Showing 147001 words to 150000 words out of 355604 words

Chapter 50 - Triplets Book 2 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2828

tare" to Rimsha ta amsa mata da shi, sannan suka koma saman carpet ɗin suka fara cin abincin a tare da spoon ɗaya, wannan ta ci ta bawa wannan kamar sun jima a tare haka suka yi sabon lokaci guda.

A ɓangaren Aafia kuwa, tun da ta suma a wajen bata farka ba sai washe gari da safe da Umaisha ta zo ta tashe ta, lokacin already ta mance komai kuma lokacin da dodannin suka ɓace ta farfaɗo daga sumar sai dai kuma barci ya ɗauke ta shiyasa bata tashi ba. Wanka ta je ta yi ta shirya zuwa school, bata zo da motar ta ba kuma Akil baya nan hakan yasa ta hau abin hawa zuwa school ko breakfast bata tsaya ta yi ba domin burinta kawai su haɗu da Rufee.

Karfe 8 daidai ta shiga cikin school, kai tsaye wajen da suka saba zama ta nufa, ai kuwa a nan ta isko Rufee tana zaune ta dukar da kanta kasa. Kusa da ita ta je ta zauna tana faɗin "Good morning Rufee, where is Anisa?" Ɗago kai ta yi bakinta a kunbure saboda dukan da Akil ya yi mata jiya, ganin bakin nata a kunbure yasa Aafia ta fara bata hakuri domin ta san menene sila. B komai Rufee ta ce mata sannan ta ɗaura da cewa "Aafia ina son ki rakani wani wajen idan ba damuwa" to Aafia ta amsa mata da shi sannan suka miƙe a tare suka nufi motar Rufee ɗin.

Rufeen ta ja su suka bar school ɗin. "Ina zamu je Rufee?" Aafia ta tambaya tana ƙoƙarin sanya wayarta a silent. "Wani waje zaki raka ni, ke dai ki zuba ido ba zamu jima ba" "A'a Rufee bana son yin nisa da school dan kin ga yaya Akil ya ce zai yi bincike kuma ga yaya Irfar yana gari, ina tsoron su zo school ba su same ni ba" ta yi maganar cikin raunanniyar murya.

"Kai A'afia kin cika tsoro wlh, to ba wani jimawa za mu yi ba, minti 40 ya yi zamu dawo" Allah ya dawo da mu lafiya shine abin da Aafia ta faɗa kawai, daga nan bata sake yin magana ba.

Sun yi tafiya mai nisa ya yin da suka sauƙa daga kan titi suka keta ta cikin daji, Aafia ta fara tsorata domin bata taɓa wuce school, shopping, kasuwa, sai kuma gidan su Imran, iya in da take zuwa kenan, amma yau ga shi har cikin daji suka shiga, hakuri ta yi ta jure ta zuba ido tana kallon yadda Rufee ke keta cikin dajin da motarta.

Wajen wasu guntayen bishiyoyi masu cikar ganye ta tsaida motar, sannan ta ce Aafia ya jirata tana zuwa, to A'afia ta ce mata amma zuciyarta tsorone a cike a cikin shi fal, kijinta har kerma yake yi, dan bata taɓa zuwa makamancin waje irin wannan ba, ita kuma Rufee fita ta yi daga motar ta kama hanya.

Cikin dajin ta kuma ketawa da kafarta, tun A'afia na iya ganinta, har ta kurewa ganinta. Wajen malaminta ta je, nan ta sanar mashi da cewa tana son ya kwance aikin da ya yi wa Abbi ya mai da shi kan daddyn Jelly, sannan ta bashi hoton Akil ta ce tana son a haukata mata shi, ya shiga duniya kowa ya huta, to bokan nata ya ce sannan ya karɓi hoton ya gaya mata kuɗin da zata biya, buɗe jakarta ta yi ta zube mashi kuɗin sannan ta masa sallama ta dawo wajen A'afia.

"Rufee me kika yi a cikin wannan daji haka?" A'afia ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki ga tsoro kamar zata yi fitsari a wando, shiru Rufee ta yi mata bata tanka ta ba ta kunna mota suka kama hanya.

Suna tsaka da sharara gudu suka ga an tare hanyar da wasu duwatsu, wani irin mahaukacin burki Rufee ta ja, domin basu san da wayan nan duwatsu ba, dan a lokacin da suke zuwa babu su a hanyar, kuma yanzu ma basu lura da su ba har sai da suka iso wajen, saura kaɗan ma su bi ta kai, Allah dai ya tsare suka gani.

Suna taka birki Rufee ta buɗe kofar motar zata fito kenan, wasu mutane suka fito daga cikin dajin hannayensu ruƙe da bindigu, ihu Rufee ta fara kurmawa ita kuma A'afia ta fara salatin annabi kawai. Cikin tsawa ɗaya daga cikin mutanen ya ce su fito daga cikin motar. Gaba ɗaya mutanen sun rufe fuskokinsu da irin rawanin buzayen nan, baka iya ganin fuskokinsu sai dai idanuwansu da hujin hanci da baki.

Ba musu suka fito jikinsu sai kerma yake yi, Rufee kuwa wage baki ta yi tana kurma ihu ko wani zai kawo musu ɗauki, ba imani bare tausayi ɗaya daga cikin bandit ɗin nan ya sanya bindiga ya harbeta a tafin kafarta suna faɗin "Idan baki yi mana shiru ba, sai mun harɓe ki a in da zaki mutu" Wani irin azaba take ji amma haka ta sanya hannu ta toshe bakinta tana hawaye.

Tasasu a gaba suka yi suka shige cikin daji da su, wani irin bakin azaba Rufee take ji, ga shi kuma sun ce sai dai ta taka kafar nata idan ba haka ba su fasata da bindiga, haka ba yadda ta iya ta fara taka kafarta suka bar wajen, suka bar motar a buɗe wayoyinsu da komai yana a ciki.

Cikin wannan azabar suka rinƙa taka kafafunsu a cikin wannan ƙungurmin dajin, banda sunan Allah ba abin da A'afia take kira, ita kuma Rufee kuka kawai take yi, azaba ya yi mata yawa, ga wahalar tafiya ga azabar sun fasa mata kafa ɗaya, sai jini yake zuna kamar me.

Sun yi tafiya mai nisan gaske, har suka wuce wani katon dutse kafin su iso wani waje kamar cam haka wajen yake, an yi ɗakuna da irin manya-manyan tampol ɗin nan.

Gaba ɗaya wajen kewaye yake da manya-manyan maza madaka kanti suna riƙe da bindiga suna tsaitsaye, da alama gadin wajen suke yi.

Suna isa wajen ɗaya daga cikin bandit da suka taho da su Rufeen ya ce "Kai Habu ku shigar da wayan nan ciki zuwa anjima idan su garba sun dawo, sai mu haɗa su mu ga yau mutane nawa muka kama" Wadda aka kira da Habun ne ya kariso wajen hannunsa riƙe da bindiga ya sanya irin rawanin buzayen nan shi ma ya rufe kai zuwa fiskarsa, baka iya ganin komai na daga fuskarsa sai ido, jikinsa na sanye da kaki na sojoji, a shekaru ba zai wuci 22 years ba.

Tasa su ya yi agaba zuwa cikin ɗaya daga cikin ɗakunan tampol dake wajen. Rufee dai ya sha azaba iya azaba, ga shi ba halin ta yi wata magana za su harbeta suka ce, ita kuma A'afia tunanin ta ɗaya shine idan su yaya Irfan suka je school ba su same ta ba me zata ce musu, ba ta yi tunanin cewa matsalar da take a ciki yanzu ya ci uban wanda take hangowa ba, a'a ita tunanin hukuncin yaya Irfan take yi, domin ita bata san kidnaping ba, labari kawai take ji, bata san yadda ake yi ba.

Habu na kai su bakin kofar ɗakin ya ce su shiga sannan ya juya ya bar wajen, jikin su a mace suka ja kafafunsu zuwa cikin ɗakin. Mata ne za su kai mata 30 a cikin wannan ɗan ɗakin, gaba ɗaya matan dake a wajen suna ƙoɗe alamar sunci bakar wahala, duk sun yi futu-futu da su, mafiyawancinsu akwai busasshen hawaye a kan fuskarsu alamar sun sha kuka, wasu kuma iyayene da yaransu kanana, wasu yan mata wasu kuma sun manyanta, abin gwanin ban tausayi, duk wata zuciya mai imani idan taga wayan mata sai ta zubar mu su da kwalla, saboda yana yin da ke a kan fuskokinsu ma kawai ya isa ya karyarwa da ɗan adam zuciyarsa, ya sanya shi kuka, ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar kasancewa a waje irin wannan ba.

Babu wadda ta kula su kowacce daga cikin matan nan tana fama da kanta, tsuru-tsuru su A'afia suka tsaya sun kasa gaba sun kasa baya, ga kuma Rufee kafarta na mata ruwan bala'in azaba. Wata wace ce wadda take zaune daga ta bakin kofa ta miƙe kafafu yarta wadda ba zata fi shekara 14 ba ta tada kai da cinyoyinta ita kaɗai ta iya ce da su A'afia su shigo su zauna, ba musu suka je kusa da ita suka zauna a takure, dan dama sun ga ji, A'afia da ta zo zama sai da ta kakkaɓe wajen tas sannan ta zauna, ita kam Rufee zaman yan bori ta yi tare da ciki hannunta daga bakinta ta fara kuka kasa-kasa dan kada su ji.

"Sannunku da zuwa" matar ta sake yi masu magana, Aafia ce ta iya amsa mata ita kam Rufee ba'a magana da kyar ma take iya fidda numfashi.

"Da kin dai na wahalar da kanki kina zubar da hawayen ki a banza ma da ya fi maki, idan baki daina ba hawayen ne za su kare a banza" Cewar matar ta kuma yi maganar tana kallon Rufee.

A'afia ce ta yi karfin halin cewa "To saboda me zata daina kuka? Baki son su ji kukan nata har a sami wani mai tausayi ya tausaya ya taimaka matane?" "Taimako a lallai ke yarinya ce sosai" matar ta bata amsa ta kuma ci-gaba da cewa "Ai tun da ba su ji tausayinku wajen ɗauko ku su kawo ku nan ba, to fa duk abin da za su yi muku ba za su taɓa jin tausayin ku ko kaɗan ba, babu zancen imani a nan wajen, kawai ku yi addu'ar Allah ya kuɓutar da ku, amma a halin da muke a ciki yanzu ma ko an kawo kuɗin fansa suna karɓa sai su ki sakin mutun ya koma gida, mafiyawanci haka suke yi, mu samman idan suna son mace, wlh aurenta suke yi wata zubin suce da yan uwanta yaransu sun kasheta da basa nan wata zubin kuma idan suna son mace taki yarda tofa suna kashetan da gaske kuma su karɓi kuɗin fansa ba yadda aka iya da su, ba mai iya tinkararsu, sun fi karfin kowa ne nake ga a kasar nan, ku dai tun da kuka shigo nan sai ku kama addu'a a cikin zuciyoyin ku domin ko sallah ma basa bari bawa ya yi bare kuma har ya samu damar kai kukan sa ga Ubangiji, amma duk da haka ku dage da addu'a cikin zuciyoyinku dan Allah ya kuɓutar da ku, a yanzu kuɗi baya kuɓutar da mutun daga hannunsu".

"Amma su ɗin su waye ne a kasar nan har da suke aikata hakan ba mai kama su ayi musu hukunci?" A'afia ta tambaya tana kallon yarinyar dake kwance kan cinyar matar "Ya naga yarinyar nan kamar bata da lafiya?" Ta sake cefawa matar tambaya. Nisawa matar ta yi kafin ta ce "Su ake cewa masu garkuwa da mutane wato kidnapas, yarinya kuma e bata da lafiya, zazzaɓi take yi, amma sun bamu magani ai ta ji sauki".

Shiru A'afia ta ɗan yi tana jujjuya kalaman matar, sun bata magani kenan suna da asibiti ne a nan wajen? Ta tambayi kan ta a cikin zuciyarta, kidnapas dama haka suke? Ta sake tambayar kanta.

Sake ɗagowa ta yi ta kalli matar sanna ta ce.......... Dole na dasa aya a nan na don na so ba sai dan page ɗin ya cika da yawa, mu haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

💖TRIPLET'S💖💖

Episode 43-44


This page dedicated👇

*Aisha baita Jiddah, Ruky Aunty, N Hidan, Hafiza ayuba*



Shiru A'afia ta ɗan yi tana jujjuya kalaman matar, sun bata magani kenan suna da asibiti ne a nan wajen? Ta tambayi kan ta a cikin zuciyarta, kidnapers dama haka suke? Ta sake tambayar kanta.

Sake ɗagowa ta yi ta kalli matar sanna ta ce "To suna da likitoci a nan ne da za su bata magani?" Girgiza mata kai matar ta yi sannan ta ce "Ni dai tun da nake nan wajen yau tsawon wata uku ban taɓa ganin wani likita ba, sai dai idan suka ga baki da lafiya sosai sai kiga sun kawo maki magani, ban san daga ina suke samo maganin ba" "Wata uku!" A'afia ta maimai a fili tana zare ido, gyaɗa mata kai matar ta yi tana faɗin "E wata na uku a hannunsu, kuma sun karɓi kuɗin fansa daga wajen yan uwana har sau biyu amma sun ki su sake ni na koma gida" Zaro ido sosai A'afia ta yi domin bata taɓa tunanin hakan ba, ita a nata zaton idan suka kama mutun suna bashi kulawa saboda za su samu kuɗi, kuma tana tunanin da zarar an basu kuɗin fansa suke sakar mutun ya koma gida, bata taɓa zaton wajen nasu haka yake ba.

Jugum jugum su ka zauna abin gwanin ban tausayi.

Can kuma Aafia ta sake cewa "To amma ke meyasa basu barki kin koma gida ba tun da sun karɓi kuɗin fansa?" Wani dogon numfashi matar ta ja tare da sauƙewa a hankali sannan ta ce "E wannan ne ban san ni ba, abin da dai na sani shine da suka buƙaci kuɗin fansa sai suka ce mace ce zata kawo musu kuma macen ma babban ƴata mai shekara 17 shine yan uwana suka ki yarda suka ce mace ba zata zo wajen ba, sai aka bawa yayana kuɗin ya kawo, basu musa ba sai da yayana ya zo ya kawo musu kuɗin a in da suka yi da shi zai zo, bayan sun karɓi kuɗin sai suka sa bindiga suka harbe shi, wai dan saboda sun ce mace suke son ta kawo kuɗin yan uwana sun bujirewa umarnin su, haka yan uwana suka sake ba su hakuri suka rinƙa rokansu a kan su yi hakuri su sako ni, nan suka sake cewa sai an basu million biyu kuma kanina suke son ya kawo kuɗin, a cikin kannena ɗin ma sai suka zaɓi jarumin gidan mu, mai faɗa da kuma zafin rai, ni na rasa waye yake gaya musu family ka idan suka kamaka, sai kiga kusan komai naka sun sani, to da kanina ya kawo kuɗin sai suka yi ƙoƙarin jan ra'ayinsa a harkar dama haka suke yi, shiyasa suka yi yawa a cikin al'umma, idan sun ga namiji lafiyayyen mai karfin zuciya mara tsoro sai suyi ƙoƙarin jan ra'ayinsa, idan ya ki sai su yi mashi yankar rago, su yi video su turawa duniya amma ba za su taɓa faɗin abin da ya sanya suka yanka shi ba, sai dai suce ba'a kawo kuɗin fansan shi ba, abin da ya faru da kanina kenan, ya ce musu shi ba zai iya wannan harkarba, wlh a saman dutsen da suka karɓi kuɗin a nan suka ɗaure shi suka yi mashi yankar rago, sai bayan sun dawo suna magana na samu labari daga maganar da suke yi da ogan nasu, sannan dan su huce haushi suka zo suka ɗauki yarinyar nan suka tafi da ita shekaranta 14 a duniya amma haka shaiɗanunan suka lalata mata rayuwarta, na yi na yi su kashe ni na huta da wannan bakin ciki amma sun ki kula ni, kuma tun daga lokacin da suka yi wa wannan yarinyar aika-aikan nan ba su sake bi ta kai na ba, ni yanzu bani da wata bukatar da ta wuce su kashe ni, na yi kuka har hawayena sun kafe, yanzu zuciyata ta kekashe bana tsoro ko shakkar komai" Ta kai karshen maganar tana shafa kan yar tata dage kwance saman cinyarta gwanin ban tausayi.

Sosai A'afia take zubar da kwalla yau ta ji abin da ya fi karfinta, wannan rashin imani har ina, su sace mutane bayan haka kuma su rinƙa lalata musu rayuwa sannan suna kashe masu yan uwa, wannan bala'i dame ta yi kama, idan ba Allah maɗaukakin sarki ba ba wanda ya isa ya fitar da bawa daga cikin irin wannan bakin zalincin.

Dafata matar ta yi tana faɗin "Ki daina kuka domin kada hawayen ki su kare, abin kuka yana gaba, domin baki ga komai ba, tun kina da sauran hawaye har ma su ƙafe, ni yanzu addu'ar da nake yi maku Allah yasa kada su lallata maku rayuwarku, domin da wuya yanzu su ɗauko mace ba tare da sun kwana da ita ba su mai da ta, ɗazun da asuba ma naga sun kawo wasu mata sun zuba su cikin wancan ɗakin, an jima kaɗan za su zo su fitar da mu tsakar wajen cikin ciyayin can dan su azabtar da mu da rana, haka suke yi, idan rana ya yi sai su fitar da mu rana, idan yamma ya yi su dawo da mu, to idan sun fitar da mu sun haɗe mu waje guda ne sai kiga suna zaɓar mace da ta yi musu suna sanyawa yaransu na kasansu suna shigar musu da matan ɗaki, ina rokan Allah ya tsare ku yasa kada su lalata maku rayuwar ku, mu kam sun gama da mu saura su karisa mu kawai mu huta, ni na rasa ma me ya sanya basu kashe ni ba".

Banda kuka ba abinda A'afia take yi, ita kuma Rufee tuni ta sulale kasa ta kwanta kamar bata numfashi sai dai hawaye kawai zaka gani yana bin kuncinta.

(Toh fa su Aafia kuna cikin garari, na barku lafiya na tafi izuwa wajen Rimsha, kada ku manta part na Aafia True life story ne!)

A ɓangaren Rimsha kuwa, tare suka ci abincin ita da Akila, su na ci suna hira gwanin ban sha'awa, bayan sun kammala ne suka fito Palo, zaune suka isko Imran saman sofa, ya tattare komai na kwanikan abincin da ya ci, har da goge wajen ya yi bawan Allah.

Saman sofa mai zaman mutun 3 suka zauna Akila tana faɗin "Yaya Imran Aunty Aafia bata dawo ba fa, kuma yaya Akil ya ce idan ta je school ta dawo, to tun jiya bata dawo ba". Ba tare da kalle su ba ya ce "To bata da ra'ayin zama a nan ɗin ne shiyasa, sai ku kyaleta ta zauna in da take so, ko ana dole ne?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba'a dole.

Shiru sukayi ba wanda ya sake magana, wayar Imran dake saman bed nasa a cikin bedroom nasa ne ta fara ruri tana neman agaji, da sauri Akila


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login