da aka koya mashi
Sai wutaren karfe 11 sannan ya tashi ya yi wanka ya yi shirin kwanciya tare da tattare takardun ya mai da su in da suke, shiryawa ya yi cikin wando dogo da riga mai ƙaramin hannu, kayan ba su da nauyi, suna da kyau sosai launin brown colar, kalar gashin kansa kenan.
Bayan ya gama ne sai ya fesa air freshener a ɗakin nasa tare da rage gudun Ac ya fito waje, kai tsaye word room ya sake nufa, kamar dai ɗazun Musharraf na ta barci har lokacin, yanzu ma addu'a ya yi mashi tare da manna mashi kiss a goshi ya gyara mashi bargon da likitocin suka rufesa da shi, ya haurar mashi zuwa saman kirjinsa sannan ya koma bedroom nasa.
Addu'ar barci ya yi ya kwanta tare da kiran Lion video call dan suka ga juna. Umm jini ba wasa ba.
A lokacin Lion ya na zaune a tsakiyar bed nasa, ya yi sallar isha tare da wanka ya shirya cikin kayan barci launin sky blue masu shegen kyau, ba karamin kyau ya yi wa kayan ba, ga idanuwansa nan sun yi wani irin yanayi mai kayatar da mai kallonsu saboda yana jin barci, barci ne a cike a cikinsu amma bai kwanta ba, yau idanun nasa sai suka yi kama da sleeping eyes, sai wani lumshe su yake yi, ga red lips nasa nan har wani ja suka kara suna kyalli kamar ya shafa lips balm, shi dama haka face nasa take, tana sheki kamar me, soft skin ɗin nan nasa ba'a magana wajen laushi da sheki.
"My Lion barci kake ji ne?" Da gera ya amsawa Michael ɗin akan yes barci yake ji.
"Okey to ka kwanta mana" ɗaura wayar ya yi a gaban laptop dake a gabansa domin ya sami dama yana aiki yana kallon Michael ɗin da kyau "I can't sleep now" Cikin sauri Asif ya ce "James ko?" Gera ɗaya ya ɗaga mashi alamar e.
"Allah zai biya ka da gidan aljanna My Lion" sai lokacin ya dawo da kallon shi kan Micheal ɗin daga kan laptop ɗin, ba karamin daɗin furucin da Asif ya yi ya ji ba, amma ba wanda ya iya gane cewa ya ji daɗin hakan saboda bai nuna alama ba.
"Yaushe zaka dawo?" Michael ne ya tambaya. Sai da ya ɗauki 1mins sannan ya ce "I don't know but know good night" ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin katse kiran "I really missed you my Lion" shine abin da Asif ya faɗa wadda yasa Lion dakatawa bai katse kiran ba.
Kallon kasar ido ya yi mashi kafin ya ce "Ba zaka canza ba kenan?" Cool murmushi Asif ya sake yana faɗin "Yah in dai akan kune ina nan yadda nake" Shiru ya yi mashi bai sake magana ba.
Sai hira Asif yake yi mashi amma yaki tankawa kawai aikinsa yake yi, idan da sabo sun saba, hakan yasa Asif bai damu ba, can kuma sai ya ce "Asif you have class by 7, so good night" ya yi maganar a sanyaye.
Mamaki ne ya kama Michael, yaushe Lion kuma yasan suna da class karfe 7, kenan yana bibiyarsu ne? Ko me.
Yana tsaka da tunani ya ga Lion zai katse kiran "I love you" shine abin da ya furta jinjina mashi kai Lion ya yi tare da katse kiran ya ajiye wayar a gefensa ya cigaba da abin da yake yi.
Sai wuraren karfe 1 na dare sannan ya ajiye laptop ɗin ya fito palonsa ya ɗauki maltina da glass cup ya zauna saman sofa, bayan ya sha ya ɗan jima a wajen yana tunanin rayuwa, haka kawai ya ji lallai yana son taimakawa yan Nigeria, domin ya san suna da kwakwalwa da basira kawai masu taimaka masu ne suka rasa. Sai wuraren karfe 1:50 sannan ya miƙe ya shiga cikin ɗakinsa.
Kara fesa air freshener ya yi bayan wanda Imran ya fesa mashi, sannan ya kure gudun Ac, sanyayyar sanyin Ac da kuma kamshin air freshener ne kawai ke tashi, abin ba'a magana, ya kayatar matuka.
Ya haye saman lallausan bed nasa ya yi addu'ar barci ya kwanta, tun da ya zo Nigeria baya shiga cikin bargo saboda zafi, haka yake kure gudun Ac ya kwanta, amma sai ya ce a hakan ma zafi yake ji.
Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, asuba ta gari.
Washigari su Akil suka shigar da rahoto da komai wa yan sanda dan gane da Aafia, kamar yadda ya yi wa su Rimsha alkawari haka ya kai su gyaran jiki da kunshi tare da wanke kai, kuma har da Umaishansa ya haɗa.
Suna a wajen gyaran jikin ne Imran ya zo ya same su, a nan Akil ke gaya mashi abin da yake faruwa na ɓatar Aafia, ta shiga tashin hankali sosai shima, sannan ya fara tunanin ko dai bibiyar family'n su ake yi ne, ga Jelly shiru yanzu kuma Aafia anya lafiya kuwa?.
Tunani cike fal ransa ya karisa cikin saloon ɗin wajen su Rimsha, tana zaune ta bakin kofa a palo kenan, da yake ciki da palo ne, to a can jiki ake gyaran kai da jikin, palon kuma na zaman wayan da suka yi rakiya ne, akwai kujeru har da Ac, wajen gyara ne babba na ƴaƴan manya.
Imran ya samu an gama wa Rimsha nata ana yi wa Akila da Umaisha kuma suna ciki, ta yi kyau sosai da sosai, kunshin ba karamin kyau ya yi mata ba, amma sai da suka goge ɗan ragowar nata da ya rage a kafar tata kafin su yi mata wani, ga shi ta sha gyaran jiki, an kara fito mata da soft skin ɗin nan nata sosai da sosai, sai wani kayatatcen sheki take yi, abin ba'a magana.
Imran. Lokacin da idanunsa suka sauƙa a kanta sai da ya ji wani irin, sai da gabansa ya faɗi, ta fito kamar tauraruwa mai haske a sararin samaniya cikin hudun dare.
Kujerar gefenta ya zo ya zauna, ya jiki ya fara yi mata, da fara'a ta amsa mashi da sauki. Rimsha kenan idan kaga fara'arta to da Imran ne ko Akila, su kawai take yi wa dariya a yanzu.
Hannayenta ya riƙo cike da kulawa ya fara magana "Rimsha zuciyata ta kasa yarda cewa ba wani abin da yake damun ki, dan Allah ki gaya mani menene yake da munki? Ni fa yayan ki ne, idan har baki gaya mani ba waye kike da shi yanzu a duniyar nan da zaki gaya mawa?" Sunnar da kanta kasa ta yi tana ɗan mutsu mutsu da hannunta alamar bata ji daɗin riƙeta da ya yi ba.
Ganin haka yasa ba musu ya saki mata hannun nata yana kara nanata mata tambaya akan me yake damun ta.
"Yaya Imran ba wani abin da yake damu na, idan da akwai da zan gaya maka".
Nisawa ya yi kafin ya ce "Amma me yasa da kika ga Saif kika suma? Me yasa a ganin sa na biyu ma kika suma? Ranar da hakan ta faru naje bedroom naki da daddare dan na duba ki saboda sumar da kika yi, ina tsoron kada ya ja maki wani ciwon da cikin dare, shiyasa na shiga ɗakin ki da daddaren, na same ki kina kuka kina faɗin Allah ya cire maki son shi ki huta, wanene wannan? Tun jiya na kasa runtsawa saboda kina cikin damuwa, abin ya tsaya mani a raina, idan na barki haka to tabbas ban riƙe amana ba, sannan duba da abin da Dr ya ce na akwai abin da kike so wadda ya haifar maki da matsalar nan, da kuma abin da nagani kuma naji da kunnena kina faɗa daren ranar, hakan yasa na tabbatar da e da gaske akwai wanda kike matukar so ne, dan Allah kada ki ɓoyewa yayan ki wanenen? Ko dai Saif ɗin ne?".
Zaro ido sosai waje ta yi, nan take ta ji numfashinta na fita da sauri sauri, dafe kanta ta yi tana faɗin "A'a yaya Imran ba shi bane, ni babu wanda nake so".
"Rimsha ko ki ƙi ko ki so Saif shine wanda kike so, domin daga kiran sunan sa kin razana, sannan ranar nan da kika kawo mashi ruwan sha, yanayin yadda kika kira sunan sa kafin ki suma hakan ya kara tabbatarwa da lallai akwai wani abin a kasa wadda sai yanzu na gane menene, yanzu haka da ga gida nake na je ne ba wanda ya ganni, na bincika dan na gano menene ke damun ki, a cikin kayan da kika zo da shi naga zanen fuskar Saif wadda wannan zanen kuma ba jiya ko yau aka yi shi ba, ya ɗan jima, hakan yasa na kara tabbatarwa da e tabbas Saif kike so, na tambaye ki ne kawai dan ina son in ji da ga bakin ki, akwai hujjoji da dama wadda suke nuna e lallai Saif shine mutumin da kike so, amma meyasa zaki ɓoye mani? Nifa yayan kine, bugu da kari kuma ni kaɗai ne wanda zai iya haɗa ki da Saif a faɗin Nigeria, ko dai so kike ki cuci abokina ne? So kike ki hana shi samun zankaɗeɗiyar mace kamar ki" ya yi maganar sa ta karshen cikin raha, kuma ya yi ne dan yasa ta dariya saboda yaga ta shiga matsanancin yanayi mara kyau.
Ai kuwa tana jin maganar tasa ta karshen sai da ta yi murmushi, gyara zama ya yi ya ci-gaba da magana "E mana naga alama so kike ki hana Abokina samun mace ɗaya tamkar da million, amma fa Jelly na tafi tom, nima jelly ta ɗaya ce tamkar da million a waje na, kina son kiyiwa Lion bukulu ko? Ki yi mashi bakin cikin samun wannan zankaɗeɗiyar, kyakkyawar, kuma.....". Bai karisa ba ya yanke maganar yana kallonta
Dariya ta yi har sai da dimple nata gefe dukka biyu suka lotsa sosai, cikin dariya ta ce "Yaya Imran ka bari bana so".
Ɗan kwanto da kansa kaɗan ya yi ya leƙo fuskarta yana faɗin "Eyee waya ganta a gidan Lion matsayin amarya, wow gaskiya abin fa zai bada wani kala mai kayatarwa, ni dai koma me ni zan rako ango sayan baki". Ya kai karshen maganar yana dariya
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana ta dariya, ga flowers da aka zana mata a hannun nata ba'a magana, sun fito sosai, da ta rufe fuska ba karamin kyau ta yi ba.
Zuba mata ido ya yi yana kallon tsantsan farincikin dake a kan fuskarta, wadda tun da suka haɗu bai ganshi a tattare da ita ba, hakan yasa ya fara tunanin ya zama dole ya san taya zai ɓullowa lamari har ta samu kusanci da Lion, dan ta dawwama a cikin farinciki haka, a nasa tunanin idan ta samu kusanci da Lion shikenan one day one time zai fara sonta, bai san cewa abin dai to ga shi nan ne, yana ɗaukar kamar zuciyoyin iri ɗaya ne.
Sosai ya nutsa cikin tunanin yadda zai ɓullo wa abin, har aka gamawa su Akila gyaran jikin, suka fito palon wajen suka same shi, gaisawa suka yi sannan ya biya masu kuɗin suka fito suka isko Akil cikin mota zaune yana jiransu.
Yana ganin su ya fito wai zai je ya biya kuɗin, Akila ce ta gaya mashi yaya Imran ya biya, to ya amsa da shi sannan suka shiga cikin mota, Imran ya tambaye shi ya batun school na Rimsha, nan ya gaya mashi ai kamar yadda ya yi alkawari to ya cika, gobe zata iya fara zuwa, amma da kayan gida zata je kafin nan a bata uniform daga baya.
Sosai Imran ya ji daɗi sannan ya musu sallama ya tafi. Sayyaya Akil ya kai su, suka sayi kayan makarantar Rimsha, irin su jaka da takalmin da sauransu, sai murna take yi, har suka dawo gida bakinta ya ki rufuwa.
Bayan sun dawo ne, suka haɗu su ukun suka fara aikin girki da gyaran part ɗin Imran ɗin, shi kuma Akil ya wuce aikin neman Aafia.
Suna aikin suna hira, Akil tana ba su lecture