Showing 186001 words to 189000 words out of 355604 words
abin da ba ka sani ba game da Lion, wlh duk kansu har Michael suna da zuciya mai kyau, ba su mance alkhari, kawai dai dan suna kafurai ne, shiyasa ba zaka yi zaton hakan ba, amma ba dan haka ba suna da zuciyoyi masu kyau, musamman ma James yana da kirki sosai, shi Lion ne dama ya fisu taurin zuciya, amma shima lokacin ɗaya daɗin kira'ar Alqur'ani mai girma da nake yawan yi a school Allah yasa ya ja hankalinsa ya yadda da Ni, so ni yanzu wlh ba zan iya tinkararsa in ce kana son yin magana da shi ba gaskiya, saboda na san ma ba zai yi wu ba, kawai ka yi hakuri, ni yanzu zan tafi za mu yi waya idan na isa gida". Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar jiki a mace.
Sai mamaki da al'ajabi tare da jimami Nawid ya ke yi, wai GAR ne a Nigeria.
Taɓa shi Imran ya yi, yar firgita ya yi tare da dawo da kallonsa kan Imran ɗin, a hankali ya koma ya zauna saman chair nasa yana faɗin "Dan girman Allah Prof ka taimaka ka haɗa ni da shi, ko hoto mu ɗauka" Shiru Imran ya yi yana tunanin taya zai fara tinkarar Lion da zancen, domin ya san halin kayansa, ba yau suke tare ba, Allah ne kuma ya haɗa zuciyoyinsu, Allah ne ya kaddara wa Lion Kaunar Imran ta sanadiyar kira'ar Alqur'ani mai girma da yake yawan zama yana yi a Library su, shi kuma Lion yana zama karatun a wajen, daga haka suka haɗu, daga haka Alqur'ani mai girma ta fara shiga zuciyarsa har ya ji yana son karantata, bai karɓi Addinin Musulunci ba har sai da ya samu ilimi mai zurfin gaske dan gane da addinin, sai da ya yi haddar Alkur'ani mai girma sannan ya haddace manya-manyan daga cikin littafan musulunci, ya jima yana nazari akan addinan guda biyu domin ya tantance ta gaskiya, baya yanke hukunci haka kawai da ka, sai ya yi nazari da bincike, wannan dalili yasa, ya samu ilimi sosai akan musulci haka akan kiristanci, daga karshene ya yanke wa kansa hukuncin da ta dace da shi, ya karɓi Addinin Musulunci bayan ya gano cewa ita ce ta gaskiya, amma bai wani jima da musulta ba, ya dai ɗan jima da fara bincike a kan addinan guda biyu.
Story💖
"Nawid duk da nasan Lion yana kaunata ba zan iya tinkararsa da maganar ba, saboda na san ba zai yi ba, idan baka sani ba ma yau ka sani familynsu gaba ɗaya basa son mutane ko kaɗan, ka taɓa ganinsa tare da wani ko a Tv ne bayan James ko Michael?" Girgiza kai Nawid ya yi alamar a'a "To ka gani, amma dai In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ko da da idone ka ganshi kafin ya koma" to Nawid ya amsa mashi da shi tare da zuba mashi ruwan godiya sannan suka yi musabaha Imran ya miƙe ya nufi in da Akila ke kwance yana faɗin "Za mu iya wucewa da sister yanzu ne?" "A'a Prof na yi mata karin ruwa, sai dai zuwa yamma irin karfe 4 haka" To Imran ya amsa da shi tare da tashin Akila daga barci a kan su tafi, nan fa ta ce a'a ita kam zata zauna da Rimsha gaskiya, ba dan ya so ba haka ya wuce shi kaɗai ya barsu amana a hannun Nawid ya tafi neman Lion.
Yana tuki yana tunanin ai na zai fara neman Lion ne ma wai, dan dai yasan bai koma ba yana nan Nigeria, sai ya wo yake yi da motarsa bai san ina ya nufa ba, wata hanyarma sau biyu yana kewaya wa ya sake kewayowa, duk ba tare da ya sani ba, hankalinsa na can cikin tunani.
Wayarsa da ke a zaune a gefensa ne ta ɗan yi kara alamar shigowar saƙo, cikin sauri ya ɗauki wayar, ganin sunan Saif ya sa ya gangara gefen titi ya tsai da motar.
Buɗe massage ɗin ya yi ya fara karantawa, address ne a rubuce a jiki tare da faɗin kasame ni yanzu, jinjina kai Imran ya yi yana faɗin Alhadulillah a ransa. Cikin sauri ya juya kan motar ya nufi wannan address ɗin.
💖UNGUWAR ISHAKU ROAD💖
Tampatsetsen gida ne na gani a faɗa, hawa ɗaya ne, irin dai manya-manyan gine-ginen na nan Naija, gaba ɗaya komai dake a cikin gidan daga waje a ka shigo da su, ginin ya tsaru sosai, irin gidan nan ne da akeyi a shirya komai su Furnitures da komai sai a sai da haka, to shine, sai mamaki Imran ya ke yi, yaushe Lion kuma ya san Nigeria har ya iya zuwa ya sayi gidan nan? Yana ta tunani har ya iso bakin gate ɗin, horn ɗaya ya yi, da ya ga ba a buɗe mashi ba sai ya san e lallai babu mai gadi, hakan yasa ya fito da kansa ya shiga cikin gidan, ya wangalewa kansa katafaren gate.
Bayan ya buɗe sai ya dawo ya shiga motarsa ya ja izuwa cikin gida, tsayawa zayyana maku yadda kawatuwan cikin gidan nan ya yi zai cinye mana ɗan sauran filin dake a gare mu, ku kawata yadda manya-manyan gine-ginen mu suke a ranku.
Kai tsaye parking space ya wuce, bayan ya kashe motar ne ya fito ya nufi tampatsetsen kofar da zata sadaka da cikin palon, daidai zai shiga kamar an ce ya ɗago kai sama, can ya hango Lion tsaye a balcony daga shi sai Short a jikinsa, dama Imran ya san halinsa akwai shi da san tsayuwa a balcony yana kallon yanayin gari daga ta sama.
Shiru ya ɗan tsaya yana tunanin ko dai ya koma ya kwaso mashi kayan sa ne, dan yadda ya ganshi da short ɗin nan ya san ya yi wanka ne, kuma ba zai iya mai da kayan da ya cire ba, kayan da ya zo da su kuma suna gidan su Imran ɗin, da alama kuma bai fita ya sai wasu kayan ba, ba karamin aikin shi bane yanzu ya ce kayan Nigeria ba su yi mashi ba, duk da cewa rabi da kwatan kayan Nigeria ma daga waje ake shigo da su.
Ganin ba abin da tsayuwa zata kara mashi ne yasa ya shige cikin gidan kawai yana duba time a agogon hannunsa. 1:30 lokacin sallar azahar ta yi.
Wow gaskiya palon kasar nan ta haɗu sosai, kusan komai na cikin palon fari ne da ash color, sai tashin kamshi perfume ɗin jikin Lion take yi, da alama ya ɗan zauna a palon, gaba ɗaya furnitures dake a cikin palon set biyu suna cikin ledojinsu ba'a ɓuɗe su ba, komai tsab-tsab da yake sabbine, kuma sai da aka share aka gyara mashi komai kafin ya shiga ya zauna.
Abin da ya faru bayan ya baro gidan su Imran, kai tsaye bakin titi ya wuce, a nan ne ya tsaya ya kira kakansa a waya a kan ya kira President na Nigeria yana buƙatar number dillalai masu dillancin gidaje, His Excellency ya tambaye shi me kuma haɗin sa da Nigeria, nan ya ce da His Excellency Nigeria ya zo, sosai His Excellency ya yi mamaki sannan ya ɗaura da cewa to ya sauƙa a gidan Gwamnati mana, a'a ya ce baya buƙata domin aikin sirri ya zo yi, shi kawai number yake buƙata, ba tare da ɓata lokaci ba aka fara aiki a kai, cikin kankanin lokaci kakansa ya gama komai, har in da yake dillalan suka zo da motarsu suka same shi, bayan ya turawa kakansa address ɗin wajen ta hanyar tambayar sunan wajen. Kin shiga motar ya yi ya ce ba ta yi mashi ba, nan ma sai da His Excellency ya sa aka tura mashi wata dankareriyar mota daga gidan gwamnan Kaduna, su dai sai karɓar umarni suke da sun tambayi waye ne sai ace ba ruwansu.
*Abun ku da kuɗi da kuma karfin mulki, kada ku mance Nigeria dai a kasan Usa take, dama kullun sai yadda suka yi da mu😭 su mulki kasarsu kuma su kulkemu, abin da suke so shi ya zama dole gwamnatin mu ta yi😭 hakan yasa a cikin wannan dare a ka yi wa Lion komai dan dole.*
To daga nan ne suka wuce ya je ya ga gida je, wajen gidaje biyar aka nuna mashi, duk ya ce basu yi mashi ba, da kyar ya karɓi wannan gidan, ita ma lallaɓawa kawai yake yi ba wai dan ta yi mashi ba, haka dillalan suka saka yaransu suka share mashi ko'ina aka gyare tsab, ya shige, kuma har suka gama aikin ba wanda ya samu damar sanin wanene shi, saboda akwai face mask a fuskarsa, kuma ma bai tsaye a in da suke ba. Wannan shine abin da ya faru
Mu koma kan story.
💖Imran💖
kai tsaye staircase ɗin ya nufa yana sauri sosai. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga palon saman, ɗakuna uku ne a cikin palon, tunanin ta balcony da ya hango Lion ya yi, daddɗar Kamshin perfume ɗin Lion ɗin ne ta isar mashi da sakon ga ta in da Lion ɗin yake, cikin sauri ya nufi in da kamshin ta fi yawa, yana tafiya yana jinjinawa karfin perfume ɗin nan, domin kwata-kwata yau Lion bai sanyata a jikinsa ba, saboda ya baro ta a gidan su Imran ɗin, tun wadda ya sanya jiya ne ta bule gidan da daɗin kamshi.
Sallama ya mashi kafin ya shiga cikin ɗakin, kai tsaye balcony ya nufa, Lion na tsaye, yana kallon birnin Kaduna, kyakkyawar halittar jikin nan nasa a waje, dan short ɗin nasa ma, iya rabin cinyarsa ta tsaya mashi, subhanallah kyawun ainahin surar Lion ba zata iya zayyanuwa a baki ba, saboda ta wuci baki ya faɗe ta, sai wanda dai ya gani a zahiri, soft skin ɗin nan nasa sai wani kyalli na musamman yake yi, ga bala'i laushi kamar bai taɓa fita waje ba, kamar fatar jariri, wannan kwantacen bakin gashi siɗif ɗin dake kwance a saman cinyoyinsa da hannayensa, ba karamin kyau ta yi ba, ga wani gashin a kwance a buɗaɗen faffaɗar kirjinsa, damatsan hannunsa kuma ba'a magana sai wanda ya gani, kallon kasa yake yi wa garin Kaduna, irin mutun ya sunkuyar da kansa kasa ya kuma ɗaga idanuwansa yana kallon waje, to haka ya yi shima,
Imran yana zuwa ya miƙa mashi hannu dan su gaisa, ba tare da ya kalle shi ba ya miƙo mashi nasa hannun suka gaisa.
Shiru suka tsaye kamar kurame, wayar Lion dake a cikin ɗakin ne ta fara kara tana kira mashi number mai kiransa tare da suna da location, Imran na kokarin zuwa ya ɗauko mashi wayar, ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu alamar baya buƙata, bari Imran ya yi suka ci-gaba da tsayuwa shiru.
Kira ta farko ta yanke ta biyu ta shigo, ita ma ta yanke sai a karon na uku ne ya juya a nutse ya nufi cikin bedroom ɗin, girgiza kai Imran ya yi yana addu'ar Allah ya shirya mashi Lion, wato haka ya ke yi shiyasa su yi ta kiran shi baya ɗagawa, sai lokacin da ya ga dama sai ya kira su. Lion duniya
Yana zuwa ya duba wayar Tyrone ne ke kiransa, picking ya yi tare da kara wayar a kunnansa ba tare da ya yi magana ba, ya zauna a saman gefen katafaren gadon dake a cikin ɗakin.
Ya ɗauki good 5mins wayar na kunnansa bai yi magana ba, da alama yana sauraron abin da Tyrone ɗin yake faɗe ne, a haka ya sake kara 2mins sannan ya cire wayar daga kunnansa ba tare da ya yi magana ba ya katse kirar, daidai lokacin Imran ya kariso cikin ɗakin.
Saman bedside drawer ya zauna yana faɗin "Ya akayi ka samu wannan gidan a cikin daren da ka fita?" Shiru ya yi yana rubutu a wayarsa, da alama sako zai tura.
"Saif ka yi breakfast kuwa?" Sai lokacin ya ɗago da kallonsa a kan fuskar Imran ɗin, kallo ɗaya ya yi mashi wadda bata fi second 2 ba, ya kawar da kallon nasa izuwa kan wayarsa.
"What is wrong with you Prof?" Shine abin da ya furta cikin sanyin murya, ajiyar zuciya Imran ya sauƙe tare da jan numfashi, dama yasan da kallo ɗaya Lion zai gane yana da damuwa, dan shi haka yake kawai bala'in kaifin kwakwalwa, da gane abu cikin ƙanƙanin lokaci.
"Amana ta ce bata da lafiya shiyasa, bana cikin mood". Daga nan bai sake magana ba shima Imran ɗin bai sake yin wata magana ba, tsawon minti 20 a haka sannan Lion ya fara magana cikin sanyin murya.
"Gaskiya Prof ban taɓa jinjinawa ko wace kasa ba bayar tamu, amma a yau na jinjinawa Nigeria da yan cikinta".
*Ni ko nace ba dole ka jinjina mana ba, ai mu saboda baiwar mu ba kalar iskancin da ba mu iya ba, idan musulci ne to mun fi kowa, haka tsiya da kaifin ƙwaƙwalwa, basira, son Allah da annabi, zalunci, ta'addancin, taimakon wata ƙasa, mu bada rayukanmu kan taimakon abin da ma bai shafemu ba, bayan ga matsala a cike a kasarmu, mun kasa kula da ita dan warwareta, sai shiga harkar da ba tamu ba, kai mu fa idan aka mana tsiya har president bamu kyalewa zage shi muke yi fes, kuma haka idan muka zage shi zai sa a nemo mu a duk in da muke, a kamo mu a ladabtar da mu, amma an kasa neman in da bandits suke a kwamuso su😭 a mana maganin su, anya wannan abin?, a Nigeria ne aka je gasar karatun Alkur'ani mai girma ɗan Nigeria ya buge manya-manyan larabawa ya ɗauko mana first ya dawo mana da ita, mu baiwar mu wlh ta wuce misali, a Nigeria ne zakaga an taɓa annabi musulmi sun fita a guje kamar mahaukata, amma hauka na son manzon Allah, a Nigeria ne zaka ga ɗan bandits ya shigo gida ya ce maka ka fita zai yi amfani da gidan, a Nigeria yan bandits suna da damar rike bindiga su kashe al'umma, amma kuma al'umma basu da damar riƙe bindiga ko wani makami dan su kare rayukansu da dukiyoyinsu, ƴaƴa da matansu😭, kai mu fa baiwar mu bata faɗuwa da baki, sai dai Allah ya mana Albarka kawai, amma ko mai muka ce za muyi, to mune a kan gaba, am proud to be Nigerian💪*
Story
Yar dariya Imran ya yi kafin ya ce "E haka ne gaskiya akasar mu babu abin da bamu da shi, ta ko wani ɓangare mun haɗa". Shiru ya ɗan yi kamar mai nazarin wani abin, still har lokacin hanunsa na a kan wayarsa yana typing.
"Saif lafiya? Tunanin me kake yi?". Ya ɗan ɗauki lokaci kafin, ya fara magana gently "Da mutanen Nigeria za su samu wasu abubuwa kamar su kula da sauransu, da kasar ku sai ta zama ta farko a duniya, ban taɓa ganin mutane irin yan Nigeria ba, gaskiya karo na farko da abu ya taɓa burgeni a rayuwata shine yan Nigeria, amma to meyasa duk da tarin wannan ilimi da basira da kuke da shi baku amfani da shi?".
Mamaki ne ya kama Imran, tunani ya shiga yi me Lion ya gani a Nigeria da har yasa yake yabon yan cikinta haka?.
"Saif amma me yasa kake yabon yan Nigeria har haka? Tun da nake da kai ban taɓa jin ka ce ga abu ya yi maka kyau ba, sai yau, to why?" .
Ajiye wayarsa ya yi a gefensa, da alama ya gama abin da yake yi, "Ba iya burgeni kuka yi ba, har da ɗan mamaki kuka bani". Jin abin Imran ya ke tamkar mafarki, wai yau Lion ne ya ce abu ya burge shi kai, ya zama dole mu san menene yan Nigeria suka yi haka wanda ya birge shi.
"Dan Allah Saif tell me now, am desprate to hear abin da Nigerians suka yi maka, har ya birgeka haka".
"Abin da ya sa Nigerians suka birgeni shine, James ya tsallake kasashe da dama, ya yi ta'addanci da yan ta'adda da dama, kungiyar da ya shiga ta sanya shi ya kashe yan ta'addan kasashe da dama, Dubai, India, Spain, England, Usa, duk ya shiga har cikin yan ta'addan su ya kashe wanda aka turoshi ya kashe, babu wata kasa da ta iya kamashi sai yan Nigeria, Nigerians akwai brain sosai fiye da tunanin mai tunani, abinciken da na yi jiya da daddare, ba karamin birgeni Nigerians suka yi ba, lokaci guda suka kama James wow".
Cikin sauri Imran ya ce "Kana nufin ka gano a in da James yake ne?" Jinjina Mashi kai kawai ya yi alamar e ya gano ba tare da ya yi magana ba.
Tsabar murna miƙewa tsaye Imran ya yi ya fuskanci gaban ya yi sujudur shukur dan godiya ga Ubangiji, da kuma taya aminin nasa murna, domin James ma babban abokinsa ne.
(Masoya James Lion ya gano a in da yake, ko wani hukunci kuma zai yanke mashi?🤔😭)
Bayan ya ɗago daga sujjadar ne ya ɗaga hannu ya rinƙa zubawa Allah kirari tare da godiya mai tarin yawa, sannan cikin zumuɗi ya ce "Saif yau she zaka ta fi ɗauko shi?".
Girgiza kai ya ɗan yi kafin ya ce "Ba in da zan je ni, su Tyrone za su yi aiki, idan sun gama kashe yan ta'addan zan je na ɗauki James ɗin".
"To dan Allah Saif kada ka yi wa James hukunci mai tsanani, ko iya wahalar da ya shama ka barshi a haka". Shiru Lion ya yi bai sake yin magana ba, jin ya yi shiru Imran ya san ba makawa kenan sai ya hukunta James, duk sai ya ji jikinsa ta yi sanyi, kansa har wani sara mashi ta fara yi, yana matuƙar kaunar James sosai da sosai.
Jiki ba kwari ya kiƙe ya shiga toilet ya ɗauro alwala dan gabatar da sallar azahar, shi Lion already ya yi sallar tun karfe ɗaya,.
Allah sarki Imran gaba ɗaya jikinsa ya saki lokaci guda, har wani zufa ke ta faman tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa.
Bayan ya yi alwala ya fito ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana faɗin "Saif dame ka yi sallah? Dan dai nasan already ka yi sallah" Da hannu Lion ya nuna mashi wata kyakkyawar labule dake kusa da kofar toilet ɗin ba tare da ya yi